ya fada ba tareda ya wani damu da abunda amar ke fadaba
Nunfasawa amar yayi kafin yace ‘’do your worst’’ yana kaiwa nan ya kashe wayan, zuciyanshi zafi take mshi sosai, bai taba tunanin idan har yayi confronting hammam abunzai mashi zafi haka ba, ko lokacin daya gano komai game da sa hannun hammam wajen rufe duk wani hanyar samun evidence na kama kungiyar ba saidai yasan cewa akwai mastermind behind hammam din shima yana kyauta zaton manipulating dinshi akeyi wanda dalilin hakan yasa baita ba nuna mashi ya san komai ba don tun lokacin da yaje wani secret operation tare da m5 don kamo su ya gano cewa da hannun hammam.
Washe gari kuwa sakon gaggawa ya iso mashi wanda ya katse masu training din da ya kamata su gama cikin kwana hudu, koda helicopter ya iso daukan gaba daya freshers hardashi yayi mamakin ganin yanda security dinshi ya karu sosai, saiya zamana kamar criminal akazo dauka, bai kawo komai a ranshi ba don yasa ko baibada umarni ba dole yana da nashi security din, suna isa headquarters kuwa ya wuce direct inda ake emergency meeting security dinshi biye dashi a baya, tunda aka bude kofan shiga ya shige ba tare a wani tunani bay a zaune a kujeran dake tsakiyan wajen, daman yayi expecting hakan, saida ya sara masu don manyanshi ne sosai kafin ya zauna.
Wani solder ne ya matso ya aje mashi wasu papers a gabanshi kafin ya koma ya tsaya kyam,
‘’General Muhammad Taura’’
‘’yes sir’’yayi saurin amsawa
‘’mun samu labarin kana da sa hannu cikin illegal auren da kasan government din uae sun haramta hakan, wanda we believe kasan cewa hakan is not accepted a nan kasar, wannan gaskiya ne’’
Kallon papers din gabanshi yayi ya som karantawa tsaf kafin ya dago yace ‘’yes sir’’
Daga daga cikin manyan ne su uku yace ‘’did you know the consequences of that’’
‘’yes sir’’ ya amsa babu tsror babu fargaba
‘’did you know that this will affect your job with no plead’’
‘’yes sir ya sake amsawa
‘’did you know that this will ban you and your citizenship of the uae’’
‘’yes sir ya kuma amsawa
Shuru wajen ya dauka kafin su cigaba
‘’we hearby declare you under suspension of favourable personnel action, youll be under our supervision for more investigation’’
Mikewa duk sukayi kafin ya sara masu suka fuce, kanshi ne ya soma sara mashi don baiyi tunanin abunzai kaiga haka ba idanunshi kuwa sunyi jaa sosai, sanin abunda suke nufi ya sashi wucewa securities din biye dashi har wajen da floor din da ake investigation daki ne babba wanda shi kadai ne a floor din an zagaye dakin da sound proof glass, saida aka amshi riganshi dake da rank dinsa a jiki ya zamana daga inner white riganshi sai dogon wandon army nashi hatta wayoyin duk sun amshe, zama yayi kan kujeran dake dauke da table din kafin ya dafe kanshi dake sara mashi, bayason tunanin komai hakan yasa ya dafe kanshi don samun sauqin ciwon kan dake damunshi sosai.
M5 ne ya shigo dakin tare da sara ma ogan nashi, dago rinannun idanunshi yayi ya kalli m5 kafin ya gayar zamashi ya fuskanceshi ‘’have you done it’’
Da sauri m5 yace ‘’yes sir everthing is ready, and im sure she has arrived by now’’
Resting bayanshi yayi kafin ya cigaba ‘’in 2 days I will ban from the uae government, just as we planned, I have prep all the evidence through secretive portal,nayi linking dinka to the portal, don’t take any action until you receive my alarm’’
Kamewa m5 yayi kafin yace ‘’yes sir’’ ya sara mashi ya fuce.
Tun baya fitar m5 babu abunda ke mikar dashi sai sallah da zuwa toilet a cikin dakin, koda aka kawo mashi abunci baima bi takan abuncin ba.
Bari mu leka amra…
Tun bayan tashin datayi da asuba ta tashi da fargaba, jikinta gaba daya yayi weak tana jin alamun kamar wani mummunan abu zai faru, wanka tayi hade da sallah kafin ta zauna nan kan sallaya hawaye na zubo mata don idan taji irin wannan halin tana alaqanta shi da qila wani mummunan abu ne ya faru da kannenta, wunin ranar tayi shi ne cikin sanyin jiki hade da ciwon kai mai tsanani karfe bakwai na dare taji karar door bell, mamaki ne ya kamata sosai hade da tsoron daya dirar mata babu zato ba tsammani, miqewa tayi sanye da hijab dinta har kasa ta wuce parlor, jin an sake danna door bell din ya sata saurin budewa, ganin m5 yasata mamakin zuwanshi a daidai wannan lokacin, babu wani bata lokaci ya gaisheta kafin ya mata bayani tafiyanta ‘’maam, you will have to leave the country now’’
Hankalinta ne ya sake tashi dan ta kasa gane me yake nufi dakewa tayi kafin tace ‘’may I know why’’
‘’in 24hour you’ll be arrested for trying to get uae citizenship’’
Hankali a tashe ta kalleshi tace ‘’whatt, please explain to me the way I can understand kamin bayani yanda zan gane?,’’
‘’we don’t have time now, ma’am, your flight is in 30 minutes,’’
Juyawa tayi hankali a tashe ta koma dakin, hawayene ya soma gangaro mata a fuskanta wanda ta kasa gane dalili, meke shirin faruwa Kenan, bude closet tayi ta dauka bakin abaya ta saka kafin ta janyo karamin box dinta tayi ta zuba few kayanta a ciki kafin ta janyo laptop dinta da wayanta, fitowa tayi yanda tabarshi anan ta sameshi tsaye bakin kofar, karban box din nata yayi kafin ya rufe kofa tabi bayanshi, cikin motar yasa mata box dinta kafin ya bude mata ta shiga shima ya shiga suka wuce, abubuwa ne da dama ke yawo a kanta ciki kuwa harda general da makamin karatunta, kukane ya kufce mata mara dalili, wannan wace irin kaddara ce, ta kasa gane inda aka samu matsala, general ne ya fado mata rai yanxu shi wani hali zai shiga kenan, inhar ita kamata za ayi shi kuma aikinsa fa shida yake babban mutun a kasar kuka ne ya kufce mata hankali tashe ta kalli m5 tace ‘’uhm please whats going to happen to him, dan allah ka fada min meke faruwa’’
Cikin airport din yayi parking kafin ya zaro mata wasu takaddu ya bata hade da passport dinta ganin yanda take kuka ya sashi cewa ‘’karki damu, he will be fine,ga passport dinky, ive made an arrangement, akwai motar dazai daukeki idan kun isa, sir will join you soon’’
Innalillahi ta soma furtawa, dakyar m5 ya tausasa ta ya mata sauran abubuwan daya dace ya mata sallama ya tafi.
Samun waje tayi a airport din, nan komai ya dawo mata kamar mafarki, tundaga lokacin data iso kasar, allah kadai yasan irin farin cikin da take ciki sai gashi yanxu kuma zata koma kamar mafarki take ganin komai, yanxu ya makomar karatun nata Kenan, me zata cema daddy idan ta koma, mai zata tarar idan taje chan, runtse idanunwata tayi hawaye na kwaranyo mata, gaba daya baifi mata wata uku ta gama housemanship din shima sbd extention data nema ne anan asubiti na haousemanship da takeyi na additional 3 months don ta don samu ta tara kudin da zata biya daddy bayan wannan ma gashi kuma yanxu komai ya juya, cikin yan mintuna akayi announcing jirginsu, mikewa tayi hawaye sharr a fuskanta harta wuce harabar jirgin, koda suka tashi tunani iri iri ne a ranta, yanxu makomar karatunta ma bashine damuwanta ba, sir general ne damuwanta, wani hali ta jefa shi, da career shi, idan har ita arresting dinta za ayi shi kuma fah, a wani hali yake ciki, koma wani hali yake ciki ita ta jefa shi tunda itace ta nemi taimakonshi daya ya aureta dukda sunsan illegal ne a kasar, idanunta ne sukayi jaa sosai, anya ta kyauta kuwa, tanajin kamar tayi butulci, tambayoyi ne burjik a kanta wanda ta rasa wanda zai amsa mata su, na farko ya akayi m5 yasan za ayi arresting dinta, ya akayi asirinsu ya tonu, sannan a wani
hali yake ciki yanxu ganin babu mai bata amsosahin ta yasata fashewa da matsanancin kuka sosai har baccin wahala ya dauketa.
Sama sama ta dunga jin Magana akanta, bude rinannun idanuwanta tayi da sukayi jaa sosai kafin saukesu akan crew din dake tashinta, ‘’ma, weve arrived’’
Juyawa tayi ganin bbu kowa cikin flight din har garin ya waye yasata mikewa ta janyo karamin box dinta hade da laptop bag dinta da wayanta, takowa tayi ahankali tare da shaker kamshin kasar najeria, nan take komai ya sake dawo mata, runtse idanunta tayi kafin ta soma takawa gabanta na mugun bugu sosai harta futa daga harabar jirgin,saida ta tsaya ta gama clearing komai don daman daga dubai to Abuja ne booking din da m5 yyi mata,duban wayanta tayi da charge ya sauka kasa, rasa abunyi tayi don babu kudi kwata kwata a jikinta gashi booking daya ne daga dubai to Abuja, gashi bata taba zuwa Abuja ba balle tasan inda zatabi taje car park, futowa tayi daga cikin airport din inda taxis da motoci suke dagowa tayi nan idanunta suka sauka kan wani mutumi daya daga katon board da sunanta a jiki, tunawa da abunda m5 ya fada mata na cewa yayi making arrangement dinda zai kaita gida yasa tayi handala ta daga hannunta da sauri mutumin ya karaso gabanta tare da welcoming dinta, karban box dinta yayi kafin tabi bayanshi, idanunta a kasa yace ‘’bismillah hajiya’’
Dagowa tayi ganin zabgegeiyar motar dake gabanta, ba tareda wani tunani ba ta shiga baya yaja motar suka wuce.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 106
Update…..
Tun akan hanya driver ya isheta da surutun da ba gane kan zancen nashi take ba iyakacin ta uhm sai kuma murmushi, sam hankalinta baya jikinta karhse ma dai lumshe Idanunta tayi don wani irin ciwon kaine ke damunta sosai, tunda suka karyo kwanan layin ta bude idanuwanta, fadin tsaruwan anguwan ma bata lokaci ne don daga gani kasan anguwar manya ce bata kananu ba,ko ina fess fess babu hayaniya sai kamshi ciyayu da sukayi tsayi, idanunta ta soma rarrabawa har suka karaso wani hadadden estates mai suna LARICS ESTATE qasan kuma aka rubuta TAURA COM, jerin securities dake wajen ma abun kallo ne, bayan fargabar da take ciki saida tsoro ya durar mata ganin yanda wajen yake da tight security, babu bata lokaci driver ya fidda wani kati da
alamu na company ne kafin suka bude gate din, yana kutsa kai kuwa komai ya dauke mata lokaci guda, ita data dawo daga kasar waje saita zama yar kallo, gidaje ne da aqalla bazai wuce guda goma ba don estate din bashida wani girma, idanunta ta sauke kan gidan da yake tunkara wanda ya gaji da haduwa tundaga waje, don yafi duk sauran gidajen dake cikin estate din, don shi kanshi gidan ma daga kan titin estate din kake hangoshi don yana da girma da tsayi, daidai gaban gate din din ya kara horn, wani armed security ne ya fito, ganin plate number motar yasa shi juyawa ya danna remote control din gate din ya zuge da kanshi, tunda suka shiga tsakiyan compound din ta wangale bakinta don saita rantse ma ba a Nigeria take ba, daga waje ashe gidan ba komi bane saida aka shigo, parking driver yayi daidai inda motoci kusan guda uku suke a jere an rufe su da car cover, fitowa driver yayi da sauri ya bude booth ya fiddo da akawatinta kafin yayi saurin zagayowa ya bude mata kofar bayan, rarraba idanunwata ta soma yi kafin yace ‘’welcome ma,’’
Idanuwa kawai take zuba mashi don ta zama kamar kurma, babu abunda take buqata sai bayanin ina ne nan aka kawota, jagora yayi mata zuwa main entrance din gidan kafin ya danna door bell din, babu wani bata lokaci wata mata ta bude kofar tare da saurin yin baya tace ‘’sannu da zuwa ma’’
Saurin mikawa wanda tayi Magana akwatin drivern yayi kafin ya juya ya kama gabanshi, murmushi yake kawai amra tayi don komai y agama kulle mata,
‘’bismillah!!’’ matar ta fada yayinda ta shige da akwatinta ciki, da bismillah amra ta sanya kafafunta cikin gidan, don tsoron shigama take, tunda kan walk way ta soma yaba irin tsarin gidan, gidan ya kawatu da luxurious kayan alatu, ganin inda matar ta bi ya sanya ita bin hanyar ta, duk inda ta taka sai haske wajen ya bayyanu da alamu wutar gidan ma censor ne, cikin parlor ta sanya kafafunta wanda tana shiga wani irin sanyi da kamshi ya buget lokaci guda, fadin tsaruwan parlor kanshi bata lokaci ne don ya hadu ba kadan bag aba daya tsarin kasar waje ne a cikin gida, nuna mata wajen zama matar tayi kafin a tsorace ta dake ta zauna kan hadaddun kujeran kafin matar tace ‘’ina wuni ma ya hanya’’ fuskanta dauke da murmushi ‘’lpy alhamdullah thank you’’
Juyawa matar tayi kafin ta mike wata hanya ta shige kitchen, fitowa tayi hannunta dauke da katon tray na kayan marmari da juice mai sanyi, tunda matar ta fuce amra bata dago ba harta dawo, duk ta gama takurewa, so take taga mutanen gidan saidai bataga kowa sai wannan matar dake kiranta da ma
Aje tray din matar tayi a gabanta kafin tace ‘’bismillah ma’’
Kallonta amra tayi tace ‘’no thanks, dan allah ina mutanen gidan’’
Shuru matar tayi don itama mamaki take da tambayar amra din don gaba daya kwananta daya a cikin gidan don hiring dinta akayi daga wani company dake kawo house keeper koda aka daukota bayanin da aka mata shine zata dunga kula da gidan har madam dinta ta karaso daga kasar waje,
‘’ma, ni kadaice a gidan, an daukoni ne don nayi house keeping gidan’’
Kasa tantance maganar matar amra tayi saidai tayi shuru kawai, maganar matar ne ya katse mata tunanin data tsunduma a ciki
‘’kina buqatan wani abu ne ko zaki fara hutawa?’’
‘’please ko zaki nunamin bathroom’’
‘’okay ma’’
Mikewa amra tayi ta fara bin matar har suka bi hanyar da zai sadaka da stairs, staircase dinma kanshi abun kallo ne, har wani curvy yayi gashi yasha carpet mai kyau, gidan is so cozy, bin bayar matar tayi har suka hau benen farko wanda keda dakuna biyu manya manya da parlor hanyar parlor sukabi kafin matar ta bude dakin dake facing parlor, tunda suka shiga ta soma raba idanuwa, dakin yasha kayan alatu, gado ne royal Turkish bed mai kyau yasha gyara da zanin gado wanda daga gani kasan na masu kudi ne, an jere dakin da pillows masu kyau, sai tsakiyan an kawata shi da carpet mai laushi gefe guda kuma wardrop din gadonne shima babba wanda ya shanye gabada wall din wajen, matsawa gefe matar tayi kafin tace ‘’ga toilet nan ma’’ ta fada tare da nuna mata wata kofa daga gefe chan, shigewa amra tayi ciki kafin matar ta rufo mata kofar ta fuce, takowa amra tayi ta aje jakanta da wayanta akan gadon kafin ta soma nannade mayafin abayan dake jikinta don ji take kamar shaketa yake, hanyar bathroom din da matar ta nuna mata tabi, koda ta shiga nanma toilet din ya gaji da haduwa, saida ta fara rage mararta kafin ta dauro alwala ta fito don sai a lokacin ta tuna da sallolin da ake binta, futowa tayi lokacin matar ta bude kofar itama ta shugo hannunta duke da box din data aje mata a parlor, kauda kai gefe amra tayi kafin tace ‘’thank you, please ina buqatan sallaya’’
Da sauri matar tace ‘’okay ma’’
Takowa tayi ta bude slide wardrop din ta fiddo da sallaya katuwa ta ta shimfida mata, godiya amra tayi mata kafin ta fuce, mayafin abayrta ta dauka ta nade wuyanta dashi kafin ta tada sallah, koda ta idar ta dade sosai kan sallaya tana addua akan lamuranta, ciki kuwa harda general da bata san a wani hali yake ciki ba saidai tana jin zafi don duk wani hali yake ciki a yanxu itace ta jefashi, wannan kadai idan ta tuna yake sata kuka sosai, ta dade akan sallaya kafin ta miqe ta raqube a gefe guda ta zauna ta doka uban tagumi.
Tana nan ta janyo wayarta, tama rasa me zatayi sai hawaye, tana nan zaune akayi knocking kofar, dagowa tayi ta bada izini aka shigo, matar dazun ce sanye da uniform din aiki, ktakowa tayi kafin tadan rissina tace ‘’me food is ready, ko akawo maki nan’’
Shuru amra tayi don yanda matar dai a grime ta girmeta amma sai rissina mata take yasa taji babu dadi tace ‘’nagode zan sauko naci’’
Juyawa matar tayi ta rufe mata kofa kafar.
Koda ta kasa kanta ne ya rabu gida biyu don bata gane inane hanyar dining dinba, saida matar ta fito ta jagorance ta har dining din shima dai ba a Magana, zama tayi idanunta kan jerin warmers din, da sauri matar ta soma bude warmer din tace ‘’wanne za ah saka ma’’
Shuru amra tayi kafin ta dan dago fuskanta dauke da murmushi tace ‘’zaki iya saka ko wane ma’’
Murmushi itama matar tayi kafin ta zuba mata fried rice da tasha veggies da hanta sai shredded beef sauce a gefe, tana gama zuba mata ta aje mata spoon a gefe kafin ta janyo wani bowl din ta zuba mata green salad, tana gamawa ta janyo hadadden glass jug din da yasha apple juice ta zuba mata ta aje a gefe, kallon plate din amra tayi, abuncin yayi kyau a ido ga kamshin sa daya bade dining area din gaba daya saidai gaba daya damuwan dake cikin ranta yasa batada appetite gaba daya, dagowa tayi fuskanta dauke da murmushi tace ‘’thank you so much’’
Murmushi matar tayi matai tama don haka kawai taji amra ta shiga ranta sbd calmness dint aba kamar wasu madams din ba da kudi ke sasu jin kansu har suna wulaqanta wanda suke masu aiki,
‘’if you need anything ma, zaki iya kirana, sunana nadine’’
Girgiza mata kai amra tayi kafin matar ta juya zuwa kitchen ita