Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   28 / 74

81K to 84K   out of 221K words

mu kuma loƙacin aka basa sarauta yazama sarki arana daya akadauramana aure tare da kishiyata da kuma nadin sarautar sa duk arana daya akayi,
ina da yara biyu kuma duk maza amma daya ya ɓata har dakina aka shiga adauke minshi kuma akaƙi fito dashi wannan abun yamin ciwo amma haka na haƙura ban tada hankali na bawai dan banaso ba kawai dan asamu kwanciyar hankali,
nadaɗe ba Allah yaƙara bani wani ɗan gashi yanzu shima anrabani dashi tun yana ɗan ƙarami nasan Allah sarki sameer duk ƙulaficin sa dani gashi ya taso batare dani ba ko yanzu yana ina ko me yakeyi nasan yanzu ya girma wataƙila ma yayi aure ko kuma ya mutu Allah masani shikaɗai nakeson gani...taƙarasa maganar cikin sanyin murya harda dan sakin murmushin dole saboda tunawa da tayi dashi tare da sa hannu ta share hawayen ta,

gaba dayansu tausayi yabasu jin yanda ta ƙarasa maganar sun san tana jin ciwon abun aranta,

shiru sukayi sunkasa magana kowa yana nasa kallar tunani ashe nan matar sarkice azaune agabansu cikin wannan halin lalle dole ajinjinawa duk wanda yayi sanadin barin ta gidan nan dan sun fahimci dole anasane aka koreta zaman tane kawai ba aso shiyasa akayi mata haka sai kuma gashi Allah ya yafisu ya tashi kafaɗunta sosai kowa yafaɗa duniya tunani kowa da kallar tunanin da yake yi,

MEER da sai yanzu yasamu bakin magana yace to me yasakika fita daga ciki ko masarautar ba tsarone?
kallon sa tayi jin tambayarda yayi mata yasata sakin murmushi me ciwo sannan tace yaro bani na fita dakaina ba fitar dani akayi ta dole saboda son zaciya daman sarauta ta gaji haka ba a iya zaman lafiya aciki duk da bansan waye ya aikata min hakan ba amma masan dole acikin kishiyoyi na ne kamar yanda naji kunce malam Yahaya muku kuma badan komai sukayi hakan ba sai dan saboda kawai ina da ɗa namiji shiyasa sukayi min haka da sun kwantar da hankalin suma ni daman basarautar nake soba koda yagirma bazan taɓa bari ya hau kan mulki ba saboda iya fara zamana acikin sa na fahimci abubuwa da dama shiyasa banayiwa ɗana sha'awar sa,


  "amma saboda rashin sani da son zuciya irin nasu suka zaɓi jefa rayuwara ta cikin garari bayan sace min da da sukayi duk nayi shiru na rabu dasu yanzu kuma sun tarwatsa  rayuwata da ta ɗana wayasani na ko shima sun kasheshi tunda basason ganin gudan jinina adoraon duniya,
shiru ta ɗanyi wani abu na taso mata daga ƙasan zuciya cikin ɓacin rai tafara magana adake tare da damke hannun ta tace ada na rabu dasu amma wallahi wallahi wallahi yanzu bazan rabu dasu sai na shigar dasu ƙara sai sun fito min da ƴaƴana kuma anbimin haƙƙina da suka zalince na rabani da ƴaƴana da kuma jefa rayuwata irin cikin wannan halin nayi shekara da shekaru akwance wallahi bazan taɓa yafe musu ba sai na dauki fansa saina biwa ƴaƴana haƙƙin su na rabasu da gidan ubansu da sukayi idan kuma kashe su sukayi suma sai na kashe su da hannu na duk wani me hannu acikin tarwatsa rayuwata da ta ƴaƴana sai yagane kuren su koda mahaifin sune keda hannu acikin wallahi bazan barsa sai naga bayansu ɗaya bayan ɗaya,
nasan bantaso cikin gata ba bansan dadin iyaye ba amma naso inbawa nawa ƴaƴan kulawa fiye da yadda nataso amma suntaso cikin iyayen su cikin gata amma wasu banzayen mugayen masu son kansu sunzo sun lalata komai tunda na taso nake fuskantar wahala arayuwata nayi auren ma masamu miji me sona ina murnar rayuwata zatayi daɗi amma suka juya komai to wallahi ƙarya kuke yanda kuka tarwatsa ni kuma sai naga bayan ku bazan taɓa bari kucigaba dajin daɗin rayuwa ba duk wata hanya ta farin ciki sai na katse muku ita da zarar na dora ƙafata acikin garin Kano kowa sai nasaka shi girbar abun da ya shuka na rantse da wanda raina ke hannun sa taƙarasa maganar cikin ɗaga murya kamar su sukayi mata laifin ko kuma waɗanda sukayi laifin suna gabanta haka take magana tana wani huci idonta duk sun firfito waje sunyi jaa kana ganin su kasan tsantsar ɓacin raine acikin su zuciyar ga kuwa jitake kamar ana gasata da garwashin wuta  sai tafarfasa take,

gaba ɗayan su babu wanda bai tsorata da yanayin ta ba ganin loƙaci daya ta burkice sai sambatu take kamar ma bata cikin hayyacin ta idan sukayi tunani kuma sai suga dole tayi fiye da hakama saboda kowa ma akayi wa haka dole yaji ciwo aransa dan haka basuga laifin taba,

"cikin daga murya tare da sakin wani kukan me ciwo tace ƙarya kuke wallahi sai naga bayanku dakain zan kwatar musu ƴanci sarautar kuma da bakwaso suyi sai sunyi uban wani yahana idan ya isa azzalumai kawai mugaye duk inda ƴaƴana suke sai naje na nemosu dan nasan basu mutu ba suna raye kuma zanje duk inda suke zankawo muku su har inda kuke...!!!! ( Ehhh... jaruma marar tsoro sabreena🤣😂sai dake😜) karfa wani yace banda tausayi jarumtar tatace ta burgeni shiyasa na ɗan dara sannan daga baya nayata jimamin daga baya Allah sarki taban tausayi😱)
taƙarasa maganar tare da  buga hannu ta akan kujera sannan ta miƙe tsaye tana ƙara sakin wani kukan tana rufe bakin da hannun ta saboda ta fahimci idan batayi wasa ba kuka ne zai ɓalle mata me sauti hanyar wajen ƙofa ta nufa dan ita kanta wasu maganganun bata san tanayinsu dan tafara fita hayyacin ta sai yanzu wasu abubuwan suka shiga dawomata nadaga irin rayuwar da tayi acikin gidan shiyasa abun yake ƙara yimata ciwo take ta faman zuba batare da tasan abun da take cewa ba,

da sauri sukayi kanta gaba ɗayan su,
   ummy ce tayi saurin rungumeta itama tana sakin kuka cikin kukan take tabata hakuri banda haƙuri babu abun da takeyi sai kuma kuka ita kukan nata ma har yaso yafi na nata saboda tsabar tausayi (kunsan mata da rauni abu kadan ma kuka yake sakasu bare taga babbar mace agabanta tana kuka dole itama ta zubar da nata)
 
   Abu da meer duk tsaye sukayi suna kallon su kowa yakasa magana dan suma abun ba ƙaramin raɗaɗi yayi musu ba suma kawai daurewa suke amma zuciyar su ba ƙaramin karaya tayi ba dande mazane shiysa basuyi mata kuka ba ammade tabasu tausayi iya tausayi kai duk wanda yaga yana yin datake magana tana kuka dole ya tausayawa mata halin da take ciki,

Abune yadafa su gaba ɗayan su yashiga rarrashin su sannan ya kamo hannusu yamaida su kan kujera ya zaunar dasu saidai yana zaunar dasu ma'ana(sabreena) ta ƙara miƙewa tsaye tare da cewa nifa bazan ƙara zama ako ina ba ayau nake so zuwa kano duk dare agarin Kano nake son kwana dan inbagani acan ba zuciya ta bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba dan haka kawai kubarni intafi nagode da kulawar da kuka bani da kuma irin taimakon da kukayi min bazan taba mantawa daku ba Allah yabiyaku da mafificin alkhairi nasan kungama yimin komai badan kuba da tuni wani zance ake ba wannan da tuni ina nan akwance kamar yanda sukeso su taganin na ahaka,
dan haka dan Allah kurabudani in tafi ko nasamu sauƙin abun da nakeji idan naje a aiwatar da ƙudurina,
yanzu zan tafi Allah yabar yabiyaku idan komai ya tafi yanda nake so har nan zan kawo muku ƴaƴana kugansu zan kawo muku ziyara dan bazan taɓa mantawa daku ba acikin rayuwata kuɗin na musamman ne agareni nabaku wani gurbi acikin raina domin kuntaka muhimmiyar rawa acikin rayuwata duk godiyar da zanyi muku bazan taɓa biyanku taimakon da kukayi min,
ni zan wuce Allah yaƙaddara saduwar mu tafaɗa tana ƙara miƙewa tsaye da sauri ummy tayi saurin dafa kafaɗunta ta tace dan Allah kaikitafi kibarmu kibari mutafi tare muma bamason kiyi mana nisa duk inda zaki munata tare dake zamu biki tayi maganar ta ƙokarin ganin ta zauna amma bata zauna ba taci gaba datsayiyuwa batare da ta tafi ba......✍️



                 
                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(mrs bmb)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
           
[6/9, 10:08 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️53&54

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️


    "Abu ne ya fara yi mata magana cikin  sanyin murya yafara cewa baiwar Allah kiyi haƙuri banga lafinki ba nahakan amma de zakai kiyi haƙuri abi komai asannu baikamata kije ahakaba kibari sai mun fara bincike kafin kije cikin gidan tunda kikaga haka tofa ba ƙaramin abune me sauƙi gurin gano koma waya yi miki haka Yakamata mufara zama ayi nazari akan  waɗanda kuke mu'amala dasu da kuma abun da yataɓata shiga tsakanin ku na saɓani ko makaman ci haka ko kuma faɗa dade sauran abun da ba arasa na zamantakewar yau da kullum wannan ce hanya me sauƙi kawai wajen gano wanda ya aikata miki hakan amma garaje da sauri duk bana mubane sai munbi komai asannu amma dan Allah ki ajiye batun tafiya ke kadai kibari tare zamu tafi sai mufara binciken ko ya kikace shiru yayi yana jiran jin amsarta
     
" shiru tayi tana nazarin maganganun sa kafin daga bisani ta kalle sa sannan tace naji bayanin ka kuma hakan yakamata ayi banyi Wannan tunani kwata kwata idona ya rufe tabbas bincike yakamata infarayi kafin su san da inaraye dan nasan yanzu gaba ɗayan su babu wanda baiyi tunanin na mutu ba mugaye kawai wallahi inna tuna abun da sukayi min sai naji kamar yanzu inganni agaban su in caccaka musu wuƙa musamman ma idan na tuna raba ni da ƴaƴana da sukayi tsakanina dasu saidai Allah ya isa Allah ya tona asirin su, "Ameen duk suka amsa mata dashi"   bayan tayi shiru ta cigaba da cewa  ammade kuyi hakuri bazan iya zaman nan ba zantafi kano acan zan zauna inyaso duk abun da zanyi nayi acan,
  "ummy tace ai ba matsala duk sai mukoma can din amma to idan munje a ina zamu sauka?
   Abu yaya saurin tarar numfashin ta kafin maama tayi magana yace habade gurin zama ai bazai mana wahala ba akwai wani abokina acan sai insakashi ya samo mana gida asaka duk abun da ake buƙata sai kawai mukoma gabaɗayan mu,
    "Nifa yau nake son tafiya maama taƙara gaya musu,

   "Abu ne ya bata amsa da cewa maama yanzu fa babu loƙaci kinga la'asr ta wuce magariba ake shirin yi kafin muce munje ai dare zaiyi mana kuma kinga ko gidan da zamu zauna ba asamu ba idan munje ina zamu sauka acikin dare, kiyi haƙuri kibari ko nan da jibi ko gata sai mutafi San  anshirya komai atsanake,

   batare da ta tanka masa ba ta juyar dakai tayi irin alamun nifa ko me zakuce bazan yarda ba,
  
  jin shirun nata yasa Ummy ƙara bata baki akan tabari din sa tafi nan da jibin ko gata, amma itama tace a'a itafa bataso ta kwana ako ina inba Kano ba batason ta ƙara kwana awani wajen sai acan garin,
  
duk yanda zasuyi mata bayani ta fahimta tabari din amma taƙi aminta tace ko ita kaɗai ce su rabu da ita ta tafi idan yaso su sako duk sanda suka shirya,
  
    "meer ne yasaka baki shima ya gwada sa'arsa yace dan Allah kekwa kibari mana ko zuwa gobe amma yanzu kafin kije dare zaiyi sosai ga hanya bata da kyau sai kinke ansace ki  ahanya kinga ba ke ba daukar fansa kuma bazaki ga ƴaƴan naki dakikeso kigani ba,
amma inbaki yarda ba   ga hanya nan inkinfi so a kwamishi ki sai ki tafi saidai muce ki gaida waɗanda suka kwamishe ki dan ba inda zamu,

    "zazzara ido ta shiga ys tana tunanin maganar sa to kode da gaske yake kai kumafa hakan zata iya faruwa asace tadin koma aje idan ansace ta din aje akasheta ma gaba ɗaya kai inaa tafasa tafiya saboda maganar gaskiya ta yarda da maganar sa kuma tana tsoron hakan,
  
   "dan murmushi Abu yasaki irin nasu na manya, yana ɗan satar kallon ganin yanda tayi zuru zuru da ita alamar tsoro, fakar idon ta yayi ya kalli meer tare da daga masa gira sannan yayi masa alama da hannu da yacigaba da abun da yake ma'ana yaci gaba da tsoratar da ita ɗin,
  dan ya fahimci wannan tsohuwar taurin kai zatai baza a iya lankwasa ta  sauƙin rai ba dole sai da dabara,
 
  "Meer yacigaba da cewa Ni wallahi ma kitaso in rakaki ki hau mota amma mu fara yin sallamar bankwana dan nasan bazamu ƙara haɗuwa ba saidai muce Allah ya jiƙanki dan kamar sunan ki gawa suna daukarki zasuje suyi romon ki abawa dodo jinin ki ya shanye shikenan ke kuma saidai idan munzauan muce Allah sarki baiwar Allah nan da muka taɓa haɗuwa da ita ansace ta akan hanyar ta ta tafiya daukar fansa da take ƙudirin yi,

  "dan Allah yaro wai da gaske kake tafaɗa cikin nuna tsoron ta afili kai yaɗaga mata tare da cewa gasu Ummy ki tambaye su kiji idanni kin ƙarya ta ni idan kikaji daga bakin su sai kifi yarda tunda ni kin maidani maƙarya ci yanzu.... kaga ni rufe min baki da jawowa mutane bala'i fayaƙu khairan au liyasmut(kafaɗi alkhairi ko kai shiru),
  
   da haka suka ci gaba da tsoratar da ita gaba ɗayan su babu wanda bai faɗi albarkacin bakin sa ba wajen tsoratar da ita ɗin aikam kuma sun ci nasara dan ta tsorata kam ba ƙarya amma fa duk da haka bata ce musu tayarda zata zauna ɗin ba,
 
saida suka sha wahala kafin ta amince musu shima kuma zuwa gobe da safe suka ce mata sun yarda da hakan,

bayan da suka iya dole suka fara shirye shiryen tafiya kano gobe,
  tun aloƙacin batare da kowa ya tafi ba Abu yakira abokin nasa yasanar masa buƙatar sa ya kuma tabbatar masa da zuwa gobe yake son komai ya kammala, abokin nasa ya amsa masa da angama bashida matsala za'asamu ko yau yake so zaiyi ƙoƙari yasa asamomu su,   nande yayi masa godiya sannan sukayi sallama,
anan sukaci gaba da zama har aka kira sallar magariba sannan suka tashi Abu da meer suka ta tashi suka tafi masallaci ita kuma Ummy ta kai maama dakin da ta kaita ɗazu tana nuna mata de komai sannan ta fita itama dan gabatar da tata sallar,

                *Kano*
*___S&S__ sam&sumy

    "kiran sallar magariba ne ya farkar dashi daga baccin da ya daukeshi ba shiri,
  ahankali ya shiga buɗe idonsa bai tun yana ganin dishi dishi har ya ware su amma baigama tantance a inda yake ba, dan yana budesu yaƙara rufesu tare da ɗaga hannayensa zaiyi  miƙa dan yama manta a inda yake yana ɗaga hannu sai ya bude idon sa basu sauka ako ina ba  sai suka sauka akanta da take kwance kan cinyar sa bacci yasa daga kan kafaɗar sa ta dawo kan cinyar sa baccin ta take hankali ta kwance kamar tana ɗakin uwarta..

ai baigama yin miƙar ba ya katseta tare da zaro ido da mamakin kansa sai yanzu ya tuna wai bacci yayi agurin nan zuba mata idanu yayi yana kallon ta ganin ko motsawa ma batayi baccin ta kawai take yana so ya motsa amma yakasa hakannan yaji bayaso ya tashe ta,
mayar da kansa yayi jikin seat din motar tare da ƙara lumshe idon sa hakan nan yaji duk wata kasala ta saukar masa kodan daman ance ba kyau bacci bayan sallar la'asr idan ka tashi sai kaji jikin duk ya mutu ga ɓacin ra da zaka tashi dashi to watakila shima hakan ce ta faru dashi,
    yana ahaka shi ba bacci ba shi ba ido biyu ba yanajin har aka tayar da sallah a masallaci amma yakasa motsawa Saida aka kusa idarwa sannan yasamu damar buɗe idon sa still de ya da take tunɗazu ha take har yanzu bata motsaba, ahankali ya shiga ɗaga hannun sa za tashe ta sai kuma yafasa yana tunani ta yanda zai tashe ta din tsoron shima kar ya tasheta tazo taci gaba da yi masa kuka kamar ɗazu,
    ba yanda ya iya haka ya daure yakai hannun sa zai ɗan daki gefen ta sai kawai yaga tayi juyi ta juyo da fuskarta gabansa da fuskarta can wajen staring take kalla yanzu kuma da ta juyo sai yazamana suna facing din juna yana kallon fuskarta sosai,
acikin rashin sani cikin magagin bacci ta ɗora hannun ta akan cinyar sa ashe shikuma hannun ta tunda ba controlling dinsa akeba sai ya wuce inda ba a akeshiba, ya sauka akan Alulun sa (bana dinsa sandar girman sa) ,
zabura yayi jin inda ta taɓa tare da kallon gurin zaro ido yayi ganin batama san tanayi ba kuma hannun nata nakan Alulun sa bata cire ba runtsi ido yayi ƙam jin wani abu ya taho masa tundaga kan ɗan yatsan sa ƙafa harzuwa can ƙololuwar kwanyar kansa take yaji jikin yayi masa yimmm gaba ɗaya sai kace wanda sanyi yake shiga haka yake jinsa yimmm abu na mishi yawo acikin kansa,

shide tunda yake baitaɓa tsintar kansa cikin irin wannan yanayin ba duk dazaman waje da yayi amma baitaɓa riqe wata maceba bare har ya haɗa jiki da ita bare kuma takai ga antaɓa masa babbar masarautar sa,
shiyasa yake jin abun kamar a mafarki

28 / 74