Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   37 / 74

108K to 111K   out of 221K words

saida suka ga yasa hannu yakamo duka hannayen su ya shiga jansu kamar wasu sukaye haka suka shiga binsa abaya batare da kowa yaqara magana ba suka nufi hanyar waje ahaka suka cigaba da tafiya har sukaje part din fulani ba wanda yayi magana, duk sun zuba ido suga iya gudun ruwan sa,

saida sukaje bakin qofar sannan yasake su tare da tura kofar suka shiga ciki su shettima mane suka samu damar yin sallama amma banda sam da ahalin da yake ciki bazai iyayin magana ba bakin sa yayi masa nauyi,

fulani ce zaune kan kujera tana waya shigowar su yasa tayi saurin katse wayar tare da amsa musu sallamar su ba yabo ba fallasa suka gaisa amma banda sam da suna shigowa ya wuce part dinsa,

fulani tace lalle yaran nan kuna sha'anin ku yanzu kaima saikaga dama kake zuwa inda nake yanzuma nasan badan munhadu ba wucewa zakayi baza kanemeni ba daman ance zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai yanzu kaima kafara daukar dabi'ar wancen marar mutun cin da baya ganin mutane da gashi kaima haka kake so ka koma kaima ko to sai kuje kuyi tayi kar kufasa,

dan shafa kai shettima yayi sannan yana dan murmushin dole sannan yace tuba muke mama wallahi ba abun dakike tunanani bane abubuwane yanzu sukai min yawa nan dinma yanzu ba kullum nake shigowa ba wataran kuma idan nashigo bana samun ki anan shiyasa amma de kiyi hakuri za'a gyara,

kai kasani bawani ba ka shigowa jinake ko jiya dare anan yayi muku amma baka nemeni ba idan baka gani anan ba bakasan inda dakina yake ba ko kodan baikamata ma inga laifin kaba wanda kaci kashin sama kaci futsarin sa baigirmamakaba baka da daraja awajen sa bare kuma wanda bakai mishi komai ba shi kallon arziki ma wataran baka isa kasamu daga gurin sa bare har yadaga kai yazo inda kake ya gaida kai, nidai shawara wallahi ku gyara halinku dan wannan ba hali na gari bane,

to mama fulani zamu gyara in sha Allaha kiyi hakuri yanzude komai ya wuce tuba muke kanmu bisa wuya,

"zadai ka canza amma wancen murdadden bazai taba canzawa ba,

kidai yimasa addu'a zaidaina in Allah ya yarda,

tabe baki tayi tace oho de kuka sani,
dahaka de sukayi sallama da ita suka bi bayan sam daman Allah Allah suke tayi ta sallamesu tabi ta tsaresu da surutu,

suna karasawa suka shiga da sallama abakin su,
can kan kujera suka hango sa ya hada kai da gwiwa ya kifa kansa akan gwiwowin sa da sauri suka karasa inda yake shettima ne yafar zuwa yace,

"Subhanallahh"

"sam lafiya meyake damunka haka me yake faruwa?

dagowa yayi yana kallon su daya bayan daya da jajayen idanun sa da suka canza kala,
kawai kallon su yake yakasa ce musu komai.
kallo daya zakai masa ka fahimci tsatsar bacin rai da damuwa da yake ciki,
sosai suka shiga damuwa ganin damuwar da yake ciki,

cike da damuwa shettima ma yace haba sam kasanar damu abun dake faruwa duk kasakamu acikin damuwa,

bossay ne shima da yagama karan tar yanayin sa yaji gaba daya jikin sa yayi wani irin sanyi ya mutu dan haka kawai jikin sa yaba sa damuwar sam ta dagan ta da Ameesha tunda mahaifiyar sa taja sa daki dan sanar dashi abun dake faruwa tundagana kawai yaji something is wrong game da Ameesha zuciyar sa tabasa Ameesha ba lafiya take ba,

shettima ne yaci gaba da cewa sam bansaka da shiga damuwa ba irin haka ba kaida nasanka da jarumta nasanka haba saikace bakai ba ka kwantar da hankalinka ka sanar da mu matsalar da take damun ka matsalar ka matsalar muce ka gaya mana ko zamu iya magan ce maka ita, danshi baitaba kawo wani zancen Ameesha ba duk atunanin sa ko wata matsalar ce da ta shafeshi ko kuma ta family ce...

cikin sanyin murya bossay yace "Ameesha ko wani abunne yasame ta??

  
                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[6/25, 10:58 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️67&68

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

             
  
    cikin sanyin murya bossay yace "Ameesha ko wani abunne yasame ta??

da sauri sam ya ɗago yakallesa sai kawai yaji yabashi tausayi daman yasan sai yafisu shiga damuwa saboda sunfi sabawa da ita dan ya ɗan fahimci ma kamar da so atsakanin su a iya zaman da sukayi yafahimci hakan dan yasan da shaƙuwa atsakanin su ita dashi yanzu ta ina zaifara gaya masa aya zai ɗauki maganar shide yau yaga takansa yau ina zaisaka ransa inajin tunda yake bai taɓa shiga damuwa irin wannan tayau,

tundaga irin kallon da yaga sam yana masa hakan ya tabbatar masa da tunanin sa gaskiya ne tabbas zarginsa ya tababbata ko da baigaya masa yaga amsar sa a cikin ƙwayar idon sa,

dan haka baiƙara ce masa komai ba kawai ya miƙe daga kusa dashi tare da komawa kujerar gefen su ya zauna kawai shima yazubawa Sameer ido zuciyar sa na wani irin harbawa, yanajin tsoron abun da zaiji daga sameer tunda haryagansa cikin damuwa irin haka to yasan ba ƙaramin abu bane yasaka shi hakan ba,

shettima ne da yaji tambayar bossay wata iri kamar daga sama shima sai yanzu zuciyar sa da ɗarsu da farko baiyi tunanin wani abun ba amma da yaga sameer yayi saurin kallon bossay hakan ne yasa shima yafara tunanin ko hakanne,

gyara zaman sa yayi ya kalli sam da kyau sannan yadafe kafaɗar sa tare da kiran ainahain sunan sa yace sameer kasanar damu abun dake faruwa shirun baida amfani sanar damu ɗin shine mafita asan yanda za a shawo matsalar,

wani irin numfashi me zafi sam ya fitar daga bakinsa tare da iska sannan ya nufasa batare da ya kalli bossay ba dan yanzu yafi jin nauyin haɗa ido dashi akan shettima dan haka sai yakalli shettima cikin sanyin murya yace shettima bansan taya zaku fahimci maganar nan ba sunƙara ɓata mana aiki shirin mu yadawo baya kaina ya ƙulle mutanen nan basu da imani abunsu kullum gaba yake muna murnar munyi nasara ashe abun bahaka yakeba wani abun suka ƙara shirya mana mutanen nan suna sane damu duk inda mukaje idon su yafara yawo akan mu, duk yanda akayi shiga da fitar mu akan idon su mukeyi bamu sani ba yazamuyi dasune dannidai wallahi abun yafara bani tsoro anya baza musa hukuma aciki ba?

duk shiru sukayi suna sauraron sa da sun kasa fahimtar inda maganar sa ta dosa, shettima yace sam wai me kake shirin cewa ne nifa bangane bayanin ka ba me kake so kace,

"Sun ɗauke yarinyar nan da mukawota gidan nan sun sace ta ɗazu"

"ME...!?"
bossay dake ɗayar kujerar yataso da sauri yazo gaban sameer yace "kamar ya sun saceta kana nufin kace duk girman gidan nan suka iya shigowa har ciki suka ɗauki baby ko kwa ya akai tayama hakan zaiyiyu me yasa duk rashin tsaron gidan da take zaune basu shiga sun sace taba sai nan gidan da yafi nasu tsaro shine zasu iya shigowa su sace ta wannan wacce irin maganace?
[6/25, 5:05 PM] #momyn twins#: shettima ne ya miƙe tsaye shima yana kallon bossay yace "kamar ya wannan wacce irin magana ce kama nufin kenan baka yarda ba ko kuma da sanan su hakan tafaru ko su suka ɗauketa wanne kake nufi daga ciki?

"nima bansani ba kawaide maganar naji wata iri wai ansace tayaya hakan ta faru gaskiya wannan maganar da sake dole a fito da wanda ya ɗauke ta adaren nan tunda de tana cikin gidan nan ba fita akayi da ita ba idan kuma fitama akayi da ita to dole za asamu wanda yaga anfita da ita nan gidan ba kamar ko wane gida bane tunda kuma da tsaro bazaiyiyu ace anshigo daga wajeba anɗauke ta anfita da ita batare da sanin wani ba,

"shettima yace yakamata karinga gyara kalaman ka katsaya kaji ta yanda akayi aka ɗauke ta ɗin baikamata kazo kana faɗar abun daka ga dama ba kasan a inda kake da kuma wanda kake magana dashi kai ko halin da kaga ya shiga ma ai baikamata ka faɗi wata maganar da bata dace da shiba idan kai lura da yanayin sa ai kasan baƙaramin tashin hankali yashiga ba amma memakon mubi komai ahankali muji yanda za amagance matsalar amma sai kazo kana surutun banza haba Aliyu wannan abun dakake kwatakwata bai dace ba,


"bossay yace nifa ba wata magana nafaɗa ba kuma banyi dan ina zargin wani abun ba kawaide abunne yaban mamaki amma tunda haka kuka ɗauki maganata kuyi haƙuri bazan sake saka muku baki aciki ba kuyi duk yanda kuke so tunda duk abun da zan faɗa laifi zai zama awajenku,

yana kaiwa nan ya nufi hanyar waje batare da yaƙara waiwaiyen suba ya fice daga ɗakin zuciyar sa nayi masa wani iri,
haka suma basu dakatar dashi ba har ya fice......

shettima ne yaƙara dafa sameer yace "dan Allah ka kwantar da hankali ka abi komai asannu ni ina ganin wannan ba abun tada hankali bane ai cikin nan yana da tsaro kaga nemanta bazai bamu wajaba koda ace ma sace tan akayi zamu samu wanda yaga anfita da ita tunda ko daddare mutane basa kasa yawo anan bare kuma ace da rana kaga idon kowa yana kai zamuyi saurin samun labarin ta ni banga abun shiga damuwa ba har haka,

ɗan numfasawa sameer yayi tare da kallon shettima da kyau sannan yace nima da hakanne ai bazan damu ba dole insa afito da ita duk inda ta shiga to amma matsalar ba anan gidan aka ɗauketa ba Ammar ne ya fita dasu ita dasu Hamra to awajen shopping ɗin aka ɗauke ta to abun kuma da yafi bani mamaki wai tare suka fito da ita daga ciki amma suna ƙarasowa wajen motar suka neme ta suka rasa tunda kaji haka kwa kai kasan da shiri akayi hakan zai iyayiyuwa ma tun fitar tasu ake bibiyar su ba asamu damar ɗauke ta ba sai loƙacin da suka fito aka faki idon su aka ɗauketa ta hanyar da bazasu ji ba,

"wai daman ba acikin nan aka ɗauke taba??
shettima yayi maganar shima cike da shiga ruɗani danshi duk atunanin sa anan aka rasata shiyasa baidamu ba sosai,

"nima shine abun da yasani shiga tunani shine dalilin da yasa nama kasa sanar daku,

"to yanzu meye mafita"?

"Ina tunanin fa saidai gobe mukoma can inda sukaje ɗin nasan baza arasa CCTV camera ba awajen inyaso sai aduba mana muga tayanda aka ɗauketa ɗin nasan ta nanne kawai zamu ɗan gane wani abun amma inba hakaba tofa saidai mu roƙe Allah ya kare ta ya bayyana ta ni tsoro nama karsuje su cutar da ita,

"insha Allah ma babu abun da zai sameta tunda basuci masara akanta ba tun loƙacin baya yanzuma bazasu taɓa ciba da yardar Allah,

"to Allah ya yarda"
cewar Sameer"

"Ameen "

nande kowa yayi jigum jigum suna tunani kala kala a ran su....


Bossay yana fita ya nufi wajen motar da suka dawo da ita yanzu sai kawai ya tsaya abakin motar tunawa da yayi ashe ba muƙullin motar a hannun sa sai kawai ya kifa kansa ajikin motar ya shiga tunani wai Ameesha ta taɓata ansace ta abun yakeji kamar almara juya jiya suka kawo yarinyar amma ace wai yau ansaceta gaskiya wannan maganar da alamar tambaya shide har yanzu yakasa yarda mutanen nanne suka ɗauketa da tuncan baya basu ɗauke taba sai yanzu ace sun shigo har cikin masarauta sun sace ta gaskiya bazai taɓa yarda da hakan ba saidai kawai idan da wani abun da yasa ɓatan nata acikin nan wataƙil ma tana wani wajen acikin Masarautar da yasa ta kasa fitowa tunda masarautar da girma sukuma basu bincika ba kawai suka yanke shawarar ta ɓata anzo ansace ta, ,"sosai ya shiga tunanin yanda zai ɓullowa al'amarin yama rasa wane kalar tunani, yakai wajen awa ɗaya agun yana tsaye yarasa mafita kuma baikoma ba kuma bai kuma tafi ba, tuna rayuwar su ya shiga yi tun loƙacin haɗuwar su wata yayi murmushi idan kuma ya tuna wani abun sai yaji ransa ba daɗi wani irin ɗumi yaji akan fuskar sa hannu yasa ya shafi gurin da yaji danshi saboda tsabar shiga da damuwa da yanda yakejin zuciyar sane yasa hawaye sauko masa daga ido batare da ya shirya yinsu ba sosai yakejin sonta naƙara shigar sa
ahankali ya furta I love u baby Ameesha Allah yakare min ke aduk inda kike Allah ya bayyanaki sosai ya shiga jero mata addu'a tare da goge sauran hawayen da yaji sun ƙarasa sauko masa yanke shawara yayi kawai yaje ya tari napep yatafi gida dan bayajin zai iya komawa wajen su yayi musu magana.....

ɗagowa yayi yana niyar barin wajen kawai sai idon sa ya sauka akan wata inuwa da tayi saurin giftawa wani lungu da sauri ya juya gurin amma sai yaga ba kowa da har ya basar amma sai wata zuciyar take ingizashi akan yaje yaga komenen ya wuce yana gama ayyana hakan ya nufi wajen saidai yana zuwa yaga wayam ba kowa ƙarewa ma hanyace miƙaƙƙiya awajen hanyar yaci gaba da bi dake gurin da haske dan haka yana ganin komai kawai yaci gaba da bin wajen saida de yaga kamar ma idan yabi ƙarshen sa dajine ba wani kwana ko kuma ɗaki awajen dan baka kawai sai ya juyo yadawo yana cikin tafiya kamar amce masa ya kalli ƙasan sa idon sa na sauka ya sauka akan wani abun hannu da sauri ya tsugunna yana tunanin a inda yasanshi saurin miƙewa yayi daga gurin tunawa da inda yasanshi a fili ya furta tabbas natane wallahi na gansa a hannunta ji da muna mota loƙacin da ya riƙo hannun ta yaganshi....

damƙe abun hannun yayi yanajin kewarta tabbas wannan abun hannun tane to me ya kawo shi nan to sunzo wajen tayardashi wata zuciyar kuma tace masa to kode nan tashigo ta ɓata agun takasa komawa gida saka abun hannun yayi a aljihu yashiga dudduba gurin har inda yabaro ya koma amma baiganta ba da sauri yabaro wajen ya nufi inda part ɗin da yabaro wajen su sam,

da sauri yake tafiya dan har yana harɗewa wajen tafiya da haka ya ƙarasa part ɗin kamar daga sama suka gansa ya turo ƙufar da ƙarfi dukan su suka zuba masa idanu suna tunanin kuma me yadawo dashi dan atunanin su ya daɗe da tafiya ma,

ƙarasawa yayi inda suke tare da zaro abun hannun ta yana nuna musu batare da yace komai ba da sauri shettima ya miƙe yace a ina kasamoshi ko ka ganta ne naga abun hannun ta agunka, yaƙarasa maganar tare da karɓar abun hannu yana kalla yace ai jiya jiyanannan nasiya mata loƙacin da muka fito tanuna tanaso nasiya mata a ina ka ganshi?

"awani guri na tsince shi acikin nan basu labarin abun da yafaru har yaje gurin daga nan kuma yagansa ya kawo musu,

da sauri Sameer ya miƙe tsaye shima ya karɓi abun hannun yana mamakin jin inda aka gansa to me yakai abun hannun ta gurin gurin da ba kowa bane yake zuwa dan yana da tabbacin babu abun da zaisa su Hamra zuwa gurin barai ace garin zuwa ta jefar dashi bata sani ba....
to yake shirin faruwa abun hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....




                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[6/26, 9:53 PM] #momyn twins#: ,  ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️69&70

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

             
   to me yake shirin faruwa abun  hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....

 shettima ne ya karɓi abun hannun daga hannun sameer yana ƙara nazarin abun acikin ransa shima abun da sam yayi tunani shima ai yayi tunani maida duban sa yayi ga sam sannan yace sameer ina twins suke yakamata muji ta bakin su ko iya zuwan ta sunje wajen idan kwa bataje wajen ba tofa akwai matsala yakamata musan wani abun game da ganin wannan abun hannun ace inda aka ɗauketa daban kuma a tsinci abun hannun ta acikin nan to taya hakan tafaru anya ka tabbatar

37 / 74