kallon yanda suke hira, salima na gefen ammah tana matsa mata kafa while salim na gefen ammah shima ya lafe a jikinta, kallonshi Amar yayi sai a lokacin ya tuna da rashin maganar salim din, nan ya fara tunanin maybe ya kurmance ne don haka ya yanke shawarar bayan komai ya lafa zai fitar dashi zuwa india don anan Nigeria an tabbatar da yana magana kawai dai he’s not ready to talk.
Daura kafarshi daya kan daya yayi ya maida idanunshi kan salima da kanta ke qasa tana matsawa ammah kafa at the same time tana mata hira, zuba mata idanu yayi sosai yana Ganin kamanni ta da yar uwarta sak, Har kammanin sun baci sosai, wani tunani ya fara yi, gaba daya he’s lost in his thoughts, ya kasa deciding komai, na farkon he’s worried about them, bayason komai ya samesu musamman yaran da ammah, don ya tabbatar Alhaji kabiru can do worst than he thinks, na biyu baisan yanda zaiyi ya kubtar dasu ba, at first yayi tunanin ya kaisu dubai saidai yasan dole
Ammah will question him dalilin kaisu da zaiyi cikin gaggawa, na biyu because of her health he’s scared, baya son tayi finding out akan aurenshi ya fison yayi komai silently tunda ya tabbatar amra batada cikin shi, na uku kuma yaronnan suma baya son saka su cikin hadari tunda Har dasu ake zaune da Alhaji kabiru a gidan, he can’t risk their life dan he has a lot for them, yasan basu da kowa ayanxu saishi da ammah, he needs to act fast”
Da wannan tunanin ammah ta waigo ta kalleshi Ganin yanda ya kafa ma salima idanu lost in his thoughts yasa ta danyi murmushi don this is not the first time tasha ganinshi yana glaring yarinyar don haka ta dauka ko son yarinyar yake, “son? Son Is everything okay?”
Dan dagowa yayi ya kalleta yace “yes ammah come again?”
Dariya tayi tace “is everything okay? Ka saka yarinya agaba da idanu” salima dai bata san me ake ciki ba don haka bata ma kawo da ita amma take ba.
Dan tabe baki yayi yace “yes ammah I’m just thinking of taking you and the kids on a vacation”
Dan shuru tayi tana nazari kafin tace “Vacation? Ay ba ayi holidays ba, koka manta yara na zuwa school”
Murmushi kawai yayi mata yace “oh!!! Yea haka fah”
Basar da zancen yayi ya miqe ya wuce dakinshi.
The next day…
Washe gari wajen karfe sha daya ya fito ya shige motarshi, saida ya biya ya dauki asad kafin su wuce kauyen fatakum don zuwa taaziyar meeda na sadakar uku.
Suna isa garin basu karasa har wajen gidan ba suka gangara da kafa, babu mutane da yawa a gaban gidan don haka suna gaggaisawa suka sa almajiri yyI
sallama da mai zogale, fitowa tayi da dan lullubinta suka gaisa, Amar ne yayi mata taaziyya kafin suyi mata sallama, bandir din dubu guda biyu Amar ya zaro ya bata yace ayi abuncin sadaka, ba karamin dadi taji ba sai a lokacin ta dan saki jiki dasu dukda tasan asad, Har sun juya zasu tafi mai zogale tace “ku dan tsaya ruwa ne akawo maku mana”
“Ah ah kaka Mun gode” asad ya bata amsa
Shuru ta danyi chan kuma tace “dan Allah inason nasan alakarku da jikata”
Ba tare da boye boye ba asad yayi mata bayanin komai, ba karamin kuka kaka tasha ba kafin tace “kaddarar ta ce yazo a haka, Allah ya yafe mata” atare suka amsa da Ameen
Juyawa tayi tace “ku dan tsaya Ina zuwa”
Suna nan tsaye ta fito da jakar meeda tace “dan Allah Zan baku wata amana, kafin jikata ta rasu ta bani wannan jakar, ta shiada min kan cewa ko bayan ranta nakai wannan jakar olis teshen, ni banma san Ina ne nan ba”
Da sauri Amar da asad suka kalli junansu kafin asad ya karba yace “ba damuwa zamu kai police station din”
“Yauwa nan tace kuwa olis tehen”
Dariya kawai asad yayi shidai Amar baice komai ba kafin suyi mata sallama, suna shiga cikin motar asad ya kalli Amar yace “I’m sure Akwai abunda ta aje a cikin jakar”
Ya fada yana kokarin bude jakar, bincika wa ya soma yi babu wani abun kirki a ciki sai kayan kwalliya su janbaki hoda da sauransu, tsaki Amar yayi ya dafe kanshi “oga!!!!”
Da sauri ya dago jin Kiran da asad yayi mashi, flash drive ne data saqala chan saqon jakar, kallon juna sukayi shida asad yace “are you thinking what I’m thinking?”
Da sauri asad yace “it’s a flash drive”
Wani irin dadi ne ya ziyarci Amar da sauri ya tafa motar suka kama hanyar zuwa gida, yaran Alhaji kabiru dake binsu kusan kullum a suna biye dasu a baya.
Suna isa office sukayi saurin wucewa office, suna shiga asad ya jawo laptop dinshi yayi connecting, gaba dayansu jikinsu Har bari yake, there are so eager to see what’s inside, danne danne asad yayi ganin file Daya a ciki tayi saving da Alhaji kabiru empire, da sauri asad ya Danna file din, nan take file din ya nuna sai an rubuta password, Amar ne ya naushi iska yace “god damn it”
Asad shima wani iri yaji hankali a tashe don basu san yanda zasu samu password dinba gashi ita data samo evidence din ta rasu, Amar dai kamar zaiyi hauka ga samu ga rashi…….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 126
Update!!
Dubai uae.....
Headquarter…
Karfe hudu daidai suka fito ita da haifa daga cikin asibiti, sanye yake da abaya baqa, sunyi anko ita da haifa don ita black abaya ne a jikinta, kallon inda m5 ke tsaye haifa Tayi kafun ta maida idanunta kan amra tace “babe ga bodyguard dinki nan tsaye”
Kallon ind a yake amra tayi kafin ta tabe baki tace “ay bakisan dadin da nake ji Allah ya kusa rabani da wannan wasifar”
Dariya haifa Tayi kafin ta kalleta “kiyi kokari ki karasa report din zuwa gobe saimu kaima head tayi signing”
Daidai inda m5 yayi parking ya tsaya kafin tace “in sha Allah yau Zan karasa ma, bye sai gobe”
Hannu haifa ta daga mata ta wuce wajen da take parking nata motar.
M5 na bude mata kofar ta shige tare da Rufuwo, kallon report din hannunta ta soma yi, ahankali wani irin murmushi ke wanzuwa akan fuskanta, she’s so excited, komai yazo karshe Alhamdulillah shekara uku da watanni, wani irin hawaye ne ke gangarowa akan fuskanta, tunawa da kannenta da lokacin data zo, ayanxu a shirye take ta karbi Duk kaddarar datazo mata.
Tana cikin tunani kala Kala suka iso gida, Har m5 yayi parking bata sani ba saida ya fito ya bude kofar ta ankare, ba tare da ta kalli inda yake ba ta fito hannunta rike da laptop dinta da handbag dinta.
Daidai entrance door ta tsaya ta Danna door bell, cikin few second Nadine ta bude mata kofa fuskanta dauke da murmushi “welcome back ma’am”
Murmushi itama amra tayi mata tace “thanks nadine”
Ciki ta shige bata tsaya ko Ina ba zai dakinta,tana shige ta watsar da komai kan gado, kafin ta soma sabule kayan jikinta, toilet ta wuce direct domin watsa ruwa, wani irin fitsari ne taji ya tunkaro ta gadan gadan, da sauri ta zauna kan wc, tana gamawa ta jawo hand spray washer, tsarki ta fara yi tana gamawa ta mike domin yin flushing, idanunta ne ya sauka kan blood stain akan toilet seat din, zaro idanu tayi tabi cinyarta da kallo, “blood!!!” Ta furta da dan karfi, mamaki ne ya cikata sosai don batayi expecting period dinta so soon ba, normal batayin tracking circle dinta don tun 1week kafin yazo zata fara jin back pain, da muscles pain saidai this time around kwata kwata bataji pain dinba, shuru tayi tana nazari, tunawa da ita da ba budurwa bace ayanxu yasa jikinta yayi sanyi, don yasan yawanci idan mace na yawan yin ciwo haka idan ta samu na namiji yana raguwa sosai wasu ma idan suka haihu gaba daya daina ciwon sukeyi saboda change of hormones.
Jiki a mace tayi wanka ta gyara jikinta tsaf kafin ta wanke inda ta bata.
Fitowa tayi daga cikin bathroom din daure da brown towel dinta, cikin walk in closet ta shiga ta jawo wata doguwar Riga mai dan kauri sosai ta saka ta fito.
Zama tayi bakin gado ta rafka uban tagumi, yunwa ne yadan fara damunta don haka ta miqe jiki a mace ta fuce daga dakin don kwana biyu tunda yayi tafiya yake dan fitowa.
Tunda ta sauko take bin ko’ina da kallo kamar this is the first time take Ganin gidan, wani irin mixed feelings yake ji aranta mai wayar fasaara, sai ayanxu take tunani ko ita wacece, arayuwa zata ce Tayi experiencing abunda bata taba zaton zatayi ba, na farko auren yarjejeniyar datayi, na biyu irin rayuwar da take yi anan, haawayen da take hana kanta ne ya soma zubowa kan fusknta, saurin gogawa tayi ta wuce kitchen.
Tana shiga kitchen ta hango Nadine gaban gas da alamu girli takeyi, kamshin abuncin Duk ya gama bade kitchen din, kallonta amra tayi tace “uhmm wannan kamshi haka”
Dariya Nadine tayi tace “ma’am favourite dinki ne a menu”
Da dan sauri amra ta karaso gabanta don Ganin abunda yake dafawa, baki tadan bude don she’s surprised “wow ya akayi kikasan pasta is my favourite”
“It’s been almost 3months zamanmu dake fah, Ay dole nasan abunda kika fi so”
Dariya amra tayi don abun ya mata dadi sosai, bata taba sanin bayan haifa Akwai wanda zai kula da ita genuinely kamar Nadine ba.
Kallonta tayi tace “thank you so much for everything nadine”
“Please don’t thank me ma’am it’s my duty”…Nadine ta bata amsa
Gaban fridge amra ta bude ta janyo wani milk drink kafin tace “na gaji yau Wallahi daman I’m so hungry”
“Ma’am kije ki zauna ki huta, yanxu Zan karasa Ay” Nadine ta fada mata tana kallonta
Juyawa tayi ta fuce fuskanta dauke da murmushi, zama tayi a parlor ta doka uban tagumi, abubuwa da yawa na yawo a kanta.
Tana nan zaune nadine ta dawo hannunta dauke da plate mai kyau sai warm bottle water, tsayawa tayi daga dan nesa tace “ma’am zakici anan ko na aje maki akan dining”
Dan dagowa amra tayi tace “aje anan zanzo naci thank you”
Aje mata nadine tayi akan dining kafin ta koma kitchen don gyarawa.
Ta dauka kusan minti biyar anan zaune kan 3 Seater tana tunani Kala Kala,jin yunwa na damunta sosai yasa ta miqe ta wuce dining ta zauna, anatse ta bude plate din kamshin abunci ya bugu hancin, runtse idanunta tayi kafin ta fara kaiwa bakinta, bataci da yawa ba tasha ruwa ta wuce sama.
Tana shiga dakin ta zauna kan gado, gaba daya ta rasa abunyi,zamanma ya isheta, janyo report dinta tayi ta soma filling inda yayi saura da bata karasa ba, tana nan zaune Har lokacin sallar magrib yayi, harta miqe zuwa bathroom tana shirin dauro alwala ta tuna bata yi sallah din haka ta sauya wani pad din ta fito.
Wayarta ta janyo ta kunna, shiga cikin messages tayi ta kurama wajen kallo kamar mai jiran saqo, idanunta ne ya sauka kan number wannan saurayin dake mata message wanda tayi mashi saving da friend don ko sunanshi bata sani ba, yau kusan sati guda kenan rabon da ya tura mata message tun haduwar a hanyar masid dake cikin headquarters,tabe baki tayi ta fita daga messages dinshi ta shiga contact, nanma idanu ta zuba ma number last caller, tasan number shi don tsaf ta Kara ce number akanta, tsaki ta danyi ta fita daga number nashi tayi dialing na haifa, ringing wayan yayi kafin ya shiga number busy, ganin haka yasa ta aje wayan a gefe kawai ta jawo report dinta, after an hour saiga call din haifa, janyo wayar tayi ta dauka muryarta chan kasa tace “babe soyayya ya rufe maki ido,sai yanxu kuka gama?”
Dariya haifa Tayi tace “sorry babe, Wallahi Hammam yana acting kamar wani baby, Wai he’s having fever shine yake ta min shagwaba ya hanani picking call dinki, sorry for not picking”
Dan shuru amra tayi kafin tace “don’t be sorry babezz, kinga Har nama manta dalilin Kiran danayi maki, I was feeling down ne dazun shiyasa”
“Kin gama report din?” Haifa ta tambayeta
“Almost,” amra ta amsa ta
Shuru ne yadan ratsa tsakaninsu kafin amra tace “babe ya zanyi? He called yesterday kuma baice min komai ba? Kinga sauran mu 1 week kawai”
Sauraronta haifa Tayi kafin In a calming way tace “babe calm down, Ki kirashi anjima nasan it’s midnight achan,saiki mashi bayani”
“Babe maysa Saina mashi magana?” Amra ta fada Adan hasale
“Idan baki mashi magana ba zaki zauna a haka kuwa, nifa gani nake kamar mutumin nan dinki yake”
Azafafe amra tace “babu so tsakanina dashi, bai taba sona ba ko sai daya, after all yarjejeniya ya hadamu kuma ita zata rabamu Ina sha Allah, ni yanxu Duk abunda ya shafesa bana don jin shi” ta karashe tare da sauke ijiyar zuciya kamar wadda tayi gudu,murmushi kawai haifa Tayi tace “sounds like you’re upset, kodai kema kina….”haifa ta fada cikin zolaya
Da sauri amra ta katse ta ta hanyar cewa “babe stop it please, karki ma taba yin tunanin wannan, I can never give my heart to someone that cause me so much pain”
Dariya ce ta kubcema haifa saida tayi mai isarsa kafin tace “sorry mrs general”
Azafafe amra ta kashe wayar tare da jefar da ita gefe.
Shifa mai hakuri bai iya fushi ba kwata kwata, tana da hakuri sosai saidai bata kaunar wulaqanci wanda ta sha a gidan uncle ma ya isheta, don tun bayan rasuwar iyayensu take Ganin wulaqanci Har izuwa yanxu, ya kaita bango sosai to the extent that bata jin zata taba son hada hanya dashi bayan sun rabu, fatanta dai su rabu lafiya ta samu ta koma wajen Yan uwanta.
Report din dake gabanta ma ture shi tayi gefe ta kwanta, runtse idanunta tayi tunani Kala Kala
Na mata yawo akanta musamman na shawarar da haifa ta bata akan ta kirashi, why zata kirashi, saboda menene zata kirashi ta tambayi kanta, zuciyarta ce ta bata amsa “idan baki kirashi ba haka zakiyi ta zama Har sai lokacin dayaga dama ya dawo”
Da dan karfi ta bude idanunta tace “no bazan zauna ba, menene amfanin zaman?”
Janyo wayarta tayi ta bude, number shi ta shiga ba tare da tunanin komai ba ta soma dialing, Har wayar ya tsinke bai daga ba, wulla wayar tayi chan gefe don babu abunda yazo ranta sai maybe yana Ganin call din nata bazai dauka ba, wani irin tukunya baqin ciki ne ya tsayar mata daya sata hawaye Har barci ya kwasheta.
Abuja…
Lokacin da amra ta kirashi yaje masallaci don lokacin sallar asba ne, bai fita da wayarba don haka yana dawowa ya tube jallabiyan shi yabi lafiyar gado don kwana biyu baya samun barci saboda abubuwan da suke gabanshi, cikin kwanakin nan hankalinshi a tashe yake Dukda daddy baya gidan, shi ba tsoron shi yake ba saidai yana tsoron abunda zai iyayi,kwanciya yayi tare da tun da ciki yana nazari, kanshi ya gama daukan zafi, daga ranar daya sa abu Aranshi baya taba samun sukuni sai ya kawo karshen abun, wayarshi ya jawo don yasata a silence saboda ya samu yayi barci don kiraye
Kirayenda ake mashi cikin kwanakin sunyi yawa,idanunshi ne ya sauka kan missed call akan screen din wayar, duban time din call din yayi 5:10 Ganin haka yasa ya bude wayar ya shiga wajen recent call, idanunshi karau ya Sauk kan call din nata, he was so surprised, cikin hanzari yayi dialing number nata, amra da barcin wahala ya dauketa tayi saurin bude idanunta jin karar wayarta agefen kunnenta,
Da kyar ta bude idanunta Ganin number shi, saurin picking tayi tana kokarin gyara natsuwarta don ta dan tsorata da Kiran, “assala alaikum” ta mashi sallama cikin zazzaqar muryarta.
Saida ya dauka wajen minti biyu kafin yadan nunfasa “Wa alaikum salam” ya amsa mata cikin natsuwa da muryarshi mai dadin sauraro
Shuru ne yadan ratsa tsakanin su, jin shurun yayi yawa yasa yace “why did you call at this hour?”
Yanda ya fada so calmly yasa ta danji sauqin bugun da zuciyarta keyi, tayi mamakin yanda yake magana calmly saidai tunawa da bakinshi yasa ta kama kanta don yanxu zaka jishi soft anjima Ka jishi harsh, “Ina wuni?” Ta tambayeshi
“It’s morning over here” ya bata amsa, dan tabe baki tayi kamar bazata sake magana ba tace “good morning”
Rufe idanunshi yayi kmar mai jin barci ya gyara zaman wayar a kunnenshi yace “morning…..”
Rasa abun cewa tayi saida taji yayi Gyaran murya alamun baya son jira yasa tace “uhm daman gobe zanyi submitting report dina,”
Shuru ta danyi ta sauke shi yar zuciya, shima baice Kala ba saidai yana sauraronta,
Muryarshi ne ya katse mata tunanin data Somayi akan abunda ta fada, don saida ta fada take regretting fada mashi, why zatayi mashi wani dogon explanation kawai tace ya saketa, zuciyar ce ta haneta da gangancin abunda yake shirin yi “uhmmm so???” Ya katse mata tunanin nata.
Ahankali ta rage muryarta cikin lallami tace “shine daman Nace this Friday zamuyi signing out, and inason Zan koma gida”
“Wani gidan? Nan inda kike daji ne?” Tambayarshi ta katseta,
Hawaye ne ya soma fitowa daga fiskanta ta kasa cewa komai
Jin haka yasa ya katse wayar ya wullata gefe ya gyara kwanciyar shi rai abace ba tare da yasan dalilin ba, shi Duk wannan abun da take tana wasting time dinta ne kawai ta kasa fuskantar shi mutun ne idan yace ga abunda za ayi shi za ayi,baya chanza magana.
Da haka Har barci ya kwashesa.
Washe gari da safe ya fito cikin jallabiyanshi fara sol, direct dining ya wuce Ganin ammah a zaune, kallonshi tayi taga ya dan rame, tausayin shi ne ya gama yawo a cikin ranta, Har lokacin tunaninta baya kaiga