Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   69 / 94

204K to 207K   out of 279.4K words

aka baki kiyi ba daidai bane kika karba kikayi, kinci albarkacinta don saboda ita ne kike nunfashi Har yanxu,”

Yana kaiwa nan ya fuce fah dakin asad na biye dashi, ganin yana shirin sauka kasa yasa asad saurin cewa “ oga Dayan doctor fah?”

“No need, Zan wuce gida yanxu saikazo” ya fada yana mikama asad hannu, sallama sukayi kafin ya fuce daga cikin headquarters din ya nufi inda tayi parking motarshi.

Yana shiga motarshi ya sauke nauyayyanijiyar zuciya yana jin zafi aranshi sosai, saidai yanda ya saki komai a hannun asad sai yaji kamar ya sauke wani nauyi ne daya rataya akanshi, ya dauka kusan minti goma a zaune kafin ya kunna motar shi ya fuce daga headquarters din.

Gidan gona…

Futowa malam labaran yayi daga cikin gidan gonar ammah bayan ya gama ban ruwa saboda cikin kwanakin Ana rana sosai,gidan gonar nada girma sosai don babu abunda baya shukawa a ciki Harda kiwon kaji Duk yana yi, fitowa yayi hannunshi rike da buta, sanye yake da triga da wando da yadi fari, ya rame sosai ba kamar yanda yake abaya ba saboda rashin lafiya da yayi ta tsawon sati uku, don hakan ne ma bai samu yaje ya kaima ammah abunda ya fidda na cikin nima wanda ya gyara, don Duk shekara saiya fara kai mata gida idan ta diba sauran sai akai kasuwa idan an sayar sai ya maido mata da kudin dukda kusan Rabin kudin take bashi a matsayin ladan shi wani sa’in ma haka zata ce ya rike gaba daya kudin, ammah wadda yake kira da hajiya ta gama yi mashi komai sosai, don yanda take kyautata mashi, bata sanshi ba bata san asalin shi ba hasalima tsintarshi tayi ta bashi ci ta bashi sha da sutura da yanda ta damka mashi amanar gonarta ba tare da ta waiwayeshi ba hakan na sashi jin Duk duniya babu abunda zata nema a wajen shi da bazai yi mata ba, fatanshi kullum Allah ya kawo ranar da zai saka mata da alkairin datayi mashi.

Zama yayi bakin bishiyar dake gefen gonar yayi ya daura alwala, yana gamawa ya shimfida abun sallah ya tafa kabbara yana idarwa ya zauna yana lazimi yana bin tsirarrun mutane dake yawo, 

Mikewa yayi ya tattare abun da yake sallah dashi tare da butarsa ya shige cikin gidan gonar, bin ko’ina ya soma yi da kallo yau sati shi guda kenan rabon da yazo gona sai yau saboda rashin lafiyar da yayi na zazzabi da matsanancin

ciwon kai dake hanashi yin komai don Har dishi dishi yake gani idan ya Tashi da safe don haka ya zauna a gida ba tare da ya futa ba Har saida ya danji dama dama. 

Gaban buhunhunan shinkafa kusan guda talatin ya tsaya ya bude yana duba su sosai, shinkafar tayi kyau sosai daman ya bari sai ya tara bugu talatin kafin ya kaima hajiya don ta gani, saida ya duba duka kafin ya zaro wayarshi dake cikin aljihun wandonshi, yar Nokia ce karama da ya saya cikin Albashin da ammah ke bashi dukda yana da kudin da zai saya babba hakan baida ya saya ba saboda babu wani amfani, he’s leaving a lowkey life.

Kira ya fara yi ana daga ya kafa wayar a kunnenshi “iruu ya aiki, Ina buqatar akori kura karama wadda zata diba buhu talatin gobe”

Shuru ya danyi yana sauraron shi daga chan kafin yace “yauwa Nagode sosai.

Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya futo daga gonar ya rufe inda yake Adana shi kafar kafin ya wuce bakin titi, tunda ya taaya bakin titin ya dafe kanshi dake Sara mashi sosai, wani irin dishi dishi yake gani, kwata kwata baiyi tunanin tsaywan shi kan titi ke kawo mashi ciwon kai ba sai yanxu, da kyar ya samu ya tsallaka ya tari mai machine don ya kaishi GRA.

Tafiyar minti a shirin ta kawosu high way dake hade da titin taura estate don mashin baya  wucewa ta wajen,saukowa yayi ya zaro dari biyar ya bama mai napep, godiya yayi mashi ya fara takowa zuwa eatate din, tafiyar minti goma ta kawoshi taura estate, bai wani sha wahalar shiga ba don an sanshi, yana shugowa ya wuce babban apartment din estate din kai tsaye, da sallama ya karaso inda securities suke dukda ba musulmai bane hakan baisa basa amsawa ba, gaisawa sukayi kafin su bude mashi ya shige ciki, da baba mai gadi yaci karo a compound din gidan yana  zuba ma flower ruwa, yana ganinshi labaran yayi saurin karasowa inda yake suka gaisa tare da yaushe gamo.

“Kayi wuyar gani labaran, yau kusan wata guda rabonka da gidan nan” mai gadi ya fada yana zuba ma flower ruwa

“Wallahi baba nayi rashin lafiya ne sosai, baba iya futa ma, sai cikin kwanakin nan na samu zuwa gidan gona” labaran ya fada yana dariya

Kallonshi baba mai gadi yayi ya aje tiyo din ruwa yace “Allah sarki shiyasa, Ay hajiya ma an kwantar da ita a asibiti yau sati biyu kenan, jiya aka sallamesu”

“Subhanallahi Allah kasa kaffara ne ay ban sani ba dana zo”

Dan matsawa baba mai gadi yayi labaran na Ganin haka yasan gulma zaiyi don haka ya dan dara kawai baice mashi komai ba yana sauraron sa, “labaran baka da labarin abunda ya samu hajiya?”

Da mamaki labaran yace “ah ah fatan dai ba wani munmunan abu bane”

“Hmm rayuwar nan dai babu tabbas, Ka janyo mutun Ka sashi a inuwa ya jefa Ka a rana, wannan la’ananniyar matsiyaciyar yarinyar nan ya take da suna yar aikin nan”

Da mamaki labaran yace “lantana?”

“Ee ita fa, la’ananniya aje guba ta dunga zubawa hajiya a abun sha, rana daya Allah ya tonu asirinta matar yallabai ta kamata”

Da mamaki labaran ya zaro ido yana innalillahi, “yaushe akayi hakan” labaran ya tambaye da yana kallonsa 

“Ay nake fada maka dalilin da yasa hajiya ta fadi kenan an dauka ma bazata rayu ba” baba mai gadi ya fada yana sauke muryarshi kasa

Zaro idanu labaran yayi yana jin tsanar lantana yace “gaskia wannan matar anyi azzaluma,allah ya saka ma hajiya ya tsareta,”

“Ameen fah, Ay badan matar yallabai ba da tuni saidai gawar hajiya” baba mai gadi ya fada yana jimami

Wani irin kallo labaran yayi mashi najin rashin dadin kalamanshi na karshe, saurin katseshi labaran yayi don yasan baba maigadi Akwai surutu haka zai dunga zance babu kan gado don haka yace “godiya ta tabbata ga Allah, Allah ya tsare wannan ahalin gaba daya”

Tabe baki baba mai gadi yayi yana yau at goro baya son zancen yayi ending don haka yace “Ashe shi yallaban aure yayi achan wata kasar, itace matar tasa data taimaki hajiya ay”

Jinjina kai kawai labaran yayi ba tare da yace komi ba kafin yadan nunfasa yace “yanxu ana iya Ganin hajiya?”

“Haba kai kuwa, jiya fa ta dawo Ka bari sai zuwa jibi saikazo” baba mai gadi ya fada yana daukan tiyo yana Jan ruwa,

“Toh shikenan bari na koma baba, sai zuwa goben” sallama sukayi labaran ya juya, 

salima ce ta futo daga ciki main entrance hannunta rike da flasks “baba bismillah ga abunci”

Da sauri baba mai gadi ya ajiye tiyo din ya taho da gudu ya karbi Kumar yace “Nagode karantar hajiya Allah ya Baki miji na gari”

Murmushi kawai tayi mashi ta Mika mashi ta juya zuwa ciki.

Malam labaran dayaji muryarta Har tsaki Yan kanshi yayi saurin tsayawa, kanshi ne ya soma juyawa yana falshing wasu memories da bai gane daga inda suke ba, saurin juyowa yayi don Ganin koma wacece, bin bayanta yayi da kallon don harta shige cikin gida, dafe kanshi yayi dake Sara mashi yayi yana jin kamata rawar tasu tsaye akanshi, saida ya dauki kusan minti biyu a tsaye kafin komai ya kafa mashi ya fuce daga gidan.

Katsina…..

Yau kusan wata biyu kenan hankalin hajiya kareema atashe, ga ciki nan sai girma yake dukda bata laulayi saidai kumburi, kana ganinta kasan ciki gareta don yana da girma sosai, komai yanxu ya tabarbare mata, hanyar samun kudinta Duk ya toshe saboda ciki da yayi mata cikas rabonta da talatu tun bayan

dawowarsu daga wajen malami , ta daina daukan wayarta koda ta kirata, ga talauci daya fara masu katutu don yanxu makarantar government dinma ta gagari yaran gaba dayansu, khadi dai bata fasa Sana’a ba don harda saida gwanjo yanzu takeyi, ta zama wata bugaggiyar Yan matan tasha babu mutunci, saboda da dan abunda yake samu suke samu au daura sanwa, yanxu muhammad ya rage tura masu kudi sosai saboda yabar Jordan ya koma France, nan kuma yanda zai tura masu kudi ya zama wahala saboda idan ya  tura kudin saiya dauki watanni kafin yazo masu wanda ko yazo ma a banza yake tafiya don daddy ke cinyeshi tass ah harkar chacha daya koma da bariki, don yabar harabar dillanci don babu cigaba kwata kwata,daure baki kam anyi mashi don yaga ciki a jikin Haj kareema saidai baice komai ba game da ciki, haka ta dunga rainin cikin nata yau lafiya gobe jinya khady ce kadai tasan cikin shege ne a jikin mummy, tun tana damuwa itama harta watsar ta daina damun kanta akan abun kunyar uwartata ta cigaba da harkokinta na Sana’a, asma is useless batada wani amfani kwata kwata, kullum tana fama da kafa daya a tsakar gida don ko shafa bata iyayi,  akan haka kuwa babu irin zagin da bata sha wajen Haj kareema ita da ko dukansu bata yi ada chan baya balle akaiga zagi.

Zaune suke akan tabarma a tsakar gida gaba dayansu, khady na arranging gwajunan data saro while haj kareema na zaune tana jefa gyada a baki asma na yi mata tausa a kafa, su jalal ma na gefenta suna cin gyada, sallama akayi daga waje, kallon jalal hajiya kareema tayi “kai jeka ga da wa ake sallama”

Mikewa yayi tsaye ya fuce, da gudu ya dawo yana haki, “daddy ne daddy ne”

Mikewa haj kareema tayi ta janyo mayafinta khady ma mikewa tayi don Ganin yau wace irin masifar ya kwaso, futa sukayi gaba daya kafin su tsaya chak a bakin soro, daddy ne kwance jini na bin jikinshi yana wayyo Allah na Zan mutu, hannu aka kareema ta dora tana kallon yanda kafarshi ta karkace ta juya baya, kallon dandazon mutanen dake bakin kofar shugowa tayi da waenda ke gabanshi hankali atashe “na shiga uku meya sameshi yau wace irin masifa ce wannan Ka kwaso mana”

Kallonta mutanen sukayi suna Allah wa dai da halin mata irin wannan, wani daga cikin mazan ne yace “accident yayi a bakin titin, munyi munyi yabari akaishi asibiti shine yace akawo shi gida shine muka kawoshi nan”

Cije yatsa hajiya kareema tayi don yasan dalilin dayasa yace akawo gida saboda baya son fidda kudi, “Toh Ay shikenan kuje ku barshi anan tunda hakan ya tsaba”

Mikew Duk sukayi suka barshi anan kwance, alamajirai biyu manya tasa suka shigo dashi cikin gida suka kwantar shi anan kan tabarma, zagaye shi duka sukayi yaran harma da kareema “Yanxu kai fisabillilahi kayi mana adalci kenan? Kullum cikin masifa muke daga wannan sai wannan ni Wallahi ba gaji”

Yana jin azaba haka ya dunga surfa mata masifa yana kwashe mata albarka, “kinsan Allah kareema ki fita a idona, nine Ruffin asirinki don haka mu taru mu rufama juna asiri kawai”

Yana kaiwa nan ya kwala uwar kara, wani irin murmushin takaici kareema tayi ta kalli khady “ki tashi kije gidan malam mai Gyaran hannu ki rokesa kozaizo ya duba”

Tsaki khady tayi ta kalleta “nifa kinga Wallahi yau ban fita siyarda gwanjon nan ba saboda jin rikeni Saina yi shara da wanke wanke, ko tura wannan mara amfanin taje ta kirashi”

Tana kaiwa nan ta mike ta kwashi kullin gwanjonta ta fuce daga gidan, shuru kareema tayi tana debe mata albarka a zuciya don bata tankwabarta ko musa mata saboda ita kadai tasan sirrin ta, kallon asma kareema tayi tace “Toh mara amfani ay gaskiar ta ne bazaki zauna ba bakya amfanuwa, mike kije gidan malam ki kirawoshi”

Sauke kanta kasa tayi tana hawayen cin mutuncin da ake mata kafin ta zari mayafi ta fuce tana dogara sandarta.

After like 20 mins saigata da mai Gyaran targade, da sallama suka shugo nan kareema ta bashi waje don ya duba daddy, kallon hannunshi yayi da kafarta daya yace “karayar hannu ce sai targade a kafa”

Tun kafin ya kaiga fara wa kareema tace “kuma Nawa za a baka”

“Dubu daya” ya amsata 

“Haba malam ina laifin dari uku” kareema ta fada,

Mikewa yayi yace “ku nemi wani yayi maku”

Da sauri daddy yace “kutmaa kareema Allah ya tsine maki yanxu dari biyar ce bazaki iya badawa ba don jaraba ayi min gyara”

Gyaran murya mai Gyaran yayi yace “dubu daya nace ba Dari biyar ba”

Wani irin banzan kallo tayi ma daddy, yana Ganin haka yace “toh ki bada Dari biyar Zan bada Dari biyar nima”

“Ay Wallahi baka isa ba, dari uku nayi niyar bayarwa idan bazaiyi ahaka ba Ka zauna Ka rube ma”

“Ke wai wace irin Mara imani ce” daddy ya fada yana hawayen azaba

“Akwai nada imani sama dakai azzalumi” kareema itama ta maida mashi martani, tsaye a mai Gyaran yayi yana kallon ikon Allah yanda suke zagin juna agaban yayan su, tsaki kawai yayi yace “ni kunga tafiya ta”

Da sauri dady ya tsaidashi “ki bada Dari ikon Zan cika sauran”

Zama mai Gyaran yayi ya gyara mashi hannu da kafa kafin ya daure ko Ina “a dunga gasashi da ruwan zafi kullum sannan Zan dawo jibi na duba hannun” mai Gyaran ya fada yana mikewa

Karema ce ta katse shi “Ay basai Ka dawo ba don sisi na bazan sake bayarwa ba”

Maida kallonta tayi ga dady tana kokarin zaro dari uku daga gashinta datake kullewa tace 

“Aikin banza asararre ashe da kudin Ka ajikinka amma bazaka fidda sai na bada a nawa ” ta fada tana kallonshi bayan ta mika ma mai gyara dari uku, saida ya tabbatar ta bada kudin ya zaro nashi daga aljihu da hannu daya kafun ya kalleta

yace “Ay babu asarriya kamar ke, keda y kikayi cikin shege da auranki Ay kece asarrariya”

Idanun mummy ne sukayi jaa sosai, batayi expecting hakan ba daga wajen shi, ashe yasan komai, shiko mai Gyaran hannu saida ya taaya ya sake kare masu kallo yaqi fucewa don jin abunda zata ce 

“An fada maki ban sani bane? An fada maki bansan ta yanda kike samun kudin da kike kashewa a cikin gidan nan bane? Tun Ranar da kuke maganar da diyarki na san komai? Saboda haka ki kama kanki wallahi”

Tsit kareema tayi bata Kara ce mashi Kala ba karshe ma dai daki ta wuce tana hawayen bakin ciki da dana sani.

Abuja Nigeria…..

Yau kwanan ammah goma da dawowa daga asibiti, taji sauqi sosai don tana takowa Har kasa tana saukowa, Duk bayan kwana biyu Amar ke kaita asibiti Ana mata general checkup, gaba daya yanxu health dinta shine damuwanshi, baya zaman hour guda koda baya gidan bai kirata a waya ba yaji yanayin jikinta, tun tana hanashi Har tazo ta saba ta hakura don gaba daya yanxu ya zama very strict akan komai, Har yau kuwa baiyi gigin kawo masu house help ba, salima da amra keyin komai dukda salima ce karfin aiki sosai don amra na kwance kullum bata da aiki sai barci sai cin abunci kamar kasa, ammah na kura da ita sosai don yanxu tafi damuwa da ita agidan akan kowa, kowa mamakin hakan yake Harda Amar saidai babu wanda ya taba tambayarta dalilin da yasa take damuwa akan amra da bata so much attention dinta gaba daya don Kowa yanaa Ganin hakan ne a matsayin saboda ta bata jininta ne alokacin da yake buqata, bangaren ammah kuwa ita kadai tasan komai haka zalika bata fada ma kowa ba tayi shuru abunta Harda amra ma.

Bangaren Amar yanxu babu laifi yana dan nuna kulawa ma amra don tun bayan da sukayi wannan maganar da ammah yake dan shiga sabgar amra, haka Duk Safiya idan yaje gaisheda ammah in ya fito zai wuce dakin ta don ya duba lafiyar yanda ta tashi, Duk sanda yake zuwa tana barci don haka yana shiga yake futowa baya zama ko na minti daya, ammah na Lura da hakan da yakeyi kullum kuma ta nuna mashi jin dadinta akan hakan sosai.

Tskanin Aman da salima kuwa yanxu sai fada kamar kaji haka zai biye mata suyi ta fada,Akwai ranar da tana shara a kitchen ya shugo, yana shugowa ya zubarda banana daya ci anan kasa inda ta share, ranar tayi masifa kamar menene haka nan ya tsaya yana kallonta  ta rike kugu idanunta a rufe tana masifa “kaje Ka kira budurwar kanta share maka ni ba yar aikin ka bace”

Kallon cute face dinta yayi, ba karamin burgeshi takeyi ba da yanda take masifa abun yana kunnashi sosai “Ay baby na bata shara, yar hutu ce shiyasa nake sonta sosai”

Ya fada yana sake kunnota,

Wullata da tsintsiyar tayi ta wuce sama tana kuka. Tana futa kuwa ya tuntsireda dariya abunshi don ya gama gano ta, ko ba a fada mashi ba shi da kanshi ya shaida irin mahaukacin son da take mashi, shima dai daman ba wani giving up da yayi kawai dai yana son ya tabbatar tana sonshi.

Ammah ne ta fito daga part dinta ta wuce dakin amra, a kwance ta taddata wujiga wujiga daure da towel, da sallama ammmah ta shigo dakin “daughter barcin ne Har yanxu kusan sha biyu ko breakfast bakiyi ba”

Da kyar amra ta dan gyara zaman towel dinta gaba dayanta kana ganinta kasan she’s weak don ta dan zabge sosai tace “barka da rana ammah bismillah”

Karasowa Ind a take ammah tayi ta kalleshi tana murmushi “ya jikinki daughter? Hope baby baya baki wahala sosai?”

Da mamaki amra ta dago ta kalleta tana neman Karin bayani, hannunta ammah ta kama duka biyu tana murmushi tace “nasan baki sani ba,shiyasa nayi deciding na fada maki”

Nunfasawa ammah tayi ta sake kallonta ya cigaba da magana “wannan

69 / 94