Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   66 / 94

195K to 198K   out of 279.4K words

ask you to eat?” Ya tambayeta kai tsaye ba tare da ya kalleta ba, “bana jin yunwa” bata gama fada baa cikinta ya fara qugin yunwa qiii, atare suka dago ya daga mata gira daya alamun karya kike yi, saurin sauke kanta qasa tayi ta hade rai tam, harya kusa cinye nashi wanda ta zuba mashi a plate din tana zaune ta nade hannunta akan tudun kirjinta daya dan futo sosai, kwata kwata baiyi gigin kallonta ba saboda komai nata haukatashi yake, abuncin ma zai iya kasa ci idan ya dago,saida yaci kusan rabi kafin ya tura mata gabanta ya dago ya kalleta fuskanshi babu wasa yace “eat!!!”

Dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta maida idanunta kan plate din nashi, shuru ta danyi tana nazari, me yake nufi kenan da ita? Saida yaci ya rage zaice taci,

Ay kuwa ko sama da kasa zata hade bazata ci ba,, maidoda kallonta tayi zuwa gareshi “bana ci”

“You know I….” 

“You hate repeating your self na sani, bana jin ci ne kawai” tayi saurin katseshi kafin ta miqe tsaye ta juya zata wuce, bata idasa taku biyu ba taji ya janyo waist dinta baya ya hade da gabanshi ya rike tam “why are you so stubborn huh?” Shuru tayi mashi batace komai ba tana sauraron yanda nunfashinsa ke sauke a shoulder dinta don ya dan rankwafo wajen wuyanta, daidai ta natsuwarta tayi ta soma kokarin same jikinta daga nashi, yanda ta soma jaa baya haka ya sake janyota sosai zuwa jikinshi ya yi mata rikon daya fi wanchan ma, saurin runtse idanunta tayi ta budesu tace “dan Allah inason zanje na kwanta kaina na ciwo”

Daidai kunnenta ya sauke bakinshi ya fitsari mata da nunfashinsa mai fidda kamshin dadi yace “bazakije ba Saina bada umarnin haka”

Tunda yayi maganan bata sake gigin kwace wa ba ta saki ragamar jikinta do Yanxu ta gane musu ma dashi bata lokaci ne don ba’a iya mashi, haka zalika ita kuma yanxu bashine a gabanta ba, bata buqatan surutanshi kwata kwata, barcin da take ji ma ya isheta, jin tayi mashi shuru yasa ya juyo da ita gabanshi ya kura mata idanu yace “meysa kika bama ammah jininki?”

Dagowa tayi ta kalleshi kafin ta kauda kanta gefe tace “saboda tana buqata shi fuye dani”

“You’re sick meysa baki je doctor ya dubaki ba?”

Dagowa tayi Ganin yanda yake magana calmly kamar bazai yi halin nashi ba na wulaqanta mutun, turo baki kawai tayi tace “lafiya ta kalau bana buqata”

“Why are you talking to me like that?ni Sa’am kine ?” Ya fada yana hade rai 

Itama hade ran tayi tau ta kalleshi cikin ido tace “yanxu kuma me nayi? Tambayata kayi ni kuma na baka amsa,?” Ta bashi amsa itama tana kallonshi, matso da ita yayi gab da jikinshi yace “bakida kunya”

Bai gama sauke nunfashinsa ba ta matso daidai da fuskanshi har nunfashinsu na gaurayewa ta dan dingila kafarta gab dashi tace “mey nayi na rashin kunyar uhm,”

Kasa ce mata komai yayi saima kallon juna da suka tsaya yi kamar Ana magnetising idanun suu, saida ta dan gaji da dingile kafafunta datayi ta fara kokarin saukesu kasa Dan ta bar wajen yayi saurin taro waist dinta da hannu biyu ya dauketa gaba dayanta, sai jinta tayi a sama, baiyi wata wata ba ya wuce bedroom dinshi da ita, bata ce mashi komai ba saida ya sauketa bakin gado ya wuce bathroom kamar bashi ba, Binshi da kallonta tayi harya shige bathroom din aranta tana ayyana halayenshi, mey yake nufi kenan daya kawo ta dakin shi ta tambayi kanta, badai yana nufi anan zata kwata ba ta sake tambayar kanta, “chap lallai ma, jiya Ka gaya min bakar magana Ka min korar kare yau kuma Ka wani lallabo Ka shugo dani dakinka kamar babu abunda ya faru, Ay Wallahi tunda Nace na daina kawo kaina inda kake bazan Kara ba” tana kaiwa nan ta miqe tsaye ta fuce daga dakin tana gunguni, tana hawa sama kuwa ta shige daki ta rufo kofarta tayi kwanciyarta akan gado.

Yana fitowa daga bathroom yaga daki wayam, babu ita babu inuwarta, saida yadan cije lebenshi kafin ya kwanta.

Washe gari da sassafe ta Tashi ta hada masu break ta jera kan dining, tana gamawa ta debi naga ta wuce sama abunta, tana shiga daki ya zauna bakin gado ta soma cin breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta ture abuncin ta karasa shirya wa, wata atamfa ta janyo holland da akayi mata dinkin Riga da skirt ya janyo, atamfar sai kamshin bakhoor wardrobe balls din amrukht_incense take saboda ta saka balls din a cikin wardrobe dinta wanda ya bi kayan nata da kamshin dadi sosai, agggauce ta shirya ta zura skirt din, saida tazo zuge zip din skirt din ta tabbatar da ta karu sosai, tayi qiba, da kyar ta samu ta zuge skirt din ta zura rigar, bata wani iya daurin dan kwali ba don haka ta daura dan medium mayafinta akanta ta fito hannunta rike da dankwalin atamfar, cikin natsuwa ta sauko kasan, kanta a kasa ta wuce kitchen ta dauko basket din abunci data dafa ma su salima aggauce, tana fitowa ta tsaya gaban dining ba tare da ta dago kanta ba, kamshinsa ne yayi mata sallama Tayi saurin daga kanta, anatse yake takowa daga dakinsa yana kokarin gyara agogon hannunshi, kasa dauke idanunta tayi daga kanshi, yayi masifar kyau sosai, komai nashi with class da gayu naira ta gama zama a jikinshi sosai, saurin kauda kanta tayi don ya dago ya kamata tana kallonshi, tabe baki kawai yayi ya zauna kan dining, “Ina kwana” amra ta fada ba tare da ta kalleshi ba, “lafiya” ya amsa ta kai tsaye, baima buqaci ta zuba mashi komai na ya deba coffee kawai ya fara sipping anatse, ya dauka kusan minti goma yana sha anatse ba tare da ya dago ya kalleta ba itama bata sake gigin kallonshi ba harta kwashe basket din ta dawo parlor ta aje ta zauna zaman jiranshi.

Yana gamawa ya bar dining din ya koma dakinshi ya dauko wayanshi da ya manta a dakin kafin ya wuce hanyar futa ba tare da yace mata qala ba, batayi wani mamaki ba don ta gama karantar halayenshi yanxu, shidai kamar wahainiya yake, yau ya chanza launi gobe ma haka zai chanza wani Launin, tana Ganin fucewar shi  Tayi saurin miqewa ta wuce inda ya fidda motar, anatse ya karaso inda yayi parking ta bude motar ta shige gaban motar, tana rufe kofar yaja motar suka bar compound din gidan.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yace ci kanki ko ci kanka ba Har suka karaso asibitin, shi ya fara futowa yana kashe motar kafin ta fito itama tabi bayanshi, anatse take tafiya da basket din hannunta tana haki kamar wadda tayi gudu, mamakin yanda take zama weak takeyi sosai, saida ta dan tsaya ta huta kafin ta dauki basket din, wani saurayi ne yayi saurin saka hannunshi kan basket din shima zai taimaka mata Ganin yanda take haki sosai, hannunshi rike da lapcoat da alamu likita ne shima, saurin dagowa tayi ta kalleshi tana sauke nauyyayiyar ajiyar zuciya, murmushi yayi mata “let me help you, you look

stressed” ya fada anatse, turanci shi ma dadin sauraro, qaqalo murmushi tayi tace “no thank Zan iya”

“No ma’am let me help bai kamata kina daukan abu mai nauyi ba” ya karashe sounding so caring and calming, ba tare da ta kalleshi ba tayi gaba yabi bayanta, Amar daya hangosu tun daga nesa don tana biye dashi harya wuce ta yazo gab da kofar dakin ammah, yana shirin budewa ya waiga ko zai hangota nan take idanunshi ya sauka akansu, dabanshi ne ya bada dam idanunshi Har sun fara yin jaa ganinta da yayi da saurayin suna tahowa, Har suka zo gab da kofar amra tayi saurin jaa da baya ganinshi a tsaye ya kafa mata jajayen idanunshi, ko ba a fada mata ba tasan wannan yanayin nashi da take gani kwance akan fuskanshi, he’s pissed kuma ranshi a bace yake, gabanta ne yadan fadi dukda bata san dalilin fushin nashi ba don haka gudun karya dizgata Tayi saurin juyawa ta kalli saurayin fuskanta dauke da murmushi tace “thank you I will

Take it from here”

Ba tare da musu ba ya miqa mata yana mata murmushi yace “it’s my pleasure”

Yana kaiwa nan ya juya yana murmushi don tayi capturing dinshi wanda yaso ya karbi number ta saidai mutunmin daya gani tsaye ya kafa masu idanu kamar zai cinye su ya hade rai yasa yayi tunanin maybe mijinta ne ko yayan ta don haka ya juya kawai ya wuce paediatric ward daman nan yake aiki.

Tunda ta karbi basket din ta juyo batayi gigin dagowa ba ta wuce cikin dakin.

Tana shugowa ta tsaya chak tana shirin sakin basket din Ganin ammah a zaune, salima a gefenta da aman sai wata nurse a tsaye tana examining dinta, da sauri amra tace “ammah!!!!”

Hakan ya fargar dashi daga sake sakin da yakeyi na magani ta da zaiyi na abunda tayi, da sauri ya shugo cikin dakin jin ta ambaci ammah, da sauri ya karaso ya tsaya kyam shima ya kasa motsawa yana kallon ammah dake kallonshi fuskanta dauke da murmushi tana miqa mashi hannu shida amra, cikin sauri ya karaso inda take salima na Ganin haka ta matsa fuskanta a washe dan dadi, aman ma wani irin dadi yake ji tun daga dare jiya zuwa yau don tun wajen karfe biyu ta farfado, dukda batayi magana ba alokacin Har zuwa yanxu,

Hannunta yayi saurin kawowa ya rungumeta sosai fuskanshi dauke da murmushi da farin ciki, gaba dayansu. Kallonshi suka fara yi don kusan zasu ce this is the first time suka ganshi cikin farin ciki babu abunda yake cewa sai “Alhamdulillah ya Allah alhamdullah”

Saurin dakin ammah yayi yayi sujudul shukr ya godema allah, dukkansu suka kallonshi sukeyi kowannanen su fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, amra dai baya ta danyi ta kafa masu idanu shida ammah, babu abunda yake hangowa sai tsantsar kaina da yake yima ammah sosai, saurin mikewa yayi ya sake rungumeta yace “ammah na ammah!!!”

Shafa kanshi tayi hannuna na yin karkarwa tace “so…son” runtse idanunshi yayi don bai taba tsammanin zai sake jin sunan a Bakinta ba, fadin irin farin cikin da yake ma bata lokaci ne, “son tun yaushe nake kwance anan?”

Dagowa yayi ya kalleta tare da riko hannunta biyu murya shi chan kasa yace “don’t worry ammah, Zan fada maki komai”

Maida kallonshi tayi kan nurse yace “yaushe ta farfado, why didn’t you inform me?” Ya karashe yana kallon Aman, shuru Aman yayi kafin ammah ta kalli Amar “son ina daughter?” Waigowa sukayi nan amra ta tako Har inda ammah ke zaune akan gadon marasa lafiya an tokare bayanta da pillow, hawaye ne kwance fuskanta tayi saurin karasowa inda yake zaune, zame hannunshi ammah tayi ta rike na amra tace “daughter ya kike? Meysa kika rame sosai”

Fashe wa amra tayi da kuka har tana dan tureshi ta rungume ammah sosai a jikinta “Alhamdulillah ammah na Allah Kun Gode maka, mun shiga fargaba sosai ammah”

Shafa bayanta ammah tayi kamar ba surukarta ba tace “why are you crying dear, ya isa haka kukan, sai mu gode ma Allah ko” kallonsu Amar yayi ya kalli amra ya tabe baki, mamakin yanda ammah ta nuna damuwa akanta karara yakeyi daga farfadowarta

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 140

Update continuation

Matsowa su salima suma sukayi don ayi dasu,kowannen su kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki, kallonsu ammah tayi gaba ayansu tana jin wani dadi a cikin ranta sosai dukda bata san dalilin kawota asibitin da ayi ba saidai doctor da yazo daxu yayi mata bayanin kusan satinta guda akwace anyi mata operation saboda zuciyanta daya buga, suna nan zaune doctor ya shugo fuskanshi dauke da murmushi yace ‘’masha allah, hajiya allah ya albarkaci zuria arki, babu wanda ya runtsa gab dayansu saida kika farfado, allah ya kara lafiya’’

Godiya sosai duk sukayi ma doctor kafin ya buqaci ganin amar a cikin a office dinshi, mikewa yayi ya bi bayan doctor, yana tashi amra na zauna a inda ya tashi tana jin dadin, kallon ta ammah ta sakeyi tace ‘’daughter meysa kika rame? Bakya cin abunci ne?’’

Salima ce tayi karaf tace ‘’wallahi ammah bata ci, kullum sainayi mata Magana batason cin abunci saidai barci kamar shine abuncinta’’ juyowa amra tayi ta galla mata harara,

Murmusawa ammah tayi tana jin wani irin dadi aranta ta riko hannunta tace ‘’allah yayi maki albarka daughter, allah ya tsareki ya sanya farin ciki a cikin rayuwarki, doctor yayi min bayanin komai’’

Sunkuyar dakai amra tayi tana jin wani iri, muryanta chan kasa tace ‘’ameen ammah, allah ya baki lafiya’’

Gaba daya suka amsa da ameen, salim ne ya sake mastowa inda ammah take ya rike hannunta, kallonshi ammah tayi ta shafa fuskanshi ‘’hope kaima kana cin abunci?’’

‘’chap wannan ay baya barin kwano’’ salima ta fada tana hararshi, dariya sukayi gaba dayansu banda aman daya sunkuyar da kanshi, saida ammah ta dago ta kalleshi ‘’son, zo’’ ta fada tana kallonshi, amra ce ta matsa mashi gefe ya zauna ya riko hannun ammah ya sumbaceta yace ‘’allah ya baki lafiya ammah, we miss you a lot’’

Shafa kanshi ammah tayi tace ‘’I miss you all too,ka fito min da mata aurar dakai kaima zanyi karka tsufan min a gida’’ dariya sukayi gaba dayansu

Banda salima data hada kirar sama da kasa gabanta na faduwa, dan dagowa yayi ya kalleta ganin tayi gum kamar ba itace ke zolayar amra da salim ba, kauda kanshi yayi daga kanta ya kalli ammah yace ‘’insha allah very soon ammah’’ ya fada yaan murmusawa, gaba daya hira suka dunga yi mata suna saka ta dariya banda salima data koma gefen kujera ta hade rai jikinta a mace da maganar da aman yayi, tuaani ta soma yi aranta wato harya samu wata Kenan, saurin danne abunda ke ranta tayi don tana gab da fashewa da kuka, ya lura da ta don haka bai damu bay a kauda kanshi ya cigaba da hirar da sukeyi dasu ammah.

 

Amar na shiga office din doctor ya zauna ya kalleshi, nunfasawa doctor yayi yace ‘’alhamdullillah sir saidai mu godema Allah, jikinta yana da kyau sosai don masu larura irin tata da wuya ake samun waenda suka rayu, bazamu sallameta yanxu ba saboda zamuyi watching jikinta for couple of days don mu tabbatr da komai koma normal, bayan wannan inason nayi informing dinka akan abu daya da bamu fada maka ba saida mukayi bunciken mu tukunna, a cikin magungunan da akeyi ma hajiya prescribing wanda doctor hafiz ke bata mun gano akwai maganin da bai kamata ya bata ba, wanda yayi violeting medical rules dinmu,board member sunyi suspendin dinshi akan wannan dukda yanxu kusan sati guda Kenan rabonda yazo nan asibitin, bazamu hanaka kai kara ba idan har zakayi dukda zaiyi tarninshig imagine din asibitin, saidai muna neman alfar..’’

Dagowa yayi ya kalli doctor din ya katse shi ‘’no need for that, saidai inason ku duba staffs dinku da kyau, I will turn a blind eye on this saidai babu next time’’

‘’yallabai muna fatan hakan bazai s aka cire membership din asibitin’’ doctor ya tambayeshi.

‘’duk wani tallafi da company sukeyima asibitin nan baza a daina ba saidai bana buqatar service dinku’’ yana kaiwa nan ya mike ya bama doctor hannun shi kafin ya fuce daga office din a wuce dakin ammah, da sallama ya shugo, gaba dayansu waigowa sukayi suka zuba mashi idanu suna kallonshi, wani irin mugun kallo ya zabga ma amra dayasa ta dauke kanta daga kanshi ,ammah ta lura dasu saidai bata ce masu komai ba saima kallon amar da tayi tace ‘’son

harka dawo?, yaushe zasuyi discharging dina? Kasan yanda bana son zaman asibiti kwata kwata, kaarsowa yayi cikin dakin ya zauna bakin gado yace ‘’no ammah ba yanxu ba tukuna sai doctor sun tabbatar komai ya dawo normal tukunna’’

‘’no son, kaje ka masu Magana su bani sallama naji sauqi’’

‘’ammah please to ki bari zuwa gobe, kinga ko dinkin da akayi maki baiyi healing ba’’ ya fada a marairaice, amra ce tayi saurin kaste ammah dake shirin mashi Magana tace ‘’ammah please, ki bari kiji sauqi sosai saimu koma gida’’

Kallonta amah tayi tana murmushi tace ‘’toh shiknan daughter allah ya kaimu’’

Gaba daya suka amsa da ameen banda amar dayake kallon ammah da amrar yana mamakin yanda ammah keyi mata ba.

 

‘’sister inalw yau babu breakfast ne’’ aman ya fada yana kallon inda amra ke zaune don ya tashi ya bata kujerar gaban ammah, sai alokacin tama tunada basket data shugo dashi, kallon inda salima ke zaune lost in her thought tayi tace ‘’laa bata zuba maku ba, nazo da breakfast gashi nan a basket’’ amra ta fada tana mikewa ta bude kwandon ta zaro kulas din abuncin gaba daya da plates, kallon inda ammah ke kwance tayi tace ‘’ammah fa? Doctor yace zata iya cin abunci ‘’ amra ta tambaya tana kallon inda salima ke zaune, aman ne ya amsata don salima kwata kwata batsan sunayi bama ‘’no not yet saboda operation di da akayi mata’’

Sauke kanta kasa tayi ta zuba ma aman abunci kafin ta zuba ma salim ta miqa masu, godiya aman yayi mata kafin ya koma wajen carpet ya zauna ya soma cin abunci.

Ammah ce ta kalli salima dake zaune akan kujera tace ‘’daughter bazakici abuncin ba kema’’

Takowa inda take zaune amra tayi ta dan buge kafadarta tace ‘’bakiji ana Magana bane’’

Furgigig ta dago tace ‘’naam? Kinyi Magana ne?’’

‘’abunci? Bazakici bane ke, tunanin me kikeyi’’ amra ta tambayeta

‘’sai anjima bana jin yunwa,’’ salima ta fada tana doka tagumi, yar tsuka amra tayi ta wuce inda basket din yake ta fiddo da plate zata zuba mata tana dan haki,kallonta ammah tayi tace ‘’daughter ki kyaleta idan batasonci yanxu, kizo ki zauna ki huta haka nan ki daina wahalar da kanki’’

66 / 94