Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   72 / 94

213K to 216K   out of 279.4K words

saboda cikin’’

‘’alhamdullah alhamdullah’’ abunda amah ke fada Kenan har doctor ya rubuta masu magungunan da zata buqata ayanxu da allurai.

Godiya amah tayi ma doctor suka futo tana rike da hannun amra dake ta faman sunnar dakai, ta kasa believing cewa wai ciki ne da ita cikin ya muhammd, shes so emotional right now, bata san me zatayi ba farin ciki ko akasin haka,  shi uban dan ma ba sonta yake ba,saidai ganin yanda amah ke farin ciki yasa hankalinta ya dan kwanta, yanxu koba komai ta sakama amah da yanda ta rike yan uwanta ta zama gatansu kuma ta riksu amana.

 

Cikin awa guda aka gama yima amra komai aka bata magunguna akayi mata allura, ba laifi tunda akayi mata alluran nan taji wani dadi a jikinta da kuzari, nan nurse ta bata shawaran ta dunga shan ruwa sosai da lots of milk, godiya sosai amah tayi mata kafun su fuce daga asibitin, yanda amah ke lallabata kamar kwai abun har kunya ke saka ta don koda ska karaso wajen mota da kanta ta bude mata ta shiga cikin motar ta zauna kafin ta zagayo ta kunna motar, ‘’daughter me kike son ci?, please ki fada min kinji? Ko zakici cake naga kinason kayan zaqi’’

Ganin yanda ta damu sosai yasa amra ta dan murmusa tace  ‘’zanci cake din ammah’’

Cikin murna amah tace ‘’yauwa my dear, bari na kaiki wani cake shop, akwai different varieties saiki zaba

wanda kike so’’

Tada motar amah tayi ta juya akalar motar suka bara harabar asibitin, wayanta dake ruri ta daga tana ganin sunan amar ta ajiye a gefe yanxu batashi take ba ta amra take.

Koda suka iso cakemeaway shop, amra bata shiga ba saboda tana jin jiri amah ce ta sayo mata different types, flavors and toppings of cake kusan guda goma, haka aka biyota da ledoji har cikin mota kafin subar wajen.

Suna kan hanya ammah taga mai agwaluma, da data, nan ma saida ta tsaya ta saya mata kafin su bar wajen, har lokacin amar waya yake mata yayi mata missed call yafi talatin hankalinshi duk y agama tashi, karshe ma message tayi mashi ‘’son were fine, please stop calling’’

 

Horn din motar amah ne ya karade gidan, securities ne suka bude gate, amar dake safa da marwa a parlor yana jin horn yayi saurin futowa tsakar gidan, sanye yake da shorts sai vest gaba daya bashida natsuwa tun bayan daya tashi saida yaji horn din motar amah.

 

Amah na parking yazo gaban mazaunin driver, bude kofar amah tayi tana murmushi, babu zato ba tsammani ta rungumeshi, da mamaki ya tsaya shima ya rungumeta, ‘’alhamdullah alhamdullah son, im so happy today’’ ta kaarshe tana dariya, amra ce ta fito daga motar tdan deba kayan da suka shigo dashi zata wuce amah tace ‘’noo noo kawo nan, muhammd zai dauka, ay shine da wannan bake ba diyata’’

Kallonshi amma ta sakeyi tace ‘’karba kayan chan ka wuce mata dashi dakinta,’’

Kallon inda amra ke tsaye tayi tace ‘’zaki iya kuwa daughter ko ya daukeki kema ya kaiki saman’’

sauke kanta kasa tayi tana jin kunya sosai, amar dai baki sake ya tsaya yaan kallon yanda amah ke cikin farinciki da annushuwanda bait aba gani a tattare da it aba, ‘’ammah whats the news? Why are you so happy’’

lakatar kumatunshi amah tayi tace ‘’it’s a secret’’

tana kaiwa nan ta shige ta barsu tsaye shida amra, karasowa yayi ahankali yazo gabanta, kamar baa mar bay a miqa mata hannunshi don ta bashi ledojin, dan dagowa tayi ta kalleshi nan ta shagala harta fada tunani, ‘’ya Muhammad is the father of my baby? Hes going to be a father, allah sarki ashe yana da rabon ganin danshi shima,’’ saida ya dan gyara murya ya daga mata gira daya ta ankare da kallonshi da takeyi, saurin sauke kanta kasa tayi tana tausayin kanta, ayanxu data tsaya agabanshi sai taji wani irin dadi sosai koba komai zata saka mashi da alkairin da yayi ma yan uwanta ta hanyar protecting dinsu ya kula dasu ya basu ci da sha, badan shiba qila da sun salwanta saidai tausayin kanta take ayanxu kuma, don ta rigada tasan bazai tabasonta ba bazaitaba kallonta a matsayin mace ba. Fatanta allah yasa taci albarkacin abunda ke cikin ta ta samu kwanciyar hankali a cikin aurensu da soyayyarsa.

 

Ganin batada niyar bashi yasa ya karba daga hannunta kawai yace ‘’muje ciki’’ sata yayi agaba yabi bayanta.

 

Suna shiga ciki suka tadda ammah ta tara su salima dasu aman da salim tana masu kyautar kudi, yaudai kowa ya shaida ammah na cikin farin ciki dukda sunyi sunyi ta fada amsu taki.

Amra dai sama ta wuce amar ya bita da kayanda ammah tace nata ne, yana shiga yaso ya tambayeta inda sukaje saidai kuma wata zuciyar ta haneshi da hakan don haka ya fito daga dakin ba tareda yace mata qala ba yana futa tabi lafiyar gado itama.

 

Monday morning…

Yau su salima zasu koma school don by next week zasu fara waec da neco don already bandasu yan ss3 za ayi exam din school sais u salim dake ss1 going to 2.

Haka suka jera kwanaki suna zuwa school kullum ita da salim, ta maida hankali sosai kan revision da practice exams da akeyi masu saboda preparing dinsu akeyi for waec da neco.

Amra dai kullum tana kwance, ammah na kula da ita sosai har lokacin babu wanda yasan abunda suke ciki, ammah bata yarda ta fada ma amar ba don tace sai when the right time comes.

Shima bai damu ba don bai tambaya ba, haka ya dunga harkokinshi, yanxu kokari yake y agama komai don ya samu ya wuce bakin aikinsa.

Gyaran da ammah tace yayi bai fasa ba, yasa anyi refurninshi gidan gab daya an saka furnitures din da sukaci uban nada, fadin irin yanda gidan ya chanza ya kaar kyau ma bata lokaci ne don komai yaji zam zam, ko a kasar waje sai haka.

 

After 3weeks….

Yau saura sati guda salima su gama neco don already sun gama waec, gaba daya ta rame sosai sai karatu takeyi kullum tana daki, salim kuwa ya gama school exam, kullum yana zaune yana games dinshi sai salima ne ke zuwa school itama in a week zata gama, gaba daya ta fidda tunanin aman aranta saina karatunta , shima ya bata space sosai don baya son ya takura mata saidai duk sanda suka hadu koda a wajen dining ne nan suke aika ma knsu kallon love wanda kowa ya shaida soyayya mai karfi ce a tsakaninsu…

 

 Amra ta shiga 6month harda sati biyu, har lokacin cikinta bai fito ba don bazaka taba cewa tana dashi ba inka kalleta saidai wanda yasan ainihin ciki ko yayi experianceing zai gane dashi ajikinta. duk ranar Wednesday ammah ke kaita antenatal babu wanda ya sani a gidan amar ne kawai ke yawan tambayr inda suke zuwa,shima lokaci guda ta taka mashi burki don tasan zai iya yin buncike don haka ta shaida mashi bata san shishigi, he should behave him self, nan take kuwa ya shiga taitayin shi bai sake tambay aba kuma baiyi gigin yin bunciken ba.

 

Friday morning..

Tunda amra ta tashi yau ta tashi da son cin yalo, avocado, gurjiya  da agwaluma gaba daya at the same time, haka ta dunga zarya adaki harda kukanta ta rasa yanda zatayi, cravings din kamar zai saka ta hauka, babu shiri ta daura hijab dinta akan towel dinta don yanxu dashi take wuni idan tayi wanka bata son saka kaya kwata kwata, ta na fiowa ta wuce dakin ammah direct, da sallama tashiga dakin harda hawayenta, ammah na ganinta ta mike ‘’daughter lafiya? Akwai abunda ke maki ciwo ne?’’

Karasowa amrat tayi kanta akasa ‘’ammah dan allah inason yalo da data, da gurjiya, da avocado da dayan banma don sunanshi ba but kinsaya min lokacin da mukaje asibiti’’

Murmuhsi ammah tayi ta rike hannunta, ‘’haba daughter yanxu saboda wannan kike kuka? Share hawayenki bari na kira muhammda yaje ya nemo maki, yanxu kuwa kiji,’’ ammah na kaiwa nan ta dauki wayarta, amar dake shirin futa don harya riko keysa dinshi ya nufi inda motarshi take wayar ammah ta shugo mashi, saurin dauka yayi yasa a kunneshi ‘’muhammad kana ina’’ ammah ta fada tana sauraronshi

Daga chan ya amsa ‘’yanxu zan fita, inzo ne?’’

‘’no basai kazoo ba, daughter na son cin yalo da data da avocado da agwaluma da gurjiya da dinya’’

Zaro idanu yayi waje don tunda ta fara Magana baima gane abunda take nufi ba ‘’sorry come again ammah’’

Ya fada surprisingly

‘’nace maka my daughter nason cin yalo da data da agwaluma da dinya da gurjiya sai avocado, ianson kabar duk abunda kake kaje ka nemo mata’’

‘’what!! Ammah, menene wannan din, kuma….’’

Saurin katseshi ammah tayi ‘’look babu wani kuma, kaje duk inda zakaje nab aka nan da 1hours’’ amra ce ta katseta yayin da ta fashe da kuka, 1hour ina bazata iya jira ba, ammah na ganin haka ta gane don haka tace ‘’kaii nabaka 30mins, ka nemo su duka duk nda zakaje kaje ka nemo su yauwa’’

Tana kaiwa nan ta kasha wayar dipp ta juyo gaban amra ‘’daugter, ki kwantar da hankalinki kinji, zai akwo aynxu yanxun nan, bari na yanko maki avocado ki fara dashi don naga akwai anan kitchen kafin ya kawo sauran’’

Ashagwabe amra tace ‘’thank you ammah’’

‘’ki kwanta ma anan ki huta yanxu zan dawo my dear’’ ammah ta fada tana mikewa

‘’amra kuwa janye hijabin tayi ta kwanta abunta nan take barci ya kwasheta………….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 143

Update

Unedited page

Kasa motsawa yayi daga tsaye da yake bayan ammah ta katse wayar, gaba daya baima gane kan zancen ammah ba kwata kwata, meysa ammah zatace yaje ya nemo waennnan abubuwan da baima sansu ba? Ya tambayi kanshi, dan shuru yayi tunawa da wadda tace tana son abubuwan, ranshi ne yayi mugun baci lokaci guda, may yarinyar nan ke nufi kenan? Saboda ya saukar mata yanxu shine take neman kawo mashi raini? Inba raini ba Har tana da guys din da zata hadashi da ammah? Wani abun ya sake tunawa kafin ya danyi yar tsuka ya wuce cikin motarshi azafafe, yana shiga motar ya kunna yayi reverse, already securities sun bude mashi gate don haka ya fusgi motar ya fuce da high speed.

Tunda ya hau kan titi ya rasa tunanin da zaiyi, babu abunda yake sai cije lebe yana tunanin kalaman ammah, Ina take cewa “Duk inda za kaje Ka nemo su na baka nan da 30mins”

Haka ya dunga nanata kalaman ta a zuciyarshi yana tunanin meysa ammah ke bama yarinyar nan too much attention, yanxu abun Har yakaiga sai abunda take so za a sayo kuma ma babu wanda ta raina da zai sayo mata useless abubuwan nan sai shi saboda ta gama rainashi, and she’s shamelessly asking for too much, shi kalaman ammah ne sukafi tayar mashi da hankali yanda take nanata mashi akan dole saiya nemo abubuwan da baima taba ganinsu ba baima sansu ba sai avocado kawai alya sani, haka nan dan dolenshi ya fara tunanin yanda zaiyi karshe sai gashi a wani babban grocery mall anan cikin guzape, yana karasowa yayi parking, saida ya danyi jim a cikin motar kafin ya fara kokarin tunanin abubuwan da ammah tace ya siyo, wayarshi ya fara janyowa ya fara kokarin browsing abubuwan, “what is agbalum” ya fara searching, haka ya dunga browsing dinsu daya bayan daya yana duban sunayen su da turanci, yana gamawa ya fito daga motar ya saka dark shade dinshi don Ana kwala rana sosai, cikin mall din ya shige atsanake cikin kamewarshi,Duk wanda yazo wucewa cikin mall din saiya juyo ya kalleshi.

Kai Tsaye ya shige cikin mall din yabi direction din wajen groceries, yana zuwa ya dan tsaya yana duban wayanshi, haka ya zagaye wajen nan baiga ko daya daga ciki ba, yanda yake zagaye wajen shi kanshi mamakin kanshi yake, don saida yaga 30mins sun da ammah ta deba mashi ya kusa karewa hankalinshi ya Tashi sosai, wani attendee ne dake kula da harkokin kayan lambu a wajen ne ya karaso inda yake don yana daga zaune yana kallon yanda yake zagaye wajen, “good day sir” mutun ya fada yana karasowa inda yake,kallonshi Amar yayi ganinshi da uniform din workers din wajen yayi saurin cewa “thanks”

“Sir kana neman wani abu ne?” Mutumin ya tambayeshi yana kallonsa,

Sauke glass din fuskanshi yayi ya kalli mutumin yace “yauwa, kunada uhm… agbalum, gunji and uhm…” ya dan tsaya yana nazari, Yalo”

Dariya mutumin ya danyi kafin yace “yallabai Ay bazaka samu agwaluma anan ba da su data, saidai irin kan hanya haka,”

Shuru Amar yayi yana tunanin wani kan hanya kenan, “ inane kan hanya kuma? I mean wani direction kenan?”

Gaskia oga bazan iya cewa ga inda zaka samu saboda yawanci masu baro ne zakaga suna yawo a hanya haka, abunda na sani shine bazaka samesu a presidential root ba saboda basa bin irin manyan hanyoyin nan”

Kallon agogo Amar yayi ganin 30mins din  ya cika, baima kaiga gama tunanin ba wayar ammah ta shugo wayarshi, cikin sauri ya dauka yakai kunnenshi, “Muhammad kana Ina ne? What’s the meaning of this?”

“Ammah please ina nema ne, nazo mall

Babu,” Amar ya fada yana kokarin yi mata bayani 

“Yanxu ina Ka taba ganin Ana saida irin waennan fruits din a mall? Kaje kasuwa fruits Ka nema, na baka nan da 1hr, Wallahi son karka bari na sake kiranka baka dawo gida da wannan fruits din ba, kuma duka zaka sayo mata karka bar ko daya”

Ahankali ya soma magana “tohm” 

Bata ma amsa shi ba ta kashe wayar, sauke wayar shima yayi daga kunnenshi yana cije lower lips dinshi, “pack those avocados”

Kallonshi mutumin tayi jin abunda yace “sir duka??”

A harzuke Amar yace “yes all”

Shuru mutumin yayi ya fara packing duka avocados sun wajen don yakai kusan katon kwado daya, saida ya fara weighing kafin ya daukar mashi suka wuce wajen cashier, tunda suka tsaya mutanen wajen suka bisu da idanu dashi da wanda ya dauko avocado din niki niki,, 

Kallonshi cashier din  yayi “sir 50k ne balance dinka”

Ba tare da tunanin komai ba ya zaro wallet dinshi daga aljihun sa ya ciro black unlimited card dinshi ya miqa mashi, da mamaki cashier din ke kallon card din don bai taba ganinshi ba kafin yau I inserting cikin pos, yana gama payment ya fito wannan mutumin na biye dashi Har wajen motar shi, boot ya bude mutumin ya saka mashi uban tulun avocado din da sukayi mashi packaging a manya manyan kwalaye kafin ya rufe.

Cikin motar ya shige ya zaro kudi daga cikin dash board dinshi da baima san adadin su ba ya miqa mashi, cikin jin dadi mutumin ya karbi kudin yana godiya don kudin yakai kusan albashinsa koma yafi haka, yana bama mutumin kudin ya zuge glass din motarshi yayi baya da motar ya fuce daga mall din.

Haka ya dunga zagaye akan titi yana tunanin ko maybe zai ga masu sayarwa saboda mutumin yace mashi akan hanya ake samun su, haka ya kusa cinye Rabin awa, ganin yana Jan lokaci sosai gashi yana tsoron bacin ran ammah yasa yayi parking gefen titi ya soma dialing number asad don shi kadai ne abokinsa anan Nigeria.

Ringing biyo asad ya daga wayar tare da sallama, gaisawa suka farayi kamar yanda suka saba kafin amar ya danyi jim yace “Ina san zamu wasu fruit anan abuja?”

“Wani irin fruit kenan oga?” Asad ya tambayeshi 

“Uhm Wai abaluma da data da guji da sauransu”

Shuru asad yayi kafin yace “Toh fah, gaskia bansan inda ake samun su ba, saidai maybe fruit market Koh ya tsaya irin su hanyar waje wajen garin abuja zaka samu, yawanci dai nafi ganin irin Abubuwan nan a buari”

“Ina ne buari?” Amar ya tambayeshi 

“Hanyar fita daga abuja, zaka dauka wajen awa daya kafin kaje wajen”,asad ya bashi amsa

“No it’s urgent, Ina ne fruit market din?” Amar ya sake tambayarshi 

“Akwai a garki2, Ka duba map” asad ya sake bashi amsa 

“Okay thanks” 

“Zan zo gaisheda hajiya anjima da daddare ” asad ya fada yana sauraron amsarshi  

Kai tsaye yace “okay” yana kaiwa nan ya kashe wayar ya bude map,

Yana saka wajen a map ya kunna motar ya hau titi a guje, haka ya dunga wuce motoci yana kutsawa Har yakai fruit market, koda yake da kyar ya samu Yalo da agwaluma nan ma saida ya saya kusan kwando kwando, kafin yayi payment ya koma motarshi hankali atashe, haka ya juya akalar motar ya bar wajen, haka ya dunga bin hanya yana fatan samun masu saidaga akan hanya, yana cikin driving kuwa ya hango wani mutumi yana tura baro, da sauri ya gangara motarshi gefen titi wajen da mutumin ke tsaye da baronshi a tsaye, sauke glass din motar yayi ya kalli mutumin “barka dai malam”

“Barka yallabai”

Kallon abubuwan da yake sayarwa yayi kafin yace “menene wannan kake sayarwa?”

“Wannan gurji ne yallabai sai kwakwa”

Hamdala Amar yayi ya kalli mutumin ba tare da bata lokaci ba yace “Nawa ne duka?”

“Dubu goma ne yallabai” ya bashi amsa

“Hada mun duka” Amar ya fada yana kwaso sauran cash din dake cikin dash board din, baima taaya irgasu ba ya Mika ma mutumin, karba mutumin yayi kafin ya Mika mashi duka Gurjin da kwakwar “Nagode yallabai bismillah”

Karba Amar yayi ya ajiyesu agefen seat din gaba, baima tsaya sauraron mutumin ba da yake cewa “kudin sun haura yallabai” ya fuzgi motar yabar wajen.

Haka ya dunga zagaye, baiga wasu ba don haka ya wuce gida kawai jiki a mace, cikin minti biyar saiga shi a gida, yana shugo wa wayar ammah ta sake shigowa, saurin dagawa yayi yace “ammah gani nan na iso,”

Kashe wayar tayi tana kallon amra dake faman kelayar da amai, ta kasa cin komai, avocado dinma ta cinye shi tass tana neman

72 / 94