sa,
"Musa bin motar yayi da kallo sannan ya juya yacigaba da tafiya a fili yake cewa ni da wa yakaini jawa kaina ai ko baka faɗa ba bazan taɓa faɗa ba koda ta tambaye ni shikaɗai yana tafiya yana zancen sa tunawa da gargaɗi da akayi masa yasashi ɗaga ƙafa yafara sauri yana addu'a Allah yasa yasamu abun hawa da wuri,
Allah yasoshi yana fita yasamu me napep yahau yagaya masa inda zashi tundaga dan nesa ya hango motarsu saboda ba gudu suke ba shiyasa,
Me napep din yacewa dan Allah yadan qara gudu yanason sukamo waccen motar yanuna masa ita da hannu nan kwa me napep yaqarawa adaidai tarsa mai yafara gudu har suka kamosa sannan ya rage gudun suka cigaba da bin bayansu shaka har suka isa gidan yayi horn me gadi ya bude masu suka shiga shima Musa fitowa yayi yabisu kafin ma yagama daidaita parking Musa har yaqarasa yayi bude masa qofa idan kagani sai ka rantse tare suka dawo fitowa yayi Musa na shirin budewa matar dake dayan gefen meer yayi saurin dakatar da shi yace yaje kawai da kansa ya bude mata qofar sannan yakamota yafito da ita yanda sukayi dasu haka sukayi yanzuma har suka qarasa bakin qofar su me tafiya da imanina dan bazan taɓa deba gajiya da kallon ta,
yanda tayi rannan haka yanzuma tayi ta rabe a hudu sannan suka shiga ciki suna shiga sukayi karo da ummy tana shirin fitowa mutuwar tsaye tayi ganin matar da bata taba tunanin ba ko da a mafarki cak ta tsaya takasa motsawa tare da sakin baki tana kallon ikon Allah,
"ummy meer yakira sunan ta ahankali kallon sa tayi tama kasa magana qarasawa yayi kan kujera ya zaunar da ita,
ummy ce ta qaraso gun sai yanzu tasamu bakin magana hayatee me nake gani haka kode mafarki nake,
ummy ba mafarki kike ba gaskiya ne yaude Allah ya amshi addu'ar mu ummy taji sauki ta dawo hayyacin ta cike da farin ciki har rungume ta yayi sai yanzu murnar tasa ta bayyana nan ya kwashe duk yanda yaje yasameta da maganar da tayi masa komai dai ba abun da yarage mata tundaga A har Z sakin shi tayi itama cike da murna haƙoran ta sun kasa rufuwa ta koma kusa da ita itama ta rungumeta tana tafam bita da idanu kamar zata maida ita cikin ta hannuwanta ta ruqo cikin nata,
"itade tana zaune kamar gunki sai faman binsu da kallo take takasa gane inda maganar su ta dosa ita da tace akaita gurin babyn ta amma kuma yazo ya kawota nan da batasansu ba,
maida kallon ta tayi ga meer tayi shima da yadawo gefen ta yazauna wani irin dadi na ratsasa yau ya tsinci kansa cikin farin cikin da baitaba jinsaba tunda yake arayuwar sa baitaba jin farin ciki irin na ranar yau ,Yau ranace ta musamman awajensa yau ranace da bazai taba mantawa da itaba,
"Wai inane nan ka kawoni kace zaka kaini gurin babyna amma kuma kazo ka ajiye ni anan ku suwa ye me yasa ka kawoni nan dan Allah kukaini gurin su ina son ganin su,
" sosai ummy ta ƙara ruƙo hannuta duk da bata san sunanta ba amma sai kawai takirata da maama sunan da suka rada mata kenan tun kan farkon zuwan ta meer yasaka mata,
cike da nutsuwa ummy tace maama ki kwantar da hankalinki yanzu kina buƙatar hutu kibari yanzu muje kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta idan kin tashi sai muyi maganar kinji,
bude baki tayi zatayi magana meer yayi saurin dakatar da ita yace dan Allah kar kice komai maama kibari sai anjiman kinga yanzu safiyace kibari zuwa dare sai muyi maganar,
kai ta girgiza musu tace bazanyi komaiba indai baku kaini wajen suba ni bansankuba bazan zauna dakuba kumayar dani gida kawai,
duk yanda sukaso su shawo kanta ta amince da hakan amma taki yarda da ƙyarde tace musu tayarda zatayi wankan amma bazata yi bacci ba tana gamawa zasu gaya mata inda danginta suke da haka suka amince mata ta yarda,
tashi sukayi gaba dayan su ummy tacewa meer yatafi yaje ya huta zata kaita daki idan ta shirya zata kirasa,
ahaka suka rabu shi yatafi part dinshi
ita kuma saboda yanayin jikin ta ummy da kanta takaita dakin dake qasa saboda tasan bazata iya hawa sama ba shiyasa takaita wani dakin bayan ta shiga taje ta haɗa mata ruwan wanka sannan ta dawo da taimakon ta takaita banɗakin sannan ta bata waje fita tayi daga ɗakain taje ta dubo mata kayan da tasan zasu yi mata saboda yanayin jikin su daya kawaidai ummy ta ɗan fita ƙiba da kuma mulmulewa saboda hutu amma kuma kana ganin maama kasan ta girme mata nesa ba kusa ba dan a haifema ta haifeta shiyasa jikin su ya bambamta ga kuma halin da ta tsinci kanta duk ta rame tsufanta ya bayyana sosai,
Atamfa ta dauko mata riga da zani wadanda de tasan zata iya sakawa batare da sun ta kura mata ba dawowar ta dakin yayi daidai da fitowar ta daga bathroom din bakin gadon dakin tasamu waje ta zauna ƙarasowa ummy tayi gabanta tabata tace maama gashi kisaka bari inje inkawo miki abinci bata jira amsartaba ta tashi taƙara fita daga dakin ba jimawa taƙara dawowa da try ahannu ta yanda tafita tabarta haka tadawo ta sameta zaune agun ta zabga tagumi tana kallon gu ɗaya,
dasauri ummy ta qarasa gaban ta tare da ajiye try din tace subhanallah maama me nake gani haka ya baki saka kayan ba kallon ta tayi bata ce komai ba ta dauki rigar kawai tasaka sannan ta tashi ta daura zanen sannan ta koma ta zauna,
shayi ta haɗa mata me kauri ta miƙa mata ta karba ahankali tafara kaiwa baki tana sha saida tasha rabi sannan ta miƙa mata tace ya isheta haka,
kiɗan ƙara cewar ummy,
"Maama tace mata a'a ya isa haka nagode,
bata takirata ba ta karɓa ta ajiye sannan ta zuba mata soyayyen dankallin turawa da ƙwai bayan tagama haɗa mata ta miƙa mata amma sai tace ta ƙoshi inma zataci sai anjima yanzu shayin da tasha ya isheta da Allah da Annabi ta hadata akan ta daure tace amma taƙi bayanda ta iya da ita dole ta rabu da ita saboda ba Safar tabace bekamata ta ringa jayayya da itaba,
hade kwani kan tayi ta fita dasu sannan ta dawo ta zauna kusa da ita tace maama yanzu babu abun da yake miki ciwo babu abun da kike buƙata,
buƙatata bata wuce sanin inda dana da 'yan uwana suke da kuma abun da yakwoni wajen,
dan numfasawa ummy tayi tare da gyara zamanta tace bayan wannan buƙatar ba kya buƙatar komai?
"eh" tace mata...........
[5/29, 9:40 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿41&42
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"Ɗan numfasawa ummy tayi tare da gyara zamanta tace bayan wannan buƙatar ba kya buƙatar komai?
"eh" tace mata....
"tom shikenan maama yanzu zakisani amma bari nayiwa zauji magana yanzu yatashi daga bacci yana shirya wa ne yana gamawa sai mu zauna mu tattauna tafada tana miƙewa tsaye,
idan ya shirya zanzo inkiraki ki jirani dan Allah,
afito lafiya cewar maama,
fita tayi tabarta adakin,
dakinta ta koma tasamu mijin nata har yagama shiryawa yana zaune a falon sama yana breakfast ƙarasawa tayi gurinsa tare da join dinsa suka cigaba dayin breakfast tare tunda suka fara ba wanda yayi magana har saida suka gama wannan tsarin sune ahaka idan suna cin abinci basayin magana indai ba wai maganar takama dole ba to basayi harsai sun gama,
"miƙewa tayi tana goge bakin ta da tissue sannan ta dubi minjin nata tace masa muje ko tanacen tana jiran mu fa,
shima miƙewa yayi yana gyara zaman galas din dake manne akan fuskarsa
cikin yaren su na larabci yake cewa nifa wlh har yanzu nakasa yarda da abun da kike fada dan wallahi abun yaban mamaki sosai ace mata tayi tsawon shekaru a kwance amma ace yau rana daya ta mike harma tana magana gaskiya wannan abun mamaki ne dan ya matuƙar daure min kai,
"kamo hannunsa tayi tare da daga kai tana kallon sa tace haba abu meer dan Allah kade ana maganar wannan kwa ba wani abun mamaki bane babu yanda Allah ba yaso yayi yanda yaso shi ya dora mata kuma shi yaye mata lokaci guda dan haka ni banga abun mamaki ba daman kullum addu'ar mu kenan Allah ya tashi kafaɗunta kuma Allah ya amshi addu'ar mu kaga sai mu ajiye batun mamaki munan farin cikin mu da godiyar mu ga ubangiji Allah ya ƙara mata lafiya kuma yabamu ikon gano inda danginta suke domin muqarasa ladanmu da mukayi niyya Allah ya cika mana burinmu akanta musauke nayin da muka daukarwa kanmu,
dan shafa fuskar ta yayi yana dan murmushi yace to shikenan na dena mata tagari Allah yayi miki albarka shiyasa nake sonki saboda sanin yakamatanki da kike dashi Allah yabaku lada keda babana du kuka tsaya ganin tasamu lafiya gashi kuma yau Allah yayi tashin nata Allah yataimakeku yabaku ikon cika aikin da kuka dauka,
"itama cike da jin dadin maganar mijin nata tana ta faman smiling tace Ameen ai hardakai, "yace a'a ni mainayi akanta ai kune duk kuke dawainiya da ita saida Allah yabiyaku Ni ba abun da natsinana mata tunda tazo kune komai nata amma yanzu nima zan shiga ciki domin asamin ladan naku yafaɗa yana ƙara sakin wani murmushin rungume shi tayi kadan sannan ta sakeshi tace muje dan Allah nasanka zancen ka baya ƙarewa yanzu sai mufi awanni amma batare da ka gama ba to meye aciki dan nayi zancen da yar aljanna idan banyi dakeba dawa kikeson inyi,.
bana gajiya wane dake shiyasa kikaga idan munatare inata riƙeaki da zancen,
to naji tace tare da kamo hannun sa suka fito atare kamar wani ƙaramin yaro saida ta zaunar dashi akan royal chair din sannan ta juya ta tafi dakin da ta bar maama,
yanzuma de kamar dazu haka tadawo ta same guri guda idan batayi ƙarya bama da saitace ko motsawa batayi ba,
jin anshigo yasa maama dagowa ta dubeta, fuskar ta cike da murmushin farin ciki taƙaraso gabanta tana cewa afuwan nadade ko nsbarki kina ta jira,
ba komai wlh cewar maama,.
yafito zamu iya fita,
tana rufe baki, maama ta miƙe tace yauwa to nuje ko dan jinta take kamar akan ƙaya take zaune ta matsu su mayar da ita gida,
yanzuma saida ta kama riqeta sannan suka fita daga dakin,.
suma ƙarasawa sukayi tare da zaunar da ita kan kujerar da take facing din ta Abu,
Suna fitowa saiga meer shima ya fito tare da qaraswa kan kujera shima yasamu waje yazauna tunda yafito idonsa akanta har yakai ga zama bai janye ba saida bisani yajanye idon sa daga kanta tare da mayar dasu kan Abu sannan yace sabahul khairi ya Abu,
ɗagowa Abu yayi yana duban nadan nasa sannan yace yau kuma ahaka za agaidani to ban amsaba yaƙarasa fadi yana sakin wani murmushin.
kai kasamu gaisuwar ma ni yau ko irinta bansamu ba cewar ummy
tunda suka fara maganar ba wanda ya tankawa hasalima daga ƙarshe mayar da kansa yayi jikin kujera ya kwantar harda rufe idon sama,
tunda ta zauna bata dago ta kalli kowa daga cikin su duk datasan su kallonta suke,
ummy ce tafara magana "to Alahamdulillah sai mufara dayiwa annabi salati kamar yanda ya kamata (yana da kyau idan za ayi zama anaso afara bude taro da addu'a koda mutum biyune kufara dayiwa annabi salati sannan kuyi addu'a kafin kufara abun da ya haɗa ku)
suma hakan sukayi bayan sungama salatin Ummy ta ɗora musu da addu'a,
Sannan ta dubi abu tace to Abu meer ko kai zakayi mata bayani?
a'a kawai kiyi mata wannan ai aikin kine kiyafi cancanta dakiyi shi,
dan hararar wasa tayi masa taƙasan ido batare da kowa ya lura da su ba, be kulata ba sai kawai murmushi da ya mayar mata dashi, kawar da kanta tayi gefe sannan tace tom maama takira sunan ta sai lokacin maama ta dago ta dubi inda suke idonta tafara saukewa akan ummy sannan ta mayar dashi kan abu da ya sunkuyar da kansa yana ƙokarin ɗaukar glass dinsa da tun shigowar sa falon ya cire yanzu kuma yaji yana bukatar sa shiyasa bata samu damar kallon fuskar saba,
ina saurarinki cewar maama, tare da mayar da kanta ƙasa,
cikin nutsuwa maama tafara yimata bayanin yanda suka hadu da ita tun lokacin da aka kawota daga wani asibitin zuwa nasu da adadin shekarun da ta dauka akwance awajen su kafin gurin suma kuma tayi shekaru da yawa awancen asibitin dan a ƙalla de a ƙiyasi zatakai wajen shekara ashirin da wani abun tana kwance babu hankali ajikin ta basu rage mata komai ba saida suka bata labari har zuwa yau data farfaɗo,
wannan labarin ba ƙaramin girgizata yayi ba jin adadun shekarun data dauka kuma batare da wani ɗaya daga yan uwanta tane taba to me yafaru da ita, itade abun datake iya tunawa shine danta da kuma mijin ta sai kuma iyayen ta amma fa sudin ma bazatace gasuba kawaidai aranta tasan dasu,
Ummy ce ta katse mata tunanin ta dacewa amma yanzu Alahamdulillah maama tunda har kindawo cikin hayyacinki munason kigaya mana ko ke wacece kuma awane gari kike kinga sai mu hadu gaba dayan mu muje,
ɗagowa maama tayi tana dubasu da kyau sannan tace maganar gaskiya bansan daga inda nake ba abunde da zan iya tunawa shine nasande ina da da kuma ina da miji amma ko kammanin su bazan iya tunawa ba bare kuma garin da nake,
Amma kubani lokaci ko Allah zaisa intuna koda garin da nake ne amma daga wane gari aka kawo ni nan kugayamin ko zan iya tunawa taƙarasa maganar muryarta cike da rauni ga hawayen da ya ke zubowa daga idonta ita kanta batasan da zubarsuba wani iri take jin jikinta kamar tana son tuna wani abun amma takasa ga wani irin ciwon kai da taji yana shirin rufeta hannu kawai tasa ta dafe danji take kamar zai tsage gida biyu kuma dazu batajin sa yanzu kawai tafara jinsa lokaci daya,
Abu ne dubi meer yace kasan daga inda aka kawota tunda kai aka kawowa ita,
kai ya girgiza masa sannan yace amma de inada Number dinsa bari in kirasa daukar wayarsa yayi yashiga laluben number wancen mutumin da suka kawota cikin sa'a kwa yasameta danna masa kira yayi tare da sanya wayar a speaker yanda kowa zaiji cikin rashin sa'a kam yana kira akace layin akashe yake ƙara kirayayi nanma still akashe sai da ya gwada wajen sau biyar amma duk taƙi shiga dole ya haƙura yadena kira,ummy tace zuwa anjima ya gwada ko Allah zaisa ta shiga,..
Abu ne ya kalli maama yace maama yanzu ko sunanki bazaki iya tunawa ba kinga da sai muje gidan Radio da kuma gidan tv da jaridu sai a watsa cigiyar ki ako ina ko Allah zaisa adace,
ɗagowa tayi taba kallon suna hada ido taji kanta yaƙara sara mata da ƙarfi da harsaida takaita da sakin ƙara tare da cewa kaina kaina wyyo kaina tafaɗa ta na sake riƙe kan da hannuwan ta sosai take jinsa kamar zai rabe gida biyu,
da sauri duk sukayi kanta suna mata sannu amma ba wanda ta iya saurara ciwon saima ƙara gaba yake,
nanfa hankalinsu yaƙara tashi suna ta tunani abun yi ummy ce ta zauna kusa da ita tare da tayata riƙe kan ganin de abun is not easy yasa ummy cewa muje asibiti kawai meer kamota muje Abu ne yayi saurin dakatar dasu yace a'a wannan inma kunje asibiti ba abun da zaku iyayi mata saboda baku da maganin da zaku bata ko kun bata bazai taba yimata aiki bashi take buƙata ba a halin yanzu, yaƙarasa maganar tare da zaro wayar sa yace bari akira malami kawai shikaɗai ne solution a halin yanzu,
Meer yace amma Abu....
Ummy ta daga masa hannun tare da cewa karkace komai hakan shi yakammata nikaina mantawa nayi da batun malamin da haryasa nace muje asibiti amma yanzu nagane hakan bata buƙatar wani drugs addu'a kadai take buƙata,
shiru yayi be ƙara magana ba tunda sunrunjaye sa dole yabisu a yanda sukeso ,
cikin sa'a kuwa bugu daya malamin da abu yake kira dagawa akayi tare da cewa "Assalamu alaikum warah matullah amsawa abu yayi sannan suka shiga gaisawa kafin daga baya yayi masa bayanin abun dake faruwa ,
ba bata lokaci kuwa malamin yace gashinan zuwa abashi minti talatin zai iso daha sukayi sallama ya ajiye wayar,.
yamaida kallonsa garesu sannan yasanar dasu yanda sukayi da cewa gashinan zuwa,
Sosai sukaji dadin hakan cigaba sukayi da yi mata sannu,.
ummy dake riƙe da ita duk addu'ar datazo bakinta yitake tana tofa mata,
gaba dayan suma haɗuwa sukayi suna yimata amma fa shiru kakeji itade bawani sauyi datake ji dan jitake ma kamar wani zafin suke ƙara mata,
ahaka suna tsaye akanta cikin rashin hankali da damuwa da kowanne su ya tsinci kansa,
ita kuma tanata faman damke kannata ga wasu zafafan hawaye masu dumi da suke zubo mata duk wanda yaga baiwar Allahn nan sai ya tausaya mata,
Suna cikin haka wayar abu tafa ringing da sauri yayi picking din call din yana dagawa yace kazo ne? ok kashigo kawai yana ajiye wayar yabar wajen ya nufi hanyar waje dan shigowa dashi,
yana fita badadewa suka dawo tare ƙarasowa sukayi inda take kallo daya malamin yayi mata ya kawar dakai tare da dan girgiza kai sannan yacewa su Ummy su saketa dakinta tayi tare da tashi daga kan kujerar tabashi waje,
wata roba yadauko ajakar da yazo da ita farin ruwane acikin ta budewa yayi sannan ya miƙamata yace ta sha ɗagowa tayi ta kallesa da jajayen idonta