uwar masarauta meji da kanta kenan itadin fa ta bance a masarauta haka take tafiya har suka qaraso wajen fadawan sarki ne suka fara yi mata kirari da gimbiya gimbiya matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki Allah yaja da ranki Allah ya kawar da idon maqiya akanki Allah yakara girma da daukaka tafiyar kide ahankali uwar gida agun sarki mahaifiya ga abun alfaharin mu sarki me adalci kowa nakine komai nakine kiyi yanda kikeso acikin masarauta masarauta takice kece uwa agunta kece gatan masaurata saboda jajircewar kine ba ataba samun matsala ba komai yake tafiya daidai da bake da bamu tunda dake muma muna nan duk inda kike nan muke Allah yaqara muku lafiya ke da sarkin mu abun alfaharin mu Kowa yace zaiyi dake shi zaiga daidai duk wanda yayi ba daidai ba dole yaga ba daidai ba duk wanda yayi da kyau shizaiga da kyau,
saiwani cika take tana batsewa tare da zama tana dora qafa daya kan daya tare da kafe dukan ilahirin muatanen dasuke gurin da kallo ganin ta zauna yasa gurin ya kidime da hayaniya kowa nafadar albarkacin bakin sa wajen gaida ita hannu ta daga batare da tace komai ba kowa nagurin yayi diff shiru gurin yayi kamar babu kowa kamar wadanda ruwa yacinye yatafi dasu haka sukayi shiru tare da sada kansu qasa kowa na fargabar abun da zasuji daga gare ta babu wanda yadago saima qara danna kai qasa suke kamar zasuyi sujjada,
acikin rashin sani Azeema ta dago dan ganin matar da tazo tana tunani ita kuma wace tunda ba sosai take jin kirarin da akeyi ba bare tayi tunani ko mahaifiyar sarki ce hakan ta dago tana qare mata kallo caraf kwa fulani ta kamata tana kallon saurin dauke kallon ta tayi daga gare ta ganin irin kallon da ta watsa mata tsayawa fulami tayi tana qare mata kallo da tunani kuma wannan daga ina saboda kaf ma'aikatan babu wanda bata sani koda sabon zuwane tasanshi idan kuma wanine zaiyi bako to nan ma sai yasanar da ita kuma idan bakon yazo anje ta ganshi kafin yazauna amma itade batasan wannan fuskar ba amma yanzu ba lokacin tambayar ta bane zata bari idan an watse zata sa akorawota taji daga gidan uban da take dan haka kawai tayi saurin ajiye tunanin agefe tare da sawa ayi mata hukuncin dagowar da tayi alhalin kowa kansa na qasa amma ita tafi kowa tafi qarfin ta sunkuwayar da kan,
bazato ba tsammani kawai taji saukar bulala agadon bayan ta ba shiri kwa ta hau susa bayanta saura qiris tasaki kuka dan ba qaramin shigarta tayi taji zafi sosai kawaide dan tana da dauriya ne amma da sai tayi kuka wata aka qara mata akaro nabiyu wanda bata tunanin zata iya jurewa dan haka tasaki kukan ta amma bata bari ya fito ba kawaide hawayene suka shiga wanke mata fuska cike da takaici ta dago tana duban me dukan nata sannan tace kayi hakuri dan Allah wani kallo ya watsama ta me kama dana tsana yanaso ya gargadeta akan abun da tayi saidai fulani bata bashi daman ba tace kawai ya hukun tata abun da tace masa kenan shiyasa ya daketa kawai yaja bakinsa yayi shiru tare da barin wajen ya koma can inda yake ya cigaba da tsayiyuwa
tunda ga lokacin Azeema bata sake gigin dago kanta ba ta sunkuyar dashi kamar yanda kowa yayi.
*Bossay*
cikin shirinsa tsaf yafara saukowa daga matattakalar benen yana ta faman sauri yana gama fitowa kwa sukayi karo da Ammi tsayawa yayi itama ta tsaya tana binsa da kallo kana tace kai kuma fa ina zuwa daman wajen ka zanzo abban ku ya kirani yace yana hanya gobe zuwa jibi zai dawo cike da murna yace Allah yakawosa lafiya muna jiran dawowar sa yafa yana shirin barin wajen ta qara dakatar dashi tace ai bakasan me zai dawo dashi dinba wutar da ka kunnowa kanka kasan yanda zakayi ka kasheta dan yace tunda har shi zaka mayar qaramin mutum to ka shirya yana da wowa za afara shirye shiryen bikin ku yace insanar dakai aure ba fashi ko mutuwa kayi sai andaura da gawarka dafe qirji yayi yana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nashiga uku Ammi dan Allah da gaske kike tace daman nataba yimaka wasa irin wannan wai mema kayiwa yariyar da har yakai haka kaga fadan da yakira yake min yace duk ni nake sangartaka kana abun da kaga dama dan haka yagama yanke hukunci inshirya yana dawowa za afara shirye shirye duk yanda naso inganar dashi duk dade bansan me yafaru tsakanin kuba amma naso inkareka da roqan alfarmar yabari adan qara lokaci ayi komai a tsanake yace shi sam besan zance ba yanda yace dole haka za ayi dan haka sai kafara shiri tun wuri danni kaina bani da abun fa zan kuma cemasa ya yarda ya hakura,
Ammi wlh ni banasonta kice masa banason ta karya min haka wlh ko na aureta bazata taba jin dadin rayuwarta ba gwarama kar ayi auren naan dan wallahi banasonta nifa nama tsaneta gabadaya dan nadade da cire batun auren ta araina kuma nagaya mata amma dayake ita mayyace shine zata bullo min ta wani wajen to muzuba dani da ita bade aure ba zata ga aure dai tayi danasnin aurena wlh a'a Aliyu kar nakuma jin kafadi haka kanaso ubanhiji yayi fushi dakai tundade kai kafara cewa kanasonta kuma har anriga da ankai kudi kaga baka da bakin cewa bakaso dole kayi hakiru ka karbeta hannu biyu kabi umarnin mahaifinka sai kaga daidai nima bason hadin nan naku nakeso ba kawaidai dan ba yanda zanyi kawai kaima kayi hakuri wallahi Ammi bazan iyaba zuciyata yanzu ba ita take so ba tace to komade menene yanzu zacen gama yagama sai kabari idan ka aure tan sai ka qara wanda kake so daga baya kasande magaifinka baze taba canza maganar saba kamar yayi kuka haka yake ji saboda tsabar takaicin da yake ciki yama kasa qaratanka mata kawai yayi gaba zai fita yaje daidai qofa zai fita dadda da fitowarta daga daki taji zancen da suke saida tabari yakai qofa sannan tace mutum sai munafurci yanaso yana kaiwa kasuwa da wayace kace kanson ta da baka sonta ai da baka bari har akai kudiba dan haka aure ba fashi ko anfasa nidakain zan dauramaka kinibabai kawai wallahi yaran zamanin nan baku da ta ido ko kulata beyiba yayi ficewar sa ita kuma taci gaba da surutanta akansa kamar yanajin ta Ammi ce tace dadda gaskiya de dande bakisan yarinyar nan ba amma da ko ke dakanki sai kince kar ga aureta bata da tarbiya ga rashin sanin kanta bata da kamun kai ko kadan nasan wallahi ya aurera zata bashi wuya shiyasa nima banaso ayi aure nan gashi kuma wai nan da sati daya zuwa biyu dadda tace to meye aciki wanann abu dan sulula kawai dauka zaki ki sulalawa mutane waya ki sanar dasu nibanga abun wuriba anan yaro ya girma har yakusab wuce aure amma yaqiyi ni wallahi yama yimin daidai da ya yanke masa wannan hukun cin amma itama yarinyar zataci qaniyarta bari ta shigo hannu nida kaina zan bata kashi in koyamata hankali sai ta nutsu duk haukan dake damun ta zansa ta saukeshi kedai bari ayi auren kikagani shima zai dena fadar bayason ta watakil sun samu sabanine shiyasa zuciya take dibansa amma da zaran anyi auren to anyi me wuyar kar ki wani tada hankalinki akan wannan dan qaramin abun daga qarshe ma kizo kiji kunya idan kika gansu suna soyewa dan haka kiyi shiru da maganar zakiga abun mamaki nafada miki dan murmushi Ammi tasaki sannan tace to dadda shikenan Allah yazaba masa mafi alkhairi agare sa idan kuma ba alkhairi bane Allah yakawo masa mafi alkhairi ya musanja masa da alkahairi Ameen dadda tace daga nan de suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin bikin da yazo musu barka tatan lokaci guda..........✍
Malejjj
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿21&22
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
*FULANI*
"saida ta gama shan qamshinta da yi musu kallon wulakanci sannan ta budi baki da kyara tafara magana,
"kowa shiru yayi yana sauraronta"
shekara da shekaru masarautar nan tana zaman lafiya amma yanzu da alama munafukai sunyi yawa ana daukar zancen masarauta anakaiwa wani lokacin to daga yanzu zamu qarfafa sa ido akan kowa zamu kwarara bincike ganin mungano wanda yake mana zagon qasa yana daukar zancen wani ana kaiwa waje,
daga rana irin ta yau mutum yasani duk wanda aka kama dahaka to hukuncin kisane zai tabbata akansa ko da alamar rashin gaskiya aka kama mutum da ita to yasani masarauta baza ta kyaleshi ba kuma hukuncin mu baibar kowa ba kama daga kan mace ko namiji ba ruwan mu da girmanka ko qanqantarka duk tsufanka baka fi qarfin mu ba hukunci dayane gaba dayan ku dan haka sai akiyaye......
"dan dakatawa tayi tare da jan numfashi sannan taci gaba.
Sannan abu nagaba shine daga yanzu za ayi canjin aiki kowa zaibar akin da yake acanza masa da wani hakane zai qara bamu damar gano me yi mana sa ido....dan haka yanzu nan za afara ba tare da bata lokaci ba,
nan ta umarci dogare da fadawan sarki da sufara kiran mutane daya bayan daya aka ringa kiran su suna fitowa za atambayesu abun da sukeyi da kuma inda suke aikin idan suka fada sai ace to daga yanzu ga inda zaka koma haka aka ringayi har aka kai qarshe duk wadan da aka kira suna gefe,
gaban Azeema ne yafara dukan uku uku gani ita kadai tsulum aguri guda ba a kirata ba saboda ba asan sunan taba gashi mutane duk sunbi sun zuba mata ido suna kallon ta saboda kaf gurin in kacire mary babu wanda yasan da zaman ta agidan dan me gadin ma da yabarta ta shigo zuwa yanzu ya manta da fuskarta bazai iya gane taba,
duk sai take jinta atakure gashi ba ace mata ta tashi ba kuma tanaso ta tashi amma tana tsoron jawa kanta wani laifin sai da nasani fitowa take dama bata fito ba haka take ji gashi kuma wanda ta fito saboda shi bata gansa ba,
babu wanda yabi takanta har aka gama warwarewa.
wanine yaje kusa da fulani murya qasa qasa da ni kaina bansan me yace ba bayan yagama kitsa mata ya matsa gefe ya koma inda yabaro,
girgiza kai fulani tayi cike da qara tamke fuska sannan tace ina sarkin dorina matsowa yayi jikin sa na bari yace Allah qara miki lafiya Allah.......
zai fara yimata kirari ta dakatar dashi cike da bacin rai tace aje afito min da Hamza da kuma wannan mutumin da suke tare har yanzu basu rabuba kenan aje afito min dasu yau za akoya musu hankali tunda basu dashi tafada tana ta faman hura hanci
da gudu sarkin dorina ya tafi wajen da yasan suna can,
bayan tafiyar sa fulani tasa aka kirama ta A Azeema jiki asanyaye ta tashi tazo kusa da ita tare da durqusawa kamar yanda ta ga anayi saida fulani tagama qare mata kallo kamar me son gano wani abun sannan daga bisani tace daga ina kike da iznin wa kika shigo gidan nan batare da sani naba tafada tana qara zuba mata idanu ,
itade Azeema tashiga tashin hankali batasan wane abu zatace dan jitayi jikin ta gaba daya ya hau bari kar taje ta fadi wani abu da zaisa agano qarya take gashi kuma ko sunan wacce take zaune awajen tama bata sani ba bare tace ga gurin wace ta tazo,
tana cikin tunanin abun da zatace kamar daga sama taji ance maryama bakuwatace jiya tazo gaba dayan su suka juya suna kallon Ammah da ta qaraso wajen daman tasan za arina shiyasa tunda ta duba dakin taga batanan tunanin ta yabata watakil tace zata bi mary shiyasa ma hankalin ta yakasa kwanciya ta taho gurin da sauri gudun kar wata matsala ta faru ilai kuwa tana tunkaro wajen taji abun da fulani kecewa kuma bisa ga dukkan alamu bakuwar tata take tuhuma shiyasa tayi saurin katse ta ta bata amsa,
gaban fulani ta qaraso suna fuskan tar juna sannan tace ayi min afuwa ban sanar dake tun jiyaba daman bari nayi sai daddare sai inzo da kaina ma insanar dake,
kallonta fulani tayi sannan tace bakuwa daga ina nidai nasan ban taba ganinta a dangin kuba bare kice min yar uwarkice tafada tana qara maida hankalinta tana jiran taji amsar da zata bata,
dan murmushi tayi sannan tace ayya ai ba yar uwata bace daman kawaide wata qawata ce da muke mutun ci da ita shine tace min in taimaka inne mawa yar me aikinta aiki anan saboda ita bata da halin da zata riqe uwar ta riqe yar ga dan qaramin yaro agaban ta idan kuma tace yarinyar tabar mata gida to batasan inda zataba gashi kuma suna buqatar taimako dan me gidan ta ya rasu sannan kuma dangin ta bamasu hali bane name taimaka mata shiyasa tayi min magana nace mata ba matsala ta kawota baza arasa ba to kinji dalilin da yakawota gidab kamar me nazarin wani abu haka ta tsaya tana kallon su suduka kafin da ga bisani tace to shikenan amma akiyaye nan gaba kafin wani ya kwana acikin masarautar nan yakamata ace ansan da zaman sa bawai kawai inganta ba Ammah tace in sha Allah za akiyaye yanzu gata nan idan da aikin da za abata sai abata in kuma babu sai inzauna da ita ashena tana taimakawa mary da aikace aikacen shiru tayi tana buqatar jin abun da zatace,
itama fulanin shiru tayi kamar bazatayi magana ba sai kuma can tace a'a da akwai daman yanzu ancanzawa kowa me aiki kema wacce take miki da ba it zata ci gaba da yimiki yanzu ba,
dan murmushi Ammah tayi duk da bahaka taso ba aranta amma afili sai ta nuna halin ko inkula fuskarta asake sai kawai tace to ai shikenan duk yanda kikayi ai daidaine ni zan wuce idan angama sai tazo ta kwashi kayanta ta fada tana juyawa tare da barin wajen,
da wani irin kallo fulani ta bita tana hararar ta dan haka kawai bata yarda da ita aranta tace basai in kin qara ganin ta ba zata zauna dani zan saka ido akanta inma qarya kike zan ganoki nan bada jimawa ba,
tana gama tunanin ta maida subanta ga Azeema sannan tace wannan amaida ta party dina anan zatana aiki daga nan kuma tace kowa yakama gaban sa kai tsaye kar wanda ya nufi inda yabaro yanu fi inda aka canza masa duk wani abu da yake buqata acan zata sa aje a amso masa daga baya amma bata yarda wani yake inda yabari ba,
haka aka ga ma yanke hukuci zama yatashi kenan amma ko A sarki bece ba sunan yana gun azaune amatsayin sarki saboda inde tana gurin bashi da bakin magana dole yayi shiru sai abun da tace dan koda wani abun yayi masa ba daidai ba to beda ikon tanka mata dande kawai kar ace masarautar ba sarki shine amfanin sa amma baya ga haka bashi da wani amfani aciki komai a hannuta yake sai yanda tace akeyi....
Kamar yanda tace hakan kwa akayi kowa ya nufi inda aka canza masa tare da raka ko wannen su saboda ba kowane yasan ko inaba aciki shiyasa tasaka akayi wa wasu jagora zuwa inda basu sani ba,
gurin yazamana babu kowa duk sun watse daga ita sai sarki sai muqarrabansu da zasu mara musu baya idan sun tashi tafiya saida taga kowa yatafi akan idonta sannan suma suka miqe dan barin wajen.
suna shirin tafiya kenan saiga su sarkin dorina tare da Hamza da baba suna qarasowa wajen dakatawa sukayi da tafiyar suna kallon su dan ita har tama manta dasu sakamakon maganar yarinyar nan da sukayi shine ya kawar mata da hankalinta akansu tama manta dasu gaba daya,
suna zuwa gabansu suka zube agabanta baba na gaida ita amma banda hamza ko motsa bakin sa beyi ba bare tasa ran zai gaida ta,
wani abune yazo mata wuya ya tsaya mata cikin hargagi da masifa kamar zata rufesa da duka tace kai gaka isasshe damai ko waikai dan gidan ubanwaye da uban me kake takama naga take taken yayi yawa agidan nan kullum rashin mutun cinka qaruwa yake naga alamar baka jin duka ko uban me ya hanaku fitowa saboda ba a isa daku ba hardaki tsofe tsofe dakai baka gudun abun da zai tabaka to kasani ko kadan baza kaban tausanyi da zansa a horaka ba cikin rawar murya baba yace wallahi banji ba lokacin da aka sanar ina bacci sai yanzu da akasa akiramu aka tasheni amma bada gangan nayi hakan ba kimin afuwa agafarce ni bada son raina hakan ta faruba yafada yana sunkuyar da kansa qasa,
banza tayi masa sannan ta mayar da dubanta ga hamza da duk abun zancen datake masa ya nuna kamar ma badashi take ba ko kallon inda take beyiba,
dubanshi ta qarayi tace kai kuma uban me kakeyi baka fito ba ko isarce tasaka qin fitowar,
sai alokacin tasamu yadago yana kallon ta ido cikin ido sannan yace bana jin dadine shiyasa banfito ba yana gama rufe bakinsa tace qarya kake shiru yayi be tanka mata ba qara harzuqata yayi tayi gaba kawai tacewa maidorina ya hukun tashi da dorina sannan sukashi dakin qasa tana gama fada ta tafi fuuuu kamar zata tashi sama sarki ma gaba yayi abunsa be saka musu baki ba,
Sarkin dorina matsowa yayi kusa da hamza amma yakasa daga dorinar bare ma yakita jikinsa saboda har yau tabon da yayi masa bai goge ba yana nan shiyasa yake tsoronsa kuma tunda ta tafi kwa ba abun dazaisa yadake sa gwara yabarsa zaidai kaisa godan qasan shima saida yace