dagowa yayi ya kalleta fuskanshi babu yabo ba fallasa yace ‘’thanks’’
Juyawa tayi ta koma kitchen ta dafa simple abunci, coucous da beef sauce, agurguje ta gama ta zuba cikin warmers masu kyau ta saka a basket ta hada dasu plate da serving spoon da bottle water ta fito dashi parlor ta zauna ta doka uban tagumi, after about 30mins sai gashi ya futo daga dakin, ya shirya cikin riga da wando English wears na brand din nike, kayan sunyi mashi kyau sosai, anyways shi komai ma kyauyake mashi, fuskanshi yadan fada kadan, takowa yayi har inda take zaune ba tareda ya kalleta bay ace ‘’muje’’
Mikewa tayi tsaye ta gyara zaman hijab dinta ta dauki basket din tabi bayanshi don harya fuce daga parlor ya shige cikin motar.
Suna isowa asibitin dakin ammah suka wuce, yana gaba amra na biye dashi abaya basu kaiga karasawa bay a dan tsaya, yana duban wayanshi, itama tsayawa tayi daga bayanshi ganin hakan yasashi juyowa yace ‘’go in first’’ yana kaiwa nan ya juya domin picking call din daya shugo wayarshi, shigewa ciki
tayi bakinta dauke da sallama, gaba dayansu suna zaune kan kujeran visitors, salim na gefen aman yana barci while salima na zaune gefen gadon ammah tana kallonta,
Juyowa duka sukayi atare suka kalleta, da sauri salima ta miqe ta karbi basket din hannun nata tace ‘’adda har kun dawo’’
Kaarsowa amra tayi bakin gadon muryanta chan kasa tace ‘’ya jikin ammah’’
‘’Alhamdullah’’ salima ta amsata kafin ta gaisheda aman dake zaune a gefe shima.
Abuncin salima tayi serving aman da salim don basuci komai bag aba dayansu, suna cikin cin abuncin saiga amar ya shugo da sallama, gaishesa su salima sukayi kafin ya wuce gaban gadon ammah, kallonta yayi kafin ya maido da dubanshi kana man yace ‘’any update’’
Aje plate din dake hannunshi yayi ya kalli amar yace ‘’no amma doctor ya shigo dazu ya duba heart rate dinta da pulse dinta yace komai yana daidai tuwa, kuma zata iya tashi anytime’’
Amar baice komai bay a zauna gefen gadon nata ya kafa mata idanu tare da riko hannunta, kallonshi amra tayi don tana daga dayan gefen gadon tace ‘’yaya a zuba maka abunci’’
Dan dagowa yayi ya mata kallo daya fuskanshi na nan yanda take bazaka taba tantance ta ba kafin ya kauda kasnhi gefe yace ‘’no thanks bana buqata’’
Sauke kanta tayi kasa bata kuma cewa komai ba.
Suna nan zaune har aka kira sallan la’asar, futowa mazan sukayi suka wuce masjid while matan sukayi alwala anan dakin ammah suka yi sallah akan carpet,
Basu dade da idarwa ba saiga su aman sun dawo gaba dayansu,zama sukayi gaba dayansu jugum har doctor ya sake dawowa ya duba ammah.
Karfe tara daidai duk suna zaune suna saka ran tashin ammah, kallon amar aman yayi yace ‘’kuje zan zauna da ita yau’’
Dagowa amar yayi zaiyi Magana salima tace ‘’nima zan zauna yaya, ku tafi da adda’’
Shuru amar yayi kafin yace ‘’okay’’
Karfe goma daidai suka fito, amra da aman da salim, cikin mota suka wuce gaba dayansu kafin aman yaja motar.
Suna isa gida kowa ya wuce bangarenshi, haka suka kwana sukuku kowa da abunda ke yawo a zuciyarshi.
Achan asubiti suna tafiya aman ya kalli salima yace’’maysa baki bisu ba’’
‘’inaso na zauna ne’’ ta bashi amsa, tabe baki kawai yayi ya zauna kan kujera ya lumshe idanunshi, daga nan zaune barci ya daukeshi, mikewa salima tayi ta bude locker na patients da ake blankets da sauran abubuwan amfani, blanket din ta janyo ta rufe closet din kafin ta karaso inda yake zaune, blanke din ta rufa mashi a jikinshi kafin ta kafa mashi idanun ganin yanda yake barci peacefully
ba tare da yasan ya dauke shi ba, ‘’I missed you, allah ya bama ammah lafiya mu koma gida cikin farin ciki kamar da, I have so much to tell you,’’
Ba tareda ya bude idanunshi bay ace ‘’you can tell me now’’
Da mamaki ta miqe tsaye donta dauka yayi barci
‘’what o you want to tell me?’’ ya sake tambayarta
Gynguni ta soma yi kafin ta kauda kanta gefe tace ‘’nothing’’
Tana kaiwa nan ta koma bakin gadon ammah ta zauna, yana ganin haka ya maida idanunshi ya rufe.
After 2days, haka kullum suke yin switching, yau idan su aman sun kwana gobe su amra su kwana, gaba dayan su sun damu da ammah sosai cikin kwanakin, dukda likita ya shaida masu cewa shes out of coma zata tashi anytime.
Daga 2 days haka kwanaki suka dunga jaa har zuwa sati guda babu abunda ya chanza, a wannan lokacin asad y agama buncike gaba daya akan lantana da abubuwan daya samu daga wajnta don tayi confessing, tunda ya kira amar ya shaida mashi ya kamata yazo yaji komai nan ya fada mashi cewa su riketa kawai kar a shigar da ita kara, saboda bashi da time yanxu, yanxu time dinshi da tunaninshi duk yana wajen ammah, don haka ya tsaida komai akan saita farfado kafin ya ji daga wajen asad akan buncikenan nashi.
Lantana dai tana kulle a wajen headquters din sojoji, bata tsaya yi masu gardama ba lokacin da suka fara interrogating dinta don sun shaida mata zasu ci ubanta idan bata fada masu komai ba, ganin yanda suka hayayyako mata zasu iya kasheta yasa ta yarda ta fara masu bayani.
‘’mene alaqarki da alhaji kabiru’’ asad ya tambayeta
‘’aiki nake yi mashi’’ ta bashi amsa
‘’wani irin aiki kenan’’ ya sake tambayarta
‘’sunana lantana achan kauye, ni haifafiyar kauyen masari ce, neman nakai ne ya kawo ni burni saboda wulaqanci danake fuskanta a kauye saboda cikin shege danayi harna haife dana na barshi a wajen babata achan kauye, lokacin dana dawo nan birni na kama haya na fara sana’ar cigari da goro da safe zuwa rana, da daddare kuma ina saida tuwo a bakin layi, akwai wata rana bazan manta ba na fito kan titi ina kuka saboda kirana da kawuna yayi kan cewa dana da mahiafiyata suna aisbiti basu da lafiya babu kudin magani, inda babata take fama da cutar daji shi kuma dana baya samun ishashe abuncin kirki saboda rayuwar kauye kafarshi ta shanye, ina kuka akan titi ina kokarin na sayar da goro ko zan tattara abunda na tara nakai a masu magani, nan allah ya hadani da alhaji, ya tsaya sayen goro,yana tsayawa ya sayi goron, ganin ina kuka ya tambayeni dalili nan na shaida mashi komi inda nake fada mashi kudinake mena, nan take yace zan iyayin komai don na samu kudi, nan na shaida mashi zan iya, ba tareda da tunani komai ba yace koda kisa ne, nan nashi mashi zanyi saboda bana cikin hayyacina kwata kwata,nan take yace na shiga motarshi, ina shiga kuwa ya kaini har gidanshi, anan cikin motar yace min zan zauna a gidan a matsayin yar aiki, zan dunga fada mashi duk abunda ke faruwa a gidan, in
exchange zai biyamin kudin maganin uwata da dana, nan take na amince muka shiga gidan hajiya, nan ya mata bayanin komai, ba tareda hajiya ta musa ba ta amince harna fara mashi aiki, acikin kwanakin kawu nay a kirashi ay shaida min wani alhaji yazo ya biya komai na maganin uwata da dana harda abunci ya saya masu wanda zaikai masu shekara guda, alokacin naji dadi sosai inda na samu alhaji nayi mashi godiya sosai na sake tabbatar mashi da zanyi mashi duk abunda yake so,
Har shekara daya ta wuce banji daga bakin alahaji ba akan abunda zanyi mashi, shekara ta wuce har muka shiga shekara ta biyu inda sabo ya shiga tsakanina da hajiya sosai, hajiya uwar marayu ce, tayi min gata sosai dukda batasan daga inda na fito ba, ta bani ci ta bani sha ta barni na yagi arziki daga jikinta, rana daya alhaji yazo har dakina ya sameni yace aikina ya kusa faraway, nan ya bani wata kwaya yace insan yanda zanyi in dunga sakama hajiya a cikin abunsha, inajin haka nasan so yake ya illatata, da farko daga tambayeshi dalili nan take ya shaken yace idan har nayi mashi gardama ko nayi kokarin bata mashi plans dinshi zai kashe min uwata da kanina harma dani, hankalina ya tashi sosai inda nace mashi zanyi ba tare da gardama ba, nan take ya shaida min duk wata zan dunga ballan kwayar rabi ina saka mata a cikin abunsha, sannan idan yakare zai karo min wasu, haka ya bani na wata biyar kuda shida guda uku Kenan, watan farko babu wata fargaba na samu hanyar saka ma hajiya a cikin abun sha wanda take yawan shansa kusan kullum, haka na dage da hada mata wannan abun ina saka mata duk wata har wata shida ya gifta, abunda na fuskanta a cikin wannan lokacin shine tunda na fara sakama hajiya wannan abun ta fara kananun rashin lafiya ahankali ahankali har shakru suka shude wajen shekara bakwai Kenan da zamana a gidan duk bayan watanni idan maganin yak are haka zai kawo min wasu har takaiga wata rana ta hajiya fadi zuciyarta ta samu heart attack, alokacin hankalina ya tashi sosai nan ya sake tunzurani akan cewa zai kashe min uwata da dana haka na hakura na cigaba da bata, duk wata kuwa haka zai tura min dubu dari a account dina harna mallaki kusan miliyan goma..’’
Tana kaiwa nan ta sauke kanta kasa tana hawaye hannunta dun an nade da bandage, kallonta asad yayi yace ‘’bayanke akwai wanda kike tuanin yana mashi aiki’’
Shuru ta danyi tana nazari kafin tace ‘’gaskia ban sani ba saidai ranar da aka kama alhaji, wani ya kirashi yayi threatening dina kan cewa idan har ban cigaba da abunda alhaji ya dorani akaiba zasu kashe min dana’’
Zaro wayarta asad yayi ya tura gabanta yace ‘’wannan ne number’’
Kallon wayar tayi ta dago ‘’eh shine number’’
Mikewa asad kawai yayi ya fuce daga dakin bayan y agama recording conversation din nasu, direct ya bude whatapp dinshi ya tura ma amar, kasan video yace ‘’you need to listen to this’’
After like an hour saiga amar ya kirashi, asad na dagawa yayi shuru, nunfasawa asad yayi ya gasihesa ya tambayi jikin ammah kafin ay soma mashi bayani
‘’nasan ka saurari confession din datayi, bayan wannan akwai mutun daya wanda suke aiki tare’’
Akusashe amar yace ‘’waye!!!’’
‘’doctor hafiz, family doctor ku’’
Saurin runtse idanu amar yai ranshi ya mugun baci, shiyasa ya gudu Kenan don ranar da aka kawo ammah asibitin yasan cewa rana irin haka zatazo shiyasa tun kafin a kamashi ya gudu, jikin amar har bari yake, bayaji idan har yayi arba dasu zai iya bari su sake nunfashi a dorar kasa, don sun nemi su hallaka amman shi, mahaifiyarshi, mai share kukanshi, jin wannan zancen kadai ma da asad keyi mashi ya gama bata mashi rai sosai, yana jin wani irin zafi aranshi, a fadace ya miqe yace ‘’duk inda dan iskan nan yake ku nemoshi ku ci ubanshi, I will make sure there suffer’’
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya wurgar da ita gefe harta fashe tanasauke wani irin huci mai zafi kamar zaki, da sallama amra ta shugo dakin nashi hannunta dauke da coffee ta karaso inda yake tace ‘’ga coff….’’
Juyowa yayi azafafe idanunshi sunyi ya buge coffee din, jijyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rudu rudu bai iya fushi ba kwata kwata saboda yana da zafin rai ‘’gettt outtttt’’ ya daka mata tsawa, tsayawa tayi tana kallonshi galala ta kasa motsawa ‘’I said get outtt, do I have to repeat my self kafin kiyi sticking hakan a dummy kwakwalwarki,’’
Saurin sauke kanta kasa tayi daman mai hali baya taba chanza halinshi, duk a tunaninta yanxu ya sauya saboda yanda yayi sanyi sosai, ba kamar yanda yake ada ba ashe bai sauya ba
Dago da jajayen idanunta tayi tana hawaye ‘’insha allahu rabbi daga yau bazan kara zuwa inda kake ba, basai kayi min korar kare ba, daman nasan banida wani daraja a idanunka, bazaka taba chanza yanda kake kallo na,’’
Tana kaiwa nan ta fuce daga daki fuuu ranta yayi mugun baci tana hawa sama ta afshe da matsanancin kuka sosai.
Tana fita ya zauna bakin gadonshi ya dafe kanshi ya furzar da nunfashi, gaba daya baiyi tunanin zai sauke fushin da yake ba akanta, addua ya soma yi har zuciyanshi ta danyi sanyi, toilet ya shige yayi wanka ya futo ya zauna yana tunani, saida zuciyanshi ta lafa ya tuna da abunda yayi mata dazu, tabe baki kawai yayi ya miqe ya shirya.
Ranar ma bata bishi asibiti ba haka ya wuce sukayi switching su aman suka dawo gida, dakinta salima ta shige don taji dalilinta na kin kwana yau, lokacin data zo dakin amra na zaune ta doka uban tagumi tunanin abubuwa na yawo akanta, karasowa salima tayi ta zauna gefenta ta dafa kafadarta tace ‘’adda are you okay’’
Kamar jira amra take nan take ta fashe da matsanancin kuka don yanxu kuka ma baya mata wuya, haka ta dunga kuka salima na patting bayanta saida tayi mai isarta salima tace ‘’adda maisa kike kuka’’
Kallonta amra tayi tana share hawayenta tace ‘’ba komai kaina ke ciwo’’
‘’adda please dan allah ki daina boye min damuwarki, we only have each other now, ki fada min bakida kamarni duk duniya’’
Wani kukan ta sake fashewa dashi tace ‘’salima na gaji da abubuwan da yake min, bansan meysa yake treating dina kamar trash ba, kamar baisan daraja na ba’’
Hannunta salima ta rike saida ta gaam sauraronta tace ‘’adda kiyi hakuri komai mai wucewa ne, watarana sai labara, allah yaga zuciyarki akan lamuranki’’
Ba karamin sauqin abunda takeji ta samu ba da sukayi Magana ita da salima, karshe har suka kare da hira kafin su sauka kasa atare su daura dinner.
Washe gari madina tazo gidan, direct dakin amra ta wuce jin abunda ya faru, da sallama ta shiga, amra na ganinta tayi saurin rungume ta tace ‘’anty madina ina kika shiga kwana biyu ba waya’’
‘’sorry dear wallahi nayi tafiyar gagagwa ne zuwa Singapore munje wani semina’’
Zama sukayi bakin gado madina tace ‘’ya jikin ammah, banje asibitin ba saboda bansan wani asibiti aka kaita ba’’
‘’alahmdulllah da sauqi saidai bata farfado ba, yanxu muke shirin zuwa ma’’ amra ta fada tana kallonta
‘’yauwa shikenan saina biku ma ko , Allah ya bata lafiya ya Tashi kafadun ta ’’ madina ta fada tana kallonta.
Karfe sha biyu daidai suka wuce aisbiti a motar aman, amra kuma ta shige motar madina har suka iso asibitin……….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 139
Update
Unedited
Suna karasowa Madina tayi parking gefen da Aman yayi parking motarshi, atare Duk suka fito, amra ba gefen Madina while salima na gefen su itama sai Aman da Salim da sukayi gaba.
Anatse take ta kawa kanta a kasa, Madina ta Lura da yanda tayi sanyi sosai saidai bata tambayeta dalilin hakan ba, anatse suke tafiyar Har suka karaso dakin ammah, Aman ne ya bude kofar Duk suka shigo atare, babu kowa a cikin dakin sai ammah da nurse dake tsaye a gefenta tana goge mata jiki da towel
cikin wani warm towel, juyowa nurse din tayi suka gaisa daman ta gama goge ma ammah jiki don haka ta wuce bathroom ta zuba Mr da ruwan ta fuce daga dakin.
Takowa Madina tayi tare da amra gefen ammah suka tsaya, kallonta suka fara yi, babu abunda ya sauya a tattare da ita sai nunfashi da take fitarwa ahanakli, kallon amra Madina tayi tace “Allah ya bata lafiya ya Tashi kafadunta,”
Madina ta fada fuskanta na nuni da jimamin da take yi, salima ce ta karaso inda suke tace “Ameen anty Madina mun gode”
Amra dai bata ce komai ba tana tsaye ita ma gefen gadon ta kame jikinta, sanye yake da abaya baqa tayi rolling kanta, gaba daya itama she looks pale,suna nan tsaye Aman ya shugo tare da doctor, gaba daya matsawa sukayi daga gaban gadon don su basu waje, Madina ce ta fara gaishesa, bai ma kalli inda take tsaye ba kamar kullum fuskanshi a hade babu fara’a ya amsa kafin su salima suma gaishesa, amra dai na daga gefe, don koda ya shigo bata dago kai ta kalleshi ba balle ta gaishesa, gaba daya wani irin haushinsa take ji sosai, don ko muryarshi bata son jin, shima koda ya shigo bai dago ya kalli kowa ba so bai wani damu da wanda ya gaishe shi ba da wanda bai gaishesa ba,
mikewa Aman yayi ya bashi hannu shida doctor sukayi misabaha, kafin doctor ya sake duba jikin ammah, Yan gwaje gwaje yayi kafij ya waigo ya kallesu yace “Masha Allah, tana healing cikin ikon Allah, don yanxu bata buqatan oxygen sabod nunfashinta yayi stabilising,sannan rashin farfadowartaba matsala bane saboda dole daman zata dauka dan lokaci kafin ta farfado sannan alluran da mukayi mata suna dade wa kafin su saki mutun”
Yana kaiwa nan ya miqa ma Amar hannu, godiya ya mashi sosai kafin ya fuce daga dakin.
Doctor na fita salima ta kalli Amar daya tsaya bakin gadon ammah ya kafa mata idanu tace “ya Muhammad ga abunci an kawo ko azuba maka”
Bai waigo ba cikin kamewa yace “no”
Shuru sukayi gaba dayansu babu wanda yace qala Duk suna daga tsaye, kallon amra Aman yayi yace “sister inlaw ku zauna mana bismillah” yayi masu nuni da kujeran visitors doguwa inda Salim ne zaune.
Juyowa Madina tayi ta kalleshi kafin ta maida kanta kan amra tace “Ay ni wucewa ma zanyi, amma Zan dawo da daddare Insha Allah”
Kallonta amra tayi jiki amace tace “Toh anty Madina muje na rakaki”
Tunda amra ta fara magana ya danyi jim ya lumshe idanunshi, bai yi tunanin da ita aka zo ba don bai dago ya kalleta ba, sai alokacin yayi mamaki sosai.
Sallama Madina tayi masu kafun ta nufi hanyar fita amra na biye da ita.
Tun a kan hanyar futa daga reception Madina ta dan tsaya ta kalleta “amra