Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   81 / 94

240K to 243K   out of 279.4K words

tayi mashi kafin ya fuce ya barsu suna kukan murna…

Kallon babies sun Aman yayi yace “ammah naga suna kama dake”

Dariya sukayi gaba dayansu inda ammah ta kalli babies sun for the countless times tace “gaba dayansu babu wanda yake kama dani, wannan ubansu suka dauko gaba Dayan su, kaga nan” ta fada tana nuna mashi wani dan mole din kumatunsu su duka don identical triplets ne, “kaga wannan mole din, irin na

babansu ne sal hancinsu irin na mamansu skin dinsu irin na babansu, kai ni I’m jealous ma, gaba daya mazajen Nawa basu dauko mamansu da yawa ba”

Dariya sukayi gaba dayansu daga ammah Har amra dake dan cije lebe don Har lokacin tana dan jin zafi a wajen donma basu yi mata stitches ba.

Nnamdi ezikiwe international airport abuja…..

Karfe biyar daidai na asuba sukayi landing a international airport din abuja, 

Sir general Amar taura…

Ahankali ya fara saukowa daga cikin jet dinshi Sanye yake da kakin sa na sojoji, yana saukowa ya shakur iskan Allah, garin yayi dan duhu don gari bai gama wayewa ba, ahankali yake tafiya majestically Duk da agajiye yake, cikin motar da aka tanadar masa anan airport ya shige nan driver ya jaa shi sai gida.

Tunda yayi relaxing bayanshi a cikin motar ya lumshe idanunshi, as he promised ammah suna gama operation zai dawo gida, hakan kuwa ta kasan don suna gamawa baima koma uae ba ya taho airport ya shige jet dinshi.

 Ya rame sosai wanda dalilin harbinshi da akayi a kafada wajen operation din.

Parking din da driver yayi ne yasa shi dawowa daga tunani daya tsunduma, bude idanunshi ya fara yi ahankli nan take gabanshi ya fadi babu dalili, ciwon dake cinshi a zuciya yana dannewa ya dawo sabo tunawa da yayi da ita, fadin irin kewarta da yayi cikin watannin nan bata lokaci ne, da ita yake kwana da ita yake Tashi kullum, 

Driver ne ya bude mashi kofa don haka ya saqalo kafafunshi ya fito, yana fitowa yace “thanks” tare da wucewa cikin gidan don gari ya soma haske, yana karasawa wajen entrance baima tsaya knocking ba ya Danna pins ya bude kofar ya shige ciki, futilun kasan Duk a kashe suke don haka ya tabbatar mashi da basu Tashi ba, daman abunda yake so kenan shiyasa he wanted to surprise them, yana nan tsaye yana karema parlor kallon maid ta fito daga kitchen hannunta rike da mopper, tana karasowa inda yake dukda bata sanshi ba tace “good morning sir”

“Morning” ya amsata kai tsaye kafun ya wuce bedroom dinshi, yana shiga ya watsar ruwa yayi salla yabi lafiyar gado.

Su salima Ana ta shaka barci wajen karfe goma tana Tashi bayan tayi wanka dakin ammah ta fara wucewa donta gaisheta tana zuwa taga wayam don haka ta futo ta wuce na amra nan ma wayam, hankalinta ne ya dan Tashi don haka ta sauko kasa, nan ta tadda maid tana shirya dining “cinty ammah bata nan ne?”

“Yes ma,“

“Sir Aman fah?”

“Shima bai fito ba sai dai wani daya shugo daxu da safe” maid ta fada 

“Wani kuma? Waye wani?” Salima ta tambayeta

“Wannan part din ya shige” maid ta fada tana mata nuni da part sun amar, tana Ganin haka ta gane amar take nufi, wani irin dadi ne ya ziyarceta don haka tace “laa ya amar ya dawo,Toh ina su ammah suka tafi kenan”

Bata gama tunanin ba saiga horn din motar su aman, cikin sauri salima ta fuce zuwa tsakar gida, tana tsayuwar aman na parking, cikin sauri ta karaso “yaa…yaa”

Saurin guntse bakinta tayi Ganin ammah ta fito hannunta rike da babies guda biyu, bata gama mamaki ba saiga amra ta fito da baby daya a hannunta, jikinta ne ya soma bari “ammah….. baby???? Babyn adda???”

Wata uwar kara salima ta buga ta rungume amra tare da karban babyn hannunta nan take ta soma hawaye, ganin amra zata gaji a tsaye yasa ammah cewa “yarinyar kirki muje ciki ta huta”

“Ammah I’m so happy ya Allah adda wannan babies dinki be wayyo Allah na”

Cikin gidan suka wuce gaba dayansu inda ammah tace su taci sama gaba dayansu, wucewa sukayi nan aman ya wuce bedroom dinshi shima.

Suna hawa sama salima ta amshi sauran babiea din, fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne “Alhamdulillah double celebration ammah, ya amar ma ya dawo”

Da sauri ammah ta kalleta “yaushe ya dawo,”

“Maid tace da asuba ya shugo yana bedroom dinshi”

Murmushi ammah tayi tana hamdala kafin ta kalli amra data Sunkuyar da kanta, gaba daya mood dinta ya sauya “Alhamdulillah lallai we have double celebration kam, yanxu daughter ki kwnata ki huta ko,”

“Tohm ammah”

Kallon salima ammah tayi tace “yarinyar kirki daukan min baby wannan mijin Nawa ni bari na rike amaryar dada da Dayan mijin nawa, mu bata wuri ta samu ta dan runtsa “

Mikewa sukayi atare suka bar amra ta kwanta nan take barci ya kwashe ta.

Suna fitowa ammah ta kalli salima, “muje kasa,”

Cikin zumudi salima tace “ya… Muhammad”

“Shii” ammah tayi amra nuni kan tayi shuru, ahankali suka fara saukowa kasa suna saukowa suka wuce bedroom dinshi direct, ko Ina a kashe sai karar ac daya kunna, dakinshi suka wuce direct inda salima taso yin sallama nan ammah ta ce mata tayi shuru har suka karasa bakin gadonsa yana nan kwance cikin duvet ya rufe jikinshi sai fuskansa dake a bayyane, wani irin dadi ne ya ziyarci ammah yau ga Muhammad ga yayan Muhammad, suna karasowa gaban gadon ammah ta zauna a gefenshi har lokacin baby no 1 da baby no 2 na hannunta while salima na rike da baby no 3.

Hannu ammah ta dan saka ta shafa fuskanshi tana murmushi, dan juyawa yayi kamar zai farka don barcin yayi nisa sosai, “son!!!”

Kamar daga sama yaji voice din ammah. Ahankali ya soma bude idanunshi, da kyakyawar fuskar ammah yaci karo da yake hawayen farin ciki tana murmushi, saurin mikewa yayi yana kokarin goge idanunshi da sukayi jaa alamun barci bai sakeshi ba “son….” Ammah ta sake fada

Dan dagowa yayi don baima Lura da abubuwan dake hannunta ba sai fuskanta daya kafe da idanu yana Ganin hawayenta 

Hannunta biyu ta daga ta Dora mashi su duka akan laps dinshi, da sauri ya waigo ya sauke idanunshi akan……..

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 148

Update 

Unedited page

Hannunta biyu ta daga ta Dora mashi su duka akan laps dinshi, ahankali ya waigo ya sauke idanunshi akan kyawawan babies din guda biyu da suke kama dashi kamar an tsaga kara, shuru yayi ya kafa masu idanu kwakwalwanshi ta kasa processing, babu abun da ammah keyi sai murmushi taba hawayen farin ciki, salima na Ganin haka ta ajiye baby no3 a gefen Yan uwansa,kafin ta fuce daga dakin, yanda yaran suke a jere a kan laps dinshi ya kafa ma idanu ya kasa dauke idanun nashi, baby girl na tsakiya an nade ta da pink towel, sauran mazan ma an daure su da blue towel.

“Ammah Ina kuka samu babies haka” ya tambayeta yana kallon yaron har lokacin ya kasa dauke idanunshi akan su, 

“Dawa suke yi maka kama?” Ta jefa mashi tambaya, Har lokacin idanunshi na kan yaran bai dauke ba,kanshi ya gama kullewa don yaron kamar cabon copy dinshi, kamannin sun baci sosai, babu zato babu tsammani yaji furucin ammah“yayanka ne”

Da mamaki ya dago yana kallon ammah, fuskanshi dauke son jin qarin bayani, Har lokacin ita yake kallo fuskantarta “son Allah ya azurtaka da matarka da triplet, yayan Ka ne, kuma jininka”

Bin Bakinta ya dunga yi da idanu don lokaci guda yaji kamar an toshe mashi qwaqwalwa,

“Yes son yayanka ne jininka, Ka tafi Ka bar Aisha da cikinka na tsawon wata shida a jikinta, kaga ikon Allah ko? Duk wannan futar da kaga munayi Har kake complain asibiti muke zuwa,”

Dip taga kamar baya fidda nunfashi, saida ta dan dafashi tana hawaye, “son Allah ya nuna mana ikon sa, Allah ya rubuta zaka ga jininka anan duniya, babu

ruwan allah da wani zancen likitoci idan har ya kaddara kana da rabo a duniya to zai baka alokacin da baka taba tsammani ba”

Duk wannan maganganun da ammah keyi kasa cewa komai yayi har jikinshi ya soma bari, abun mamaki saiga hawaye na saukowa akan fuskanshi, general guda yana hawaye, ammah na hawaye shima yana hawaye yana kallonta yana kallon babies din.

Kallon hannunshi ammah tayi dake karkarwa yana son taba su ya kasa gaba daya shock din daya shiga bai taba shiga irin shi, kanshi ya kasa daukan abunda ammah ke fada mashi, waennan yayanshi ne? Tabbas ko ba a fada mashi yaga kammaninshi a fuskokinsu, kamar an dauki fuskanshi an saka masu dukda suna jarirai, wani ikon Allah kenan, don gaba dayansu replica dinshi ne,

Yau ne tana ta biyu a duniya da ammah ta ga hawayen shi, don ya kasance mutun mai taurin zuciya, saidai wannan ya taba shi sosai,abunda baka taba expecting ba, abunda Ka cire rai dashi sai gashi allah ya baka lokaci guda babu zato babu tsammani.

Bude bakinshi tayi da kyar voice dinshi na cracking ya soma magana kamar zai shine “Am…mah am…””

Kasa karasa abunda yake don fada yayi hawaye na zarya a fuskanshi, hannunshi na karkarwa kamar mazari, ammah na Ganin haka ta mike tsaye ta dauka baby number 1 da idanunshi ke bude tarr yana lasar baki alamun yana son abunci, sauran biyun kuwa barcin su suke yi.

Tana daukan babyn ta Dora mashi babyn a hannunshi, saida ta taimaka mashi ta talla be babyn don Har lokacin hannunshi karkarwa yake, he can’t believe it abun kamar a mafarki, saida ammah ta daura mashi babyn a hannunshi ya tabbatar da gaske ne kuma jaririne a hannunshi, 

 Kallon jaririn ya dunga yi yana hawaye har lokacin bazaka taba tantance yanayin da yake ciki ba da facial expressions dinshi, hannunshi daya ammah ta dago ta Dora akan kirjin babyn, yana jin heart beat din yaron yayi saurin runtse idanunshi sai a lokacin ya samu kuzarin bude baki ya soma magana “Allahu akbar, Allahu akbar Allahu akbar,”

Yana hawaye yana kabbara, yana Kiran Allah, “ammah I’m I dreaming? Please don’t wake me up,”

“Ba mafarki kake ba son,” ammah ta fada tana hawaye tana mashi murmushi, kallon babyn yayi ya dagoshi zuwa kirjinshi, ya kwantar dashi, yana kwantar dashi wasu hawayen na sauka a fuskanshi, “Alhamdulillah!!!! Allah na gode maka Allah na gode maka”

Haka ya dunga furtawa, kallons inda ammah ke tsaye yayi, “ammah gashi rikemin haka inason nayi sujudu shukr,”

Karban babyn ammah tayi ta kwantar dashi gefe kafin ta dauke sauran suka ta kwantar dasu, tana kwantar dasu yayi saurin mikewa ya sauko kasa ya fuskanshi kibla, ya dade a kanshi a kasa yana godiya ga Allah kafun ya dago ya daga

hannunshi yana hawaye, jikinshi na bari kamar wanda ke jin zazzabi,kana ganinshi kasan yana cikin wani emotional moment.

Mikewa yayi cikin sauri ya tsaya bakin gado ya dan rankwafo ya zuba masu idanu, kamar wani zautacce haka ya soma dariya yana kallonsu,

Hannunshi daya ya sanya ya fara taba cute hannayensu daya bayan daya, ammah dai na daga tsaye a gefe ta rike Bakinta tana hawaye, 

Juyowa yayi a zafafe ya kalli inda ammah ke tsaye yace “ammah yarana? Yarana ne? Yayana ne ya Allah” ya karashe yana kama kanshi, fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne,this is the best day of his entire life, abunda bai taba tsammani ba kwata kwata, yanxu waennan jininshi ne yayanshi ne? Allah daya tashi bashi saiya bashi uku lokaci guda lokacin daya cire rai gaba daya ya fidda ran samu Har karshen nunfashinsa, 

“Yes son yayanka ne su duka naka ne”

Daga kanshi yayi sama kamar zaiyi ihu yace “ya Allah I’m a father, ammah I’m a father nine babansu,  ya Allah…”

Haka ya dunga maimaitawa yana kallonsu yana daga hannunshi sama, gaba daya ya gama zaucewa kamar ba Amar ba,

Ganin haka yasa ammah dake ta faman murmushi ta janyo hannunshi ta zauna dashi tace “wannan farin cikin karyasa Ka fadi fah,”

“Ammah bazan fadi ba, I’m a hero”

“Yea you are my son, and I’m so proud of you son, kayi tawakkali saiga shi Allah ya dubeka”

“Ammah Zan iya daukansu” Amar ya tambayeta kamar wani yaro yana murmushin da nan taba ganin irinshi ba akan fuskanshi,

“Kaida yayanka saika tambayeni son?” Ammah ta fada tana kokarin daukan yar jaririyar, tana dauka ta ya mike tsaye, “ka zauna son”

“Toh Tohm bari na zauna,” ya karashe yana zama cikin zumudi at the same time yana kallon sauran yaran.

Yana zama ammah ta ajiye mashi jaririyar a hannunshi, tana daurata kuwa ta bude idanunta tarr, “ammah wannan ma baby na ce?”

“Yes son Duk naka ne, baby girl ce wannan”

Maido da idanunshi yayi kanta, yana kallonta hawaye na sauka akan idanunshi baima san yanayi ba, 

Saurin rungume babyn yayi a kirjinshi, wani irin sanyi na zagaye gaba daya sassan jikinsa.

Ammah na murmushi tana kallonshi tana godiya ga Allah.

Zama dai Amar kasa zama yayi haka ya mike yana zagaye dakin da babyn a hannunshi, saida ammah ta dauki gaba dayansu ta dunga bashi daya bayan daya, yanda yake karban yaran daga hannunta ma with so much affection saida yasa ammah hawaye, da kyar ammah ta samu ya zauna Har lokacin babies din na hannunshi mazan while macen na hannun ammah, sun dauk awa guda suna abu

daya shida ammah, minti kadan zai dago yace “ammah yara ne? Jin I’m a father”

Haka zata amsa shi itama “yes son you’re a father, and you’ll be the best father to them”

Tana kaiwa karshe zai girgiza kai ya soma kissing dinsu ta ko’ina Har lokacin yana hawaye, 

Shuru ya danyi yana nazari kafun ya ajiye babies din kan gadonshi a hankali, yana ajiyesu ya sake karban na hannun ammah, ammah dai yau taga ikon Allah don ko minti biyu batayi da daukansu zai amshe, yanxu ma haka ma cewa yayi “ammah kawo ta,”

Ammah na murmushi ta miqa mashi babyn “careful ammah,” ya fada yana murmushi.

   Zama ammah tayi gefenshi bayan ta bashi jaririyar,tana zama ta kamo hannunshi daya ta rike tana kukan murna “I’m so sorry ban fada maganar pregnancy din ba son, nayi hakan ne saboda Ina son nayi surprising dinka daga baya kuma naga yanda kake treating mahaifiyarsu wanda yasa nayi tunanin gwara na bari sai kunyi settling kanku kafin na shaida maka” tana kaiwa nan ta girgiza mashi kai tana hawaye, 

Saurin kallon inda take yayi ya cire hannunshi daga nata ya maidashi kan fuskanta ya soma goge mata hawayen kan fuskanta, “ammah na, today is the most beautiful and amazing day of my life, this is the best gift of my life, bansan da wani irin baki Zan gode maki ba yanda kika kawo mun su, thank you ammah na thank you!!!”

“No son bani zaka yima godiya ba, aisha zaka yi ma godiya, ita ta haifa maka waennan angels din” Nunfasawa ammah tayi tana hawaye ta cigaba “Aisha ta gama yi mana komai a duniyar nan, having her in your life shine the best thing that has ever happen to you Muhammad, itace ta baka wannan farin cikin da babu wanda zai taba baka irin shi”

Sunkuyar da kanshi yayi yana jin takaicin kanshi da yanda yayi treating dinta, yanxu da wani ido zai kalleta kenan, ashe abubuwan da ya dunga yi mata tana shanyewa a wannan lokacin da cikin shi a jikinta, wani irin haushi da takaicin kanshi yake ji sosai, a zuciyarshi babu abunda yake nanatawa sai “I’ve messed up”

“Son” ammah ta kirashi, ahanakli ya soma dago kanshi idanunshi tayi jaa sosai, “kaga abunda nake fada maka ko? Daka rabu da ita da shikenan Ka rasa kenan gaba daya, what you’re feeling now is nothing compare to how you will feel idan da Ka  sake ta kuma Ka gano tana da cikinka, shiyasa nake na haneka da sakinta kuma na dunga nanata maka karka zo kayi dana sani, you keep on pushing her kamar ba matarka ta sunna ba, now kalla” ta karashe tana pointing triplets, “kalla abunda ta haifa maka”

Sauke kanshi ya sakeyi kasa, jikinshi yayi sanyi sosai, inda za a bude zuciyarshi a take babu abunda za a gani sai sunan aisha.

Shuru ne ya biyo bya kafun ammah tace “naka tuna munyi fushi dakai, bani jikoki na” tana kaiwa nan ta amshe baby girl, tana karban ta ta dauki baby boy, kafin ta nufi hanyar futa “ammah please ki bar min su anan”

“Inna bar maka su zaka basu Nono ne?” Ammah ta tambayeshi, saurin girgiza kanshi yayi alamun ah ah, “Zan turo salima ta daukan min mijina yanxu”

Tana kaiwa nan ta fuce, tana futa ya mike ya hau kan gado ya zauna gefen Dayan babyn daketa barci abunshi, yar mici micin hannun babyn ya dauka yana kallon fuskan babyn “ my look alike, open your and I’m your daddy”

Haka ya dunga ma babyn sambatu shi kadai Har salima tayi sallama, tana shugowa ta kafa mashi idanu tana kallonshi tana murmushi,shi baima san ta shigo ba saida tace “ya Muhammad ammah tace a kawo baby”

Kallonta Amar yayi kafin yace “kin iya dauka ne?”

“Laa na iya mana yaya” ta bashi amsa

“No jeki kawai Zan kawo shi da kaina “yana kaiwa nan ya maida kallonshi ga babyn yana sumbatar kumatu shi, salima dai yau taga sabon ya muhammd don wannan dai ba ya muhammad din data sani bane, tana shirin futa ya katseta “bude bedside drawer nan ki dauka abunda ke ciki duka wannan tukwicin ki ne”

Cikin sauri salima ta karasa inda yace taje, tana zuwa ta bude bedside drawer, 100 dollars ne wrapped biyu, saurin zaro idanu tayi waje tace “yaya dolars ne fah”

“Yes duka naki ne, tukwaicin kawomin baby da kikayi”

“Yaya sunyi yawa….”

Bata gama fada ba ya daga mata hannu don haka ta dauki wrapper

81 / 94