nashi, saida ya gama ta fara processing komai a kwakwalwarta, she can’t believe abunda kunnenta ke jiyo mata, hawayen ma neman qafe mata suka fara yi,kwata kwata ta kasa dago ido ta kallesu don wani irin kunyan hada idanu take dasu musamman amar.
Shuru ammah tayi tana nazarin bayanin nashi, bata ce qala ba ta kwala ma lantana kira, lantana na shugowa tace” ki kai baquwa sama ta huta”
Kallon amra ammah tayi tace “dear go and freshen up nasan jin kwaso gajiyan jirgi”
Tunda amma ta fara magana ta kasa dagowa kamar ruwa ya cita, gaba daya tunaninta yabar jikinta, Har saida lantana tace muje, kamar munafuka haka ta miqe tabi bayan lantana kamar Ana ingizata, don idan zaka tsaga zuciyata zaka ga yanda tayi laushi,har ta wuce ta gabanshi bai kalli gefenta ba.
Suna wucewa sama ammah ta kalleshi fuskanta babu wasa tace “go and freshen up and meet me in my room”
Tana kaiwa nan ta wuce sama zuwa dakinta,tabar nan zaune, jikinshi ne yayi sanyi don kwata kwata baiga alamun walwala a fuskan ammah ba dukda yayi mata bayanin da take nema, mikewa yayi jiki a mace ya bedroom dinshi, gaba daya haushin kansa yake ji,meysa bai sake ta tun da wuri? Maysa tun bayan daya gani she’s not pregnant bai saketa ba? Da tuni yanxu Duk haka bata faru ba, cire suit sun jikinshi yayi ya aje a bakin gado tare da wayanshi dake ta faman ruri tunda ya shigo gidan, yasan yan jarida ne don haka baima bi takansu ba, kayan jikin ya soma tube wa ya rage daga shi sai shorts kafin ya wuce bathroom don sakarma kanshi ruwa mai dumi,yana fitowa ya shirya cikin
jallabiya ya feshe jiki shi da turare kafin ya fuce zuwa masallaci don an kira sallar azahar.
Amra dai tunda lanatan ta shigar da ita guest room dake nan sama ta kasa sukuni, bin dakin tayi da kallo, dakine babba da yasha Turkish beddings, katon gado ne a tsakiyan dakin sai dressing mirror, dakin yayi kyau sosai don kana Ganin kayan dake ciki kasan foreign ne.
Karasawa tayi bakin gadon ta Raqube a gefe ta kasa motsawa sai hawaye, da sauri ta dafe kanta dake Sara mata sosai, take ta fara tariyo bayanin daya yi masu dasu da, saurin runtse idanunta tayi tana jin haushi kanta sosai, wato wannan ne dalilin da yasa ya hanata zuwa kano Har ta gudu aka kusa kidnapping dinta, tunawa da inda yake basu labarin yanda aka wulaqantar dasu salima akan titi tayi da inda yace saboda ita ne ya taimakesu,badan ita baba bazai sansu ba, so all this while shike kula da Yan uwanta, shine ya kubutar dasu daga ukubar da suka shiga? Shiya haskaka rayuwar su yayi protecting dinsu ya kawo su gidanshi ya maidasu mutane, she can’t believe it, she has been seeing him wrongly,take hankalinta ya Tashi ya soma innalillahi a zuciyarta don Har dishi dishi ta fara gani,tana nan zaune tana kukan takaici aka budo kofar, bata dago ba taji muryar matar dazu da taji suna kira da ammah, Har gabanta ammah ta karaso da zauna gefenta fuskanta dauke da murmushin, wani irin dadi ne ya dabaibaye zuciyarta lokaci guda datayi setting idanunta akan amra,
Kusa da ita amma ta zauna cikin kamala da dattako irin na manyan mata ta kalleta cikin kulawa “daughter bamuyi proper gaisuwa ba”
Kasa dagowa amra tayi sai a lokacin ta tuna basu gaisa ba kwata kwata, ahankali ta soma zamo da jikinta kasa harta tsugunna tana kokarin hana kanta kukan da yake ciyota na takaicin kanta don kunyar hada ido ma
Take da ammah, aduuniya babu matar da take Ganin qimarta ayanxu kamar ammah, ta dauki kannenta ta rikesu na tsawon watanni ba tare da sanin ko su waye ba kuma ta rike su da amana hannu bibbiyu, hawayen dake shirin zubo mata ne Tayi saurin hadiyewa arrarabe ta soma magana “Ina…wuni..Haj…ya”
Saurin tallabota amma tayi fuskanta dauke da murmushi ta dagata sama tace “please karki duqa min daughter” maido ta kan gadon ammah tayi kafin ta fuskanceta fuskanta dauke da murmushi “ki daina wannan kukan kinji, is not good for your health,ki saki jikinki, you’re part of us now”
Wani irin sanyi amra taji a ranta jin kalaman ammah,kanta a kasa ta kasa hada idanu da ammah, miqewa ammah fuskanta dauke da murmushi jin dadin Ganin yanda amra keda kunya tace “Bari na turo maki lanatana ta hada maki hot bath inkin gama saiki ci abunci ki huta ko?”
Anatse amra ta bude Bakinta da yayi mata nauyi tace “tohm, Nagode”
“Babu godiya okay???” Ammah ta fada tana kallonta
Girgiza kai kawai amra tayi tana jin wani irin nauyin ammah, don kallo daya ma tayi mata tun kasa bata kara bari sun sake hada idanu ba.
Bayan fitar ammah da Yan mintuna saiga lanatana ta shigo, toilet ta shiga ta hada mata hot bath kafin ta fito ta kallieta tace “bismillah”
Dan dagowa amra tayi ta kalli lanata kafin ta kauda kanta gefe tace “na..go..de”
Murmushi lantana tayi ta juya ta fuce tare da rufo mata kofar
Bayan fitar lantana da yan mintuna ta miqe tsaye, inda taga lantana ta fito ta wuce, jikinta gaba daya ya gama mutuwa, ahankali ta bude kofar toilet din ta shiga tare da karo kofar, bin toilet din tayi da kallo, ya hadu sosai kamar ba a Nigeria ba, mamakin irin kudin da aka zuba a gidan take don tunda ta shigo tasan gidan manyan mutane ne, tube kayan jikinta ta soma yi don gaba daya bata jin dadin jikinta, cikin bath tube ta shiga ta gatsa jikinta, ta dauka kusan 30min a cikin bath tube din tana tunani irin iri, shes feeling so guilty, tana regretting abubuwa da dama wanda bata son tunasu gaba daya, tana gamawa ta janyo sabon towel dake jere anyi hangin dinsu ta daura kafin ta fito daga bath tube din, gaban toilet sink ta tsaya ta janyo sabon brush ta wanke bakinta kafin ta dauro alwala don ko sallar asuba bata samu tayi ba saboda tafiyar da sukayi.
Agurguje ta fito daga cikin toilet din, saida ta karaso tsakiyan dakin ta fara tunanin kayanda zata saka,samun waje tayi ta zauna ta doka uban tagumi ta fada tunani, nan take ta tuna da yanda su salima suka matsa daga jikinta kamar suna kyamarta, don kiri kiri taga zallan tsanarta da fushin su agareta, wasu irin hawaye ne suka zubo mata don kwata kwata bataga laifin su ko jin haushin su don dole suji kamar tayi neglecting dinsu, tana nan zaune akayi knocking, kafin a shigo, salima ce hannunta rike da kaya ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, dan tsaywa tayi daga nesa fusknta babu walwala ta kalli amra, kukan dake ciyota take kokarin hana kanta, yanxu wannan addar su, ta chanza gaba daya, hutu a kwanciyar hankali ya zauna a jikinta, badan akwai soyayya da shakuwa tsakanin su ba bazata taba yarda wannan addan su ce ba, don ta chanza gaba daya, su suna nan suna jimamin rashinta ita kuma tana chan tana rayuwarta, tunawa da abunda ya Muhammad ya fada yasa tayi saurin korar shedan din dake mata gangar zuga a ranta tayi kafin ta tako inda amra take zaune lost in her thoughts dan ko sallamar da tayi ma bata san tayi ta ba,tsayawa dan nesa da ita salima tayi kamar wata bakuwa tace ‘’gashi amah tace akawo maki’’
Dan dagowa amra tayi jin muryar salima, da sauri ta miqe tsaye tana hawaye tace ‘’salima!!’’
Aje mata kayan salima tayi a gefe gado kafin ta juya don ko Magana bata son tayi mata, da sauri amra ta riko hannunta, ciki kuka tace ‘’salima please wait,’’
Kasa juyowa salima tayi itama tana danne kukan dake cinta,zagayowa gabanta amra tayi ta fuskanceta ‘’salima nayi kewar ku, nayi kewarku sosai,life was so hard babu ku ate dani, tunda nabar kasar nan ban samu kwanciyar hankali ba, kullum da tunaninku nake kwana nake ta…’’
Ani irin kallo salima tayi mata tare da cire hannunta daga nata cikin zafin rai tace ‘’kinyi kewar mu adda? Ah ina Kenan?, adda pleas im not ready to talk to you now”
Kallonta amra tayi cikin kunci ta fara kokarin kama hannunta tace ‘salima please believe me….”
‘’no adda,how do you expect me to believe that?, wallahi baki damu da halin da muka shiga ba da kin damu da alokacin da aka kusa kashemu na kira a waya zakiyi gagawar dawowa, kinsan irin wahalar da muka sha kuwa’’ salima ta fada tana kallonta hawaye na zarya a fuskanta, kafin ta cigaba ‘’mun sha azabar da ko a lahira sai haka, we spend months cikin daki babu haske, munyi wanka babu sabulu, mun kwana cikin dauda,abunci ma gagarar mu yake, zauciyar salim ta kusa bugawa, ya Ibrahim ya kusa raping dina, daddy yayi min dukanda saida nunfashina ya kusa daukewa, babu cima mai kyau, hatta ruwan sha gagarar mu yayi, kullum cikin kuka da fargabar abunda zai faru da salim nake, shin kinsan irin masifar dana shiga sanadiyar amfani da wayar da nayi wajen kiranki?kullum da kukan rashinki muke wuni har allah ya akwo mana ya Muhammad, our life saviour, sai yanxu daga baya zaki dawo rayuwar mu kice kinyi kewar mu and you think I will believe that?, wallahi bazan taba yarda da maganar ki ba adda, you neglect us bayan kinsan bamuda kowa sai ke’’
Ínnalillahi amra ta fara maimiata a zuciyarta, hawayen dake zarya a fuskanta na kara gudu kamar race, kalaman saima sun daketa sosai, shes regretting komai, shes regretting kaaratunma dataje tayi, duk zaman datayi achan bata taba kawo zasu shiga worst rayuwa kamar haka ba, kwata kwata bata taba imaging haka ba, and ahaka ta zauna kusan shekara uku da rabi, kannenta suna cikin azabar rayuwa da kuncin rayuwa, while ita tana chan tana cima mai kyau,
Dariyar takaici salima tayi ganin amra ta kasa cewa komai
‘’im so disappointed, as I expect, adda baki da explanation din da zaki yi min da zan yarda’tana kaiwa nan ta fuce daga dakin tabar amra a tsaye tsayuwar ma data gagareta sulalewa tayi kasa tana kuka sosai a fili, ta dade anan tsugunne ta kasa rarrashin kanta,ta dauka kusan rabin awa kafin ta lallaba kanta ta miqe don wani irin jiri jiri takeji sosai, baking ado ta koma ta zauna tana kukan zuci don hawayen ma kafewa yayi, ganin kukan bashi da wani amfani yasa ta janyo doguwar rigar mai hade da mayafi cutton da salima ta aje mata,ta saka, saida ta
gama sawa aka sakeyin knoking, lanatana ce ta shigo hannunta dauke da tray na abunci, a tsakiyan dakin t aje mata tray din tace ‘’bismillah ga abunci’’
Mikewa amra tayi fuskanta babu walwala ta kalleta tace ‘’dan allah ina ne gabas’’…nuna mata alkibla lantana tayi kafin tace ‘’bari na kawo maki abun sallah’’
Gaban wardrop lantana ta tsaya ta bude tare da zaro sallaya, tana daukowa ta tako gaban amra ta shimfida, kallonta amra tayi tace ‘’nagode’’, murmushi kawai lanata tayi kafin ta fuce daga dakin, tana fita amra ta fara gaba tar da sallah, tana idarwa ta doka uban tagumi,kalaman saliama suna tsaya mata arai sosai, data tuna da abunda ta fada sai hawaye shar har saida ta gala baita, kanta ne ya soma sara mata sosai ga yunwa dake ciyota don bata ci komai ba throughout the flight,jiki a mace ta mike ta nannade sallayan tare da zama gefen gadon, kallon haddaen tray din da lanatana ta aje mata tayi, kwata kwata yanxu ma tsoron cin abunci takeyi, don gani take she doesn’t deserve to eat, kiri kiri ta hana kanta cin abunci saida taji yunwar na neman nakasa ta, kafin ta sauko kasa, bude warmers din ta fara yi, fried rice ne sai gizzard sauce harda pepper chicken daga gefe, yawunta ne ya tsinke don abuncin yayi kyau a ido ga kamshin abuncin dake bugarta, anatse ta janyo plate ta danyi serving kanta kadan ta soma ci, loma daya biyu tayi ta aje don jin kamar zatayi amai, tunawa da hours din data dauka babu komi a cikinta yasa ta aje abunci ta hakura kawai don normally idan bataci abunci ba takanyi amai idan taci mai nauyi yunwar bazai sa abuncin ya zauna ba saidai ruwan tea, aje abunci tayi ta koma bakin gado ta zauna tana tunanin rayuwa.
Bangare amar bayan ya dawo daga masjid sama ya wuce direct saida karaso yabi lanatan dake fitowa daga cikin daya daga cikin bedrooms din dake nan saman,tabe baki yayi ya wuce part din ammah, da sallama ya bude kofar bedroom dinta, a zaune ya taddata kan royal bed dinta, tunda ya shugo ta bishi da kallo masu ma’anoni daban daban,kafin ta kauda kanta, still yanayinta bai sauya ba game dashi.
Jiki a mace ya karaso ya zauna kan carpet din dake tsakiyan dakin zuwa gadon, kanshi a kasa ya anaste soma magana “barka da rana ammah na’’
Kai tsaye ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba ‘’barka’’
Dan shuru ne ya ratsa don ya kasa cewa komai, itama dai karantarshi ta fara yi, kafin tayi gyaran murya, ‘’muhammad’’ ta kira sunanshi a kausashe babu wasa, dan dago da jajayen idanunshi yayi ya kalleta yace ‘’naam’’ kafin ya sauke kan kasa, kasa hada idanu yayi da ita, tana ganin haka ta cigaba ‘’ina fatan duk bayanin dakayi min shine abunda nake buqatar ji aka rage ba kuma baka kara ba’’
Bai dagoba ya bata amsa ‘’eh’’
‘’kayi bayanin dalilin auren yarinyar nan dakayi don ka taimaketa kuma saboda yarjejeniya da kukayi tsakaninku saidai baka fahimtar dani naka dalilin auren ta da kayi ba ta bangarenka?, bana son ka boye mun komai, ko dazun da kake bayani banyi tambayar nan ba sabda inason muyi maganar tsakanina dakai’’
Kasa dagowa yayi haka zalika ya kasa cewa komai, tana ganin haka ta gane kunyar ta yake ji ita kuma tana son tasan komai don jin dalilin auren don abunda yafi fado mata arai idan ta tuna da auren da yayi shine maybe ko buqatar mace ne ta sashi yin hakan ba tare da ya shawarceta ba ko ya fada mata, don matse fuska tace ‘’this should be the last time da zanyi maka Magana kayi min shuru Muhammad, im all ears explain’’
Runtse idanunshi yayi gam kafin ya budesu, kanshi har wani sara mashi yake yace ‘’na aureta ne saboda doctor yace I have only one chance, kuma dole na kusanci mace idan banyi ba bazan taba haihuwa ba, I have no other option shiyasa na aureta’’
Wani irin tausayinshi amah tashi, batayi tunanin ospermia nashi yakai last stage ba, zuciyarta ne ya karye sosai, tausayinshi y agama baibaye ta dama tausayin kanta, ashe dalilinshi nayin aure Kenan, allh yaso batayi saurin judging dinshi ba don data biye zancen da daddy yake dole zata yarda kila fasikanci yakeyi da neman matan banza, ashe auren ma da yayi don yak are martabarshi da mutuncinshi yayi don tabbas duk wanda yaji cewa he has last chance of having a child dole kota hanyar fasikanci ne zaiyi abun,
Nunfasawa tayi ta danne zuciyarta tace ‘’tun yaushe ka kai ospermia yakai stage 3’’ tambayanshi tayi tana mai kallonshi yanda ya sunkuyar dakai, amar dai yayi mamkin jin tambayar tata don baiyi tunanin tasan ospermia dinba, saidai sanin mahaifiyar tashi wayyayiya ce kuma mai ilimi dole zatayi research yasa yace ‘’stage 3’’
Ahanakli ta soma furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun a cikin zuciyarta bata bari ya dago yaga yanayin ta ba don saida hawaye ya zubo mata, don tasan daga last chance din nan indai ba a samu ba shikenan, ‘’toh yanxu is she pregnant?’’ ta tambayeshi kai tsaye
Shuru ya danyi chan kasan maqoshinsa baka ma jin abunda yake cewa sosai yace ‘’no’’
Daidaita natsuwarta tayi cikin tawakkali ta kalleshi ta soma magana
‘kayi babban kuskure Muhammad, shiyasa naji zafin yin gaban kanka da kayi ba tare da shawara dani ba, duk abunda babba zai hango yaro bazai iya hangowa ba koda ya hau kan dutse ne,da tunaninka da hankalinka? Na farko dai banga laifinka nayin auren da kayi ba don ka kare martabarka da mutuncinka, na biyu haihuwa ta allah ce basai nayi maka dogon bayani ba tunda gashi allah ya bamu kai because dada also battle with the same ospermia that you had which kayi inheriting’’
Kanshi a kasa feeling so sad yace ‘’im so sorry amah, ban fada maki bane saboda banason ki zama disappointed,saboda you always want me to have a family and naga yanda kikeson jikoki im so sorry’’
Saurin tarar nunfashinsa tayi tace ‘’don’t be sorry son, haihuwa na allah ne, how could you think that I will feel like youre a disappointment to me?im very proud of you, I will always be by your side saidai bakayi daidai ba kuma dole na nuna maka hakan, you made a mistake, tun farko ni mahaifiyarka ni ya kamata ka fada ma damuwarka,yanxu dub aka gani, aure fa baa bun wasa bane, haihuwa idan kana da rabo zaka samu’’
Dan dagowa yayi ya kalleta yace ‘’ammah bawai auren zama dindin din bane, its just a contarct marriage, kuma duk mun samu abunda muke nema, nayi alqawarin sakinta ma ayau daman tun farko that was the plan, idan na saketa saina hadata da yan uwanta, ‘’
Da sauri ammah ta dago ta kalleshi ranta adan bace tace ‘’this is what I’m talking about, ku yaran zamani kun maida aure ba komai ba, kun maidashi kamar wasa, yanxu duk iliminka da wayonka muhammad?allah baya son saki amma ya halasta shi, meysa bakayi tunani ba kafin kuyi auren? Yanxu kace sakinta zakayi ko?shin kasan idan ka saketa ka maidata bazawara? Yau ko ta sake aure bazata taje a matsayin budurwa ba koda kuwa duk duniya babu wanda yasan kunyi aure daga kai har ita, saboda haka yanda kukayi aurennan ba tare da sanin kowa ba haka zaku zauna bazaka saketa ba,tunda nake da mahaifinka saki bait aba shiga zukatanmu ba don haka kaima bazakayi ba,