hannun taba yana cikin haka shikadai yakai wajen 20 minutes agaban ta sannan aka turo qofar dakin ahankali batare da anyi sallama ba,
jin anbude qofa kuma ba ayi magana ba yasa shi yadan dago tare da juyowa yana kallon qofar shigowa matar da yagani ce yasashi dan sakin murmushi buda masa hannu tayi daga inda take itama tana sakin murmushi ahankali yataso duk da ayanayin da yake bayason tashi amma ita ta wuce haka agurin he can't reject her hug dole yayi accepting dan haka jiki babu kwari ya taso yataho wajen ta yana qarasowa yafada kanta rungume shi tayi sosai ajinkin ta tana qarajin sonsa na ratsata shima awajensa hakance take faruwa yaji dadin zuwan nata be saketa ba harsai da yaji yadan samu nutsuwa sanna yaraba jikinsa da nata yana dagowa takamo fuskarsa tana kallon kwayar idon sa saida tagama qare masa kallo sannan tace MA ASABAKHA ya hayatee (me yake damunka rayuwata)
be bata amsaba kawai da hannu yayi mata nuni da wacce take kwance akan gadon,
kallonta tamayar gun da yake nuna mata shafo fuskar sa tayi sannan ta danyi murmushi tare da kamo hannun sa taqara dashi gaban gadon ta zaunar dashi kan kujerar da yatashi itama ta jawo wata ta dawo gabansa ta zauna tana kallon sa hannuta ta dora akan nasa sannan ta shiga cewa don't worry ur self my dear any thing will be successfully just continue pray for her it's only she need, so mind ur self in sha Allah nan gaba saidai ma abun yazama past tense sai dai story, storyn ma wataran baza ka bayar ba komai zai wuce da yardar Allah kaji kai yadaga mata tace yauwa haka nakeso kacire komai aranka bakyau yawan damuwa ko wani abunne yaqara samunta kai yadaga mata sannan yabata labarin abun da yazo ya tarar tana yi yaqara sa bata labari fuskar sa dauke da damuwa,
Sosai taji tausayin matar da kuma dana nata cikin kulawa tafara bashi baki da kwantar masa da hankali,
ahaka tacigaba da rarrashinsa har tasamu yafara sakewa da ita, yabar fushin da wadan can mutanen suka hafar masa dashi kwantar da kansa yayi akan cinyarta yana maida numfashi batare da yayi magana ba ganin hakan tagane me yake nufi dan haka ta daga hannun tana shafa masa kwantacciyar suman kansa da ta sha gyara kana ganin ta kasan ankashe mata makuden kudi wajen gyara ta murya qasa qasa ta kira sunan sa ahankali shima ahankalin ya amsa mata da na'am cikin yaren su na larabci tace nifa ina ganin maganar danayi maka tun kwanakin baya kaqi yarda nake ganin fa indai ba ita zamubi bana ganin matar nan zata samu lafiya dukdade sauqi na Allah ne amma wannan allure alluren da kuke mata da kuma magungunan da kuke bata banajin zasuyi aiki dan da zasuyi da tuni sunyi yanzu fa tsawon shekaru biyar amma anata abu daya ba wani sauyi akan lamarin nata bisa ga dukkan alamu fa banajin wannan matar akwai wani sirri ajikin ta inba asiriba to da aljanu ajikin ta wannan ba maganin asibiti ne zaiyi aiki ajikin taba dole a kira malami yazo ya dubata ko kuma mu mukaita aduba ta tuntuni nake gaya maka amma kaqi amincewa kayi hakuri ka amin ce akaita wannan shi kadaine solution idan mukaje malamin yasanar mana babu komai ajikinta sai kaga sai nudawo muqara shiri akan abun koda fitane sai muyi da ita suma su gwada tasu basirar akanta tundade mude har yanzu Allah besa munyi nata abun da zaisa tasamu lafiya kayi hakuri nu jarraba wannan din shiru tayi tana kallon sa tare da jiran jin amsar dazai bata aranta tana addu'ar Allah yasa ya amince,
shiru yayi yana nazarin maganar ta saida yadan dauki lokaci sannan murya cikin rauni yace ummy nima maganar da nakeson nayi miki kenan saboda naga abun yaqi ci yaqi cinyewa gashi haryanzu bata magana ba wani alamar zata samu lafiya musamman ma abun da naga tanayi dazu bakiga abun da tayiba ta tsorata ni sosai saboda bata taba yin abun da tayi yauba harni da take yarda dani inriqeta amma yau da qyar na riqeta amma abun da yafi ban mamaki shine maganar da tayi tsawon lokacin nan bata taba furta ko A ba amma yau naji tayi saidai kuma yanayin natane na daban da sauran da takeyi yaqarasa maganar cikin murya me cike da rauni da tausayi,
Shafa fuskarsa tayi itama cike da tausayin dan nata tace plss ka kwantar da hankalin ka in sha Allah komai yazo qarshe bi iznillah muna zata samu lafiya zaka cika burinka kayi hakuri kaji,Kai ya yadaga mata sannan yace ummy yaushe za akira shi tace duk sanda kake so ko gobema zansa ka anemo mishi zaizo harna yadubata kar kadamu ka barmin komai a hannuna taqarasa maganar tare da miqewa tsaye tace oya get up qintashi yayi saboda yasan me take nufi shiyasa ma beso ta biyosa ba dan ko gaya mata ma beyi ba ya fito amma saida akasamu munafikin da yagaya mata yafito ba,
ganin yaqi tashi tasan zancen daman yace mata anan zai kwana bazai bita ba ganin hakan yasata ta dan hade rai tace I get up ko bakaji ba tafada tana kama hannuwan sa tare da miqar dashi tsaye dan marairaice fuska yayi alamar tausayi, "kawar da kanta tayi tare da cewa u know de I can't leave without u dan haka don't waisting my time dare nayi ba yanda ya iya dole yabita suka fito daga ward din har sunzo bakin qofar ya tsaya tare da dubanta yace ummy bari ingayawa wadanda zasu kula da ita saboda wadancan nayi firing dinsu daga wajen ta saboda basu san me suke ba kallan sa tayi tace kar kadamu da wannan muje kawai idan munje gida zan kira insanar da wadan da zssu kula da ita nabar wayar agida bahaka yaso ba amma ba yanda zaiyi dole yabi bayanta suka tafi suna fita driver yaqarso wajen da sauri ya bude musu suka shiga shikuma ya shiga driver seat ya zauna tare da tayar da motar yaja suka fita daga asibitin tunda suka tafi bawanda yaqara cewa komai har suka qarasa bakin wani tanqamemen gate wanda girmansa yakusa cinye layin gidan kuwa yafi kowanne gida girma acikin unguwar horn ya doka tun kan yaqaraso gurin da sauri gate man din ya wangale musu gate din sukuma suka danna kai cikin gidan,
Wow masha Allah saidai muce Allahumma arzukuni fi hazal bait,kana shiga gidan saboda tsabar fitulin da suke ciki masu tsada da yawa babu abun da baka gani komai tarwai kamar ma ba dare ba saboda ko allura kayar idan ka duba sai ka ganta wani qaton gidane wanda kana ganinsa kasan bana kananun mutane bane na masu hannu da shune manyan mutane masu kudi iya kudi saboda tundaga yanayin ginin zagane hakan ga gefe da aka zagayesa da fulawoyi koraye can gefe kuma guiding da aka qawatasa ga gurin shaqatawa acan gefe shima da fulawoyi sai tsuntsaye da suke sha qagi agun wani guri na qara hangowa inda tafkeken swimming pool yake ga kujeru agaban sa iska sai kada ruwan take gwanin ban sha'awa da burgewa kalar sa sky blue ne kalar sararin samaniya gashinan de abubuwa da yawa harabar gidan wanda wasuma bansan suba wasu kuma idan na tsaya kwatanta muku tofa zamu iya sati bangama ba shi kansa kasan gidan abun kallo ne da burge wa saboda wani abune a shinfide shi ba tiles shi ba interlock ba shi ba tarazo dan har fakar ido nayi na tsugunna na shafashi amma ban iya tantance menene ba haka naqara bin gidan da kallo komai yayi gida iya gida ina mamaki kuma yanda wajen take haka da kyau to ina ga cikin gidan kenan tode muje zuwa dan jin yanda yake,
bayan driver ya tsaya a parking lot inda ya ajiyeta ajerin motocin dake gurin yayi saurin fitowa tare da sa hannu ya bude musu qofa suka fito ummy ce tafara fitowa yabiyo bayanta jira tayi sai da yafito sannan ta kama hannun sa suka nufi qofar wata irin qofa ce wacce ban taba ganin irin taba tunda nake adunyi ko a film ko littattafai bantaba gani ba banta jiba suna qarasowa gurin ummy ta daga hannun ta duk yatsu biyar abun mamaki sai kawai naga qofar ta rabe a hudu sama da qasa da kuma gefe da gefe suna shiga kuma sai wani abu ya fito takawa sukayi sai yayi qasa dasu dan garin leke na sai da nakusan faduwa amma de na dake bankai ga qasaba nayi saurin riqe kaina na labe abayan su inajin tsoron kar in fadi tundade babu a hause gidan miji babu mokotama kuma baza ataba baza ataba samuba bare ince wani abu kuma nasan me kuma duk babu agidanku idan akwai wadanda suke da sumin magana inzo ingani😎😎
bawani tafiya naga abun ya tsaya adaidai wani dan qareren falo me girma gaske wanda akacika shi da abubuwa daban daban abunde sai wanda yagani komai na falon white and goulding fent din falon fari sai kuma kwaliye kwalliyen falon komai fari harda labule suma farare ne sai kuma kujerun falon da suka kasance farare saiti biyu ga dinning area agefe inda can kuma daga gefe wasu twins din stairs wanda suka wani irin kanannade daya yayi dama daya yayi hagu wani babban mutum kyakkyawan gaske fari tas dashi nagani akan kujera dauke da space a fuskar sa sai kuma jarida a hannun sa gefen sa kuma wani dan qaramin table ne me dauke da fruit sai cup dake hannun sa yana sha jin sallamar su yasa shi ajiyewa tare da kawar da jaridar hannun sa gefe tare da sakar musu wani irin qayataccen murmushi irin nasu na manya,
"qarasowa sukayi itama ummy nasakar masa murmushi tare da zama kusa dashi tana cewa ANA ASIF BADRIJAKA SAMHAINI YA ZAUJ.......✍️✍️✍️
to masu karatu karda ku wahalar da kanku wajen tunanin wannan page din duk acikin littafin sarki sameer yake kude muje zuwa yanzu akafara ✍️✍️✍️
[5/23, 8:38 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿33&34
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"qarasowa sukayi itama ummy nasakar masa murmushi tare da zama kusa dashi tana cewa ANA ASIF BADRIJAKA SAMHAINI YA ZAUJ.......
"daga zaunen sukayi hugging din juna tare da manna kowa kiss agefen kumatu barin dama da barin hagu irin de yanda larabawa suke yin gaisawar su,
"duban ta yaqarayi sannan yace da MA TAF'ALU(daga ina kk) tace masa YAZ HABU ILAL MUSTASHFAH(daga asibiti muke,
tunda yaji haka yamaida dubansa ga dan nasa saboda yasan shine dalilin faitar nasu adaren nan ganin yayi sai faman qara damke fuska yake dan murmushi shi yayi sai yace kai kuma me yafaru naga kani tacin magani ko halin ne ya motsa bai bashi amsa ba illa ma tashi da yayi yana niyar barin falon,
"MEER"
Ummy ta kira sunan sa tsayawa yayi cak batare da ya juyo ba tasan bazai tasoba dan haka ita tashi taje inda yake tare da zagayawa ta koma gabansa idanu ta zuba masa tana kallon sa dauke kansa yayi daga gare ta fuskarshi ta riqo atafikan hannun ta duka biyun sannan tace to duk wannan fushin nameye ne banace za akula da itaba yanzufa zan kira insanar dasu pls kadena sawa ranka damuwa banason ina ganin ka irin haka saboda banajin dadi kaji hannun ta yacire daga kan fuskarta sannan murya qasa qasa kamar wanda bayason yi ko ince me koyan magana haka ya bude baki cikin rarraba maganar tasa yace I'm going to sleep bacci nakeji yana kaiwa nan yayi gaba abunsa batare da yajira cewar ta ba bisa tayi da kallo har ya qulewa ganin ta sannan taja qafarta ta koma wajen mijin nata,
kallon ta yayi yana dan murmushi sannan yace me yafaru ne, dan gyara zama tayi sannan tace ai kasan ne zai faru kofa gaya min baiyiba ya fita shikadai acikin daren nan shiyasa nabinshi bangayama ka ba kuma naje zantaho dashi wai bazai dawoba yanuna min acan zaikwana shine na tilasta masa muka taho shiyasa kagansa haka,
"Allah sarki hala shida mutuniyar tasane? "tace masa karshen zancen kenan nande tabashi labarin abun da yafaru da tattaunawarsu akan za akira malami gobe shima yanuna jin dadinsa da hakan da yaji sunce shima anasa wajen ba yarda beye da meer ba akan yabari akira amma yaqi amincewa dan shima yadade da sanin ciwon matar nan bana asibiti bane amma taurin kan dan nasa ya hanasa ya yarda sai yanzu da yaji uwar bari
nande suka cigaba da hirar su basu tashi daga wajen sao wajen qarfe daya da wani abun kafin daga bisani suka tashi suka tafi makwancin su domin bawa gado hakkin,
*Tambaya*
"Suwaye wadannan mutanen?
"Su 'yan garin yemen ne garin da yake yankin aqasar larabawa Alhaji Umar Ibarahim dan kasuwa ne sosai wanda shi asalin sa ba a yemen yake ba dan Nigeria acikin garin abuja yake da zama kasancewar sa me yawan fice fice saboda siye da siyarwa zuwa qasashe da ban daban saboda baya wasa da neman kudi tunda kan qananun sana'a yafara kasuwan cinsa har Allah yataimake sa yazama wani aharkar kasuwancin sa saboda rashin gata da rashin kudi da yataso yasa baiyi wata makaran tar boko ba iya kacin sa secondary hakanne yasashi dukufa gurin neman kudi wanda yace idan ya nemin kudin sai ya shiga makaranta saboda iyayen sa basu da hali gashi kuma irin kulawar da suke basa tasha bambam da yanda yaga ana kula da qannen sa tunda yafara neman kudi agarin yake shan wahala dan wataran ma sai yasamo idan yadawo sai akwace masa kuma wannan halin matar babansace saboda shi bashida uwa agidanagurin mahaifinsa kawai yake samun sauki dayagane haka sai yadena nunawa daga qarshe ma da yadan tara sai yayanke shawarar barin garin da farko da qin amincewa da maganar tasa akai saidaga baya kuma kishiyar mahaifiyar tasa ta tsaya masa tace yaje ahaka yabar gidan ya nufi garin lagos acan yake neman kudin sa be waiwayi gidaba sai bayan shekara biyu sannan yadawo ranar da yadawo kwa yaga gida agarqame da kwado alamar sunyi tafi wayoyin su yakira dan jin inda suka tafi amma sai yaji duk akashe makotansu yashiga dan tamabayar inda sukaje anan ake sanar masa da cewa sun tashi daga gidan yanzuma haka wasu sundade da shiga cikin sa yatambayi inda suke akace masa babu wanda yasan inda suka tafi hasalima ko sallama basuyi da kowaba suka tashi yaahiga damuwa sosai akan jin wannan batun aranar de sai hotel yakama ya kwana da sassafe kwa yaqara barin garin ya koma inda yafito kullum yana cikin zulimin ahalinsa da tunanin inda suke kullum waya ahannu yana gwada kiransu amma ko sau daya bata sake shiga ahaka har ayafara cire rai da su yacigaba da neman sa inda kuma maganar karatunsa ta kusan gogewa saida wani mutum yabashi shawara akan yanemi ilimi sai kasuwancin nasa yafi tafiya haka yafara makaran ta anan garin bayan ya kammala kuma sai ya watsar da wani batun karatunsa yaci gaba da kasuwancinsa dan shi agurin sa bega amafanin da zaiyi da kudin gwamnati ba dan haka bazai nemi aiki ba ahaka yafara zama wani daganan kuma ya koma yemen da nemansa anan ne Allah ya hadasa da matar auren sa Watakon ummy ummy kuma asalinta yar garin ce cikakkiyar balarabiyace kyakkyawar gaske asalin sunan ta shine ummu kursum bintu bilal(bafa kiba kirawa😜)
iyayen tama duk yan nanne dayake shima ba qaramin kyakkyawa bane gashi fari tass sai ka rantse ma shima balaraben ne haka shakuwa tafara shiga tsakanin su tun suna soyayya aboye har tarafa bayyana lokacin da yan gidansu suka gano tana soyayya da wani yaren daban kuma dan qasar bakar fata sai suka hanata kulasa amma taqiji ta nuna musu itafa bazata iya rabuwa dashi ba,
iyayen ta baqaramin bacin rai suka nunamata ba akan sai ta rabu dashi amma taqi duk da kasancewarsa fari tass amma hakan be hanasu hantarar sa ba saboda duk daya suke dakansa da sauran baqaqen babu yanda basuyi ba gurin rabasu amma abu yaki ci yaki cinyewa yarinya kullum bata ci bata sha tashiga wani hali daga qarshedai har kwantar da ita akayi a asibiti amma taqi samun sauqi dan har likitoci sun ma sana shaida musu akan tasamu ciwon zuciya kuma indai ba abata abun da takeso ba to koda yaushe zuciyar ta zata iya bugawa ta mutu,
Nanfa hankalin su ya tashi gaba daya suka rasa madafa da suka gade basu da yanda zasuyi kawai suka amince akan yaron yaturo iyayen sa tofa anan akeyin ta bashi da iyaye besan kuma inda zaifara nemansu ba tunda yayi yayi iya qoqarin sa wajen neman ahalin sa amma be samu ba dan haka kawai yace musu bashida iyaye duk sun mutu nanfa suka ce tofa saidai tai hakuri dan bazasu taba bada yarsu wanda bashi da asali ba indai yansonta saidai yaje yanemo danginsa suzo har nan sai ayi maganar nande ya shiga tashin hankali wajen inda zai fara har unguwar tasu ya koma ko anji labarin su amma shiru babu wani labari daga garesu dawowa yagaya musu akan shifa bashida kowa su taimaka subashi bazai taba cutar da itaba sukace basu amin ceba,
Ummu kursum dataga haka sai kawai tasamu waya ta kirasa aboye saboda wayama anhanata dashi amma kwace wayoyin ta gashi anhanata fita shine ta ari wayar qanwarta ta kirashi tace masa yazo ya gudu da ita suyi aurensu shikuma yace tayi hakuri su cigaba da lallaba iyayen nata da haka har su amince ba haka tasoba amma ba yanda ta iya dole tabi yanda yace ahaka kusan kullum hartafara satar hanya tana fita suna haduwa da taimakon kawarta da kuma me gadin