damuwa ta bayyana a fuskarta qarara takasa boye shi kuma bata tanka wa sam ba har yagama ya fice yabata waje amma kuma yanzu zatazo ta sauke akansa amma bari yasa aje akira masa sam yatambaye shi shin abunda yake fada gaskiya ne ko kuma qarya yake dan ya tura mata haushine kawai yasa shi yi mata hakan da tunani ka fal cikinsa har yaqara sa part din Ammah tunda daman adakin ta ya kwana yazone su gaisa da fulani sai kuma wannan abun yafaru aka rabu bata dadin raiba yana qarasawa yatarar Ammahn bata falo sai kawai yayi zamansa akankujera yana qara tunano magan ganun sam da shi kwata kwata yakasa gane inda suka dosabe dadeda zaman ba sai ga Ammah ta fito fuskarta dauke da murmushi ta qarasota zaunakusa dashi tace har kadawo kenan da wuri haka yace eh wlh dakegurin maryama nafara shiga daga nan kuma nayo nan kallonsa ta danyi sannan tace a'a to bakaje fada ba kenan yace eh fasawa nayi zanje anjima tace to shikenan Allah yakaimu jimawar yace Ameen yauwa dan kiramin me sunan baba awayarki naga har ya fita dan bansameshi a part din may arm a ba naga harya fita kitashi inji yatafi wajen aikine ko kuma yana cikin nan baikai ga fita ba tunkan yagama rufe baki ta amsa masa da to sannan ta dauki wayar tana cewa nima daman ina neman sa bari in kirasa taqarasa maganar tare da dannawa number sa kira bugu biyu ya daga yanadagawa ua gaida ita bayan ta amsa take sanar dashi cewa yazo papa nakiran sa ok kawai yace daga nan suka katse wayar ta maida duban ta ga papa tace yace gashinan zuwa yace to daga nan suka ci gaba da hirar su ko kadan be bata labarin abun da yafaru ba kawai wata hirar suka cigaba dayi...
*FULANI*
bayan fitar papa hannu ta dora akai tashiga rarraba idanu cike da tashin hankali da bata taba tsintar kanta aciki ba a fili tafara cewa na shiga uku me yaron nan yake nufi da duk wani takuna ana gaya masa waye munafikin da yake akusa dani yazama dole incanza taku agidan nan to taya ma akayi nayi sake har wannan dan qaramin alhakin yasan me nake aikatawa acikin gidan nan kalamansa ba qaramin tayar mata da hankali yayi ba dan rabon da tashiga irin wannan tashin hankalin har ta manta shiru tayi nadan lokaci sai kuma can tayi zunbur ta miqe tsaye tafara zagayawa a falon tare da saka hannuwan ta duka abaya tana zagaye tayi can tayi nan abun duniya duk yabi ya isheta tama rasa tunanin da zatayi kamar wannan yaron har yakai girman da zai zo yana gaya mata magana son ransa lalle dole tayi maganin sa inyasan wata ai besan wata ba sai ta nuna mishi shidan qaramin kwaro sai ta juyar masa da tunanin sa yanda baya zato sai ta koya masa hankali fiye da tunanin sa sai ta gasa masa aya atafin hannun sa haka tai ta faman surutai ita kadai da ayyana abubuwa iri iri da zatayiwa sam kala kala daga yau zai gane shayi ruwa ne daqarfi tace qarya kake wallahi nafi qarfinka kai ka isa kasani shiga damuwa yaushe kazo duniya to wallahi qaryane koma waye yasaka sai nakoya muku hankali sai na nuna muku kuskuren shiga gonata ba atakani in kyale sai nasaku kunyi nadama sa min ido da kukayi cikin rayuwata taqarasa fada tana fitar da wata iska me zafi daga bakin ta tare da cije baki tana karkada kai kujerar ta koma ta zauna tare da dauko wayar ta takira wata number ana dagawa ta tashi daga falon ta nufi dakinta ranta amugun bace dasauri sauri take tafiya kamar zata tashi sama tana zuwa bakin qofar ta turata da qarfi kamar zata ballata tana shiga tabugo qofar da qarfin gaske......
Sam
Ransa fess yake jinsa dan yasan ko banza de yasanya mata tsoron sa aranta duk dade yasan bata da gaskiya amma de babu abun da yasani akanta kawai de yayi mata hakane dan yagano abun da yake zargi kuma zarginsa ya kusa zama gaskiya yanzu tunda yagano logonta yanzu zai qara saka mata ido har Allah yasa yagano komai da wannan tunanin yaqara sa shoga falon Ammah da sallama abakin sa momma ce ta amsa masa sannan yaqarasa shiga cikin falon ya samu kujera ya zauna yana facing dinsu sannan ya shiga gaida momma din ta amsa masa fuskarta asake tana qara duban dan nata da kyau abun alfaharin ta Amra dake kan cinyar momma tana buga game awaya batasan wanda ya shigo ba tade ji anyi magana amma bata tantance muryar waye ba saboda hankalinta kacokan yana kan game din datakeyi shiyasa takasa dagowa taga ko waye shima kuma hankalin sa nakanta yana kallonta ganin har yanzu hankalin ta nakan game yasashi ce ke me yahana ki zuwa makaranta yafada da dan daga murya saura kadan tasaki wayar hannun ta Allah ya taimaketa tayi saurin tare ta tare da mikewa zaune tana muzurai da idanuwa sannan tashiga kame kame tana marairaice murya tace bani da lafiya fa yau kwanana biyu a kwance wani kallo ya watsamata da yasata yin shiru bata gama fadar abun da tayi niya ba shiru tayi tana turo baki tana qara matsawa kusa da momma qasa qasa tace momma kice masa banda lafiya bayan bezo ya dubani ba amma zaizo yana wani zare min ido ni wallahi ma na matsu yatafi harar wasa momma tayi mata sannan itama qasa qasan da murya tace au hakama kikace to bari ingaya masa da sauri tace rufamin asiri momma so kike yakarya miki ni tace asuwa yaza ayi inso a karyamin auta ta momma sauri nake in kuma intafi to nazo kuma kintsaya kina biyewa wannan sakarar yarinyar muryar sam takatse musu zancen da sukeyi qasa qasa dagowa momma tayi tana kallon sa sannan tace to inbazaka iya jiraba ai qofa abude take mutum dai bakin halin jaraba maganar momma ba qaramin sosa mishi rai tayi ba amma ba yanda zaiyi tunda itace dole yayi hakuri da ita miqewa yayi yace fine kawai yadaga qafa zai tafi tace wallahi idan kabar gurin nan sai na mugun saba maka har inkira kazo kuma shine zakatafi saboda gaka isashe da mai ko to bismillah jeka cak yaja ya tsaya shi be tafiba shi be zauna ba jin gakan yasa Amra tashi daga gurin ta tafi dakin su saboda duk rashin mutun cinta da rashin kunyar ta inde za ayiwa mutum nagaba dasu fada ko kuma za ayi wata maganar da bai kamata suji ba to zasu tashi subar wajen wanna tarbiyar momma ce ita ta dora su akai dan hakan yanzuma jin zata fara yimasa fada yasata tashi tabat wajen kuma daman da biyu ta tashi tasan ko ta zauna ma daga qarshe zai iya sauke fushin sa akanta shiyasa tayi saurin guduwa,
ahankali yadawo ya zauna awajen da yatashi yayi shiru tare da qara murtuke fuska ya hadeta waje daya kamar an ajiye kunu yakwana haka fuskarsa ta koma bata damu da ganin fuskarsa hakaba saboda inda sabo tasaba ganin ta ahaka dan haka tayi shiru tana binsa da kallo tare da yimasa addu'ar Allah ya shiryeshi yadena wannan dabi'un da kwata kwata bata qaunar taga yanayi duk datasan abune me wahala yadena saida tagama jan lokaci batare da tace masa komai ba shima kuma ko dagowa ya kalleta ba beyiba kawai yazauna tare da cusa lip dinsa abaki yana ciciza da qarfi daman da wani fushin ya fito gashi kuma yazo itama taqara masa wani,
dan numfasawa tayi sannan tace ya maganar da nayi maka tun kwanakin baya kamaida ni yar iska baka cemin komai ba tunda ban isa da kaiba bakai matsayin da zakace min ga yanda kukayi ba ko to ni nayi maka tunda ni nadamu shiru yayi na dan wani lokaci sannan ya budi bakin sa da kyar yace wacce maganar kuma namanta riqe baki tayi tana kallonsa da mamakin ranin hankalin sa dan zata iya rantsewa batare da rantsuwa tacita ba yana sane yasan wacce maganar kawai rainin hankali ne irin nasa cike da bacin rai tace kamanta to tashi kabarmin waje kar nasake ganin qafarka anan duk lokacin da ka tuna kazo tashi kabace min dagani ba kunya ba tsoron Allah kwa ya miqe ya tafi har yakai bakin qofa sai kuma ya tsaya tare da juyowa yana kallon ta ganin ta dauke kai daga gare sa yadan shafo gemun fuskar sa sannan yace tun lokacin nagaya miki kuma mun gama magana dake kaf matan garin nan ba wacce takai matsayin in kulatama bare in aure qarewa ma ni bana ra ayin aure yanzu saboda ba mace da ta isa ince inasonta nibanma ga abun so a mace ba da harkuke naniqamin wata kucaka wacce ake neman kai da ita ni koda zanyima ai bata irin wadanda zan kula bare kuma har takai in hada guri da ita amatsayin mata bazan iyaba kucewa iyayen nata suje su nema mata wani irin ta amma baniba dan ni ba class dinta bane ni wlh nama tsane ta da kinsan yanda na tsaneta da baku qara yimin maganarta ba,
yana gama fadar haka yasa kai yafice daga falon,
tagumi momma tayi tana tunanin maganganunsa sosai yabata mata rai itade batasan yanda zatayi da wanna yaron ba dan yafi qarfin ta zaman waje da yayi yasa gabadaya ba tsoron fadar duk kalmar da tazo bakin sa wajen wata bakwai kenan da tayi masa maganar tun awaya amma sai yayi mata banza yace shi ba yanzu zaiyi aure ba ta rabu dashi ta zuba masa ido daga baya taqara yi masa maganar akwai yar kawarta da ta nuna tana sonsa kuma iyayen tama suka goyi bayan hakan amma da yake shi be gaji mutun ci ba shine ya bijire ba a isa ayi masa magana ba sai yabarka da magana kuma ko ajikin sa yaqara gaba batasan yanda zatayi dashi ba wallahi kullum halayen sa gaba suke basa raguwa ko kadan tana cikin tunani kawai taji saukar ruwa akan fuskar ta ashe hawayen takaici take batasan ma da zuwansuba sai zubarsu da taji hannu takai zata goge taji wani hannun daban akan fuskarta an shiga share mata su dagowa tayi dan ganin me share mata dan tunanin tama yafi bata ko Amra ce saboda itakadai ce idan taga ta shiga damuwa take kwantar mata da hankali shiyasa duk tafi ji da ita saboda itama tana jin tausayin ta amma ga mamakin ta sai idanunta suka sauka akan wanda bata taba tsammani ba sam ne tsaye agaban ta ya zuba mata ido cire hannun sa tayi daga kan fuskarta tana harararsa tare da nuna sa da yatsa tace don't touch me again if not I will slap ur face tafada tare da mikewa daga gurin memakon ya bata hakuri ma a'a kawai sai yadage kafadar sa irin I don't care it's ur fault is not my fault sannan yadau wayarsa da yabari daman yazo dauka yana dauka kuma shima yayi ficewar sa yana fita drivern sa yazo ya bude masa qofa yabar masarau tar ma gaba daya yama manta da ance papa na nemansa,
*CIKIN MASARAUTA*
"shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......✍🏿
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿21&22
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
CIKIN MASARAUTA*
"shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......
dan danan gurin yafara cika da mutane kowa inka gani inma bezo ba to yana shirin zuwa wajen adan qanqanen lokaci gurin ya cika kowa ya hallara agun dai dai kune kawai basu qaraso ba,
Mery dake kitchen tana so tayi sauri taqarasa aikin da takeyi tafita kar abarta abaya Ammah ce taqaraso cikin kitchen din zata dauki abu ganin yanda mary ke sauri tace ke lafiyar ki qalau kuwa inazaki haka naga sai faman sauri kike sada kanta qasa tayi cike da ladabi tace Allah yataimakeki uwargidan sarki ai anyi shela ne ana bukatar kowa ya hallara a babban fili shiyasa nake sauri taqarasa tare da qara sunkuyar da kanta jinjina kai Ammah tayi sannan tace to kibari idan kin dawo kya qarasa kar kijawa kanki laifi kamar ta zuba ruwa aqasa tasha saboda dadi shiyasa take jin dadin aiki a qarqashin ta matar tana da sauqin kai bata da jiji dakai yanda take mu'amala da bayinta da wasu mutanen sai ka rantse ba agidan sarauta take ba bare kuma matar sarki nomal take daukan kowa ganin take daidai suke da ita,
godiya tayi mata sannan tafita cikin sauri ta qarasa dakinta tana tura qofa sukayi karo da Azeema hakuri ta bata sannan ta cire kayan jikin ta ta canza wasu duk acikin sauri takeyi tana gamawa tabude qofar zata fita Azeema tayi saurin tsaodata da tambayarta ina zataje taga tana sauri cike da qaguwa tace mata ananeman ma'aikata cikin masarautar nan za ayi sanarwa ko kuma za ayiwa wani hukunci bakinta haryana karkawar sauri wajen cewa nima zan iya zuwa ko sai iya ku karkada mata kai tayi alamar sannan tace inkinso zaki iya zuwa mana amma de kibi ahankali tunda ke bakuwace kar kije kiyi wani kuskuren da zaisa a hukuntaki dan any mistake game over zaki iya jefa kanki cikin wani halin tana gama fada tayi gaba tace kisame ni awaje banaso inzama qarshen zuwa da sauri Azeema tace to muje ai ba abun da zanyi tare da jawo hijab dinta dake jikin wardrobe ta ruqoshi ahannu saida tafito taqarasa sakawa tana Allah Allah kar ta hadu da Ammah saboda tunjiya da tace tatafi bata qara fitowa ba dan haka bata qara ganin taba daman batason su hadun shiyasa taqi fitowa Allah cikin ikonsa kwa basu haduba har suka fice daga part din suka nufi gurin tundaga nesa suke hango mutane a zazzaune wasu kuma a tsugunne kale kale Azeema ta shiga yaude gata tama yawo acikin masarauta tunda ta fito take addu'ar Allah yasa taga mahaifin ta cike da farin ciki aranta suka qarasa gurin suma suka samu waje suka zauna kamar yanda kowa ya zauna,
bayan zuwan su ma wasu suna ta qara fitowa inda Azeema take baza idanu lungu da sako duk wanda ya taho sai ta bishi da kallo amma Allah besa ta ganshi ba tunani tafara to kode baya gidan wancan mutumin qarya yake musu to amma akan me zaiyi musu qarya bama qarya bane wata zuciyar tata tabata amsa shiru tayi tana qara nazarin abun,
sunkai wajen minti goma agurin kafin daga bisani sarki yataho tare da muqarrabansa suna mara masa baya wasu kuma agabansa dukde ankare sa yanda ba kowa zai gansa ba suna tafiya suna yi masa kirari gyara kintsi da kyau gyara kintsi da kyau takawarka lafiya sarkin sarakai Allah ya kare gabanka da bayanka kafi qarfin makiya saidai kai kaga bayansu bade suga bayanka ba dan sarki jikan sarki uba ga sarki nan gaba kuma kaka ga sarki gaba sarauta baya sarauta muliki ajinin jikin ka yake babu me ja dakai duk wanda yace zai gwada saidai a haifi wani bade shiba sarki me adalci acikin masarautar adalai aikin ku na kyau komai kukayi daidai ne bakwa kuskure tsarin ku nadaban ne Allah yaqara maka lafiya da nisan kwana yabaka tsawon rai me inganci hakade suke tafaman zabga masa kirari har suka qarasa inda yasaba zama suka nufa duk wani wanda yake awajen saida ya miqe gaba dayan su suka miqe tsaye saboda sarki zai zauna dole sukuma sukasance a tsaye yafara zama tukunna su zauna,
suna qarasawa fadawansa suka baza masa babbar riga tare da juya masa baya dan yasamu damar zama (kunsan ba a ganin zaman sarki)
bayan yazauna mutane duk suka gurfane agabansa ana diban gaisuwa kowa da kallar gaisuwar da yake saida suka kai wajen minti biyar ana gaisawa sannan kowa ya koma wajen sa ya zauna ana kuma jiran isowar uwar masarauta basufi minti biyuba itama ta taho tare sa mabiyan ta guda uku daya agefen hagunta da damanta dayar kuma abayan ta haka take tafiya cikin isa da izza da takama da tinqahon ita ta isa kana ganinta kasan zallar mulki ke yawo ajikin ta tun akan takun ta zaka fahimci hakan yanda take takawa daidai kamar bata son taka qasar gimbiya maryama fulani