meke damunki? Nayi sensing abu na damunki, now tell me,meysa kika rame haka? Duk jikinki yayi sanyi”
Dan dagowa amra tayi tana dan qaqalo murmushi tace “babu komai anty Madina stress ne kawai na yawon asibiti, bayan wannan ma tashin hankalin da muka shiga na rashin lafiyar ammah kadai ma zaisa hakan”
Shuru Madina ta sakeyi tana nazari kafin ta dubi wayarta Ganin tana lattin zuwa aiki, “Zan dawo anjima da daddare Insha Allah zamuyi magana,”
“Toh anty madina allah ya kaimu” amra ta fada tana lumshe idanunta alamun gajiya da tsayuwan da sukayi, “ki koma kawai na hutar dake amaryar general”
Dan murmusawa Madina tayi kafin ta wuce parking lot amra kuma ta samu waje anan gefen reception ta zauna ta doka uban tagumi kamar wadda aka aikoma mutuwa, abubuwa da dama suna yawo a kwakwalwarta.
Cikin dakin ammah kuwa, Amar ne ya miqe ya kalli su salima da Aman yace “zan wuce gida yanxu, idan wani abu ya taso call me”
Aman ne ya kalleshi yace “okay, zaka wuce da sister inlaw ne?”
Hanyar kofa amar yabi kafin yace “no, bazan dade ba Zan dawo”
Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin ya nufi hanyar reception l, anatse yake tafiya kamar basarake Har ya kusa karasowa Inda take zaune ya doka uban tagumi ta fada duniyar tunani, Har ya kusa giftata ta dago tana shirin miqewa, kallo daya tayi mashi ta kauda kanta gefe, shikam
Bai dauke idanunshi akanta ba haka zalika bai tsaya ba ya wuce abun shi, itama tana Ganin haka ta juya ta nufi hanyarshi dakin ammah jiki a mace, da sallama ta shiga cikin dakin, kallonta Duk sukayi gaba dayansu kafin ta karaso Har cikin dakin ta zauna kan kujera ta dan jingina don gaba daya babu abunda ke mata dadi, Har akayi sallah zuhur Duk sukayi sallah bai dawo ba, Aman da Salim Har suka je masallaci suma suka dawo, suna dawowa salima ta zubama kowa abunci Banda amra wadda tace bata jin yunwa sai zuwa anjima, kallonta salima tayi tace “adda ko breakfast sun kirki fa bakiyi ba dazu? Ko baki jin dadi ne?”
Dago da jajayen idanunta tayi don ta sauke kanta kan gwiwanta tana jin wani irin ciwon kai sosai, anatse ya soma magana “kaina ke ciwo zanci anjima”
Salima naji haka ta kyale ta ta zauna gefen Aman dake zaune kan carpet ta fara cin abuncin da suka taho dashi din hankali kwance.
Har suka gama salima ta tattara amra bata dago ba kanta akasa.
Bangaren Amar yana komawa gida ya watsa ruwa ya kwanta don idan sunyi switching baya barci haka zai kwana a zaune yana yima ammah addua tare da fatan farfadowarta, sai wajen karfe uku da rabi ya Tashi daga barci, ba karamin dadin barcin yaji ba don wani irin mafarki yayi mai wuyar fasaara,dukda yajin dadin mafarki don Harda amra a ciki hakan bai hanashi tabe baki ba yayi tsaki ya wuce bathroom ya sake wani Sabon wanka kafin ya futo ya shirya cikin branded kananun kaya marasa nauyi, kamshinsa ne ke Tashi ta ko’ina harya fuce daga gidan ya kullo kofar.
Yana fitowa wayar asad na shugowa, kallon wayar yayi kamar bazai daga ba, Har ya shiga cikin motar ya fara warming dinta, nan take wani call din ya sake
shugowa, saurin daga wayar yayi tare da sallama,daga chan bangaren asad ya amsashi kafun ya soma mashi bayani, “oga mun kama doctor hafiz tun Daren jiya, naso
Na kira na maka bayani tun alokacin sai nayi tunanin hakan bai daceba saboda kana tare da Mara lafiya, jiya wajen karfe sha daya na dare kuka kamashi a nnamdi ezikiwe international airport yana kokarin gudu wa tare da iyalinshi, ayanxu haka yana cikin interrogation room ban fara interrogating dinshi ba na bari saika zo tukunna”
Shuru amar yayi yana wani nazari, tabbas ya kamata ace yana tsaye akan Duk wannan interrogation din don he needs to, saidai kuka bayajin zai iya barin ammah a yanxu inhar ba Ganin ta yayi ta farfado ba, ayanxu Duk mintuna da seconds da yake fiddau nunfashi a duniya yanada mugun amfani a wajen shi saboda ya girgiza sosai da abunda suka faru a cikin kwanakin, Nunfasawa yayi kafin ya danyi gyaran murya yace “asad, banida lokacin wannan ayanxu saboda inhar ba Ganin ammah nayi ta farfado ba bazan iya yin komai ba, kayi interrogating dinshi Duk wani abu da kasan zamu buqata, yanxu lokacina nayi dedicating dinshi to mahaifiyata ne, bazan taba samun natsuwar yin wani buncike ko interrogation, but inason Duk wani abu da kasan Zan buqaci sani Ka buncika, bazansake yin sake ba akan family na ba, this should be the last Insha Allahu”
“Okay yallabai ba matsala, zanyi kokarin rukesu for now sannan zanyi maka Duk wani buncike,”
Godiya amar yayi mashi kafin ya kashe wayar ya yo reversing motarshi ya fuce daga gidan gaba daya.
Tunda ya fara driving ya maida hankalinshi kan hanya, babu abunda ke Tashi a kofar sai karatun Qur’an na sudais, anatse yake driving harya iso asibitin, saida ya tsaye a masjid yayi sallahr asr kafin ya wuce cikin asibitin.
Da sallama ya bude kofar dakin, a zazzaune suke gaba dayansu, Aman na zaune kan carpet salima a gefenshi while Salim na zaune gefen gadon ammah, amra kuwa tana kwance akan doguwar kukerar tana barcin wahala anan zaune, kallo daya yayi masu duka ya sauke kanshi ya karaso cikin dakin, gaishesa salima tayi kafin ya tambayi jikin ammah, Aman ne ya amsashi, “doctor yazo dazu ya sake dubata, babu wani changes”
Shuru kawai amar yayi ya kafama ammah idanu, yana kallonta, aranshi yana cewa “”allah ya Baki lafiya ammah na, y kamata ki Tashi haka ammah na I miss you so so much,can’t imagine how I can survive without you,”
Saurin runtse idanunshi yayi ya kamo hannunta ya fike gam.
Suna nan zaune kowa jugum Jugum amra ta bude idanunta da sukayi jaa sosai, mikewa tayi zaune daga kwance ta tare da ta kalli bangarenshi ba ta mike tsaye kamar Ana ingizata, tafiya ta somayi harta shige bathroom, dan dagowa yayi ya kalleta yana tunani ko meke damunta, harta fito daga bandake daurw da alwala,
ruwan na diga daga fuskanta zuwa wuyanta don ta zame mayafin abayar datayi rolling don ji tayi kamar yana shaketa ta rike shi a hannu, gashinta ya sauko Har kafadunta yayi curly wanda ya karama fuskanta kyau sosai, sai asalin kyawu ta ya fito sosai kamar ba itaba,ta dan rame kadan tayi fayau,
Amar dake zaune ya zuba mata idanu harta fito daga bathroom din ya kasa dauke kanshi akanta,harta zo inda su salima ke zaune, Aman na gefenta Kowannen su da sake sake da yakeyi aranshi, kallonsu amra tayi tace “ya Aman kudan matsa min zanyi sallah”
Dan dagowa yayi ya mata kallo daya kafin ya dauke kanshi ya mike “okay sister inlaw”
Salima ma Mikewa tayi nan suka dan gwara da goshinsu don kusan a atare suka miqe, saurin kauda kai salima tayi tace “sorry”
Shima kallo daya yayi mata ya dauke ki gefe ya koma kujeran ya zauna, salima dai Kyam ta tsaya a gefe bata motsa ba tana tausayin kanta na dakon soyayyar shi, shida takeyima yanxu ya daina bata fuska ma kwata kwata.
Tunda amra ta tsaya gaban Aman yaji kirjinshi nayi wani irin bugu damm, runtse idanunshi yayi lokaci guda ranshi ya gama baci gaba daya sosai dalilin tsayuwar ta gaban Aman babu mayafi, kishi ne karara ke balbalal shi wanda baima san yanayi ba,babu abunda yake fada aranshi sai “bata da hankali ne zata futo daga bathroom kanta a bude, kuma ta tsaya gaban wani kato da ba muharraminta bane”
Yanda idanunshi ya karade yayi jaa sosai zaka gane ranshi ya mugun baci sosai, shi kanshi mamakin bacin ran nashi yakeyi saboda yasan dole bayan kishi Akwai so, tabbas yasan he’s jealous of her but so kam babu shi, bai taba jin ya sota ba saidai tausayinta ya fada aranshi, but daman Akwai kishi ne babu so? Ya tambayi kanshi,tsaki kawai yayi ya sha mur, juyowa su salima sukayi suka kalleshi Ganin yanda ya hade rai, da yanda yayi tsaki.
Amra dai bata ma san yana yi ba don tana idar da sallah ta jingina da bangon dakin, Har aka kira sallar magrib, gaba daya mazan futa sukayi suka wuce masjid while ita da salima sukayi sallah anan dakin ammah.
Karfe goma daidai ya mike tsaye yana kallon agogo, ganin haka yasa Aman cewa “zaka wuce ne?”
“Yes Zan dawo da safe” amar ya fada yana kallonshi kafun ya maida kallonshi ga amra babu wani wasa a fuskanshi yace “Tashi muje”
Bata dago ba don kwata kwata tunaninta baya wajen saida salima ta dan ta bota “adda ya Muhammad na magana”
Firgigi ta dawo hayyacinta ta dago zuba mashi mayun idanu nata da sukayi ciki ciki Ta kalleshi, bai sake maimaita abunda yace da farko ba ya bude kofa ya fuce daga dakin, salima ce ta kalleta tace “yace kuje wai”
Jiki a mace amra ta mike tsaye ta kalli Salim tace “muje Salim”
Kallonta salima tayi tace “zai tayani kwana kije kawai”
Badan taso ba haka ta nufi kofar ta fuce daga dakin jiki a mace donma tana buqatar komawa gidan ne don kwanciya anan wahala
Yake bata badan haka ba bazata bishi ba don gaba daya ya fita aranta dukda tana nan kan bakarta bazata taba rabuwa dashi ba, saidai haka kawai cikin kwanakin nan take saurin fushi da jin haushin sa da abubuwa ma gaba daya.
Ahanakli take tafiya harta zo bakin harabar asibitin wajen parking lot, Har tana shirin wucewa inda Aman yayi parking Tayi saurin tsayawa saboda horn dayayi mata, juyowa tayi gafe ta kura ma motar idanu, batayi tunanin da wata motar yazo ba don haka ta dan tsaya don tabbatar da shi dinne, saida ya sakeyi naga horn kafin ta fara takowa jiki a mace ta karaso ta bude gidan gaba ta zauna.
Tana shiga bata idasa rufe kofar ba ya figi motar, ta Lura da take takenshi don haka tayi banza dashi kamar batasan yanayi ba.
Tunda suka fara tafiya babu wanda yace Tak tsakanin su, shi gaba daya ya maida hankalinshi ga tukin da yake while ita kuma ta juyar da kanta gefe tana kallon hanyar,
Waigowa yayi ya mata kallo daya kafin ya kauda kanshi gefe ya cigaba da tukin.
A Daidai wani haddaden waje yayi parking don bazata ce ga ainahin sunan wajen ba, saidai tundaga wajen parking da ya aje motar tabi wajen da idanu, wajen ya hadu sosai don Duk manyan motoci ne a wajen.
Bai kashe motar ba ya bude ya fuce daga cikin motar, yana fita tabishi da idanu kafin ta kauda kanta gefe, zaman minti goma tayi sai gashi ya fito hannunshi rike da manya manyan ledoji guda biyu, harya shugo ya bude motar ya saka ledojin a bayan mota bata kalli inda yake ba, shima ya Lura da yanda take wani babbasarwa don haka ya kauda kanshi gefe kawai shima bai ce mata qala ba don haushinta yake ji sosai, ya kasa gane dalilin da yasa ma ya kasa mata magana akan dazu.
Reversing motar yayi ya fuce daga compound din wajen, anatse yake tukin cikin kwarewa, cikin Yan mintuna qalilan suka iso taura estate, horn yayi aka bude main gate kafin ya wuce apartment dinsu,nan ma sai dayayi horn securities suka bude kafin ya saka hancin motar wajen parking space dinshi.
Yana parking ya kashe motar ya dan saiga gefenta Ganin bata motsa ba, barcin ta take yi hankali kwance, baya Ganin fuskanta don haka bai tantance a wani yanayi take barcin ba,saida ya dauka about 10mins yana tunanin tashinta, don haka kawai ya tsinci kanshi da son barinta tayi barcin saboda yanda yake hidima da ammah gashi alamu sun nuna bata jin dadin jikin ta amma tana boyewa, shuru shuru saida suka dauke kusan awa guda, yayi relaxing kanshi a jikin kujeran inda yake zaune yana tunani wasu abubuwan.
Gyara zamanta ta yi saboda yanda kwanciyar datayi yasa jikinta ya fara mata ciwo, ahankali ta bude idanunta ta kalli gefen window kafin ta maido da kanta
gareshi, ya lumshe idanu kamar mai jin barci hankali kwance, lumshe idanun ta tayi ta kauda kanta gefe ta bude kofar motar ta fuce daga cikin motar,
Tunda ta farka yanajin motsin ta harta fuce daga cikin motar bai bude idanunshi ba sai da ya dauka kusan minti biyar kafin ya bude jajayen idanunshi ya futo daga motar ya bude gudan baya ya janyo ledojin ya rufe motar ya wuce mai entrance, lokacin daya bude kofar parlor ya shige harta hau sama abunta don haka ya karo kofar ya rufe ya wuce part dinshi da ledojin, anan parlor shi ya aje ledojin kafin ya wuce bedroom dinshi kai tsaye, yana shiga dakin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ta gajiya kafin ya soma rage kayan jikinshi, saida ya aje wayanshi a gefen bedside kafin ya wuce bathroom din ya watsoo ruwa ya fito daure da towel, bai tsaya shafa mai ba ya feshe jikinshi da turarukanshi masu sanyin kamshi kafin ya janyo pjs dinshi na cotton Riga da wando baqaqe, zama yayi bakin gadon shi ya janyo wayarshi ya soma latse latse, da message din asad ya fara cin karo, bai bude ba don yasan idan ya bude ma ranshi ne zai baci don haka ya kashe wayar ma baki daya ya aje ta a gefe ya mike cikin kamewa ya zura bedroom slippers dinshi ya fuce daga cikin bedroom din,anatse ya bude kofar da zai sadashi da parlorn shi, daga nesa ya dan tsaya ya karema ledojin daya ajiye na grilled fish daya sayo,fiddo da ledojin yayi gaba daya ya wuce dining ya ajiye kafin ya wuce sama, anatse yake tafiya kamar wani basarake harta zo daidai kofar ta, fuskan nan yasha mur babu fara’a harya danyi knocking kofar kafin ya sa kai ya shige ciki,yana shiga dakin tana fitowa daga bathroom daure da pink towel jikinta na digar ruwa tundaga kanta zuwa wuyanta, saurin kauda idanunshi yayi daga kanta ya danyi gyaran murya yace “Idan kin gama ki sakko kasa yanxun nan”
Yana kaiwa nan ya juya ba tare da ya sake kallonta ba ya fuce daga dakin, ita kuwa tunda ta fito ta ganshi tsaye batayi wani mamaki ba don ya saba shugowa babu excuse don haka bata wani damu ba a wani yanayi ya ganta don haka bayan ya fuce ta tabe baki tabi bayanshi ba tare da ta saka komi ba, haka ta sauko kasan anatse tana tafiya kamar dawisu Har wani kwarkwarsa takeyi ba tare da saninta ba Har ta karaso parlorn, tana shirin karasowa part dinshi ya katseta, “over here” ya fada anatse, juyowa tayi ta nufi inda tajiyo muryan nashi daga wajen dining, takowa tayi harta shugo dining din kanta a kasa ta tsaya qiqam a gaban dining din, tunda ta shigo ya kafa mata idanu ya kasa daukewa, harya dauka kusan minti biyu baice mata komai ba, itama bata ce mashi komai ba don bata son magana dashi yanxu kuma saidai hakan baisa taji zata ki amsa kiranshi ba Duk sanda ya nemeta, gajiya tayi da tsayuwar ta dago ta kalleshi shima ita yake kallon soma haka yayi saurin tattara natsuwarshi yace “come and serve me”
Kallon ledar gefenshi tayi kafin ta juya zuwa kitchen bata ce mashi qala ba, yayi mamaki sosai yanda take bashi wani silent treatment, haushi yaji sosai, who’s she da zata dunga bashi silent treatment tana qin bashi amsa idan yayi mata magana, kokarin danne zuciya shi yayi harta karaso dining din, Har lokacin
towel dinnan ne a jikinta haka zalika ruwan jikinta bai bushe ba yana bin lausassan fatar jikinta dake sheki babu gashi ko digo daya very soft, hannunta rike da plate da serving spoon sai spoon and fork da knife, ta karaso dining din ta tsaya daga gefenshi ta ajiye komai akan dining din kafin ta koma kitchen din, bin bayanta yayi da kallo harta wuce kitchen din ta fito hannunta dauke da bottle water da orange juice sai glass cup
a dayan hannunta, cikin natsuwa take komai harta iso Inda yake zaune ta aje mashi a gabanshi, ledojin data gani a gefe ta janyo ta soma budewa,ledar farko data bude grilles fish ne da yaji dankali dasu cabbage a ciki sai kamshi daya bade hancinta Har tana lumshe idanunta don dadi, yawunta ne ya dan tsinke kafin ta fara zuba mashi,saida ta zuba mashi yanda zai ishesa kafin ta tura mashi gabanshi ta juya zata wuce sama dukda ranta ya biya sosai,
Hannunshi ya daga biyu ya kame bakinshi yana kallon ikon Allah Har tazo fucewa daga dining din, “Aisha!!!” Ya Kira sunanta, chak ta tsaya ta kasa motsawa kwata kwata harta juyo ta fuskanceshi, “zo nan!!”
Ya sake fada yana kallonta hannunshi akan habar bakinshi, takowa ta soma yi jiki a mace ta tsaya nesa dashi batace mashi komai ba,
“Seat!!” Ya fada sounding commanding wanda abun ke bata mata rai sosai, bata musa mashi ba ta zauna gefen seat din da yake zaune, tana zama ya maida idanunshi ga abuncin dake gabanshi ya saka spoon ya soma ci hankali kwance, ta dauka kusan minti goma kanta a kasa tana jiran jin abunda zai ce mata daya dakatar da ita daga tafiya jin shuru baice mata qala ba ta dago ta kalleshi, ya maida hankali sosai ga abuncin da yake ci ahanakli kamar baya son ci, saida ya dago suka hada Ido ya kauda nashi gefe yace “lower your gaze”
Ba zat ba tsammani yaji amsarta “why? Haramunne don na kalli mijina? Why would I lower my gaze?”
Da mamaki ya dago ya mata kallo daya kafin ya dan murmusa ta gefen baki ya kauda kanshi daga gareta baice mata qala ba don da alamu ta zama mafadaciyar karfi da yaji,
Haka kamshin grilled fish dinnan ya cikata gashi baiyi mata tayi ba ga takaicin abunda yace mata don haka ta hade rai tamm kamar hadari, “are you waiting for me to