Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   34 / 94

99K to 102K   out of 279.4K words

very first kiss and it was so good da Har yake lashe bakinsa, she has this soft and sweet lips, sauke idanunshi yayi zuwa kirjinta da yana gani yasan bata saka bra ba, wani gauran nunfashi ya jaa tare da kauda kanshi, ahankali ya furta “small girl with big things mara kunya”

Murmushi tayi da gefen bakinshi ya tako gaban switch ya kunna light nan take dakin yayi bau, 

Tsayawa yayi kyam a gabanta ya hade hannayenshi kamar bashi ba ya hade rai yace “keeee wake up”

amra da baccin nata bai gama nisa ba ta dan bude idanunta ganinshi tsaye yasa Tayi saurin miqewa tare da gyara rigarta don buttons din na sama ta balle shi don samun iska,tabe baki yayi yace “no need for wani kare kare cause banga abun karewa ba anan wajen” ya fada yana nuna boobs dinta, banza tayi dashi ta kauda kanta gefe hakan yasa hade rai yace “zanyi tafiya gobe, willl be back in 2weeks or a month maybe, Duk abunda kuke buqata you can ask m5, and lastly zanyi warning dinki, me careful don’t pissed me off, my eyes are on you,if you dare try and be stubborn you’ll regret it”

Sakin baki tayi galala, tama kasa cewa komi, don abunda ta fuskanta dashi d more tayi mashi maganar rabuwa da ita the more yake hasala Har ya fada mata magana, bata ce mashi qala ba ta miqe daga kan gadon har yana hango waist beads dinta don datazo duqawa zata janyo bathroom sleepers, yana nan tsaye kamar soja tazo wucewa ta gabanshi, ranshi ne yayi mugun baci ya sanya hannu daya ya janyota baya tare da wullata kan gado yabiyo ta tare Dayi mata runfa, gwalo idanu tayi sosai hankali atashe tace “dan Allah miye haka”

Wani irin kallo ya mata yace “daman bakinki na magana?, bakida kunya ko” ya fada yana matso da fuskanshi kusa da Tata, saurin kauda kanta tayi gefe kirjinta na bugu kamar zai fito tace “dan…Allah Ka bari,”

Matso da fuskanshi yayi har yana gifta mata gashin sajenshi yace “koya maki hankali zanyi tunda bakida kunya, Ina maki magana you’re trying to walk away on me, nasha fada maki babu macen data taba yimin abunda kikeyi, saboda haka shut your dirty mouth”

Ya fada yana sauke mata nunfashi a kunnenta da wuyanta, jikinta ne ya fara karkarwa don wani irin sako ne ke shiga jikinta dalilin abunda yake mata,

“Ni fitsari nake ji dan Allah Ka kyaleni nake bathroom,”

Katseta yayi cikin wani irin tone dayake kashe mata jiki yace “shut….up, ki yi fitsarin anan”

Kokarin tureshi ta fara kuka na kufce mata  tace “Wai meysa kake min haka, don girman Allah Ka kyaleni, Ka rabu dani, na kasa gane dalilin dayasa Ka tsaneni,Allah….”

Kasa karasawa tayi jin bakinshi cikin nata, kokarin danne horanta ta fara ya rinjayeta ya tura halcenshi cikin bakinta, kissing dinta ya fara harshly, ya dauka kusan minti goma yana abu daya, yanda yake janyo lips dinta da halve ya kamar zai tsinkasu, kasa komai tayi sai hawaye dake zarya a fuskanta, hannunshi duka biyu yasa ya danne form din gadon, bai sakar mata nauyi ba kwataa kwata, kissing dinta yake with so much energy kamar mayuwancin zaki, hannunshi daya ya sanya ya janyo rigarta sama ya fara shafa flat cikinta zuwa waist beads din dake nade a wajen,saida ya gama mai isarsa ya saketa ya miqe zaune yace “this will be your punishiment dinki kenan for talking anyhow, the next time kika sake walking out on me zanyi abunda yafi wannan”

Yana fadin haka ya juya zuwa dakinshi,yana karasawa ya kwanta kan gadonshi tare da runtse idanunshi Har barci ya kwashe sa.

Amra dai ya barta kwance speechless, toilet ta wuce ta taba Bakinta Ganin yanda yayi ja tace “Allah ya saka min,ya Allah ka kawo kin dauki”

Wanke fiskanta tayi ta koma daki ta kwanta.

Thursday morning

9:00am

Amar ne ya fito cikin shiri, Riga da wando ne a jikinshi black masu kyau designers wanda suka mashi jikinsa, kafarshi wani open shoe ne daya bayyanar da kyawawan kafafunshi, kamshinsa ne ya bade ko’ina tundaga stairs, Nadine na ganinshi Tayi saurin karban akwatinshi ta wuce dashi wajen m5 kafin ta juyo lokacin harya zauna tayi serving dinshi breakfast, cikin natsuwa yake cin abunci baima ci da yawa ba yasha coffee ya miqe, kallon Nadine yayi yace “zanyi tafiya, will be back in few days, keep an eye on her”

“Okay sir”

Fucewa yayi ta mara mashi baya tare da rufe kofar ta koma kan ayyukanta.

Karfe Tara da minti hamsin suka iso airport, sallama sukayi da m5 ya wuce ciki, lokacin har an fara boarding don haka cikin yan mintuna kafan sukayi taking off.

Nnamdi ezikiwe international airport abuja….

Karfe bakwai na dare suka iso abuja,Kiran driver shi yayi, cikin mintina goma ya iso, fitowa Amar yayi cikin kasaita ya shige bayan motar driver kuma ya saka ja kanshi a bayan motar

Direct gida suka wuce din agajiye yake sosai gashi he’s eager to see his ammah.

Karfe Tara daidai suka iso gida, driver na parking ya bude mashi ya fito cikin kamewa yace “ka shugo da baggage din”

“Okay yallabai”Driver ya amsa mashi,

Cikin gidan ya shige tare da bude kofar kai tsaye bakinshi dauke da sallama.

Salima dake zaune ta doka uban tagumi Tayi saurin juyowa ta kalli kofar, da sauri ta miqe duka ta dauke da murmushi tace “laa ya muhammad Ka dawo, sannu da dawowa”

Murmushi ya danyi ya karaso parlor, da sauri ta karaso wajen driver ya karbi baggage dinshi, kallon ko’ina yayi kafin yace “Ina mutanen gidan ne”

Karasowa inda yake tayi tace “suna sama, Ina wuni ya muhammad”

Atakaice yace “lpy alhmdlh”

Kallonta yayi yace “ki jiga da baggage din”

Wuce wa tayi da jakanahi shi shi kuma ya wuce sama zuwa dakin ammah, da sallama ya bude dakinta ya saka kai, ammah dake zaune gefen gado hannunta

tiaras charbita dago ta kalleshi, ta amsa sallaman nashi,takowa yayi har inda ya zauna gefen ta yace “Ina wuni ammah na”

Fuskanta dauke da murmushi tace “lapiya Alhamdulillah ya hanya”

“Alhamdulillah ya amsa ta

Shuru ne ya biyo baya kafin yace “na sameku lpy? Ammah is there something wrong?”

Ba tare da ta kalleshi ba tace “Alhmdlh I got admitted, dazu aka sallama ni” 

Hankali tashe yace “subhanallah!! Meysame ki ammah? babu wanda yayi informing dina”

Hannunshi ta rike tace “shiyasa naqi fada maka kenan saboda nasan zaka tayar da hankalinka, hawan jini ne kawai”

Kallonta yayi yana son karantar abu yace “ammah hawan jini baya Tashi saida dalili, is there something that I need to know? Wani abu ya faru ne bayan tafiya na?”

Jero mata tambayoyi ya fara,

“Babu abunda ya faru, kaje Ka huta gobe zamuyi magana” ta fada tana kauda kanta gefe

Shuru yayi don tabbas yana sensing wani abu, 

“Ammah kodai kina fushi dani ne?”

Kallonshi tayi ta kura mashi idanu tace “meysa zanyi fushi dakai son? Ko kayi abunda zanyi fushi dakai ne nan sani ba?”

Gabanshi ne ya bada damm chan kuma ya dake yace “let me freshen up, Allah ya sawaqe”

“Ameen ta amsa mashi fuskanta dauke da murmushi tana kokarin danne abunda ke cin ranta.

Kwana biyu kenan bata gane ma alh kabiru, babu abunda ke hadata dashi sai baqaqen maganganu iri iri, musamman akan Amar wanda ta kasa fahimta don Duk maganganun da yake jifanshi dasu bana alkhairi bane don yana dangantashi da kamar manemin mata.

Washe gari da sassafe ya fuce daga gidan don Kiran gaggawa da yayi ma asad don su hadu,yana zuwa office dinshi ya zauna, gaisawa suka fara yi kafin asad ya kalleshi yace “oga, tun yaushe message din ya shigo”

Kallo da Amar yayi yana duban message din yace “about 10days ago”

Karban wayar asad yayi ya duba message din inda meeda ta turo, “sir inata Kiran line dinka baya shiga, my life is in danger zai kasheni, idan kayi reciving message dinnan please call me immediately”

Rike baki asad yayi yana nazari yace “yanxu dainya tabbata bibiyarta akeyi,“

Kallonshi Amar yayi fuskanshi dauke da damuwa yace “yanxu ya zamuyi kenan?, how can we find her?”

“Oga nayi tracking line din ko Zan samu na gano inda take saidai wayar na kashe hakan bazai yuwu ba cos babu abunda Zan samu, yanxu we have to wait for her call nasan she’s smart zata neme mu”

Buga table din gabansu Amar yayi yace” noo, bazamu saka idanu mu dole we have to do something what if ya rigamu cin mata? Bamu san mai zaiyi mata ba so please use your power da connection dinta a fara binciken ta”

Saurin tare shi asad yayi yace “oga idan muka fito fili muka nuna Muna nemanta sai fara suspecting mune muka saya aiki, bakisan ne zai iya yi ba, he’s dangerous, ni abunda yafi damuna shine yana tare daku what if he decides to do something bad?,think about it, dole fah haka zamu hakura mu jira ta”

Amar dai bai gamsu ba don haka ya kura private investigator dinshi akan ya bincika mashi.

Kwanan Amar uku da dawowa nigeria yana zulumin,gaba daya hankalinshi  atashe yake,Duk iya bunciken da zaiyi ya kasa gano inda take don kwata kwata basuyi tunanin zata tafi kauye ta boye ba, Akwai ranar da ya sa akayi buncike ko ta bar kasar still babu wani information.

Bangaren ammah bata samu ta zauna dashi ba don kullum baya wuni a gidan sai dare yake dawowa.

Kauyen fatakum …

Meeda ce kwance kakarta na dura mata maganin gargaji, yau sati gida kenan tana fama da zazzabi, duniya ta juya mata, kamar ba meeda ba ta chanza ta rame ta zama abar tausayi, kwnaanta biyar tana zazzabi, dakyar take tashi, gashi babu kudin siyam magani, masifar tayi masifa haka kakarta ta Nawa wani almajiri wayar ta don ya sayar a kasuwa mai ci don asamu a saya mata maganin bature,aranar meeda na barcin wahala batasan abunda ake ciki ba, saida aka kawowa goggon ta kudin ta fada mata, nan take ta kusa karamin hauka….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 124

Update!!!!!

Unedited

Yanda yake driving kadai zai tabbatar da hankalinshi a tashe yake,wayanshi ya janyo ya sake Kiran asad yace “karku jirani ku wuce kawai, kuyi gaggawa, karkuyi lossing track dinta”

Da sauri yake driving yana wuce motocin dake gabanshi, daman daga office din asad yake don da sassafe ya fito zuwa office din nashi,suna cikin meeting suka samu track din meeda saboda wayarta da aka kunna, suna cikin shirin fucewa driver ya kirashi akan an wuce da ammah asibiti saboda ta fadi heart attack data samu, idanunshi sunyi jaa sosai, fadin irin tashin hankalin da yake ciki ma bata lokaci ne, gashi an samu track din meeda.

Dakyar yayi parking ya fito cikin gaggawa zuwa cikin asibitin, yana zuwa Ana fitowa da ita daga emergency, salima dake gefe a zaune hawaye kwance a fuskanta sai salim dake gefenta shima kukan yake,dan dagowa tayi idanunta suka sauka kan Amar dake shigowa wajen,da sauri suka miqe daga zaune, kallonsu yayi ganin yanda suke kuka.

Salima ce tace “ya Muhammad ammah…”

Bata karashe ba ta fashe da kuka, kallon su yayi yace “stop crying zataji sauqi”

Fitowa doctor yayi daga dakin da aka kwantar da ita ya karaso inda yake ya mika mashi hannu sukayi musaba daman family doctor dinsu ne,“muje office ko”

Cikin office suka shiga shida doctor, zama sukayi kafin doctor ya fara mashi bayani, “a gaskia damuwa ne yayi mata yawa, and it looks like bata Shan medication din dana dauaraya akai kwanaki,”

Shuru Amar yayi yana nazari yace “but doctor wani irin damuwa ne zaisa ta samu attack haka?”

“Well thats case, abubuwa da yawa na janyo hakan, kamar yanda Nace damuwa da tunani duk suna janyo heart attack”

Dafe kanshi yayi yana tunanin dalilin rashin lapiyar nata, don yasan koda yaushe ammah bata da saka abu a ranta, tunanin maganganun da sukayi da ita yasa ya fara tunanin kodai sabodashi yake saka damuwa aranta, jikinsa ne yayi sanyi sosai, ganin haka yasa doctor cewa “she’s stable now, in few days zataji sauqi saidai ayi avoiding Duk wani abu dazai sata cikin tashin hankalin da zai haifar mata da damuwa,”shuru Amar yayi kafin yace “can I see her now?”

“Yes you can” doctor ya bashi amsa.

Atare suka wuce dakin da aka kwantar da ita shida doctor, fuskanta ya kafama idanu harta rame cikin kwanakin, saurin runtse idanunshi tayi don shi kadai yasan irin zafin da yake ji Ganin ta a cikin wannan yanayin.

Zaman kusan awa biyu yayi anan asibiti ya kasa yin komi,wayarshi ya zuba ma idanu yana kallon message din da asad ya tura mashi, “oga Akwai matsala”

Tunda ya kafa ma wayar idanu ya rasa tunanin da zaiyi, kallon ammah yayi dake barcin wahala saboda sedative da akayi mata,baya jin zai iya tafiya ya barta a wannan situation din saita tashi yaga yanayinta, hankalin shi ya gama rabuwa gida biyu, zama yayi gefe kan kujera yana tunani, already yasa driver ya maida su salima gida ita da salim saboda su wuce islamiyya.

Sallah ne kawai ya tayar dashi, karfe biyar daidai ammah ta bude idanunta, tunda ta bude idanunta take bin ko’ina da kallo, idanunta ta sauke a kan shi,

wayar hannunshi yake dubawa don haka bai lura da tashin nata ba, a hankali ta bude bakinta da ya zama pale tace “son”

Juyowa yayi da sauri ya kalleta, miqewa yayi ya tako Har inda take ya kama hannunta yace “ammah na, how are you feeling now?”

Hannunshi itama ta riqe gam ahankali

Bakinta ya soma motsawa tace “I’m fine son,tun yaushe kake zaune anan? How did I end up here??”

Rasa abun cewa yayi ya kalleta yace “ammah na, meysa kike saka damuwa aranki? Meke damunki? Dan Allah ki fada min,saboda ni kike damuwa? I can’t afford to loose you”

Ya fada idanunshi sunyi jaaa kamar wuta, jiniyoyin kanshi sun Tashi sosai, kallonshi tayi cikin so da kaunar danta, tasan he’s tough, bazai taba kuka ba but yanda yake da riko Har gwara yayi kuka, fuskanshi kadai ta kalla taga damuwa shimfide akan fuskanshi, 

“Son, don’t blame your self,girma ne kawai yazo”

Badan ya yarda ba yabar zancen saidai yayi alqawarin maida hankali akan ta don baya son abunda zai tayar mata da hankali don ita kadai ta rage mashi a duniya kuma bazaiso wani abu ya sameta ba.

Saida ya tabbatar she’s stable kuma hankalinta ya kwanta kafin ya dora ta under care of family doctor su, sallama yayi mata tare da alkawarin dawowa da daddare, bai fada mata inda zaije ba don haka ya fuce a zummar zaije gida.

Yana futa ya figi motarshi zuwa ga lokacin din da asad ya tura mashi, tun akan hanya ya shiada ma asad yana kan hanya.

Tafiyar awa biyu ta kawoshi garin fatagum cikin minti arba’in aabida irin gudun da yake, dan karamin gari ne don ko local government bashi dashi gaba da abuja don garin ma dajijjika ne sosai, da kyar ya shigo cikin garin don babu hanya mai kyau kwata kwata, map dinma tsayawa yayi saida ya kira asad kafin ya fito da motar shi ya daukeshi, daidai wani dan asibiti suka tsaya lokacin anyi sallah magrib,saida suka tsaya sukayi sallah a wani dan masallaci kafin su shige cikin asibitin,kallon mutumin dake kwance kamar gawa ya galabaita Amar yayi kafin ya maida idanunshi kan asad don neman Karin bayani. Asad na Ganin haka yace 

“Oga wannan ne yaron dake rike da wayar da mukayi tracking, kafin mu iso garin nan ayanda muka samu labari wasu mutanen wanda nake suspecting mutanen alh kabiru ne sun rigamu cin masa,inda muka samu sun kusa illatashi saboda irin dukan da sukayi mashi suka kwace wayar sannan agaban mutanen gari akayi hakan”

“What’s his condition now?“  Amar ya tambaya 

Girgiza kai asad yayi don yaron kamar bazai rayu ba, 

Gefe suka samu suka tsaya shida asad kafin yace “ta yaya yaron ya samu wayar?” Amar ya sake tambayar asad yana kallonshi

“Tambayar da muke neman ansa kenan, wanda dole shine zai bamu ansa idan min samu ya farfado”

Shuru Amar yayi don yana Ganin tunda sun samu wayar dole itama sai sun kamata don haka dole suyi taking action da wuri

“Bazaiyu mu jira saiya Tashi ba, inaso kayi buncike akan shi waye, da mutanen da yake muamala maybe ta hakan zamu samu mu san inda ya samu wayar”

“But oga, acikin kauyen nan bana tunanin Akwai mai arzkin wayar nan saidai probably ya tsinta ne” asad ya fada

“Baza muyi saurin concluding ba saimun tabbatar, don inhar anan garin yake to itama tana nan so kaga dole shine connection din da zaisa mu samu bayanin da muke nema”Amar ya fada yana kallon asad fuskanshi dauke da damuwa.

“Hopefully dai ya farfado” asad ya fada 

Futa sukayi daga wajen inda asad yasa aka fara bunciken yaran, cikin qanqanin lokaci aka gano ba a cikin garin yake ba ci rani ke kawoshi da siyayya,gwiwa a sage suka amar ya juya ya koma gida inda asad shi kuma ya tsaya anan garin.

Lokacin daya shigo abuja wajen karfe goma, saida ya Lela asibiti yaga jikin ammah, anan yayi niyar kwana wajenta sai dai taqi yarda, don mana ganinshi kasan agajiye yake don haka tace ya wuce gida ya huta zuwa gobe saiya dawo.

Tunda ya iso gida kuwa ya wuce daki direct ya zame kayan jikinshi ya wuce bathroom ya sakarma kanshi hot bath, yana fitowa ya shirya cikin pjs dinshi, nan take yunwa ta nuqurquso shi don kwata kwata baici abuncin kirki ba tun bayan breakfast da yayi.

Fitowa yayi ya tsaya gaban dining, ganin babu komi gashi dare yayi yasa ya juya zuwa dakinshi, salima dake saukowa tana hangoshi Tayi saurin saukowa kasan tace “barka da dare ya Muhammad, ya jikin ammah?”

Juyowa yayi ya kalleta, nan take amra ta fado mashi arai, don ya mance da ita saboda abubuwa dake yawo aranshi, “da sauqi” ya amsa

34 / 94