yellow ne dan iskancin daukar tasama kuna sai yasa stop agurin da yasa hannu ya toshe mata hanci be dauka dannan ba saikawai gurin da yasaka bakinsa cikin nata muraran kana gani zakace kissing dinta daga nan kuma sai gurin da suke kallon juna har qara zumin din fuskikin su yayi suka fito da kyau kana ganin kwalliyar fuskar ta nanma idan kaga kallon da sukewa juna zakayi zaton irin angana kiss dinnan anayiwa juna kallon love irin kowa nawa kowa kallon bangaji nan ba muqarayi wani be isheniba fassarar kallon da sukewa juna kenan awayar 😂 Lol
ganin yaqare yasashi fita daga videon yakoma ya bude hoton shikuma hoton lokacin dazata tashi yayi saurin kai hannun sa yace ta koma ta kwanta daidai inda yasa hannun sa ajikin ta daidai gurin ya daukesu jiyayi kamar ya fasa wayar dan ta qaici fasa zuwa inda yayi niyar zuwa yayi kawai ya juya tare da yin kwafa yabi bayansa yana ayyana irin rashin mutuncin da zaiyiwa sam idan yakamasa shiyasa ashe yabar falon to kwa yau zai nemosa duk ma inda ya shiga..
Azeema dake kwance jin shiru yasata dan bude ido tashi tayi zata zauna tana juyawa taga shettima a tsaye sai tayi saurin komawa ta kwanta saboda atunanin ta ko fita sukayi dataji shirun yayi yawa ashe yana nan to meyake atsaye kuma ina dayan dataji muryar sa agun shi ina yake tunda taji muryar shi taji tanaso taganshi saboda yanda yake magana muryasa tayi mata dadi murya ahankali ba wani daga murya acikin ta kanaji zakasan me ita baqaramar nutsuwa ce dashi ba tun amuryarsa zaka gane hakan tana so taganshi amma tsoron shettima yagane ta yasa takasa bude idon ta ta kalleshi amma har cikin ranta ta qosa da ta gansa amma ba hali Allah yasa wataran yaqara dawowa taganshi,
tanajin takun sa alamar ya juyo tayi saurin rufe idonta saida yagana fita daga falon sannan ta bude idon ta tare da tashi zaune zama tayi tana sauke ajiyar zuciya bi falon tayi da kallo sai yanzuma tafara tunani wai ya akayi ma ta ganta anan tunawa tayi lokacin da suka fito da papa har tazo zata gaida su to me yafaru da ita tasande Ammah tace ta gaida su yayintane hannu tasa abaki irin mutum yanason ya tuna wani abun tayi wajen minti 1 tana tunani sai kawai tayi zunbur ta miqe tsaye tana girgiza kai wlh shine shi naqara gani akaro na biyu arayuwa ta to amma meyasa inde nagansa bana qara ganin sa gashi idan nagansa rannan ance min na suma kenan yauma suman nayi to me hakan yake nufi inde ba aljani bane meyasa nake suma idan nagansa alhalin kaf duniyar nan banda wanda nake burin ingani inbashi ba banida burin da yarage min arayuwa irin inga gani gashi wake daya koda besoni ba duk danasan ma daman baze taba sona ba amma ni koda ganin sa ne ma kadai akabarni hakan ma zaimin dadi gashi kuma sai gizau yake min yana tsoratani hartakaini ga suma na shiga ukuna ni Azeema meke shirin faruwa dani kar aljanu subude min ido Allah na roqeka kaciren shi azuciya ta Allah kasa ba aljani bane idan kuma aljanine Allah kamin tsari dashi Allah kasa kar nasake ganin sa arayuwa ta mutum ne kamar ke taji anbata amsa daga bayan ta saurin juyawa tayi gabanta na faduwa Ammah ce ta qaraso inda take tana kallon ta ganin yanda tashiga tashin hankali ne yasa amma cewa dukan su da kika gansu jikoki nane kuma duk anan suke nima nayi mamakin sumanki daman saboda nayi tunanin idan kika ganshi zaki iya suma saboda kyaunshi da kuma mamakin da kika shiga duk su suka haddasa miki doguwar suma,
Jikin tane ya shiga karkarwa shikenan watakil taganota Allah yasade bataji duk zancen datakeyi ba da kyar ta iya hadiye wani abu da yatokare mata makogaro sanna ta bude baki daqyar zatayi magana kenan
Ammah ta dakatar da ita tare da cewa kar kice komai kije daki ki goge kwalliyar nan sannan kisaka kaya complete mayi maganar daga baya ina nan inajiran ki bata da zabin da ya wuce bin umarnin ta kamar wacce kwai yafashe ma aciki haka ta daga qafar ta datayi mata nauyi da kyar take janta jiki asanyaye gabanta na faduwa fat fat tabi ta gabanta batare da tace komai ba ta nufi dakin da tafito ranta fal da tunani kala kala ahaka taje dakin tana zuwa ta shige bandakin sai kawai ta fashe da kuka da ita kanta batasan dalilin yinsa ba sai da tayi me isarta sannan tayi shiru wayar ta ta dauko ta kira saleem taci sa'a kuwa bugu daya ya dauka tare da cewa salamu alaikum auta qanwata ta kaina Allah yasade kiran nan inji alkhari sunan shi takira tace "yaya"
yana jin muryarta yagane ba lafiya ba cikin dan tashin hankali yashiga tambayarta lafiya cikin shashsheqar kuka tafara yimasa bayanin duk abun da yafaru amma bata gaya masa ganin sam ba saitace masa wannan mutumin da mukaje office dinshi abokin aikin sa wanda inde taje yake cewa ta zauna agunsa yace eh yagane sa nande tabashi labari banda ganin sam alabarin nata shima ya shiga tashin hankali sosai nande yarsa shawarar da zai bata saikawai de ya kwantar mata da hankali tare da cewa ba abun da zai faru amma kartasake ta fadi gaskiya kawai tace tasaba ganin sane amafarkin ta shiyasa yau da tagansa take tunanin ko aljani ne idan tafadi hakan za ayarda to tace masa tare da daga masa kai kamar yana gabanta sannan tace ya turo mata da number shi mutumin da to yace mata kawai be tambayeta dalili ba ya katse wayar ba jimawa ya turo mata dubawa tayi ta dauka tayi saving dinta sannan ta shiga tayi typing din message zata tura masa amma bata turaba sai kawai tabar wayar awajen in case koda lokacin turawar yayi sai ta tura masa ba tare da wani ya kula da ita zatasan yanda zatayi kar akamata tunawa da anajiran ta yasa ta maida wayar gefe sannan tayi saurin daukar sabulu ta wanke fuskarta saida tayi wajen wanki hudu ta tabbatar da fuskar tafita sannan ta dauko wayarta tafito wasu kayan ta dauka tasaka amma bata fita da mayafin ba sai ta dauki wani hijabin da yayi kala da kayan ta saka ta fito das da ita farin ta da kyawunta suka bayyana tafito a Azeemar ta tada sannan tafito falon inda tabar Ammah ana ta dawo ta sameta tana zaune tana jiran ta tunda tafito Ammah take binta da kallo har ta qaraso ta zauna aqasa daga gefen qafar ta tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta gaban ta na faduwa tana jiran taji abun da zatace mata,
Ammah ta bude baki zatayi magana kenan taji sallamar shettima hakan ya dakatar da ita daga abun da tayi niyar fada qarasowa yayi yana ta kunfar baki saboda suk inda yake sa ran zaiga sam yaje begansa ba shiyasa yaqara dawowa nan ya duba ko zai gansa ya bude baki zaiyiwa Ammah magana sai kawai yaji maganar ta makale sakamakon tozali da idonsa yayi masa da Azeema qarar message dinne ya katse masa tunanin da yake shirin fara yi Ammah dake binsa da kallo tanajiran taji me zaice tace ya akayi ne ina me sunan baban yake be bata amsa ba yazaro wayar sa daganin me kuma yaqara cemasa dan shi duk atunanin sa ko shine yaqara turo masa da wani abun yana dubawa yaga bakuwar number budewa yayi ransa na qara bace gefe kuma ga tunanin ganin Azeema dayayi yarasa ma wane tunani zaiyi fara karan ta sakom yayi kamar haka
*dan Allah dan annabi na roqeka kar ka nuna
kasanni zanyi maka bayani daga baya na
roqeka kayi min wannan alfarmar banzo
nan dan na cutar da wani plss and plsss
karkace komai akaina plsssssss*
kurawa message din ido yayi bayan yagama karantawa tana satar kallon sa ta dauka ma baze taimake ta dan har tacire rai ma sai kawai taji yace Ammah daman nida wannan tuzurun naki ne yayi min wani babban laifi naje kuma na duba ya buya narasa inda yaje sai yanzu ya turo min wai inke waje insame shi yafada yana juyawa zai bar gurin tace baku gaisa da ita bafa gata ta wanke kwaliyar tayi hakane dan tanaso tagane acikin su waye yasa ta suma amma ganin yanzu ba ta suma ba yasa tagane amsarta watakon me sunan babane yasata ta suma zai fita kenan taqara tsayar dashi tace abincin naku fa kace masa yazo kuci kar ya kwanta ahaka dan nasan halinsa watakil shikenan baze dawo nan ba said da safe yace mata "to" kawai dan lokacin har yakai qofar fita budewa yayi ya fice daga falon nauyayyir ajiyar zuciya Azeema ta sauke aboye ganin ko kallon inda take ma beyiba ya fice hakan da yayi ba qaramin jin dadi tayi ba ranta taji ya kwanta tana murna aranta,
Meyasa kikeson saka rayuwarki cikin hadari kina 'ya qaramar ki nawa aka baki kika saudakar da rayuwar ki WAYE YA TURO KI!!!!!!!!!!!!??
daram daram darammmmmm gabanta yafadi yana kidan disko tambayar da tazo mata abazata duk wani jini dake kwaranya ajikin ta ya dakata da aikin dayake wani irin diff taji kanta yayi kamar ma ba aduniyar take ba.............🙆
Tab kina ruwa takwara😭
[5/11, 8:41 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526
'Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*
🅿15&16
Bismilah.......✍
Meyasa kikeson saka rayuwarki cikin hadari kina 'ya qaramar ki nawa aka baki kika saudakar da rayuwar ki WAYE YA TURO KI!!!!!!!!!!!!??
daram daram darammmmmm gabanta yafadi yana kidan disko tambayar da tazo mata abazata duk wani jini dake kwaranya ajikin ta ya dakata da aikin dayake wani irin diff taji kanta yayi kamar ma ba aduniyar take ba.......
"Tambayarki nake Ammah tafada da dan daga murya hakanne yasata dawowa cikin hayyacin azabure ta daga ido tana kallon Ammah sai kuma
jikinta gabadaya yadauki rawa bakinta harkarkarwa yake ganin yanda Ammah ta hade rai kamar ba itaba saima ta canza kamanni alokacin ta koma mata tamkar wata boss,
idanuwan tane suka cicika da kwalla amma sai tayi saurin riqesu bata bari sun zuboba jitayi bakin ta yayi mata nauyi bata san ma me zata ce mata ba batasan ta inda zata fara yimata magana ba saboda ta qara tsorata da ganin yanayin Ammah,
daurewa tayi saida tagama karanto addu'o'i acikin ranta duk wta addu'ar da tazo bakin ta yi take watama batasan me take cewa da qyar ta iya budar bakin ta dataji su tamkar andaure mata su ta ciki bakin ta na karkarwa kamar mejin sanyi tace ni ba wanda ya turo ni kamar yanda nagaya miki mahifana sun rasu sun barni wlh banzo gidan nan dan incutar da kowa ba kuma bada wata manufa nazo ba tun kan ta rufe bakin ya Ammah tace qarya kike ki fadan gaskiya tun muna shada juna tun a kallar fatar ki za agane baki kala da masu shan wahala ba qarya kike kice min baki da iyaye kina yawo a bola ai tun ganina dake tun farko nagane kalar zaren ba kalar yadin bane ina sane nabarki kika shigo dan in kamaki da hujja angaya miki bama abu da lissafi acikin masarauta zakizo ki rainawa mutane hankali bakisan bamu da yarda da mutane ba ni banma san ya akayi kika shigo ba waye yabarki saboda muna kafa kafa da rayuwar mu duniyar nan ba abun yarda bace musammama acikin gidan sarauta kowa zai iya zuwa dan ganin ga cutar da mu kawai abata mana family ko atarwatsa rayuwar wasu dan haka duk takun mutum muke lura dashi abun da yasa naqara tabbatarwa baki da gaskiya da kikaje ki kwaba wannan haukan a fuskarki alahalin watakil ma baki taba yi ba kawai danki wasa da hankalin mu kuma harda suman qarya ko kuma mamakin ganin sane wanda kike tunanin yasaki suman ko to kinfado hannun daidai dake yar qarama dake har kikasan kiyi min wayo yaushe kikazo duniyar yaushe aka haifeki tunda ta fara magana Azeema take faman kuka zuwa yanzu kam kukan yaci qarfin ta dan har bata san ma me Ammah take cewa ba jin kukan nata ya dameta yasata dakatawa da maganar da take kawai ta tsaya tana binta da idanu tana qara nazar tarta saida tagaji da kukan sannan ta dan dakata amma bata dena shashsheqar kukan ba cikin sanyin murya ta fara magana tace nasan nayi kuskure shigowa ta gidan nan kuma kinyi gaskiya bana kwanan bola kuma ina da uwa uba ne banda shi ki gafarce ni wannan qaryar danayi miki kuma nayine atunanina wannan ce hanyar kawai da zanbi incika burina amma kisani ni kwaliyar da nayi banayine dan in raina muku hankali ba kawai zaman dakinne ya isheni sai naga hoda da kwalli kuma ba mudubi shiyasa kawai na dauka nafara kwaliya dasu hasalima banga me nayi afuskar ba kuma daman niyata idan nayi sallar isha idan zanzo wajen ki sai inje bandaki in wanke kafin inzo wajenki amma banayi ba dan wata manufa wani irin banzan kallo Ammah take watsa mata me cike da fassariri iri iri hakan yasa Azeema dan daka tawa da maganar tare da shan jinin jikinta tana tunani ko kawai ta fadi gaskiya sai amfi yarda da ita tunawa kuma da cewa masarautar basu da imani koma tafada ba barinta za 'ayi ba kuma daga qarshema tazo tai biyu babu ita ahanata fita shima kuma aqara kwakwkwaron tsaro wajen riqeshi a masarautar ta yanda har abada bame fitar da su daga ciki ko kuma ma ace za ayanke musu hukuncin kisa tsoro yaqara nunnkuwa azuciyar ta shiyasa taji bazata taba fadan gaskiya ba koda me za ayi mata fatan tade Allah yasa ta yarda da bayanin da take mata,
ganin ta tsatstsareta da idanu yasata katse tunanin da take sannan taci gaba dacewa suma kuma dakike cewa nayi na qarya hasalima bansan nayi ba saidai kuma nasan musabbabin abun da yajawo min suman shine tozali da nayi dashi mamaki ne yasani suman kamar yanda kike tunani tunda nataso arayuwata bantaba jin son wani mutum ba sai akansa tunda naje wani biki qawata naga hotonsa awayar amaryar naji nakamu da sonsa bata ma san nadau hotunan saba acikin wayarta ba tundaga lokacin nake mafarkin sa kuma zuciyata takasa samun nutsuwa har saida nahau Internet na nemosa sannan nayi tambaya akansa ahaka har nasamo address dinsa ashe dan gidan sarauta ne tundaga nan nafara tunanin ta yanda zan hadu dashi kuma ance min ba anan qasar yake zama ba saidai kawai yazo yadanyi kwanaki yatafi tunda naji haka nake son inshigo gidan nan ko Allah zaisa inganshi nayi duk yanda zanyi inga na shigo gidan nan amma nakasa samun hanyar da zan shigo wata qawata ce ta bani labarin masarautar akwai tsaro dan inde ba wanine yasanni ba baza ataba barina in shigo ba saidai ta hanya dayace idan naci sa'a zan iya samu inshigo nace tagaya min hanyar shine take cemin taji ance inde mutum yazo amatsayin almajiri yaneme da ataimaka masa da abinci to zai iya samu ace yaje ya karba amma saidai inje da sassafe kafin masu gidan su fara fitowa nikuma daga nan sai insan hanyar da zanbi wajen ganin na hadu dashi koda sau dayane arayuwata hakan zaisa naji dadi araina yanda muka tsara kwa hakan nabi har nasamu sa'a tambayar farko me gadi ya amince min da nashigo naje karba nikuma da na tafi inda ya kwatan tamin sai kawai nabi wata kwanar arashin sani nabi hanyar da sarki yake bi ananne dogaren suka kamani shine kikazo kika taimakeni kinji iya gaskiyar abun da nasan ya shigo dani gidannan amma ba yanda kike tunani bane banshigo dan na cutar da wani ba amma ki gafarce ni qaryar danayi miki kuma dan Allah karki tona min asiri ki rufamin asiri kar wanda yaji maganar nan na roqeki badan halina ba kuma kar ki koreni daga wajenki dan bansan yanda zanyi da rayuwata ba wallahi ina sonsa tana gadar haka kuma sai tayi saurin sada kanta qasa zuciyar ta na bugawa da fargabar abun da zataji daga gareta batasan da wata manufa zata dauki zancen taba zata yarda da itane ko kuma zatasa a hukuntata laifin qaryar da tayi ta shigo ciki shiru falon yadauka na dan mintina saboda Ammah ta tsaya tana nazarin maganganunta saida tayi wajen miti biyar batare da tace mata ko uffan ba sai daga bisani kawai tace mata tashi kije zan nemeki kawai abun da tace kenan ta tashi daga kan kujerar ta bar falon ta nufi dakin ta tana shiga ta fara zagaye dakin tare da saka hannun ta duka biyu tana zagaye zagaye tabbas azancen yarinyar nan kamar akwai gaskiya duba da yanda take kuka wiwi kuma naga alamar da gaske tanason sa to amma hakan bazaisa in yarda da itaba lokaci guda kuma abun da takeso duk son da gake masa bazai taba auren ta ba amma tunda har ta bukaci itako ganinsane zata ji dadi aranta to zan mata wannan alfarmar sannan bazan sanar da kowa ba qudurin ta agidan zan barta tacigaba da zama acikin har zuwa wani lokaci da na daukarwa kaina kuma zan qara sa ido akanta inde har da gaske take zan fahimata idan kuma nagano qarya take tofa zata kwashi kashin ta ahannu dan bazan raga mata ba turo qafar da akayine yasata dakatawa da tunanin zucin datake papane ya shigo da dan fara'arsa yaqaraso inda take yace kinga bakuwa afalon nan kuwa naganta de azaune ta gaida ni amma de ban tambayeta saboda naga bisa ga dukkan alamu zaman jiranki take