da suka canza launi abun tsoro kamar banata ba haka ta zuba masa su shima ita yake kallo ko ƙiftawa bayayi kasa jure wa tayi sai kawai ta kawar da nata idon daga gare sa ƙara miƙa mata yayi yace tasha,
ƙin karba tayi tama fara ƙoƙarin tashi zata bar wajen,
da hannu ya mayar da ita takoma ta zauna ruwan ya ɗiba a hannun sa ya watsa mata shi a fuska wani irin dogon numfashi taja tare da saukewa duk alokaci guda ƙara ɗiba yayi zai watsa mata tayi saurin cewa karka kuma watsamin Wannan abun,
ba saurare taba ya kuma watsamata abun da tayi dazu shi ta kuma yi yanzu saida sukayi haka sau uku sannan ya rabu da ita Qur'ani yadauko ya budo surataul baƙara tunkan yafara yaji
" tace kar ka konamu zamu fita yace karma kufita gwara ikonaku din meyasa baku da tausayi ku bakuga tsohuwa bace me tayi muku kuka sakata agaba kuka hanata tuna dangin ta bayan kunrabata dasu nan sukace muma ba yin kanmu bane turo mu akayi waye ya turo ku ya tambaye bazamu fada ba to idan na konaku ai zaku fada yana fara karanta aya daya sukace karabu damu zamu fita kishiyar tace tajamata halin da take ciki saboda ba ason zamanta acikin gidan ku kuma mugaye shine kuka hanata ko to nima bazan barta kuba nan yafara yi mata ruqiya tun anajin ihunsu har akadena ji bai rabu dasuba harsaida ya tabbatar yarabata dasu gaba ɗaya sannan yaƙara shafa mata ruwan afuska atake agurin ta sume gyara mata kwanciya yasa akayi sannan yabasu wani turare yace suyi mata kafin ta tashi daga baccin su yiwa duka gidan ma,
godiya sukayi masa sannan Abu yace malam daman aljanune wajen fa shekara ashirin da wani abun tana kwance,.
dan murmushi malamin yayi yace wannan ai ba aikin asibiti bane bayan aljanu ma akwai sihiri ajikin ta sannan aka hadata da aljannu ta yanda koda sihirin yakarye su kuma bazasu bari ta tuna komai ba abun da yafaru da ita kenan watakil asamu matsala daga gurin su shiyasa sihirin yakarye dalilin da yasa ta tuna wani abun kenan amma daga na bazata ƙara tuna komai ba amma yanzu komai ya warware suma kuma sun fita tana farkarwa zata dawo daidai koma ta zai dawo zata tuna da komai,
gaba dayansu babu wanda baiyi mamaki ba dan tunda suke basutaba ganin irin haka ba saidai ko alabari ko a Film amma yau gashi anyi agabansu ,sosai suka nuna jin dadinsu sannan suka yiwa malam godiya sosai tare da yimasa alheri me tsoka dan acikin su babu wanda baiyi masa kyauta ba kuma kyauta ba yar ƙarma ba me tsoka dan aƙalla iya kudima sunkai 1.5m suka hada masa ajaka banda turaruka har da kaya shaddodi sababi waken guda goma sha haka Abu yabasa,
kowade bayan kudin da yabashi saida suka ƙara masa da abubuwa duk suka hada masa dan su aganin suma basu biyashi komai ba akan abun da yayi musu shekara nawa suna wahala da kashe kudi amma basu bata lafiya ba sai gashi shi akwana ɗaya kuma alokaci ɗaya har ya magance matsalar dole subashi abun da yafi hakama,
bakin sa harkunne sai faman washe shi yake kana ganinsa kansan ba ƙaramin farin ciki ya tsinci kansa ba malam yayi musu godiya sosai tare da yi musu addu'a sannan sukayi sallama yatafi da kyautar sa da tunda yake aiki baitaba samun irin taba cike da farin ciki yabar gidan,
"bayan fitarsa meer yakasa zaune yakasa tsaye sai faman zagaye falon yake yana alajabin wannan al'amarin kamar amafarki wai duk tsawon shekarun nan da ya dauka daman akwai ta yanda za ayi taji sauƙi lokaci daya sai yaji duk haushin kansa da tun farko beye wannan tunanin ba gashi kuma dasu Ummu sukayi masa maganar nan ma yaƙiyarda da su da ya yarda tun alokacin da tuni ta dade da samun lafiya gani yake kamar duk shi yaja mata wannan dadewar datayi a kwance sosai yake jin haushin kansa kuma yake ganin baiyi mata adalciba,
amma fa duk dahaka kuma yagani yaji da kunnen sa amma wani barin na zuciyarsa baigama yarda ba cewar ta tashi wannan dan abun da yayi mata ace wai shine silar samun lafiyarta yade yarda da aljanu kuma yasan anayin ruƙiyya amma me yasa zaice wai anyi mata sihiri kuma yakunce da kansa ajiye tunanin yayi agefe sannan yajuyo ya matsu kusa da ummy yakalle ta sannan yace Ummy wai da gaske yanzu idan ta tashi zata tuna komai kodai fadarsa nifa haryanzu I can't believe this thing, I think it's a lie yaƙarasa maganar fuskarsa cike da gasgata abun dake ransa,
Abu ne ya tari numfashin sa yace I don't think so because magic is not a lie kanade gani yanzu yayi magana dasu kuma kaji da kunnen ka amma meyasa kake son saka kanka tunanin da bashi da amfani idan ma baka yarda ba yanzu idan ta tashi ai zaka yarda,
Bansan yaushe zaka canza kadena wannan halin ba kanaganin gaskiya kuma kaima kasan hakane amma sai ka ringa takewa kana tambayar mutane tamkar bakason komai ba me yasa kake hakane,
Abu yaƙarasa maganar alamunde baiji dadin abun da meer yace ba saboda daman yasaba haka wannan halinsane,
tunda abu yafara bayanin sa bai daga kai ya kallesaba daga ƙarshema da yaji ya tsaya da maganar tasa sai kawai yatashi yabar falon tare da nufar part dinsa ransa yana mishi suya besan meyasa ba Abu yake son yayi masa fada koda yaushe ba shiyasa yafi son mahaifiyar sa bata masa fada duk abun da yakeson shi take masa bata son ɓacin ransa ko kadan al'adun Abu shikuma da yake ganin kamar ya takurawa rayuwar sa idan yana yi masa irin wannan abubuwan da bayajin dadin su ,
ganin yatafi yabarsa awajen yasa Abu jin ba dadi shima yana ganin shi yanzu bai isa ya nunawa yaron nan yayi ba daidai ba sai yakama nuna fushinsa saikace bashi ya haifesa ba a rana yace duk laifin Ummy ne da take biye masa yayi duk abun da yaga dama yanaso ya ɗorasa akan irin tarbiyyar nan amma shi kwata kwata zama da mahaifiyar sa da kuma zaman da sukayi a Yemen yasa shi dauko rayuwarsa tacen shiyasa watarana yake jin zafin abun aransa amma koda wasa baitaba nunawa mahaifiyar tasa haka ba duk wani abu da tanuna tanaso ayi yake biye mata saboda komai zatayi masa bazai taba mance halaccin da tayi masaba saboda ta zabeshi akan mahaifinta saboda son da take masa gashi ta zauna dashi a inda bata saba zamaba bata da kowa batasan kowa ba ta baro family dinta ta biyo sa dan haka shima dole ya jure duk wani abu da zataimishi domin rama halaccin datayi masa,
jin antabashi yasashi dawowa hayyacin sa tare da sauri. kawar da damuwarsa yabasar,
zatayi magana ya hanatayi ta hanyar cewa kinga kar ta tashi Yakamata kiyimata turaren kafin ta farka kamar yanda yace tafaɗa yana komawa kan kujera ya zauna,
binsa tayi da kallo tasan da abun da yake tunani amma sai tabar zancen itama kawai,
Sannan ta kira wata me aikin ta aikin ta ta haɗo mata gawayi takawo mata yanda malam yace musu haka sukayi mata turaren tare da yiwa gidan.........✍️✍️✍️✍️
[5/30, 10:26 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*littafin sarki sameer yana daya daga cikin sabon team da muka bude na marubuta biyar 5 me suna THE TALENT TROUPE WRITER'S masu tafe da nasu sabon salon nadaban domin farin cikin ku, ga dadi da ƙayatarwa da nisadantarwa da fadakantarwa masu ɗauke da zallar soyayya da ƙaunar juna kar ku bari abaku labarin daya daga cikin wadannan littafan domin za ayi babu ku........*
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(mrs bmb)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿43&44
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"Bayan sun idar da sallar sun dawo bossay da sam ne kadai suka shigo shettima ma kuma yatsaya yayo musu order din abinci sannan yadawo gaba dayansu suka zauna suka sukaci suka kora da ruwa,
Sam ne yafara miqewa daga gurin, wajen dakinsa na ajiye ajiye yanufa tare da daga labulen ya bude qofar sannan ya shiga yana shiga sai kuma yafito, dan leqo da kansa yayi yana kallon su ganin suna nan yanda suke basu da niyar tashi duk sun dauki wayoyinsu ma suna daddan nawa,
dan daga murya yayi yanda zasu fi jinsa yace zaman me kuke kuma?
miqewa sukayi gaba dayansu tare da ajiye wayoyin nasu bossay nacewa ni ai banma ga tashinka ba kallon sa sam yayi "yace daman ai baza ka gani ba tunda hankalin ka nakan waya yana kaiwa nan ya wuce ciki,
binsa sukayi abaya suma suka shiga cikin dakin ,
lokacin da suka shiga ciki har yakai ga zaunawa akan kujera tare da jawo laptop din kan table din zuwa gabansa tare da kunna ta,
tunda suka shiga dakin suke faman baza ido acikin sa musamman bossay da baitaba shigowa ciki ba idon sune yasauka akan board din da yayi rubuce rubucen sa,
da sauri bossay yaqarasa gurin ganin sunan shi ajikin board din qara zubawa board din ido yayi yafara karan ta sunayen dake jiki tabbas wadan nan sunayen da dadda tabasu labari bisa ga dukkan alamu yasaka sunayen wadanda za ayi bincike akansune wadanda ake zargi ne to amma meyasa yasa da sunan sa ajiki alhalin shide yasan ba mailaifi bane to kenan yana nufin shima yana zarginsa akan wannan case din jiki asanyaye ya juyo yana duban sam ganin hankalin sa ba akan sa yake ba yana kan laptop din dake gaban sa yasashi maida dubansa ga shettima hada ido sukayi da shettima,shettima naganin yana kallon sa kuma shima yaga abun da yagani tunkan bossay yabudi baki yayi masa magana sai kawai ya girgiza masa kai alamar shima baisan komai ba,
shiru bossay yayi bai yi maganar ba ya koma kusa da sam ransa duk ba dadi dan wani iri yake ji game daganin sunan sa da yayi,
ashe duk abun dasuke akan idon sam duk yana kule dasu amma sai ya basar ya nuna baima san sunayi ba,
"dagowa yayi sannan ya maida dubansa ga shettima yace ina wayar?
zarowa yayi a aljihunsa tare da miqa masa,
karba yayi ya zura mata USB yayi connecting dinta sannan ya maida hankalin ga computer din yafara aikin sa yadau lokaci me tsawo kafin yadago fuskar sa da alamun da muwa,
duk kallon sa sukayi shettima ne yasamu damar tambayar sa me yafaru amma banda bossay dan shide zuwa yanzu jikin sa ya mutu ya kunce masa duk wan kwarin gwiwa shiyasa baiyi gigin tambayar sa ba yaja bakin sa yayi shiru,
"Sam yace akwai matsala fa nagano number da yayi wayar saidai abun mamakin andatse duk wata hanya da zaisa abi didigin number,
shettima yace andatse fa kace yafada cike da daga murya dan abun ba qaramin mamaki yabashi ba'
cike da tabbatar wa shima sameer ya jinjina masa kai,
" to ya akai suka datse ta kode sungano mundauke shi ne shiyasa suka datse cewar bossay da mamaki yasashi yin maganar da baishirya ba yamanta da wani zacen ganin sunan shi'
"haka nake tunani cewar sam yafada tare da miqewa daga inda yake zaune ya hau zagaya dakin yama rasa wane kalar tunanin szaiyi,
Ammafa nayi mamaki tayanda suka gane har suka datse layin cewar shettima da shima abun yazo mishi wani iri,
maida kallon sa gare su tare da gyara tsayiwar sa yana fuskan tarsu da kyau,
sannan yace" yanzu dole mu koma gurin sa muci gaba da dukan sa idan yaji wuya zai iya gaya mana inda yake in bahaka ba kuwa zamusha wahala gurin gano inda yake,
"hakan yayi amma kana ganin zai iya fada mana kagafa dukan da mukayi masa dazu amma bakinsa bai mutuba gaskiya gayen yana da taurin kai zai waya yafada mana shettima ke wannan maganar,
Bossay yakarbe shi da cewa zai iya fada mana idan mukayi masa barazanar zamu kashe shi dole yaji tsoro yafada,
Sam yace ko munyi masa barazanar za mu kasheshi bazai fada saboda ya riga yasan dole baza mu masheshi ba saboda ta hanyar sane kawai zamu iya gano wancen din kuma idonsa abude yake kuma yana da wayo dan haka bazai fada mana ba,
dan dakatawa yayi da maganar tare da numfasawa sannan yace hanya daya zamu bi nasan tabbas zai fada,
" har suna hada baki wajen cewa wace hanyar?
shiru yayi baibasu amsaba saida yayi taku biyu zuwa gabansu sannan ya juya ya dauki wayar mutumin sannan ya dauki wani dan qarfe me tsini sai ya cire condem din wayar(rigar waya) sannan ya zura siririn abun awajen da ake saka sim,
Yana shirin ciro sim din kenan saiga kira ya shigo wayar da sauri yafasa cire sim din tare da kallon wayar,
Suma gaba dayansu sukayo kan wayar dan ganin me kiran,,
suna tsaye suna kallon wayar harta katse batare da sun daga ba wani kirannne yasake shigowa wayar da private number,
da sauri Sam ya daga wayar tare da sakata a hands-free tare da yin shiru daga can bangaren ma shiru akayi ba ayi magana ba,
jin anyi shiru suma yasa sukayi shiru kowa na jiran wani yafara magana,
sunkai wajen 30 second kafin daga can bangaren suka ji ance "kunyi kuskure wajen shiga abun da bai shafe kuba ina mai gargadin ku da ku hanzarta mayar dashi inda kuka dauko shi kunsan matsayin sa da girman aikin sa yanzu ina turawa cewa kun saceshine to kusani fa gaba dayan ku bamai kubuta sai anyi muku hukun cin sace shin da kukayi za ayi muku hukuncin 'yan kidnapping kuma kunsan hukun ci naku yanda zai kasance dan haka nake baku shawara da ku mayar dashi dan bazaku taba samun abun da kuke nemaba sannan shawarata ta biyu shine kuyi gaggawar zare hannun ku acikin wannan abun da bai shafeku ba hakan zaifi muku kwanciyar hankali daga ku har dangin ku kar kubari infara bincike akanku......dif ya kashe wayar batare da yajira cewar suba ya kashe wayar....✍️✍️
*Ayi hakuri da wannan yau nashiga busy dayawa*
[5/31, 8:58 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(mrs bmb)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿45&46
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
shawarata ta biyu shine kuyi gaggawar zare hannun ku acikin wannan abun da bai shafeku ba hakan zaifi muku kwanciyar hankali daga ku har dangin ku kar kubari infara bincike akanku......dif ya kashe wayar batare da yajira cewar suba ya kashe wayar.......
Gaba dayansu bin wayar sukai da kallo kamar masu son ganoshi ta cikin wayar haka suka tsaya suna kallon ta duk sun kasa motsawa daga inda suke bare kuma wani yayi magana ba wanda yake da wannan karfin halin sun dauki wasu minti na batare da kowa yace kowa wani abunba,
"da kyar sam ya iya cewa qaryane baka isa ba karya kake sai na nemoka koma waye kai aduk inda kake sai na kamoka, yaqarasa fadar maganar da daga murya hannun sa har rawa yake idon sa sun canza kala saboda tsabar bacin ran da ya tsinci kansa aciki magan ganun mutumin sai dawo masa sukeyi acikin kwanyar kansa wai shi akecewa shida family din sa zasu shiga cikin matsala yasan ko shi waye yasan suwaye family din su lalle mutumin nan yajawowa kansa bala'in da yafi qarfin sa dole yakomo shi ya koya masa hankali ko dan gidan uban waye sai yayi da nasanin sanin shi cike da taqaicin maganganun da mutumin yafada musu yadaga wayar ya bugata da qasa take agun ta tarwatse ta fashe,
sai wani irin huci me zafi yake fitar wa tare da komawa kan kujerar yazauna yana dafe kansa,
duk tsorata sukayi da yanayin da suka gansa musamman bossay da baitaba ganin shi a irin wannan yanayin ba,
inda ya jefar da wayar shettima yaje tsugunnawa yayi agaban ta tare da saka hannu ya dauketa sannan ya miqe gurin sameer ya dawo sannan yadauki abun cire sim din dake gabansa yazirashi ya zaro gaba daya sima siman dake cikin wayar,
dafa kafadar sam yayi tareda cewa colm down coll ur mind wannan abun ba wani abu bane da zaisa ka tada hankalin ka already mun riga mun dauko shi kuma bazamu mayar dashi ba idan kuma ya nemi yadaga mana hankali muma sai mu shigar dashi qara koda wannan hujjar da muka kamashi yana waya