Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   5 / 94

12K to 15K   out of 279.4K words

ko’ina, ba tare da ya kalleta ba ya raba gefenta ya wuce ciki, saida ya karema ko’ina kallo kafin ya juya ya kalli Nadine data karaso da akwatinshi da laptop bag dinshi, sama ya wuce tabu baya shi da akwatinnashi,karema gidan kallo yayi tsab babu abunda ya sauya Sai furnitures da yasa aka sauya zuwa sabbi, gidan yana daya daga cikin properties dinshi daya gina da kudinsa saidai bai banbantashi da saura gidajenshi ba da yake hadawa da inkiyar sunan familynsu wato TAURA

First stair ma ya fara hawa saida ya tsaya ya karema ko’ina kallo kafin ya hau sama da yake na master bedroom a ciki Sai tapkeken sitting area Harda dining, bude kofan bedroom din yayi direct ya saka kanshi ciki, yana nan yanda yake saidai kayan alatu shima da aka chanza, Nadine kuwa tana karasowa daidai gaban dakin ta aje akwatin tareda Rossi awara gaishesa, bai kalleta ba ya amsa da “uhm” bai sake cewa komai ba saima kafama babban frame din dake gefen bedside dinshi idanu yayi, hotone shida dadan shi lokacin da yana school yazo mashi surprise visit, muryar Nadine ne ta katse shi don yana dauka ta fuce “sir do you need anything”

“no thanks ya amsa”

Yana son tambayarta inda yarinyar nan take saidai kuma ya basar yace “you are excuse”

Tana shirin futa yace “just coffee in the next 1hr”

“Yes sir tayi saurin amsawa “

Sauko wa tayi ta wuce dakin amra, wadda tunda ta zo kwana biyu kenan bata lekowa ko’ina, abincin Ma daki Nadine ke kawo mata shi, bude dakin Nadine tayi ganin an rage hasken dakin Saina bedside yasa ta kallon fuskanta mamakin yanda ta dage da kuka kullum wanda ya sanya idanunta yin ciki ciki Nadine keyi saidai bata taba tambayarta dalilin hakan ba don ba huruminta bane, gani ko taba abuncin ta saya kawo mata batayi ba yasa ta jawo mata kofar ta rufe ahankali, Kasa ta sauka ta fara diban time gudu min karya wuce lokacin daya buqaci coffee.

Wanka ya farayi kafin ya futo daure da towel, closet dinshi ya bude ganin komai nashi yana nan yanda ya barshi yasaashi yabawa da company daya bama maintainance din gidan hatta sabulun shi da abubuwan buqatanshi Duk an zuba mashi a ciki, jallabiya ya zura ya tada kabbarar sallah, saida ya Rama Salomon da ake binshi kafin ya miqe ya sauya zuwa kayan baccinsa farare don kusan karfe 10 na dare kenan, knocking akayi ya bada umarnin shigo, aje mashi coffee din tayi kan table kafin tace “sir here’s the coffee” bai kalleta ba haka zalika bai amsa ba, ganin kamar bai Jita bane yasa ta maimaitawa

Gyaran murya kawai yayi yace “you’re excuse”

Sum sum ta fuce ganin yanayinshi na rashin magana,

Saida yasha coffee don ya janyi laptop dinshi ya soma wasu Yan ayyuka, Sai kusan karfe 1 ya aje laptop din ya rage hasken dakin ya kwanta.

Washe gari kuwa a kunnanshi aka kira sallah asuba, dadin gida kenan, muke wa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa mai zafi kafin ya futo Sai zuba kamshi baths dinshi yake, gajeran wandonshi ya saka kamar koda yaushe  kafin ya  zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin, benne farko ya fara sauko wa ganin ko’ina dim ya sashi sauka kasa, nanba dai dim dim babu hasken kirki saina censor light din daua tsaya a wajen, fucewa yayi daga gidan ya wuce massallacin dake cikin estate din, masllacinma haduwanshi ma yakai a fada, ko’ina kamshi da sanyin ac ya gama bade cikin massalaci tsaf tsaf very clean, very few mutane ne a cikin masallacin hakan yasa Ana idar da sallah mutane suka soma ficewa, zama yayi saida yayi azkar Sai wajen karfe bakwai ya fito daga masallacin, direct gidanshi ya wuce Nadine dake goge goge tana gani shi ta rissina tace “good morning sir”

Daga mata kai kawai yayi ya wuce sama direct dakinshi, jallabiya shi kawai ya tube ya fuce daga dakin, second floor ya sauka ya wuce Dayan dakin dake gefe inda yake gyming dinshi don baya sake da physical health dinshi, ya dauka kusan awa daya da rabi kusan karfe 8:30,futowa yayi ya wuce sama ba tareda kallo side din Dayan dakinba da yake kyautata satin anan take kwana, wanka ya shiga nan ma saida ya shafe kusan 30mins ya fito, shirinsa yayi kamar na jiya saidai na yau din yafi na jiya kyau, yauma wa don army ne a jiki shi hade da rigarsa saidai ya daura had dadi yar jacket dinshi a sama, briefcase dinshi ya jawo tare da wayanshi ya sauko Kasa Sai baza kamshi yake, yana sauko wa Nadine na futowa daga cikin kitchen, da sauri tace “ breakfast is ready sir”

Baibi ta kanta ba ya wuce dining tayi serving dinshi chips da beef sauce da soyayyan plantain, da coffee, kadan ya tsakura yaci kafin ya kira driver yazo, kika mashi briefcase dinshi yayi yace “get the car ready now”

A Gurguje ya gama shan coffee din ya fuce daga gidan, gaba daya, Nadine na ganin fitar shi ta tattara dining din ta deba na amra ta wuce sama don kai mata nata.

Lokaci data shiga dakin babu kowa a ciki, jin alamun saukan ruwa ya tabbatar mata tana wanka, Ajiye tray din abunci tayi gefen ottoman din dake hade da gadon kafin juya ta rufe mata kofar dakin, futowa amra tayi daure da towel dinta, gaba daya fuskanta ya dan kumbura alamun damuwa da kukan da take,ganin tray agefe ya tabbatar mata da nadine ce ta aje mata, agurguje ta shirya cikin kayan zaman gida masu kyau, doguwan rigace mai Dan hannu,kayan ya amsheta sosai, zama tayi ta tsakuri abunci ta soma ci badon ranta naso ba saidan yunwa dake nuqurqusar ta, wayanta ta jawo ta soma kiran haifa saidai kwata kwata wayan baya shiga, gaba daya ta rasa abunyi, babu irin tunanin da batayi ba, da farko ta yanke shawarar gudu kano saidai kuma bata san daga inda zata fara ba ga tsoron abunda zata tarar achan, saidai kuma tunanin qannenta ya bata karfin gwaiwar komawa don sanin halin da suke ciki gashi ba wani kudin kirki yake dashi ba gashi batama kawo zancen ragowar kudinda yake dashi cikin account dinta na chan ba don indai anyi banning dinta daga shiga kasar account dinta shima dole za ayi banning.

Tagumi ta doka don gaba na daya abun duniya ya isheta.

Wunin ranar kamar kullum a daki tayi shi bata leko koda parlor ba haka zalika nadine ma batace mata komai ba akan zuwan shi.

Karfe goma sha daya ya shugo gidan, nadine ce ta bude mashi tare da mashi barka da zuwa, baibi ga kanta ba ya wuce sama, saida ta tabbatar ya huta kafin ta Kwankwasa mashi

Kofa, tana shugowa tace “ what would you like to have sir”

“ just coffee”

Ya amsa mata,

Futa tayi ta Hado mashi coffee din kafin ta fuce, coffee din yasha kafin ya wanke bakinshi kafin ya fito yabi lafiyan gado don yasha aiki sosai.

Washe gari Ma haka ya Tashi da wuri ya fuce bai Ma tsaya yin breakfast ba, don ya samu Kiran gaggawa daga wajen asad inda yake shaida mashi sun samu clue akan wani member na empire saidai tracing dinshi ne ya basu wahala sosai don sun Kasa samun hanyar da zasu Farke mashi, sunma Kasa gane waye saidai ta wani account da akayi transacting wasu kudade in dollars wanda yanda suka gano hakan shine sun bibiyi account din suspect din da aka kama achan uae tana suka gane inda yake transacting kudin,bai samu dawowa da wuri ba Sai wajen karfe sha daya.

Washe gari kam bai Tashi da wuri ba Sai wajen karfe sha daya, wanka kawai yayi don weekends ne bashida plans din futa, sitting room ya sauko ya zauna bayan ya gama karin kumallo, wayanshi ne rike hannunshi yana receiving wasu calls masu amfani, yana gamawa ya danyi jin yanason kiran ammah ya shaida mata yana Nigeria saidai kuma yasan zata fara expecting dinshi shikuma bayason zuwa gidan saiya gama Ayyukan da yake, bayaga wannan bayason taji ya na nigeria a wani wajen, dialing number yayi, tana picking kuwa suna gaisuwa ta soma tambayanshi yaushe zai zo Nigeria ta matsu ta ganshi, 

“Ammah zanzo very soon Insha Allah”

“ babana, na Kasa gane dalilinka na qin zuwa kasarka inda aka haifeka,”

“Ammah please calm down shikenan zanzo next week Insha Allah”

Sanin baya mata magana biyu ya sata saurin cewa “da gaske son”

“In sha Allah ammah”

“Alhamdulillah Allah ya kawo ka lpy, yarannan ma are so excited to see you”

“Uhm suna zuwa school din kuwa”

“Sun fara zuwa fah, saidai Muhammad baka min bayani ba yanda Zan fahimta,”

“Amma ki bari idan nazo Zan maki bayani dallah dallah”

“Toh Allah ya kawo ka lpy”

Sallama sukayi kafin ya kashe wayan ya fuskanci katuwar tv dake aiki babu sauti sosai

Bude kofar dakin tayi ta fito, sanye take da doguwar rigar abaya sky blue tasha stones,fuskanta fayau babu walwala, idanunta sunyi ciki ciki da alamu ta danyi kukan da ta saba ne,babu komai a kanta Sai ribbom data nade jelar gashinta dashi duban parlorn ta soma yi kafin ta wuce stairs cikin nutsuwa kanta a Kasa take takawa harta kai karshe stairs din, bata tsaya dube dube ba ta gifta parlor da yake zaune ta wuce kitchen direct,alamun saukowanta hade da takun ta cikin natsuwa ya ankarar dashi,zuba mata kyawawan idanunshi yayi har ta shige kitchen, yana nan zaune idanuwanshi kan hanyar kitchen din ta fito hannunta dauke da bottle water mai sanyi tasha kusan rabi hannunta dafe a goshinta,harta sanya kafarta kan stairs ta tsaya chak, wasi wasi ne ya shiga ranta na kamshin sa dataji lokaci guda ya shiga hancinta, kalle kallen hanyar shugowa ta soma yi har lokaci. Idanunta bai sauka ga sitting room din da yake zaune ba runtse idanunta tayi ta bude jin jira na neman Zubar da ita lokacin da idanunta suka Sarqe cikin nashi, kamar a mafarki take ganin komai, rufe idanunta tayi ta sake budewa akansu, Har lokacin shima idanunshi nakanta, kafin ya kauda kanshi gefe kamar bai ganta ba, kafafunta ne suka Gaza daukanta saida ta dafe handle din stairs din,miqewa yayi ya soma takowa, Duk takun shi daya jinshi take a kirjinta, saida yazo dan da ita hannunshi sanye cikin aljihun Riga da gajeran wandon dake jikinshi ya zuba mata idanunshi kamar zai cinyeta, Kasa dauke nata

idanuwan tayi daga kanshi itama Sai wasu siraran hawaye da suka soma ambaliya a fuskanta, baya ta soma yi kamar zata fadi hannu daya yasa ya tsaidata ta hanyar janyo nata, fuskanshi babu alamun annuri akanta, kallonta yayi tsaf kafin ya kauda kanshi gefe hade da tabe bakinshi ya gifta gefenta ya wuce sama, haka kawai taji kamar kallon tsana yake mata tsabar ta rude,ganin yana neman kauracema ganin ta yasa ta saurin bin bayanshi lokacin harya wuce daki, ya rufe kofa, tana karasawa gaban dakin batayi wata wata ba ta bude kofar dakin ta shige, lokacin har yakai bakin gado jin alamun an bude kofa yasashi juyowa ya kalleta kafin ya kauda idanunshi daga kanta 

Bakinta take motsawa alamun don furta abu saidai ta rasa da wani kalamai zata tunkareshi, tsinkayar daddadar muryarta yayi a kunnenshi “I’m so sorry” ta fashe da kuka sosai mai sanya ya zuciya, runtse idanu yayi don baya Kaunar jin kuka kwata kwata 

Bai kula ta ba saida ta tako Har gabanshi ta sake maimaita kalaminta hawaye na zubowa daga kan fuskanta “ I’m so sorry”

“ what are you sorry for”

Ya mata tambayar babu alamun fara a a tattare dashi,

Kasa cewa komai tayi saima wasa da yatsunta da take kanta a Kasa, Kasa hada idanu tayi dashi, sarai yasan daman zatayi blaming kanta tunda bata samu bayanin komai a wanda ya haba m5 fada mata sbd Bayason kowa yasan plan dinsu don haka ya gyara tsayuwanshi don yagane taqamaiman abunda ke ranta

“Get out of my room”

Ya fada Adan zafafe 

Saurin dago rinannun idanunta tayi, tama rasa abunda ke mata dadi, cikin Rudu tace “it’s my fault, Duk laifina ne, nina nemi taimakon ka badan ka taimake ni ba bazan jefaka cikin wannan halin ba”

“I’m so sorry, I’m so sorry, da na san wannan kaddararren auren zai jawo Ma kowa matsala da ban nemi yin shi ba me zanyi don ka yafemin dan Allah ,”

Zuba mata idanunshi yayi yana karantarta sosai

Tamke fuskanshi ya sake yace “I don’t want to repeat my self get out of my room now”

Yana kaiwa nan ya wuce toilet, kafafunta ne suka soma sare mata don gaba daya tunaninta ya tsaya chak, ya tabbata kenan, ya rasa aikinshi ta dalilinta innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta a tsorace, 

General kuwa yana shiga toilet yadan saki murmushin gefen bakin kafin ya tsuke fuska yana jin yanda take sauke ajjiyan zuciya da sauri da sauri da alamun kuma ta da yake tsananta, saurin bude kofar yayi Ay kuwa Harda dan gudunta ta fuce daga dakin ya bita da mayun idanunshi ahankali ya furta “ cute” tare da dan murmushin da bai san yana yinshi bama.

Amra kuwa tana futa daga dakinshi Kasa ta wuce dakin da take kwana, ta kwanta kan gado hawaye nabin kuncin,gaba daya tsanarta take hango wa a cikin idanunshi, runtse idanunta tayi wani irin zazzabi na zuwan mata.

Tana nan kwancewa galabaice aka kira sallar azahar, muke wa tayi ta wuce toilet ta dauro alwala ta fito ta tada sallah tana idarwa ta miqa kukanta gurin Allah. Tana shafawa ta fito tama rasa abunda zatayi, parlor ta sauko ganin Nadine na jera abunci ya sata tsayawa gefe guda, sosai Nadine tayi mamakin saukowanta don haka tace “Ma kina buqatan wani abu ne”?

“No thank you”

Rasa abun cewa tayi don haka ta hau sama, cire hijab dinta ta fara yi kafin ta zaune gefen gado ta doka uban tagumi. Tana nan zaune Nadine ta shugo dakin tace “Ma na gama lunch akawo abinci yanxu Ko zakici a kasa”

Da sauri amra tace “barshi zanzo kasan”

Nadine na fita kuwa ta mike zumbur ta sauko kasa don dama neman damar sauka take, tana sauka kuwa ta zauna a dining Nadine tayi serving dinta, raraba idanuwa tayi tana kallon stairs saidai ganin babu alamun saukowanshi yasa ta maida hankalinta kan abunci dake gabanta don ko cokali daya bata kai baki ta ba,

Haka nan ta dunga tura abuncin badon tanaso ba don daci Ma abuncin yake mata, tana gamawa ta wuce parlor ta zauna idanunta kan stairs din shuru shuru saida aka kira sallah asr ta mike ta wuce sama.

Amar kuwa tun bayan fitar ta ya chanza kaya ya fuce daga gidan sai wajen karfe 10 ya dawo gidan yana shigowa yazo giftawa ta sitting room ya hangota shingide kanta yadan karka ce alamun barci ya kwashe ta a wajen, kauda kanshi yayi ya kalli Nadine data bude mashi kofa yace “ wake her up taje ta kwanta, and bring me just coffee”

Yana kaiwa nan ya wuce sama, amra dake jin maganganunshi da Nadine sama sama cikin bacci, Tashi ta nadine ta soma yi tace “Ma kije ki kwanta”

Cikin bacci amra tace “ya dawo ne?”

“Yes ma”

Shuru amra tayi takaici barcin daya kwasheta ne ya turniketa donta dade a zaune tana jiran zuwanshi, bata gama tunanin nata ba nadine ta fito hannunta dauke da mug da saucer, ganin tana nufa hanyar stairs yasa amra saurin cewa “ya buqaci coffee ne”

Kallonta Nadine tayi tace “eh”

Takowa amra tayi gabanta tace “kawo Zan kai mashi”

Mika mata nadine tayi kafin ta mata sallama ya wuce nata dakin, saita natsuwarta tayi kafin ta tunkari hanyar sitting room din saman, Sai a lokacin ta karema parlor saman kallo, kayan alatun parlor yafi na kasa kyau sosai, gashi da girma sosai, an kawata shi da kayan zamani masu tsada, hanyar dazai sadaka da

dakin tabi saidai tana zuwa daidai kofar gabanta ya soma faduwa, runtse idanunta tayi tare da cije lebbanta ta kwankwasa, saida ya dauka mintuna kusan biyar kafin yace “yea come in”

Anatse ta soma bude kofar harta wangale ta shugo tare da rufe kofar ta tsaya daga bakin kofar kamar mai neman gafara tunda ta dago ta mashi kallo daya yana sanye da kayan barcinsa masu santsi, Riga da wando, wandon Ma bai Halle boturanba dan tana hango kwantaccen gashin kirjinsa, jin shuru yasashi dagowa, karar idanunshi suka sauka akanta, sanye take da kayan daya ganta da gamma dog uwar Riga saidai yanxu ta saka hula ta nade gashin nata saidai yana iya hango edges din sumar gaban gashinta, kauda idanunshi yayi gefe ba tareda ya sake kallonta ba ya tsuke fuska tam ya zauna kan gado ya wulla mata idanunshi da take jinsu suna yawo a jikinta.

Dagowa tayi charaf idanunta suka sauka a nashi, da sauri ta janye nata, yanda ya tsura mata idanu ya sata jin tsayuwar na neman gagarar ta, dakyar ta tartaro sauran jarumtarta ta soma magana cikin sanyi “uhm, ga coffee din”

Jin Shuru yasata dago kanta saidai this time around idanunshi a lumshe suke ya nade hannayenshi a kirjinsa, ganin yana shirin dago nasa idanuwan yasata saurin sauke nata kasa 

“Nace maki Ina buqatar wani abu daga wajen Ki ne?”

Da sauri ta dago jin tambayar da yayi mata, idanunta ne ya soma taro ruwa

Bakinta na karkarwa tace “daa…man..naga zata kawo ne shine Nace ta bani na kaw…..” 

wani irin mugun kallo ya Willa mata tare da tarar nunfashinta yace 

“Bana buqatan abu daga wajenki, now get out with that trash”

Ya karashe yana nuna mata coffee dake hannunta

Hawayen ta dai basu daina ambaliya ba haka zalika bata fitanba saida ya daka mata tsawa arude Har tana harde kafafu ta fuce, tare da rufo mashi kofar, kukane sosai ya kufce mata, ta rasa wani tunani zatayi, ganin batada wani mafita yasa ta wuce kitchen, aje coffee din tayi ta sulale kasan tiles din ta fara kuka sosai mai ratsa zuciya 

Goga kuwa tana

5 / 94