idon ta duk sun kunkunbura sunyi ja duk ta canza kamanni kamar ba wacce ya dauko dazuba ras da ita amma yanzu ta sanadin sa ji yanda ta koma,
baisan lokacin da yadaga hannun sa ba ya shiga goge mata hawayen da yabata mata fuska,
saida yagama goge mata duka sannan ya tallafo duk fuskar ta a hannun sa sannan ya furta I'm sorry stop crying I hate it,
gefe tayi da fusakar ta sannan tace kanaso in tsaya kaci gaba da yaudarata ne ai bazan kara yarda da kalaman kai ba ba wani abu kuma da zaka kara fada min da zaisa inyarda dakai koma meye ni nace naji kaje kawai zanci gaba da zama anan duk sanda kasake shi nina na koma gidan amma ba inda zani,
dafe kansa yayi tare da rufe idon sa da bude su duk alokaci daya aransa yace yau nadaukowa kaina bala'i wannan wacce irin yarinyace da har zai bata hakuri amma taringa yi masa abun da taga dama duk irin bayanin da yayi mata amma basuyi tasiri aranta ba wacce irin zuciya ce da ita watakil sai ya nuna mata ko waye shi zata fara fahimtar abun da yake cemata dan wallahi yafa fara gajiya da ita ta fara isarsa bayaso takaishi bango yazo yanayi mata abun da bazataji dadi ba saboda yana danjin tausayinta tundazu yake danne zuciyarsa amma tana neman takaishi karshi,
taba kaiwa karshen maganar ta dan matsa daga gurin sa ta juya zata bar wajen.....
yanzuma kamar dazu haka haka yakara saurin riqo hannun ta saidai yanzu bata bari ta fada kansa ba ta tsaya da kafafunta,,
zatayi magana kenan yadaga mata hannu shiru tayi kwa saboda ganin yanayin face dinshi ba alamar wasa acikin ta itama daman karfin hali kawai take amma zuciyar ta cike take da tsoro kawaide basarwa take tana nuna batajin tsoran sa amma taciki na ciki,
"baijira wata wata ba ko jiran taqara ce dashi wani abun kawai taji yayi sama da ita, zaro ido tayi tafara kokarin saukowa amma yahanata damar yin hakan, rikon jarirai yayi mata yafara tafiya da ita, tana tafaman motsi sai wurwurga qafa take tana cewa ya sauketa amma ko kallon tama baiyi ba bare tasa ran zai ajiyeta din ahaka yafita da ita,
"Su bossay 'yan muna furci ashe suna labe suna jin duk abun dasukeyi suna jin motsin su sukayi saurin barin wajen suka koma falon tare da zama akan wani benchi dake gefe agurin,
Suna zama shikuma yafi to da ita yana fitowa suka hada ido dasu sai kawai ya hade rai kuma kallo daya yayi musu yagane basu da gaskiya dan haka bai tankawa kowa ba yayi gaba abun sa saboda bayaso ma yatsaya su kawo masa raini dan haka yayi gaba har yakai bakin qofa sai ya tsaya batare da yajuyo ba yace inkun fito make sure kunrufe ko ina yana fada musu haka ya fice,
"kallon juna sukayi sai kawai suka kwashe da dariya harda tafawa saikace wasu mata sai da suka gama dariyar tasu, Shettima ne yafara cewa lalle mutumin nan mu zaina rainawa hankali sai yayi abu sai kuma yazo yana wani hade mana rai waishi dan kar agano wani abun baisan mun ranfo jirginsa ba tun wuri,
bossay ya dora da cewa tab babbar magana karfa muje raishe ya juye da mujiya dan kwali zaija hula dan naga alamar watakil daga tsarin qarya za awuce da da tsarin gaskiya kajifa yanda yake mata magana dazu ni wai daman yana kula 'yan matane da har yasan yanda zaikwantar da murya yayi musu magana ya rarrashe su?
"Shettima yace hmm wallahi ko daya ni tunda nake dashima bantaba ganin ya kula mace ba iyakacin sa da mace kyara da hantara da fada inta kama ma aje ga mari amma kaga yau shine wai harda bata haquri abun da bayayi iya zamana dashi baya bawa mutane hakuri mutane biyu zuwa uku yake iya bawa hakuri arayuwar sa shima sai yazame masa dole amma yanzu gashi yabawa wata macen lalle yau rana ce ta musamman badan halin da muke ciki ba da sai na hada mana dan qaramin oarty a masarauta ko ya shaida, dariya bossay yayi yace aikam de yakama muyi masa gaskiya nima nayi mamaki wai hardacewa I'm sorry stop crying I hate it hhhhhh gaba dayan su suka qara saka dariya, saida suka gana dariyar tasu da gulmar tasu sannan suka miqe suma suka fita tareda kulle kofar sannan suka juya suka nufi inda sukayi parking din motar,
atare suka waro ido tare da kallon juna sannan suka qara mayarwa gurin ganin ba mota ba alamar ta,
" kamar wadanda ake juyawa atare yanzu ma atare suka juya wajen gate din ahangame suka gansa,
"Bossay ne yace wai tafiya yayi?
Shettima "yace ga zahiri kana gani kuwa,
"to ina yatafi?
ni ina zansani bayan munaa tare dakai rashin mutunci ne kawai nufin sa muhau motar haya,
tab gaskiya yagama damu to meyasa zaiyi mana haka "duk borin kunya ne nasan yasa shiyimana haka cewar shettima,
amma bari in kirasa inji wayarsa ya dauko ya kirasa saida baidaga ba wani kiran yaqara yimasa sai da takusan tsinkewa sannan yadaga shina kuma yana dagawa yace musu muhadu agida kawai ya kashe wayar,
wayar suka shiga bi da kallo kamar shi suka gani ajikin wayar,
bayanda suka iya dole suka hakura bayanda zasuyi dashi suka fita daga gidan suka rufe gate din sannan suka nufi titi aqasa shi kansa titin kafin suje aikine saboda nisan sa,
suna tafiya suna jan tsaki da hirar abun da zasuyi masa zsai sun rama abun da yayi musu ko ta hanyar tsokanar sane wallahi idan suka sakashi agaba sai ya tsani kansa dan kowa sai yasani, ahaka suna surutansu har suka ƙaraso bakin titin napepe suka tara direct suka wuce masarautar abakin gate aka ajiye su suka biyashi kuɗin sa suka shiga ciki masallaci suka shige saboda harma antayar da sallar magariba'
bayan sunyi sallar suka suka nufi can cikin masarautar inda part part suke, part din momma suka fara nufa dan sunsan bazai wuce can dinba dole nan zai fara zuwa, amma ga mamakin su suna shigowa suka duba parking space basuga motar da yataho da ita ba alamar de baidawo gida ba part din momma suka shiga,,
basu tarar da kowa ba a falon sai kawai suka zauna akan kujerar suna zama momma ta fito daga kitchen hannun ta dauke da try tana ganin su tasaki murmushi tare da cewa sai yanzu kuka dawo tunɗazu nake zuba ido ganinku, taƙarasa maganar loƙacin da taƙarasa gaban dinning ɗin ta ajiye sannan tadawo wajen su tasamu waje ta zauna tana fuskantar su,"shettima shima yana dan murmushin yace ayya momma wallahi wani aikine ya riƙemu bamusamu damar gamawa ba sai yanzu,
to ai shikenan tundade yanzu kundawo sai kuzo kuyi dinner tunɗazu daman nasa aka haɗa muku ku kadai yake jira ina me sunan baba naga kun shigo kukaɗai ko ya wuce part ɗinsa?
"shiru duk sukayi sun rasa me zasuce mata,
da har shettima zai fadi gaskiya sai kuma yayi saurin bugar bakinsa sannan yace a'a momma yana nan ƙarasowa yadan biya wani wajen ne yace mutaho yanzu zai shigo,
tace to shikenan zaku jirasa ɗin ne ko zakuci?
"a'a zamu jirasa ai yanzu zai shigo,
"tace to bari inje in kungama kwamin magana tafaɗa tana miƙewa daga gurin ta hau upstairs tabar su agun,
"hira sukaitayi abunsu suna jiran shigowar sa amma shiru har wajen ƙarfe tara bai dawo ba...
aɓangaren sam kam tunda yafita da ita tasakar masa wani sabon kukan tana cewa ya sauke, shikuma bai kulata ba, dade yagaji da kukan nata saikawai yasamu bakin titi yayi parking tare da zuba mata idanu yana kallon ta shifa yarasa yanda zaiyi da yarinyar, kai ta kifa akan gwaiwarta tana ta faman raira kuka amma jin ya tsaya yasata ɗagowa titin tashiga bi da kallo ganin ba gida bane yasata tajuyo ta kalle sa haɗa ido sukayi tayi saurin jefa masa harara sannan ta kawar da kanta,
ahankali yace dan Allah badan niba kitaimaka kiyi min shiru wallahi tun da muka hadu kike sakamin ciwon kai naji ban kyauta miki ba amma ai na baki haƙuri yakamata ki fahimceni kitaimaki rayuwata kidena wannan kukan wallahi banason kuka na tsani kuka badan nasan ninayimiki ba daidai ba wallahi da tuni na saitaki amma yanzuma bata ɓaci ba ina roƙonki da Allah da Annabi kiyi shiru wallahi karki kaini ƙarshe dan zan iyayi miki abun da baki tunani kibini ahankali, ɗagowa tayi ta kallesa ganin yanda ya hade fuska tana mamaki ace wai mutum yana magana cikin sanyin murya amma kuma har yakoma faɗa saboda tsabar yasaba da masifa wannan wane irin mutum ne haka da baƙin hali bashida tausayi,
jin tayi shiru yasa yaci gaba da tafiyar sa atunanin sa shikenan ai ya tsoratar da ita bazata ƙara damun saba, kamar kwa yanda yayi tunanin kwa hakance ta kasance bata ƙara kukan ba har suka ƙaraso gidan,
agaban gate din yayi parking tare da cire louck din motar ko kallon barinta baiyi ba yace mata fitar min amota,
yanda kasan yayi magana da dutse haka ta mayar dashi ko motsawa batayi ba jin shirun ta yasa yaƙara cewa kifitar min nace miki ko bajiki ba nan ma shiru bata motsa ba,
"afusace ya juyo zai balbaleta da faɗa sai kawai yaja stop yana binta da kallo hannu yakai saitin fuskarta da take arufe yadan hada hannun sa guri guda yabada ɗas ɗas yayi sau biyu amma bata bude idon taba,
"bacci? yafaɗa a fili rabuwa yayi da ita ya koma ya kwantar da kansa shima yayi ajikin kujera tare da lumshe idanu yana jiran farkawar ta(Tabb😬)
jin abu yayi akafadarsa ahankali yashiga bude idon sa akanta yasauke su datake kwance akan kafaɗar sa,
maimakon ya tasheta sai kawai yadan ƙara gyara zaman sa yanda zatafi jin daɗi kwanciyar ahaka ya yakomar da kansa kan kujera ya ƙara lumshe ido,
bazato ba tsammani shima baishirya ba bacci yayi awon gaba da shi ahaka sukayi bacci gaba dayan su tana kwance akansa...........
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(mrs bmb)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
[6/8, 6:28 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️51&52
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
___________*Abuja*
"tunda ta kwanta ta bata farka ba sai bayan sallar la'asr,
tun suna leƙanta suna jiran farkawar ta da wuri harde suka haƙura suka tashi daga falon amma jim kadan dai wani yazo ya duba ta,
bayan sun idar da sallar la'asr ne suka ƙara zama awajen ta gaba ɗayan su,
basu daɗe da zama ba suka ga tafara motsi dukkan su miƙeya sukayi suka koma kusa da kujerar ta suka zuba mata idanuwa,
ahankali ta shiga buɗe idanun ta tun tana ganin dishi dishi harta ƙarasa bude su tar ta sauke su akan su ƙara mayar dasu tayi ta rufe sai kuma tasake budesu jitayi jikin ta gaba daya yana yi mata ciwo ahankali ta yunƙura zata miƙe zaune amma taji takasa,
'da sauri meer yakai hannu sa ya daugota da taimakon sa tasamu ta zauna' " jigina kan kanta tayi da jikin kujera tana dan dafe kanta saboda bata danji dadin sa jitayi yana danyi mata
ciwo amma ba sosai ba,
Ummy ce tafara cewa sannu sannan Abu ma yayi mata sannun,
'meer kuma gefen ta yasamu yazauna sannan yayi mata sannun,
"bata amsa sannun kowa ba saidai duk wanda yayi mata sai ta bishi da kallo batare da amsawa musu ba,
"falon ta shiga bi da kallo tana mamaki aranta inane nan,
ba inda yake miki ciwo?
"Abu yakatse mata tunanin ta,
juyowa tayi tana kallon sa tare da kafesa da ido kamar zata ciro wani abun ajikin sa saida tagama ƙara masa kallo sannan takawar da kanta mayar dashi tayi kan meer shima haka tayi masa,
"saida ta dauki loƙaci me tsawo batare da ta iya budar baki ba tayi magana,
duk sun ƙosa da suji tayi magana amma taƙi yi,
A ina nake nan, nan gidan waye?
sukaji ta jefo musu tambaya bayan kuma kafin ta kwanta sungama magana da ita amma yanzu taƙara tambayar su ko da yake bai kamata ma suyi wannan tunanin tunda yanzu tadawo hayyacin ta watakil ta manta tattauna warsu,
' Ummu ce ta zauna adayen gefen nata tare da riko hannun bata wani dau lokaci ba kawai tayi mata bayanin yanda komai yafaru bata rage mata komai ba har zuwa yau da akayi mata ruƙeya komai Saida taba ta labari,
"kuka tasakar musu jin yanda rayuwar ta takoma tsawon wasu shekaru sosai take kuka abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba ace tana gidan sarauta da iyayen da daginta da ƴan uwanta da mijin ta ga ɗan ta da tahaifa babude abun da ta rasa amma ace rayuwar ta taso ahaka kuma batare da kowa ya neme ta ba wannan wacce irin ƙaddara ce ta same ta wane irin zunubi ta aikata musu da har zasuyi watsi da ita haka shin wai nema yafito da ita daga cikin gidan tamabayar da tafi tsaya mata arai kenan,
"cikin kukan tayi musu godiya da irin dawainiyar da sukayi da ita har ta samu lafiya,
nan suma suka nuna mata ai bakomai ayi yiwa kaine har suna nunamata rashin jin dadin yawan godiyar datake tayi musu dan su har kunyama suke ji,
' da ƙyar suka samu tayi shiru da kukan da takeyi sannan, Ummy ta gyara zama tare da cewa Abu ka zauna mana, kujera yasamu yazauna sanshi yama manta atsaye saboda gaba ɗaya hankali sa yana kan ta,
shiru falon yadauka na wasu yan daƙiƙu ,kafin daga bisani ummy ta katse shirun nasu, dacewa baiwar Allah inba damuwa ko zamu iya sanin ko ke wacece kuma daga ina kika fito dan inafatan yanzu kin tuna komai, ko ba hakaba ?
"idan bangaya muku ba suwa zan gayawa ai kungama yimin komai arayuwa badan kuba ai da tuni na dade da mutuwa amma kukataimakeni wanda su ƴan uwana babu wanda ya nemeni ace har inkai tsawon wannan loƙacin bana tare dasu amma babu wanda ya nemeni ko kunji ana cigiyata ta ƙarasa maganar cikin raunin murya dan ita aganin ta tanaganin a iya saninta suna da mukami da da kudin da za'ace sun nemi inda suke a matsayin su na manya sanannu acikin garin amma ace babu wanda yayi cigiyarta ta tabbata da sunyi da tabbas zasu samu labarin ta tundade ba ƙasar ta bari gaskiya abun ba ƙaramin taba mata zuciya yayi ba,
"gaskiya baiwar Allah bamu da masaniya akai sunyi cigiyar ki ko basuyiba saboda kinga mu ba ƴan nan bane daga baya muka dawo kuma da muka dawo gaskiya mude bamujiba Allah masani sunyi ko basuyiba, "ummy ce duk take wannan maganar,
"basuyi bama ai dasunyi da tuni sunji inda nake tafaɗa ahankali taƙarasa maganar tare da share hawayen da suka tarar mata a ido,
"kiyi hakuri kar kice haka dan Allah kidena faɗar haka nasan bazasu taba yi miki haka ba kinga ance ai da sihiri aka koreki daga gidan kinga watakil dole da wani abu aƙasa shiyasa kikaji basu nemeki ba amma nasan hakannan bazasuƙi nemankiba yanzu kawai kifada inda kike sai muje gaba ɗayan mu mukaiki har gida,
"girgiza musu kai tayi tace ba inda zani tunda basu nemeni ba nima bazan nemesuba zande sa adauko min ɗana shikaɗai nakeson gani,
Abu ya ce haba dan Allah wacce irin magana kike haka yaza ayi suƙi neman ki kinsan dole sun nemeki amma basu sameki kina da ƴan uwa fa kuma suna sonki dan haka duk inda ma suke tunanin neman ki nasan sunduba watakil ma gajiya sukayi da suka dena neman ki ko kuma ba gari daya kuke ba shiyasa cigiyar tasu da sukeyi batazo garin da kikeba kinga waɗanda suka kawo ki nan sunce agombe suka sameki kuma duk sunyi cigiya suma agarin Gomben amma basuji wani wanda yace yasanki ba tabbacin ke ba ƴar garin bace yakamata koyi musu kyakkyawar fahimta baikamata kina ganin kamar sonkine basayi da yasa basu nemeki ba,
bayan Abu yagama nasa Ummy ma ta ɗora da nata sosai suka sa jikinta yayi sanyi bata ƙara cewa komai ba a game da rashin komwarta cikin danginta duk dade wani ɓnagaren na zuciyar ta yana bata kar takoma din,
'batace musu ta amince ba bata cemusu bata amince ba tayi shiru kawai,
muna sauraron ki ummy taƙara katse shirun nasu,
" A kano nake dazama Sunana *SABREENA* ni asalana ba ƴar ƙasar nan bace ƴar Sudan ce acan duk ƴan uwana suke amma banida iyaye iyayena duk Allah yayi musu rasuwa saboda accident da yasame su tun ina yarinya,
Ina hannun ƙanin mahaifina loƙacin danafara karatu a Egypt annan na hadu da wani muka fara soyayya bayan nan kuma har maganar aure ta shiga tsakanin mu ƙanin mahaifina ya amince yabashi aurena sanadin hakan yasani baro can nadawo nan ƙasar da zama, ashe wanda na aura dan sarki ne loƙacin auren