Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   64 / 74

189K to 192K   out of 221K words

ta raɓeta ba dan kallon fatalwa zata koma yi mata, kujerar da ta zauna ma saida ta takure kanta guri ɗaya ga zufa dake zubo mata itama na tsorata da ganin  gimbiya sabreena,

shiru fadar ta ɗauka ana sauraron su,

ɗayan kanin papa ne yataso yazo kusa dasu shima yana kallon gimbiya sabreena saidai baice komai ba yazauna akusa dasu yana ɗan satar kallon ta tunda ga kan ƙafarta har fuskarta dan duk ya tabbatar wa kansa dai itaɗin ce ba aljana ba,

waziri ne yafara magana,  yace "to da farko dai zamu fara godiya ga Ubangijin mu da ya nuna mana wannan rana da bamu taɓa zaton zuwan taba acikin rayuwar mu ko amafarki bamu taɓa tunani zatazo ba sai kuma gashi Allah cikin ikon sa tazo ta riske mu da ranmu bamu mutuba, ɗan dakatawa yayi sannan yaci gaba dacewa,

"nasan kowa yana mamakin ganin ta kowa yazata ta mutu tun loƙacin baya daɗewa  sai kuma gashi kunganta da ranta dole kowa ya tsorata to amma inason ku kwantar da hankalin ku wannan ba mai kama da ita bace kuma ba aljanna bace ba kuma fatalwa bace dan naga Hajiya gwaggo abayan kukera to kifito Iran ce dai da kuka sani matar yaya sarki kuma gimbiya sabreena matar sarki zahiri gaskiya kuke gani anan ba mutum mutumi ba wannan ta gaskiyar ce ina fatan kowa zai kwantar da hankalin sa yadawo cikin nutswar sa ,nima bawai banyi mamaki bane ko ban tsorata ba  nayi amma ina da dalilin da yasa nayi saurin ganeta kuma na yarda da ita aɗan ƙanƙanen loƙaci saidai kuma nima bansan ya akai hakan ta faruba saidai mujira jin ta bakin ta ita zata sanar damu abun dake faruwa, maida kallon sa yayi ga gimbiya sabreena sannan yace "to gimbiyar mu muna sauraron ki ko zamu iya sanin abun dake faruwa domin mu anan kinriga da kin mutu tun abaya dan anan akayi miki wanka mu da kanmu mukayi jana'izar ki muka kaiki gidan gaskiya sai kuma gashi mungani ki ba zato ba tsammani nima abun da yasa nasamu damar magana da ƙwarin gwiwa da tabbacin kece tun loƙacin mutuwar taki nagane bakece kika mutuba saidai nayi shirune kawai saboda aloƙacin banda ƙwaƙƙwarar hujja kuma koda na faɗa babu wanda zai taɓa yarda dani daga bayama kuma ni saina manta da zancen gaba ɗaya amma yanzu ganin ki ya tunasar dani komai, amma inason infara jin ta bakin ki kafin in gaya muku abun da nagani ranar mutuwar taki.....shiru yayi yana fuskantar ta yana jiran amsa daga gare ta,

shiru tayi tana nazarin maganar sa hasashen ta zai zama gaakiya kenan wani irin baƙin ciki da haushi ne yazo mata wuya ya tokare mata maƙoshi tama kasa magana saidaga baya hawayen da take ta riƙewa saboda kartabari aga rashin dakiyar ta su suka shiga zubowa kan kuncin ta gefen mayafin ta takama tayi saurin goge hawayen sannan murya cikin rauni da taƙaici tace "ban taɓa tunani hakan zata taɓa faruwa dani ba tun barina gidann nan ko ince tun fitar dani da akayi daga cikin gidan nan ni kaina banƙara sanin inda kaina yake ba sai aɗan kwanakin da akayi min magani na warke daga cutar dani ɗin da akayi duk wani abu da yafaru anƙulasa ne daga cikin gidan saida akayi duk abun da akayi aka fitar dani sannan kuma aka sanar muku da mutuwa ta alhalin ina nan da raina duk ma wanda yake tunanin na mutu wanda yasan ya shirya tuggun sa to Allah yafi ƙarfin sa burin sa bai cika ba gani da raina da lafiya ta tare da zuri'ata abun da ba aso agani to gashi an rabamu kuma Allah ya haɗamu....ɗan dakatawa tayi da maganar tare da ƙara goge hawayen dake ƙara tarar mata duk son ta da ta nuna jarumtar ta da dakewar ta hakan ya gagare ta hawaye ne kawai take jin suna taho mata jin zasubo ne yasa tayi saurin dakatawa da maganar da take....

tsullum sai ga gwaggo ta fito daga bayan kujerar da ta ɓuya tazo gaban su kamar wata zararriya haka ta zube agaban sabreena ta riƙo hannun ta sai kuma ta ƙara tashi daga zaunen ta tsugunna tashiga goge mata hawayen........✍️✍️

_Dan Allah kuyi haƙuri da wannan, sannan kuma ka ƙara haƙuri da ni nasan bakwajin daɗin hakan nima kaina ba ason raina nakeson inringayin fashin rana ba naso ƙarahen watannan ingama littafin ma gabaɗaya wallahi amma hakan bata samuba kana takane Allah na tasa abubuwan sai ahankali wallahi,_

sannan ina godiya da addu'o'in ku jikina Alahamdullillh naji sauƙi saida kuma bansamu damar yi muku typing dayawa ba kawai Bama naso yauma yazamana banyi ba shiyasa nayi muku hakan da babu gwanda ba yawa ina me ƙara baku haƙuri dai akan rashin update kullum kuyi haƙuri, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri 🙏🙏🙏 nasan ma idan wasu sun idan sun fahimce ni wasu bazasu fahimce ni amma suma suƙara haƙuri...........
            

                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 95

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

   

            
  
   tsullum sai ga gwaggo ta fito daga bayan kujerar da ta ɓuya tazo gaban su kamar wata zararriya haka ta zube agaban sabreena ta riƙo hannun ta sai kuma ta ƙara tashi daga zaunen ta tsugunna tashiga goge mata hawayen..

tana ta faman tattaɓata da kyua dan taƙara tabbatar wa kanta itaɗin ce,

sai kawai itama ta fashe da kuka harda su majina sannan ta koma ƙasa tayi zaman dirshen ta fara cewa "daman nasani nima Saida nace bata mutuba akace min kin mutu shiyasa aka hanani ganin gawarki ai duk wani wanda ke cikin gidan banajin yaga gawarki saidai a lulluɓe  an hana kowa gani ki, miƙewa tsaye taƙarayi  sannan tace gaba da cewa,  "ashe ƙullalliya aka ƙula shiyasa akayi haka tokwa Allah ya kwashewa tanbaɗaɗɗu albarka tsinuwar Allah ta tabbata agare su wannan wane irin mugunta ce ashirya mutum arabasa da iyalin sa da mijin sa kuma ace ya mutu wai wane ɗan iskanne ma yafara sanar mana da mutuwar ta wallahi shi za akama aci uwar uban sa kowaye shi tsinanne marar albarka tana maganar tana ɗaga hannu harda su sakin mayafi  ya faɗi ƙasa masifa kawai take zazzago musu  kamar wanda yayi laifin yana gaban ta sai da ƙyar aka samu aka rarrashe ta ɗan dakata da abun da take cewa,

sannan waziri yacewa maama taci gaba da basu labarin abun daya faru da ita,

kuma sosai gimbiya sabreena take saboda jin yanda akace ta mutu bayan kuma da ranta hakan ba ƙaramin sosa mata rai yayi ba, saida papa ya rarrasheta sanan tayi shiru ta samu bakin magana amma duk da haka sai tace "abubuwa da dama sun faru waɗanda ni kaina ban san faruwar su ba  saidai zan wakilta wanda zai baku labarin abun dake faruwa tunda barina gidan,

ummy ta kalla sannan tace ga wacce suka tsince ni itace zata baku labarin abun da tasani kowa maida kallon da hankalinsa yayi kan ummy da maama ta nuna musu,

daga inda take ummy ta fara basu labarin ta yanda suka haɗu da ita tun loƙacin da aka kawo su asibitin su da abun da waɗanda suka kawota sukace nandai ta kwashe komai tagaya musu har zuwa loƙacin da tadawo cikin hankalin ta bayan malam yayi mata magani saidai bata gaya musu alaƙara dake tsakanin su ba na ɗa da uwa harda jika kawai ta tsaya musu zuwa inda suka baro garin abuja suka dawo kano suka kama gida anan ta tsaya da basu labarin tace ga iya abun da nasani yanzu wannan baiwar Allahn zata cigaba da baku labarin ta nuna musu dadda,

gyara zamanta dadda tayi sannan itama ta shiga basu labarin abun da tasani tunda ga loƙacin da aka bugeta a motar har baba yakai ɗanta gidan suka ci gaba da riƙesa hardai zuwa giraman sa da kuma waɗanda suka kawo masa farmaki............komaidai tagaya musu da yanda suka haɗu da su sam har suka fara taimaka mata akan zasu fara bincike sai kuma ga su maama sunzo suma loƙacin da Ameesha ta ɓata sai ta faɗa hannun ɗansu ya taimake ta daga maama ta gane cewar jikarta ce......., itama kuma bata gaya musu cewar Abu ɗan maama bane tadai sanar dasu Ameesha jikarta ce kuma ɗanta ma ana sa ran yana raye saidai ba a san inda yake ba abun da ake ƙoƙarin ganowa kenan tun kafin ma zuwan su Sameer Allah kuma baiyi ba sai yanzu da Allah yayi wannan haɗin cikin ikonsa na haɗasu guri ɗaya har sukazo nan yanzu suke bada labarin abun da yafaru,,

Kalamar inna lillahi wa inna lillahi raji'un kawai papa yake iya faɗa saboda ba ƙaramin shock ya shiga ba jin yanda ahalin sa suka kasance cikin ƙunci da wahalar rayuwa suna raye awani wajen batare da sanin saba,

bashi kaɗai ba gaba ɗaya ilahirin gurin babu wanda bai jinjinawa faruwar wannan abun ba kowa cike yake da ɗunbum mamaki tunda suke atarihin masarauta ba ataɓa aikata abu makamancin haka ba ba ataɓa mugunta irin wannan ba babu matar da aka taɓa yiwa irin wannan cin zalinci aka koreta daga gidan sarauta duk dade daman gidan sarauta yagaji irin waɗannan makirce makircen na asiri da makamancin su amma dai ba ataɓa aikata irin hakan ba,

hayaniya gurin ya ɗauka wasu na sharar hawaye wasu kuma na zufa saboda yanda hankalin su ya tashi da bayyanar ta wasu kuma na farin cikin wasu na baƙin ciki wasu kuma nayin nadama wasu kuma suna ƙara wani tunanin aransu yanda zasu ƙara tarwatsasu dan bazasu bari farin ciki yaci gaba da zama agurin su ahaka suke so su ƙare rayuwar dan haka dole su ƙarayin wani ƙyaƙƙyawan shirin akansu dan bazasu taɓa lamuntar zaman su aciki gidan fa duk da sun tsorata amma hakan baisa sun karaya ba sun saduda ba saima wani tunanin ma suke daban,

papa ne da idon sa yakaɗa yayi ja dashi saboda tsabar baƙin cikin da ya tsinci kansa ya kamo gimbiya dake kusa dashi yashiga bata haƙuri kamar shi yayi mata laifin, shi sai yanzu ma da aka bada labarin ya tuna ashe harda ɗa loƙacin da ta mutu tunawa yayi bai wanda yayi zancen ɗan tunda ta mutu kuma itama kanta aka manta da zancen ta bare kuma ɗanta kwata kwata babu wanda yayi zancen Sameer sai yanzu da aka bada labari kowa yatuna dashi anmantar dasu gaba ɗaya sai yanzu tunanin wasu yadawo,

  gwaggo cikin share ƴar ƙwallarta ta matso kusa da ita tace "Allah yasaka muku duk wanda yayi miki wannan mugunta Allah yasaka muku gaba ɗayan ku Allah ya toni asiri tsinannu wallahi duk wanda aka kama da sa hannu sa aciki Ni da kaina zan binne sa da ransa bayan angasa masa azaba in Allah ya yarda Duk dai an kama maku mugaye tsinannu waɗanda basu da imani shine bayan kunfitar da ita daga gidan hakan bai ishekuba shine kuka bi ta bayanta kuka bugeta da mota sannan kuka rabata da ɗanta shima baku barsaba kukabishi kuke azabatar dashi da ƴarsa saboda tsabar mugunta da ha'inci da son zuciya irin naku maitayi muku mai tsare muku tunda muke da sabreena bantaɓa jin kanta da wani ba kowa nata ne tana mutunta mutane kukayi mata haka dan cin amanar zama ko dan saboda kunga ɗanta shine sarki to ai bata ɓaci ba asirin ku zai tonu kuma gashi Allah ya nuna muku ishararku gasu sun dawo sai kukashe kanku dan baƙin ciki, kallon ta tamayar kan Ammah da fulani sannan tace wallahi wannan mugun zama irin naku ai ba wani ɓoye ɓoye ko rufa rufa da za a ɓata loƙacin gurin gano wanda ya koreta dole acikin kune dan haka wallahi ku za akama musamman ke ɗin nan ta nuna fulani sannan tace "ko rantsuwa ma nayi bazataci ni ba wallahi ni nasan kece ummul aba isin faruwar komai tunda gashi kinkawo mana wani ɗan kince nakine anɗau sarauta ambasa saboda ke baƙya haihuwa shiyasa kika kori mai haihuwar kika kawo wani daban akan cewar ɗankine saboda tsabar ƙwarewa da son kai da mugun ta to wallahi zakici ƙundugurin buhun ubanki sai an karkarya ki gunduwa gunduwa anbawa karnuka suncinye ki ahaka dan nasan ƙasama bazata karɓeki ba saboda mugun halinki shegiya ƴar kutumar uba mai kama tukunyar giya 🤣(oh ni ƴasu daman a tukunya ake dafa giya) tana faɗa ta ɗaga ƙafa zatayi kanta aka riƙota da daga abun da take shirin yi dan sunan idan suka sake ta sai ta kusa kaita lahira alhalin ba a tabbatar ba da zargin da take mata ba dan ahalin da suka ganta sunan halin ta zata iya aikata komai ma dan gwaggo haka take akwai zuciya bata iya fushiba idan ranta ya ɓaci bata ji bata gani tun ƙuruciyar tama idan abu ya haɗasu da wani to idan bata ganta akanka tana maka mugun duka to bata samun nutsuwa har saitaga ta ladaftar dakai da duka gata da ƙarfi kamar me aljanu haka take komawa idan tana dukan mutum shiyasa haryanzu halinta na nan ba raguba ba saima ƙaruwa da yayi ga faɗa kuma ga tsufa sai abun yake neman fin nada kunsan mutum ko baida faɗa idan ya tsufa sai kuga ya canza hali abu kaɗan zakayi masa ya hauka da masifa da bala'i duk kusan tsofaffi haka suke da zarar sun tsufa, bare kuma ita da daman can mafaɗaciyar ce ga tsufa kuma shiyasa abun yayi worse da yawa idan ranta ya ɓaci bata iya controling ɗin kanta saita koma kamar wata zararriya, abun har mamaki yake bawa mutane yanda take adore ƙashin ta da ƙwari har yanzu dan idan ta ɗaga hannu ta makama sai kaji ajikin ka ƙarfi gare ta kamar doki shiyasa har yanzu da sauranta bai gama tafiya ba,

Ammah nason yin magana amma takasa saboda tsoron gwaggo da yakamata tana tsoron tayi magana gwaggon ta dawo kanta dan haka ta ƙara jan jiki  ta takure gefe guda aƙasan kujerar san zaman kan kujerar ma ya gagareta tunda akace acikin su biyu sai sun fito da wanda ya koreta ta tsure dan bataso zargi yazo kanta dan tasan zasu iya wahalar da ita idan suka fara zarginta dole ko mai zasu ce bazasu yardaba kuma tasan Fulani ko da ita tayi bazata amsa ba nan kusa saitasa an wahalar dasu itakam ina zata tsoma ranta wannan tunanin ne yasata rawar jiki ta sauko daga kan kujerar ta koma ƙasa can lungu lungu ta zauna ta kama kanta guri ɗaya....,

nandai aka samu aka lallaɓa gwaggo tayi shiru ta zauna sannan akadai cigaba da tattaunawa akan matsalar inda papa yake cewa ayanzu dai baza a zargi kowa daga cikiba saidai za afara bincike ne har a tabbatar kuma ta inda za afara doke a fito da wanda ya sanar da mutuwar ta ranar da akace ta mutu idan akayi haka tanan za agano ko waye saboda duk wanda ya fara sanar da mutuwar ta dole shine tunda Saida yayi yanda zaiyi ta fice daga gidan sannan aka sanar ta mutu saboda kar ayi wani bincike shiyasa aka rufe musu baki da cewar ta mutu dan kar kowa yaƙara yin maganar saboda,

waziri ne yace "wannan maganar taka gaskiya ce yana da kyau afara da binciken kafin azargi wani saboda zargi bashi da kyau bamusan ta ƙamaimai mai waye da sa hannu acikiba dole sai anfara bincike dan akama mutum da hujja yanzu sai muyi tunanin wanda yasanar da mutuwar ta yanda za ayi mugano shine kowa zai tuna wanda yagaya masa shima sa a tambaye sa waye yagaya masa kunga dagana dole za aje ƙarshen inda maganar ta fito sai mukama koma waye.......,amma yakuka ce da shawarata?

kowa na'am yayi da shawarar da yabayar kuma wasu har sun fara tunanin wanda yasanar da su ɗin Saida babu wanda ya fito ya faɗa saboda ba abada damar faɗan ba,

surutunne ya ƙara yawa kowa da abun da yake fitowa daga bakinsa  sai hayaniya ta nemi ta kaure aciki akayi saurin dakatar dasu......

   da ƙyar aka dakatar dasu daga hayaniyar da suke sannan kafin wani ya ƙara cewa wani abun gimbiya ta miƙe cike da ƙasaita dan ta tuna baya takun da take na matar sarki gimbiya shi tafara yi yanzu saida taga kowa yaɗan nutsu tashiga binsu da ido tana kallon kowa da kyau sannan ta maida kallon gun Meer dake tsaye har yanzu sai ta taka taje har gaban sa sannan ta kamo hannu sa baimata musu ba ya shiga binta sai da taje gaban papa sannan ta sakesa sai ta koma gun da Ameesha take itama ta taso da ita takawo ta gaban papa da hannu tayiwa Abu alama da yazo dan haka yataso cikin rashin ƙwarin jiki dan shifa har yanzu yakasa yarda da abun dake faruwa jin abun yake kamar amafar ki da sanyayyen jiki ya ƙaraso inda suke ya tsaya,

maida duban ta tayi ga papa da ya kafesu da ido yana ta kallon su kamar yasamu T.V yasaki baki kawai,

nuna masa abu tayi sannan tace "mai martaba dawa wanann yayi maka kama inaso ka faɗa da kanka basai anfaɗa maka ba,

kallon ta papa yake cike da rashin fahimtar maganar da take sai kawai ya maida duban sa ga Abu ya kallesa sosai sai ya janye daga kallon sa yamayar kan maama sannan ya

64 / 74