itake bata shawarwari sosai idan sunyi waya don ita ta koma uk da yayanta saboda offer data samu achan,
Duk wani sirrin amra a wajen Madina zaka jishi, don ta maida Madina kamar babbar yayarta, Duk wani abunda ya shige mata duhu gurunta take zuwa ta bata shawarwari sosai, Har lokacin kuwa idan Madina tayi mata maganar Amar bata cewa komai saidai ta sauya hirar kota nuna bata ra’ayin maganar shi, tun Madina na yin shuru tana kauda zancen don ta nuna kiri kiri bata son zancen Har tazo ta fara mata fada don yanxu takaiga idan tayi mata maganar shi kiri kiri zata ce ita bata son zancen shi, auren ma bata so tunda ta haifa mashi yaya bata son zama dashi, abun yana damun Madina sosai don fada sosai takeyi mata akan wannan zancen, saboda ayanxu ne ya kamata ta jaa mijinta ta rikeshi ta tarairaye shi don ya gama saukowa sosai kowa ya shida hakan don itama ta shaida hakan musamman ranar sunan triplet, da idanu ta taga yanda yake kallon
amra da yanda yake haba haba da ita amma take waskewa tana basarwa, Har lokacin da yaso suyi hoto dashi da ita da yayansu amma ta wucewan ta sama, aranar ma Madina tayi mata fada sosai akan wannan.
Amra nada taurin kai sosai, wanda hakan yasa Madina ta soma binta da lallami tana nuna mata cewa yanxu batada wanda ya wuce shi a duniya don shine uban yayanta, babu laifi yanxu idan tana mata fada ko tana nuna mata mahimmacinsa tana dan tsayawa ta saurareta, don Har waazi tana tura mata akan mahimmacin da darajar miji a wajen mace da rights dinshi akan mace, bayan wannan Har sirrikan yanda mace zata rike miji yanda zai mace yaji Duk duniya babu wadda yake so sai ita take tura mata, wasu haka zata bude ta karanta wasu kuma haka zata barsu taqi karantawa saidai idan taji boredom, Akwai ranar da Madina ta tura mata wasu zafafan erotic ideas wanda yasa ta dauke wuta sosai, tana fara karantawa ta ajiye tana turo baki kamar yarinya, haka ranar ta wuni da wani alamari daya shigeta dalilin tunawa da tayi na intimacy dinsu ita dashi, dukda tana kokarin deceiving kanta saidai gangar jikinta bai lamunce da hakan ba, sai a lokacin ta tabbatar da tana cikin jerin mata mabuqata sosai don tanada muguwar sha’awa.
Bangaren babansu kuwa komai yanxu ya sauya mashi shima, ya zama babban mutun don jari babba Amar ya bashi dukda da kyar ya karba, bayan wannan ma da farko yayi mashi tayin aiki a company’s taura ltd nan babansu amra ya nuna mashi abubuwa da sukayi mashi na alkairi yayi yawa sosai don haka yake jin kunyar karban wannan offer din bayan wannan ma yanxu yana son yayi rebuilding kanshi don Har yanxu talent dinshi na nan.
Dukda haka amar bai barshi ba saida ya samo mashi wani project mai tsoka sosai a wani babban company, da farko company hankalinsu bai kwanta dashi ba don gani suke kamar bashida qualification sai daga baya suka fara testing dinshi, outcome din abunda suka bashi yayi blowing mind dinsu sosai don komai daki daki yayi da tsari, nan take suka daukeshi suka bashi wani babban mukami wajen yin project din Har ya zama project leader.
Wannan aiki ba karamin arziki ya kawo ma babansu amra ba sosai don he work so hard for it dukda da taimakon Amar ya samu aiki,
Har alokacin he’s leaving a lowkey life anan abuja haka zalika Har lokacin bai fasa aiki a gidan gonar ammah ba karshe ma Har expanding gurin yayi sosai ya kawo wasu ma’aikata suna taimaka mashi don yasan how ammah value gidan gona sosai.
Duk bayan sati yakan zuwa gidan ya duba yayan nashi sannan ya gaida ammah, wani irin tsaftattacen relationship sukayi buliding cikin wayewa inda Har alokacin yakan zuwa Har cikin gidan ya zauna su gaisa da ammah sannan ya
bata Duk wani update akan gidan gonar harma shawararta yana zuwa ya nema akan wasu abubuwan.
Acikin watannin nan baban amra ya lura da rayuwar auren da amra da amar ba kamar kowanne aure bane, dukda bai taba tambayarta yanda auren nasu ya faro ba don hakan bashida wani amfani ayanxu saidai yanayin yanda komai ke tafiya yasa yake jin Akwai wata a kasa.
Ranar dayazo gidan dubasu kuwa aranar ya samu ya zauna da amra don suyi magana, koda ya fara yi mata tambaya akan Amar nan ya gane kwata kwata kamar ma bata damu da Amar dinba don babu wani corner corner tace “bata sani ba”
Anan take ya tambayeta kodai Akwai wata matsala ne, abunda ta fada mashi ya girgiza shi inda ranshi ya baci sosai, babu abunda yake maimaitawa a zuciyarshi sai kalamanta “abba ni bana son shi inason araba auren mu”
Aranar dai amra taga fushin baban nata wanda zata iya rantsewa bai taba fushi da ita haka ba tun suna kananu kafin su rabu, baima tsaya ya tambayi dalilinta ba ko ya saurari bayanin nata ba ya dakatar da ita akan karta sake gangancin fadin irin wannan furucin, idan har ta sake irin haka kuwa ya tabbatar mata ta zama butulu.
Aranar dai hankalin amra ya gama Tashi, don harga Allah ita da da gaske take,kodata fada ma baban nasu ma batayi tsammanin zaiyi fushi ba dukda tasan daman bazaibi bayanta, saidai kalaman daya fada mata ya razana ta sosai inda ya shiada mata idan har tayi tunanin rabuwa da Muhammad to babu shi babu ita don akan Amar da ammah zai iyayin komai ciki kuwa Harda fushi da ita sosai,
Taurin kan amra bai sa ta saduda ba don tana kan bakarta,
Ranar wata juma’a tana zaune a daki ta kira Madina a waya don ta bata shawara akan abunda take shirin yi.
wani abun takaici da tayi wanda yasa ran Madina ma ya baci sosai shine inda ta shaida mata yanda sukayi da baban su sannan ta shaida mata zata tunkari ammah da zancen don ita kadaice ke supprting dinta.
Saida Madina ta gama sauraronta kafun ta sille ta tass ta mata fada sannan ta tunatar da ita wacece ammah a wajenta kuma a wajen amar din shi kanshi,
“Amma yau na gama tabbatar da bakida hankali amra, yanxu ke ko kunyar fadin wannan zancen Bakiji ba? Ammah zaki tunkara da wannan maganar? na farko dai Kun manta lokacin da kike fada min yanda suka rike qannenki
Amana? Sannan Kin manta yanda matar nan ta nuna maki so da qauna ta kula dake kamar ita ta tsugunna ta haife ki har yanxu ma tana kula
Dake tana kaunarki kamar daga cikinta kika fito Har kina tunanin fada mata cewa bakya son auren danta kina son a raba ku? Wai bayan wannan ma ke wace irin uwace? Bakya tunanin yayan dake tsakanin ku? Haka kike da taurin zuciya daman? Kin bani kunya amra
Ban taba expecting haka daga gareki ba Ay na dauka Duk surutan da kikeyi a baki ne ashe da gaske kike? Toh Wallahi Zan baki shawara tun wuri kafin kiyi regretting ki sauya wannan banzan tunanin naki don wannan stubbornness din naki zai kaiki ya baro ki”
Madina ta karshe ranta ya baci sosai, gyara zaman wayar amra tayi jikinta Duk ya mutu kwata kwata Duk ta manta da komai babu abunda ke ranta sai abunda yayi mata wanda yasa ta manta alkhairin da sukayi mata ita da kannenta shi da ammah,
Murya ta na Rawa tace “innalillahi wa inna ilaihi rajiun, anty Madina dan Allah ki bani shawara Wallahi bansan maysa nake waennan abubuwan ba Wallahi Ina sane da abubuwan da ammah tayi min, Wallahi sharrin shedan ne yasa nake kokarin tafka babban kuskure, ni Wallahi dalilin da yasa na fadi hakan shine gaba daya ya futa akaina, idan na tuna shi babu abunda nake tunawa sai abubuwan da yayi min”
Banza Madina tayi mata don Har lokacin haushinta take ji
“Anty Madina kuyi hkuri don Allah karkiyi fushi, ki bani shawara Wallahi Zan dauka Allah,”
Gyaran murya Madina tayi kafin ta soma magana anatse “Ay dole nayi fushi amra, fushi da taurin zuciya zai kaiki ga yin aikin dana sani, wanda zakiyi regretting daga baya, my dear Allah y baki komai, kinada kyau kinada ilimi Kn addini dana Boko, Allah ya azurtaka da family da suke sonki, Allah ya Baki suruka ta gari wadda ta duake ki kamar ya, Allah ya Baki miji na gari san kowa qin wanda ya rasa don Wallahi mijin is one in a million, ga arziki ga komai, Allah kadai yasan irin matan dake rububunsa laifi sa daya na abunda yayi maki wanda na yarda bai kyauta maki ba a matsayinki na matarsa but da
Bakinki kince yayi apologising kuma yace he wants to makeup for everything right?”
“Yes anty Madina but still ni Wallahi…”
Katseta Madina tayi tace “kimin shuru ban gama ba, kona kashe wayarta ne idan gardama zakiyi?”
“Ah ah nayi shuru anty Madina” amra ta amsata tana gyaran zaman wayar a kunnenta
“Yauwa, as I was saying ba laifi bane don kinji zafin abunda yayi maki and kinada right din hukuntashi idan kina tunanin hakan ne zaisa zuciyarki taji sauqin abunda yayi maki ammah maganar rabuwar aure ki cireta a lissafi mu mata Allah yayi mana wata baiwa da ba ko wacce mace tasan da haka ba, zaki iya rama abunda yayi maki cikin ruwan sanyi ta yanda da kanshi zai dunga binki yana baki hkuri yana lallaba ki Har sai zuciyarki tayi sanyi, bari kiji na fada maki gaskia wallahil azeem bazanyi kaffara ba kinason mijinki sosai, son da kike mashi ko ke kanki kin kasa Ganin haka saboda wani banzan fushinki da taurin zuciyanki,”
Turo baki amra tayi waje ta soma magana yanda bazata jita ba “ni babu wani son shi da nake yi”
“Kince wani abu ne?” Madina ta tambayeta
“Ah ah bance komi ba inajinki” amra ta amsata
“Yanzu shawara daya Zan baki, ban hanaki ja mashi aji ba wannan yana da kyau saidai ki jawo mijinki a jiki ki bashi kulawa ki tarairayeshi, ki sanya ya mutu a sonki yaji dukduniya bai wata mace sai ke wannan shine abunda ya kamata ki dunga tunani akai bawai ki dunga tunanin rabuwa da uban yayanki ba.”
“Toh anty Madina na dauki shwarar ki bazan Kara maganar rabuwan ba saidai gaskia Saina Rama abunda yayi mun don bazai dameni ta sauqin ba after all he has done to me”
“Kyaji dashi wannan ya rage naki, saidai kuma anan ma zanyi maki gyara, adaiyi saffa saffa don Wallahi idan kikace zaki jaa ajin nan sosai to Wallahi zaiso ya tsinke ne kizo nan ma kina dana sani, I’ve said my own yanxu komai ya rage naki”
Madina ta karashe tana sauke ajiyar zuciya
Nunfasawa amra tayi kafin ta soma magana
“Toh Yanxu anty Madina meya kamata nayi?”
“Ban sani ba, abunda ya kamata kiyi ma Saina fada maki? Kije kibi Duk videos da abubuwan dana tura maki ki karanta, saiki dawo muyi magana”
Sauke kai amra tayi kamar tana kusa d auta tace “tohm zanyi Insha Allah”
Sallama Madina tayi mata ta kashe wayar.
Tun bayan wayar da sukayi da Madina amra ta dan chanza, tundaga ranar bata kuma gangacin maganar rabuwarta dashi ba don sai daga baya ta gane cewa badan Madina tayi saurin hanata shirmen dataso yi ba da tazo tana dana sani, don duba ga Duk abubuwan da ammah keyi mata da yanda take kula da ita da son da take nuna mata dasu triplet yasa take jin takaicin kanta, what was she thinking? Maysa ta zama so stupid for thinking of that? Haka zata dunga tambayar kanta tare da jin haushin kanta gaba daya.
A cikin kwanakin ne ta sake Kiran Madina, sun dade suna waya sosai Inda ta bata wasu shawarwarin masu mahimmanci sannan ta buqace ta data kirashi a waya ko ta dunga mashi dan morning message tana jin yanda yake, da farko dai taso tayi halin nata saidaga baya Ganin ran Madina ya soma baci tace zatayi, haka dai ranar Madina ta dunga fama da ita kamar wata Mara wayo ko irin wata local dinnan, idan tace kaza saitace ita bazata iya ba Ay saiya samu damar Kara rainata ahaka dai ta dunga nusar da ita amfanin duk abubuwan da take fada mata don babu abunda zasu Kara mata a idanunshi face darajarta da zai dunga gani kuma hakan zaisa ta shiga ranshi sosai don da haka zata saye zuciyarshi.
Duk wannan abubuwan da Madina ta fada mata baisa ta kirashin ba don ita a ganinta inshi baiyi mata message ba maisa ita zatayi mashi, don haka ta watsar da zancen ma gaba daya.
Washe gari haka ta shirya ta fada ma ammah zata je saloon ita da salima nan ammah ta bata atm card din da Amar ya bari idan zatayi buqatun gabanta, da mamaki amra ta karba card din kafin tayi ma ammah godiya suka fuce ita da salima don driver ne zai kaisu,tunda suka shiga mota take kallon card din sai alokacin ta ga sunanta hade da nashi a jikin card din nan ta tuna lokacin da alert din kudi ke shigowa cikin wayarta, Nunfasawa kawai tayi tana danyi wani nazari Har suka iso saloon, basu wani jima ba don wanKi kai kawai akayi mata akayi blow drying sai stretching, suna gamawa suka fito, nan ta umarci driver ya wuce dasu mall,
Tunda suka shiga ta fara yima kanta sayyayyah sosai, salima dai kallonta kawai takeyi tana mamakin ta don ita ba ma’abociyar saye saye bace hasalima in taga anayi sosai cewa take Ana almabazaranci, batace mata qala ba haka dai ta dunga binta Har saida ta gaji suka dawo gida.
Amar…..
Yau watanshi biyu kenan da komawa dubai tun last tafiyar da yayi bai dawo ba saboda ayyuka da sukayi mashi yawa, tun ammah na expecting dinshi harta hakura,
Kwatsam sai gashi ya dawo ranar da triplets suka cika 6months, babu wanda yayi expecting dinshi don ko ammah bai fada Nawa ba.
Karfe uku daidai na rana ya shigo gidan da sallama cikin kamewa, su amra dake zaune dasu salima Duk sunsha kwalliya sai ammah da Salim, amra na rike da princess data kara girma tayi wayo sosai tayi bulbul don Har zama tanayi, tasha wata pink gown an saka mata crown pink tayi kyau sosai kumatu ta sun fito, gefe ammah ce zaune da Hamad da Hamid a hannunta sunsha riga da wando sunyi wayo sosai sunyi bul bul bakinsu an maqala masu pacifier, ammah ma itama tayi kyau sosai don jigaggaen lace ne a jikinta wanda ya amsheta sosai, gabansu cake ne manya manya guda uku akan Center table inda aka rubuta kowannen happy 6 month, cake dinma kana gani kasan yasha kudi sosai, don kowanne da sunan triplet a jiki, salima na tsaye tana kokarin daukan hoton ammah da amra da triplets sai jin sallamar shi sukayi,
Waigowa sukayi gaba dayansu suka zuba mashi idanu, yayi kyau sosai yayi kiba har wata qasumba ya Tara sosai ba kamar yanda yake barin ta ba a fuskanshi, sanye yake da kananun kaya as usual wandon jikinshi na army sai white Riga mai gajeran hannu sai jacket dinshi a hannu da briefcase, yayi masifar kyau sosai, tun daga nesa kuwa kamshinsa ya gama bade parlorn, murmushi ammah tayi “maraba lale, saukan yaushe son? Sannu da zuwa baka shaida mana zaka zo ba”
Wani kayataccen murmushi ya sauke ma ammah kafin ya karaso cikin parlorn amra dai kasa dauke idanuta tayi akanshi, she can’t lie ya gama captivating dinta, shiko baima kalli inda take ba don yana kallonta dan tsimin dayake dannewa zai taso mashi, karasowa yayi ya ajiye briefcase din hannunshi da jacket din yana murmushi “thank you ammah na, my babies haka suka Kara girma ammah”
Ya fada yana karasowa gaban ammah ya duka Hamid yayi pecking dinshi yana gamawa ya yi amshi hamad ma yayi pecking dinshi, nan take yaran suka fara mashi dariya, gaba daya mamaki ma ya hanashi magana, “I missed you my boys,” yana karashe wa ya kalli bangaren amra, saurin ajiye Hamid da Hamad yayi kan ci yar ammah kafin ya tako inda amra take ya dan duka ya kama hannun princess yayi pecking yace “my little princess, I missed you daddy girl, how are you???”
“Ya Muhammad Ay bata fara magana ba” Salim ya fada yana dariya
Murmusa wa gaba daya sukayi kafin ya mike tsaye, nan Duk suka gaishesa amra dai kanta a kasa saida ya gama amsawa tace “sannu da dawowa, ya hanya?”
He never expected that don yayi mamaki sosai, kai tsaye ya amsa ta “lafiya”
Suna nan tsaye driver ya shugo da wani katon packs din jaka guda biyar, yana karasowa Amar yace ma salima taje ta karbo, tana karbo wa ta ta kawo mashi nan ya dauka ya bama kowa nashi, pack uku ya duaka ya ajiye gaban amra yace “wannan for my babies”
Yana ajiye mata ta kalli pack din batace komi ba, waigawa yayi inda su salima suke nan ma ya basu bag daya yace “ga maki keda Salim”
Yana bata ya juya wajen ammah itama ya bata nata sauran dayan pack din daya rage, godiya Duk sukayi mashi babu wanda ya kura bai bama amra ba, ita kuwa ta qulu sosai sai dannewa datayi.
Saida ya tsaya akayi hotuna dashi kafin ya wuce bedroom, yana shiga ya sauke wata ijiyar zuciya yana dafe kirjinshi, tunda ya shugo gidan idanunshi suka sauka akanta yaji yanayinshi ya sauya, “ya Allah…. “ ya fada yana admiring irin kyau data kara, she looks so hot kamar bata haihu ba, daman wata doguwar Riga ce a jikinta dataji shape dinta tayi mata kyau sosai, dukda daga zaune ya ganta but he can imagine yanda zata kasance cikin rigar idan ta mike, da kyar dai ya samu yayi wanka ya sauya kaya yayi sallah kafin ya futo.
Karfe takwas Kow aya sauko kasa, gaba daya sun hallara a dining, abunci suka fara ci gaba dayansu Banda Aman da baya dawowa gidan sai wajen karfe