Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   29 / 94

84K to 87K   out of 279.4K words

gidan ruwa ne shiyasa gidan is always cold, ko’ina tsaftsaf white babu dogon datti ko kadan,sai kamshinsa dake tashi, daga gefe ta hango irin kofar shugowa, itama glass ne, kasa karasa wajen tayi ta dan kame daga gefe, Har kusan minti goma kafin ta fara takowa dan nesa da kofar, gabanta ne ya soma

faduwa ta rasa abunyi, juyawa tayi Har zata juya kafin ta dawo kuma fuskanta adan shagwabe tace “ni Wai mene yake buqatan ganina”

Saurin dafe zuciyarta tayi don kamar zata fadi ganin an bude kofar, tunda kan kafarshi ta dago Har Izuwa fuskanshi, ba kayan dazu ne a jikinshi ba ya sauya zuwa wasu daban,kamar yanda take kallonshi haka shima ya zuba mata nashi idanun kafin ya sauke ya raba ta gefenta zuwa sitting room.

Ganin irin kallon da yayi mata yasa taji jikinta yayi sanyi, don gaba daya fuskanshi babu wasa, kasa motsi tayi saida yace “seat!!” In a commanding way, da kyar ta tattara natsuwar ta ta juyo zuwa inda yake kafin ta zauna a chan gefen kujeran da yake zaune, ya dauka kusan minti biyar kafin ya janyo remote kunna tv tare da ya rage volume din tv, “why did you decide to disobey my rules?” Ya fada cikin natsuwa da sanyin murya wanda yasa taji jikinta yayi sanyi

Shuru ta danyi don Sai yanxu ta gano dalilinshi na kiranta akan tazo ta sameshi a saman, samun kanta tayi da qin dagowa ta kalleshi, a karo na biyu ya sake tambayarta “you know

I hate repeating my selfs, right?”

Dagowa tayi taga ita yake kallo, idanunshi cikin nata, take taji gaba daya jikinta ya mutu,

Samun kanta tayi da cewa “I’m sorry”

Ita kanta tayi mamakin furta wan hakan don bayaga dalilin da zaisa ya tsareta ba don ta gudu

“what I hate the most is stubbornness, and it looks like you’re one, idan jin manta let me remind you, na aureki saboda na taimaka maki right?, aure ne na halal, ko agaban Allah fitan da kikayi ba tareda izini na ba tsinuwar Allah na kanki, that’s not even important to me don to me this is nothing, you mean nothing to me, but amatsayinki na mace yanxu da kin shiga hannun wannan kidnappers din what do you think will

Happen huh? “ ya karashe cikin fada ahankali, sauke ijiyar zuciya yayi kamar wanda yayi race don zai iya cewa this is the first time yayi doguwan magana sosai da ita, “do you think Ina son zama dake ne?I only keep You saboda yarjejeniyar da mukayi nothing else ina samun abunda nake buqata Zan sallameki simple”

Tunda ya fara magan bata dago ba, da farko ta fara regretting guduwa da tayi don bata kawo yana da dalilan shi ba saidai jin abunda yace a karshe yasa zuciyar yin daci, hawayen da yake kokarin zubo mata ne suka fara ambaliya dagowa tayi ta zuba mashi jajayen Idan uwanta ta Kasa cewa komi shima kallon ta yayi yace “yes na taimaka maki kin samu abun da kike so, so nima Zan rabu dake ne only na samu abunda nake buqata”

Gaba daya she felt so stupid at the same time kuma tana jin zuciyarta na daci, tabbas tayi kuskuren rashin tunanin cewa yarjejeniyar aure sukayi wanda ko ba dade koba kuma zaice shima saita bashi abunda zai buqata daga wajenta saidai abunda yafi bata takaici shine ta Kasa gano takamaimain abunda yake buqata a

wajenta don tafi danganta komai da jikinta yake ao kuma ya samu tunda shine ya ta bata da budurcinta.

Idanunta da sukayi jaa sosai, ta dago ta zuba mashi tana son magana saidai tsoro na hanata, tunawa da maganganun Nadine yasa ta dake ta danyi murmushi ta gefen baki tace “me kake buqata daga wajen nawa? Bayan budircina daka karba are we not even? Daman bashi kake so ba kuma ka samu”

Wani irin disgusting look ya bata da yasa ta Kasa dauke idanunta daga nashi, fuskanta babu walwala ko Kadan don ta gama fusata da maganganunshi dukda tana tsoron shi sosai,

Shima yayi mamakin maganganun da ta fada mashi don he has never expect that from her bai taba tunanin zata iya bude baki ta fadi kalaman da ta fada ba, he’s so speechless ta gama bashi mamaki afusace ya sake kallonta yace

“What did you just said? Budurcinki?”

Dariya ya danyi wanda yasa kumatunshi don lobawa fuskanshi so cute dukda tana cikin fushi saida tayi admiring irin kyau da Allah yayi mashi.

Shuru ya danyi yana dana sanin Duk wannan yarjejeniyar da komai dama dalilin da yasa yaqi yarda yayi muamala aure da ita kenan, baya son yarinta kwata kwata, don a ganin shi raini ne sosai.

“Do you think kinkai da Har zanso abu a jikinki, ohhh so All this while abunda yasa kikayi growing wings kenan?, okay let me tell you something, I’ve never in my life think of wanting anything from a woman, babu macen da zan kalleta wanting wani abu na jikinta not even small girl like you, go back and review the contract I think you’ve missed something very important, and lastly this is the last time da zaki kalli cikin idona ki fadi min magana irin haka, you’re too young for me, you’re just like random girls around nothing special”

Yana kaiwa nan ya miqe yace “now get out of my room, I don’t want to have a glimpse of you around”

Afusace ya wuce daki, amra dai wani irin kukan baqin ciki ta fashe dashi, she has never been humiliated like today, tunda uwarta ta haifeta,Duk duniya babu wanda yake jin tsanarshi ayanxu kamar shi, maganganunshi sunyi mata babban tabo da bazata taba mantawa dashi ba, budurcinta ya tafi a banza, she has always been dreaming of getting married and giving her virginity to most important person in her life, Sai gashi wannan masifa data tunkaro ta, ta Kasa tunanin komai Sai maganganunshi, she’s nothing to him, kallon someone so cheap yake mata kenan, tasha kuka anan zaune Har saida ta soma jin haniniya kafin ta mike da kyar ta fuce mashi daga dakin, she regret having him in her life, yanxu babu abunda take buqata sai ganin basa Inuwa daya,haka nan ta sauko zuwa dakinta ta wuce cikin toilet, zaman cin doya tayi nan kasa, zuciyarta nayi mata ciwo, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” ta dunga furtawa kusan awa guda kafin ta soma jin sauqin a ranta, wanke fiskanta tayi ta fito jiki a mace kafin ta hau kan gado ta lullaba jin zazzabin da ya zo mata gadan gadan, ta dauka kusan awa guda tana rawar dari anan kan gado, fatanta dama Allah zai dauke ranta ta huta da wannan abun takaicin, barci ne yadan fizgeta a wahale,

haifa dake ta kiranta bata dauka hankalinta a tashe ta shirya domin zuwa gidan don bata san ya dawo ba kwata kwata, karfe biyu daidai saiga haifa a gidan, lokacin datazo Nadine na kitchen tana sauke lunch, fitowa tayi daga kitchen suka gaisa kafin ta tambayi inda amra take nan ta shaida mata tana dakinta, juyawa tayi ta fara hawa stairs don zuwa dakin nata, bude kofar da akayi yasa amra farkawa don daman barcin baiyi nisa ba don zazzabin ya fara dauke mata nunfashi, hankali a tashe haifa ta karaso gaban gadon jin yanda take fidda nunfashi, hankali a tashe ta yaye bargon ganin yanda tayi jargab da gumi, “subhanallah!!! Babe what’s wrong with you?”

Haifa ta tambayeta, amra da ta soma jin muryarta sama sama tace “haifff..zan ”

Kasa karasawa tayi don da kyar yake tattara nunfashinta, hankali haifa a tashe tace “meke damunki”

Ahankali amra tace “kaini toilet”

Da sauri haifa ta tallabota ta dagata suka rarrafa zuwa toilet, koda suka karasa rasa abunyi haifa tayi, ahankali amra da jikinta ke kaff kaff tace “zuba…min ruwa, Ina jin zafii a zuciya na”

Kamar zautatciya haka haifa ta janyo shower ta kunna ta fara fesa mata, ahankali luke warm wata ke sauka a jikinta, zubewa tayi nan kasa haifa biye da ita tana mata sannu don ta gama daburcewa itama, saida suka dauka kusan minti ashirin kafin amra ta dawo daidai, don zafin jikin nata da yake ji Har cikin qashinta ya ragu, ahankali haifa ta soma jin sheshekar kukanta, aje shower din tayi ta rungumo ta sosai jikinta hawaye na zubowa itama a fuskanta tace “babe dan Allah ki fada min meke damunki, what’s wrong with you”

“Haifa I hate my life, I hate everything around me tun tasowa na, bayan mutuwar iyaye na bani da gata banida koda haif, I hate coming to this country,I hate him so much, I’m in pain,nayi imani da kaddara amma da inada iko dana roki Allah bai barni darai na ba Har zuwa wannan lokacin”

Kuka sosai haifa ita ta fara aka rasa wanda zai lallashi wani cikinsu, kallonta haifa tayi itama fiskanta gwanin nan tausayi tace “babe I’m so sorry, Duk laifina ne, Nina baki wannan shawarar auuuu…”

“No stop it haif”.  Amra tayi saurin katseta kafin ta cigaba da cewa “ita never your fault babe, nice na buqaci taimakon ki kuma nasan da zuciya daya kika bani shawarar nan, Wallahi nan taba ganin laifinki ba acikin wannan abun, haba haif you’re not a friend to me but a sister, nan taba kawo tunanin zaki cuceni ba cause you’ve done so much to me, I’m d one to apologise because I share my burden with you, na saka ki cikin damuwar da bata shafeki ba”

Saurin rufe mata baki haifa tayi tace “babe no pls karki ce haka, you’re just like a blood sister to me don jin wuce friend your problem is our problem and we’ll solve it together now get up and be strong I will Alway support you, I promise this will be the last time you’ll ever cry,”

 Saurin share mata hawaye haifa tayi kafin ta taimaka mata su fito tare, bakin gado ta taimaka mata ta zauna ganin ac dakin yayi yawa yasa haifa ragewa zuwa heater kafin ta wuce closet ta zaro mata wata rigar mai kauri sosai, Nadine

ce ta shigo jin shuru don harya kammala lunch bata sauko ba,shima general din data fada mashi ouch is ready cewa yayi baya buqata.

Da sauri ta karaso gabansu hankali tashe tace “is everything okay”

Kallon amra nadine tayi tace “ma’am are you sick?should I call the doctor”

Haifa ce tayi saurin katse mata nunfashi tace “no need Nadine, please get her something simple to eat, don she’s weak”

Da sauri Nadine ta fuce zuwa kasa tana mamakin yanda amra ta koma lokaci guda don lokacin data sauko daga sama Har sukayi breakfast ba haka ta sauko ba, saidai tunawa da maganr da tayi mata cewa yana nemanta a sama yasa tayi tunanin ko yayi mata wani abun ne, shuru ta danyi kafin ta zubo white soup a bowl da dan hot tea mai kauri ta hawo saman dashi,Har gaban amra nadine ta Mika ma haifa ta soma bata kadan kadan, tana spoon biyu ta ce “ya isa babe I’m okay now”

Da kyar haifa ta samu ta bata tea ta karba shima bata wani sha sosai ba ta kauda kanta, tana son hana kanta tuna abunda ya faru dazu, don tana tuna words dinshi Sai hawaye.

Bangaren Amar tun bayan daya wuce daki ya zauna gefen gadonshi yana doka uban tsaki don  abunda ta fada yayi amshi zafi sosai, abunda yafi bata mashi rai shine tunanin da tayi ya hanata tafiya saboda yanason jikinta, “fuck”

Ya fada da karfi yana furzar da nunfashi mai zafi, baya son raini ko kadan, babu mace da ta taba stressing rayuwanshi kamar yarinyarnan, da farko daya dawo yana fatan Allah yasa she’s pregnant don yasan wannan ne last hope dinshi,yanxu kuma sai yake regretting yanda yayi stooping low to this level har yarinya kamar wannan ta kalleshi tace daman budurcinta yake ao kuma ya samu, saurin runtse idanunshi yayi ya furzar da iska mai zafi yace “this has to come to an end”

Harga Allah yana fatan tana da cikinshi saidai kuma wani bangaren na zuciyarshi na fatan karta samu cikin don yayi freeing dinta, he can’t take this burden yana jin haushin kanshi sosai. Abunda yafi bata mashi rai shine the way Duk duniya babu wanda ya taba jinta har cikin ranshi kuma yake tausayi kamar ta, lokacin da aka kusa kidnapping dinsu a cikin mota da yanda driver took the bullet meant for her yaji zafi sosai hankalinshi ya Tashi saidai babu wanda zaisan da hakan, tsaki kawai yayi tare da deciding zuwa asibiti da ita to confirm everything, don at this point Yan don sanin komai kawai don yasan

Decision din da zaiyi making don Idan Har babu cikin he will just free her and free him self from this mess.

Haifa dai bata bar gidan ba saida taga amra ta dawo daidai, harta fada masu abunda ya faru tsakaninta dashi, ba karamin zafi haifa taji ba saidai sannan yanxu idan sunce zasu kai zancen zuwa ga sharia court don a raba auren matsala zai jawo babba don dole sai an tuhume su don daman ga dalilin auren nasu so wannan is not a solution bayan wannan ma he’s so powerful, babu yanda zasuyi

suce zasu tunkareshi, solution daya daya rage shine kawai su zubama sarautar Allah idanu don ganin me zaiyi, Har lokacin basu kawo komai gane moe da abunda yake buqata ba, abunda yafi kwantar Ma da amra hankali shine Sauranta few weeks ta gama housemanship, tana gamawa zata karbi certificate dinta, daganan dai bata da dalilin zama anan kasar.

Bayan tafiyar haifa haka Nadine ta zauna kusa da ita tana tausasa ta tare da bata karfin gwiwa kan dagewa ta karbo yancinta itadai amra tana jinta kawai saidai kwata kwata yanxu bata sha’awar hada hanya dashi Ma balle ganinshi, saidai tayi alkawarin cigaba da rayuwar yanda ta fara don haka kawai saboda baqin cikinsa da impression dinshi akan ta bazaisa tayi downgrading kanta ba don she’s so strong ba kamar wasu ba da zasuyi giving up don haka

Ya dauki damarar kokarin yin harkokinta kawai.

Washe gari da kuzarinta ta tashi da marmarin cin wainar fulawa ta Tashi ta don haka tana wanka ta shirya cikin wasu shegun kaya masu kyau, wanda sukayi mata kyau sosai tabi shape dass ass dinnan ya fito sosai kamar ka sasheta ka gudu, bata saka hula ba haka zalika bata nannade gashin nata ba saboda ya dan jike wajen yin shower, haka nan ta barshi don yasha iska, sai sheki yakeyi don sabbin mayukan da take shafawa ya Kara fito da cika da silkim gashin nata, ba tare da tunanin komai ba ta sauko kasan ta wuce kitchen hankalinta kwance, fuskanta dai na nan da damuwa a kwance, tafiya takeyi amma kamar bazata Taka kasa ba don jikinta ya gama sanyi da alamarin dake faruwa a rayuwar ta ayanxu, a kitchen ta tadda nadine da sabuwar maid din dake taimaka ma pablo ayyuka, tana shigowa kamshin ta ya bade ko’ina, kallonta suka tsaya yi harta dan tsargu tace “Is there something on me” ta fada tana dan zaro ido alamun tsoro don Duk tunaninta abu ne ya hau kan jikinta da sauri maid din tayi kasa da kanta tace “good morning ma’am”

Nadine ce ta danyi murmushi itama tace “good morning, you look so beautiful”

Murmushi amra tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace “Har Kun bani tsoro, Kun Tashi lpy?”

Nadine ce tayi saurin cewa “lafiya how are you feeling now?”

“I’m okay” ya amsa Nadine tare da matsowa don ganin abunda suke yi, kallon bowl din amra tayi tace “mene ne wannan zakuyi?”

Da sauri maid din dake marinating Kazan tace “chicken nugget ne, shine za ayi for breakfast” dan tabe baki amra tayi tace “uhm, akwai sauran flour din nan?”

“Yes ma”

Cikin pantry maid din ta shiga ta zaro bucket din flour ta kawo tace “gashi ma”

Da kanta ta umarci su bata wani bowl din ta zuba flour din da pepper mix da dan seasoning kafin ta fara soyawa, hira suka dan shiga yi Har suka gama, nadine ce ta soma fita da warmers din da aka zuba breakfast a ciki zuwa dining tana shirin aje flask din coffee dinshi ya fara saukowa kasan, cikin kananun kaya gajeran wando na army sai bakin riga wanda tadan kamashi sosai don kana

hango damtsen hannunshi, da sauri Nadine ta dan rissina tace “good morning sir”

Hannu kawai ya daga mata don waya ne maqale a kunnenshi, zama yayi tavfara serving dinshi harta gama kafin ta zuba mashi coffee yanda yake buqata

Hankalinshi nakan waya inda yace “ammah  kwana na biyu fa kenan, Har kin fara tambayan dawowa, I promise Zan dawo very soon, ayyukan danazo yi anan Ma ban samu nayi ba saboda weekends,”

“Ay nasan Idan ka koma baka dan dawowa shiyasa nake son confirming, Muhammad girma fa kake yi bawai shekarunka sauka suke ba, Duk sanda na kawo maka maganar aure saikace a bari”

Dariyar ya danyi jin abunda tace kafin ya cigaba “ammah na please, za ayi Duk abunda kikeso but ba yanxu ba please when the time comes, komai yana da lokaci ya karashe yana sipping coffee,”

Ahankali ya dago idanunshi yana kallon hanyar da m5 ke tunkarowa, kauda kanshi yayi gefe Har m5 ya karaso ya Sara mashi kafin ya aje mashi files din, tsayar dashi yayi ta hanyar daga mashi hannu ya cigaba da wayan 

Daga chan bangaren ammah tace “nasan yanxu Safiya ne ko? Kayi breakfast?” 

Murmushi ya danyi don yana son yanda take nuna how much she cares for him, “yanxu zan….”

Bai kaiga karasawa ba amra ta bullo daga kitchen din hannunta dauke da plate din wainar datayi, batama Lura dashi da m5 dake tsaye ba ta tunkari hanyar dining din kanta a kasa tace “nadine zokiyi tasting kiji, kamar babu….”

Kamshinsa da taji yasa ta dago idanu, Duk ita suka zubama ido daga shi Har m5 da nadine, cikin saurin m5 ya dauke nashi idanun, nadine ma Kasa

29 / 94