zamu iya yin amfani da ita wajen shigar da qarar amma hakan baze yiyu ba dole sai munbi komai ahankali idan munaso komai ya tafi daidai duk da gargadin da yayi mana nasan shima dole yana cen cikin tashin hankali kawai kwarewa ce tahanasa nuna hakan badan hakaba kasan da tuni yasa ankamamu tunda har yasan mundauke shi to dole yana da wani labarin akan mu dole sai mun sake shiri mu juyar masa da nasa tunani ta hakane kawai zamu iya cinma abun da muke nema har mu gano inda yake,
janye hannun sa sam yayi daga dafan sa dayayi sannan ya miqe tare da juyowa yana fuskantar su da kyau sosai maganganun shettima sukayi tasiri a zuciyarsa sai yanemi duk wani bacin ran ma yarasa, saima wani irin kwarin gwaiwa da yaji yazo masa,
maganar ka gaskiya ne yanzu tunda ancire sim din sannan wayar ta fashe dan haka jefar da ita zamuyi sannan yanzu mu koma gurin shi ayau sai yagaya mana inda yake,
Shettima yace " kana ganin zai gaya maka batare da anyi masa baranar dangin saba yakamata muafara bincike akansa mugano wani wanda yafi kusa dashi wanda idan aka tabasa zaiji aransa da har zaisakashi yagaya mana gaskiya, kawai muyi binciken yau inyaso sai mukoma gurin nasa koda zuwa gobe ne ina ganin hakan sai yafimana sauqi amma bana tunanin hakan nan zai fada mana dole sai munbi ta shawarar da ka kawomana tun dazu,
Shiru yayi bece masa komai ba sai kuma yace hakan zamuyi yafada cike da qarfin gwaiwa sannan ya koma kan kujerar yazauna tare da miqa hannu ya karbi sim din dake hannun shettima,
a flash yasaka sim din ya zura ajikin system din sannan yafara aikin sa bai wani dauki lokaci me tsawo ba ya tashi tsaye tare da cewa yess yafada da qarfi yana kallon su cike da jin dadin abun da yace da kuma ganin yanayin sa da ya tabbatar musu da anyi nasara kenan,
bani wayar ka yafada yana kallon bossay da sauri bossay ya miqa masa copying din wata number yayi aciki sannan yace ka ajiye mana wannan number kayi saving dinta bayan yabasa ya karbi ta shettima ma itama wata number yayi copy ya miqa masa yace shima yayi saving sannan ya qara dauko tashi wayar yayi copy,
number suwa kagano? shettima ya tambayeshhi ,
"naduba naga numbers din da yafi yawan waya da su naga ansaka my wife itace nabawa bossay yafada yana nuna bossay,
tabiyu kuma ta mahaifiyar sa ce ita nabaka, "ni kuma ta daughter din sa nadauka kuma ina kyautata zaton duk sune dan haka yanzu su zamubi didigi mugano inda suke da zama amma zamu rabune saboda naga kamar duk ba aguri daya suke zaune ba,
bossay " yace amma aganina ai bama sai anbi diddigiba kawai kiran su zamuyi awaya? yafada yana kallon,
harar sa shettima yayi yace idan ka kirasu din kana da abun da zakace musu da zaisa suyi maka kwatancen inda suke ne ae dole sai munbi mungano da kanmu,
dan nufasawa yayi sannan yace zamu iya sani wallahi amma basu zamu fara nema ba iyarinyar zamu fara nema ko ba budurwa bace yafada yana kallon sameer,
dage kafada sameer yayi alamun shima baisani ba,
hakan kuma yayi maganar ka abun dubawa ce nasan ma dole budurwace amma de sai nake ganin tunda batare suke ba ai kamar bazamu iya snin inda sauran suke ba, bossay yace to ai ko ita muka kama shikenan zamu iya yimasa barazana da ita amma ya kuke gani,
"aa bazamu bi ta wannan hanyar ba kawaidai yanzu abar batun sauran yanzu muje tare har inda yarinyar take sai mubi location inyaso idan yaganta kuma yaqi saduda sai mukamo sauran,
duk sunyu ns'am da shawarar tasa dan haka ba bata lokaci suka tattara inasu insau suka fita daga office parking sapace suka zo kamar yanda sukazo dazu yanzuma haka sukayi bossay ne zaija motar, bayan sungama shiga gabadayan su yaja motar da gudu me gadi ya bude musu gate din ya kwasheta aguje suka fita daga hospital din,
wayar yadauko ya kunna location din number nan yafara nuna musu hanya tun yanacewa bossay ga inda zaiyi daga qarshe kuma sai kawai ya miqa masa wayar gabansa bayan sunzo unguwar da take(unguwar sharada) wani layi suka shiga sannan suka qara yin kwana adaidai wani gida suka tsaya inda abun ya nuna musu parking sukayj abakin gidan sannan bossay yace "to ya za ayi kiranra za ayi awayar ko kuma turawa za ayi akirata?
"shettima yace habade saidai akirata awayar kawai sai yafi,
kana da abun da zakace mata idan kakirata din har inama kana dashi to idan tafito baizama lalle tayarda damuba saboda batasan muba bata taba ganin muba kawai yanzu wani acikin ku yafita yaje yasa me gadi yakirata,
ko kai bossay kaje saika san yanda zakayi ka jawo hankalin ta har ta yarda tashiga mota, mukuma fita zamuyi daga motar mujiraku abakin kwanar cen idan kun fito sai ka dauke mu mutafi,
"a'a wallahi bani yakamata naje ba kai yafi kamata nasan dole intaganka zaka iyayi mata kwarjini kuma sai tafi yarda dakai bazata iyayi maka musu ba tana ganin ka handsome din nan ai da gudu zata amince dakai bai rufe baki ba shettima ma yace gaskiya ne wallahi kai zakaje bazata taba bijere maka ba kawai kaje ayi awuce gurin dan nasan kafin ma kace ta shiga zata shiga saboda qaramin tafiya da imanin ta zakayi ba bare ma taji kana sanbado mata kalamai tuni zata mace maka yaqarasa maganar yana kunshe dariyar da take son kwace masa dan yasan baqaramin abu suka daukowa kansu da wuya sam ya amince shida bama ya magana da wata macen amma shine yau za ace yayi magana da wata kuma harda kalamai tirqashi abun da kamar wuya,
wata uwar harara ya watsa musu gaba dayan su tare da nuna kansa da yatsan hannun sa cikin hade rai da bata fuska alamar ba wasa din nan yace"ni ni zanje wajen mace mai kuka daukeni ta ba inda zani ni sa'ankune danma kunga ina kulaku shine zaku wani ce inje wai harda cewa inyimata kalamai saidai uwar kalamai zanmata nibanda mace taimin laifi indauki mataki akanta me na iya kai ai kasan halina ba wani abu zan iyace mata ba dan haka kawai ku ajiye wannan maganar saboda ba abune me yiyuwa ba bazan taba zuwa ince inason maceba harkuma inyi mata kalamai kai nifa kama rainamin hankali yafada yana kaiwa shettima bugu akafada kalmar kalaman nan da yafada ba qaramin tsaya masa tayi araiba,
Wallahi ka kiyayeni kana mun abubuwa da yawa ina rabuwa dakai ko to bazanje ba shidinma yafasa zuwa kai zakaje,
gaba dayansu dariya suka saka mishi sanna shettima yace kasan Allah ba maganar wasa ba kai yakamata kaje indai bawai kanason ka bata mana shiri ba kagade layin nasu da mutane bare ace za ayi mata taqarfi tana fitowa mu dannata amota dole sai dai mushigo da ita tacikin sauqi inbahaka ba kuwa tofa aikin mu bazai tafi yanda muke so ba zamu iya samun matsala dan haka malam kawai kafita kaje,
still de kin amince musu yayi saida suka sake wani cecekucen kafin daga baya da kyar da kyar suka shawo kansa tare da yimasa dabara sannan ya amin ce da yaga ba yanda zaiyi,
murna sukayi sosai tare da yi masa godiya sannan suka fita daga motar gabadayan su key din motar bossay yabashi sannan sukace to yafara tafiya sugani sannan ya su sutafi tare da yimasa fatan samun nasara,
ko kulasu baiyi ba saboda haushin su yaje ji yayi gaba abun sa taku baifi biyu yayi ba,
shettima yakira sunan sa dan dakatawa yayi batare da ya juyo ba,
shettima tace fatan nasara fa mukayi maka bazakace Ameen ba ko duk zumudi ne yau za afara zuwa zance wajen budurwa to adai yimata ahankali kar akasheta da kalamai sanna kuma kar ashanyamu muyi tajiranku,
dannasan za ayi wucewa da soyayyar gaske amanta damu dan Allah muna roqode kar ayimana haka romio tuzuru dan nasan ba asaba ba kuma wall.........
beqarasa ba sam yayo kansa afusace,
kafin yaqaraso sukuma sukayi saurin barin wajen suna mishi dariya,
kwafa yayi ya tsaya yana binsu da kallo jiyake kamar ya fasa zuwan ma da haryayi tunanin binsu sai kuma yafasa kawai yayi kwafa tare da juyawa ya nufi qofar gidan,
yana qarasawa sai ya tsaya abakin gate din,
ya kai wajen 2 minutes agun yakasa kwankwasa gate din wani tunanin ne yaqara fado masa yanzu idan ya buga aka bude wa zaice yana nema sai yanzu ya tuna ashe duk tsare tsaren nasu sun manta basu san sunan taba sosai ya shiga tunanin abun da zaice,
wata dabarace ta fado masa da sauri ya zaro wayar sa dake aljihu sai ya bude ta ya shiga WhatsApp dinsa number ta ya lalubo sannaan yayi mata sallama da niyarsa idan yayi mata magana sai ya goge number ta ta daga kan wayar sa inyaso sai yakoma WhatsApp ya duba sunan da take amfani dashi tanan kawai zai iya gano sunan ta idan tasaka,
bayan yayi mata sai ya fita yake contact din ya goge number ta sannan ya kuma shiga WhatsApp din ga mamakin sa yana shiga dak kawai yaga anbude sallamar da yayi mata alamun tana ma online da sauri ya bude tare da duba sunan da take amfani dashi ba SUMY yaga ansaka ajiki hamdalah yayi tare da sauke ajiyar zuciya,
sannan ya duba yaga har tayi masa reply da hello
" sai kawai yace sumy yakk?
"ba jimawa ta amsa masa da lfy pls waye?
bangane me magana ba?
"bazaki gane ba daman amma fito waje ina qofar gidan ku sai kiga ko waye...
sticker zaro ido ta turo masa sanna tace aqofar gidan nufa kace anya kuma ni kake nema?
"of course yabata amsa,
gani awajen amma banga kowa ba ta maido masa da amsa,
duba qofar gidan yafara yi yana laliben ta inda zai ganta amma baiga kowa ba,
"baki fito ba yamayar mata da amsa,
"kaga malam nifa bazan fitoba saboda bansan ka ba wai waye ma yabaka number ta?
shiru yayi ya rasa amsar dazai bata shifa harga Allah yagaji saira kadan takaishi qarshe tun dazu sai wasu tambayoyi take masa,
daurewa yayi yacije yakai zuciyar sa nesa,
sannan yayi mata reply da
" idan kanason abu ai duk wani hanya dazakabi dan ganin ka mallakeshi bazai maka wuya ba dan haka samun number abune me sauki awajena dan haka kima daina mamakin inda nasamu number ki ki ajiye wannan maganar kitaimaka kifito inga kyakkyawar fuskarki ni masoyin kine na gaskiya( duk wanda ya tuba dan wuya ba lada ashede ka iya masoyin gaskiya 😂 lol),
"hmmm kawai tayi masa reply"
baƙaramin haushi reply din nata yabashi ba amma ba yanda ya iya tunda shi yake nema haka yaƙara hauƙuri yace "zaki fito din?
" a'a tace masa,
Why ? ya tambaye ta abun haushin kawai sai yaga tama sauka a online din,
mutuwar tsaye yayi agun tare da tsurawa message din da yatura mata ido lalle ma yarinyar nan mai ta maida shi suna magana tasan kuma basu gama ba amma tasauka karkada kai yayi tare da cije bakin sa aransa yana ayyana kalar rashin mutun cin dazai mata batasan ko shi waye ba 🤔,
haushi kamar yakasheshi haka yake ji zuciyarsa har wani zafi zafi take masa da radadi,
kashe wayar yayi ya mayar aljihu yana tunanin irin wulakan cin da zaiyiba su shettima dan duk su sukajawo wannan yarinyar take wulakan tasa dabasu turo shiba da tuni hakan bata faruba da girmansa da komai amma yazo wata banza can tanayi masa abun da taga dama,
babu wanda baiji haushin sa ba acikin su musamman ma su bossay sai kace su sukayi masa abun da tayi masa din,
cike dajin haushin yajuya dan bazai ƙara yimata magana ba tafiya zaiyi gwara yaje subi ta wata hanyar amma ba wannan ba,
juyawa yayi yafara tafiya har yadan yi taku waken biyar kawai yaji ƙarar bude ƙofar amma takaici bazai barsa ya juyo ba dan haka kawai yaci gaba da tafiya ya nufi wajen da sukayi parking,
"tsayawa tayi tana kallon bayan sa farace doguwar bata da jiki kyakkyawa ce ajin farko sanye take da wani maroon din hijabi har ƙasa dan hakama ganin kalar kayan da yasaka saboda ya rufe mata har ƙafafun ta,
tunda yajuya yafara tafiya take bin sa da kallo tabbas ta yarda kuma tana zaton shine wanda suke chart dashi yanzu daman ta fito ne dan ta tabbatar kuma ta tabbatar din batayi masa magana ba itama ta daga ƙafarta ta fara bin bayansa,
loƙacin data ƙarasa wajensa yasaka hannu ajikin motar zai bude,
" sai tayi sauri ta danyi gyaran murya tare da cewa nace ba... tsayawa yayi da ƙoƙarin buɗe motar da yake yi sannna ya shiga juyowa ahankali har yaƙara sa juyowa gaba daya yana fuskantar ta ƙurawa juna ido sukayi na ƴan daƙiƙu ita tafara janye nata idon daga garesa,
ahankali tace kaine wanda muke chart yanzu?
tayi maganar batare da ta kalle saba har yanzu kam shi baidauke idon sa daga kanta ba ,
jin shiru baibata amsaba yasa ta dago dara daran idon ta takalle sa ganin ita yake kallo yasata sauri ƙara kawar da nata dan bazata iya jurar kallon sa ba,
juyawa tayi da niyar barin tunda yaƙi magana,
"eh nine' taji ya bata amsa juyowa tayi ta kalle sa tace to gani idan kuma baka da abun cewa intafi,
"wani abu yaji yazo masa wuya amma sai yadaure tare da basarwa harda ƙaƙaro murmushin dole yayi mata tare da cewa agafarceni sarauniyar mata kallon kine yasani manta a inda nake dan Allah inbaza ki damuba mushiga daga ciki sai mu tattauna ingabatar miki da abun da ya kawo ni gareki gimbiyata,
tundaga kan ƙafarsa tarar kallon sa har kansa masha Allah tace aranta tare da fara kokonton anya kuwa wannan ba batan kai yayi ba kyakkyawa dashi amma yace yana sonta to a inama yasanta itade tunda take bata taba ganin saba ko a mafarki to komade meye gaskiya fa ya hadu iya haduwa tunda taganshi taji yamata ya burgeta yagama tafiya da imanin ta(tabb kina ruwa kam) saidai tasan ba class din tabane dan ta tabbata yafita komai kyau da kudi tunda alamu sun nuna hakan ajikin sa da kuma kalar kayan dake jikin sa gayen yayi ta ko ina baida makusa,
amma fa saidai duk da haka bazata bari yagane hakan ba gudun kar ajinta ya zube gara itama ta nuna mishi tana da class kar yarainata,
"Hy yace mata tare da daga mata hannu asaitin fuskarta,
hakan yasata dawowa daga tunanin datakeyi ,
dan kallon sa tayi sannan tace a'a duk maganar da zakayi kayi ta anan inajin ka basai mun shiga ba,
"hmm yace aransa tare da watsa mata kallon banza afakaice batare da ta gani ba,sannan yace "haba gimbiyata ai ba girman kibane ace kintsaya anan kowane yana wucewa yana ganin ki hakan be dace dake ba yakamata mushiga ciki hakan sai yafiye mana safe ko ya kikace ammafa idan bakyaso shikenan bazan takura miki ba duk abun da kike so shi za ayi kawaidai cancanta na nuna miki gimbiyar mata,
har cikin ranta taji dadin kalaman sa da fasa mata kan datayi tabbata wannan muƙamin da take ganin batakai matsayin nan ba,
jin tayi shiru yasashi cigaba da cewa kyakkyawa ta bakice komai ba nifa inason inji kina magana domin ba ƙaramin dadi nake jiba idan naji muryarki yakamata ace kitausayawa wannan baƙon naki wanda yagama mutuwa akan sonki dan Allah karkice a'a kitaimaka mushiga ciki muyi magana nazo da alkhairi gare ki,
yana ƙarasa maganar bai jira cewar taba kawai ya bude mata back seat yace Bismillah sarauniya ta tafaɗa yana kafe ta da ido da yasata takawa batare da ta shirya hakan ba kamar wacce ake control din ta haka taji gaba daya yagama kashe ta da kalaman sa batasan lokacin da ta shiga cikin motar ba kawaide ta ganta aciki,
tana shiga ya rufe ƙofar tare da sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ahankali ya furta Finally mungama dake,
sannan yazagaya ta dayan barin inda take ya bude ya shiga yana shiga ya rufe ƙofar tare da kafe ta da idanu hadi da sakar mata wani irin murmushi me cike da ma'anoni da ita bata gane hakan ba,
murmushin da yayi har cikin can ƙasan zuciyar ta taji shi juyar da kanta tayi tana kallon window tare da sakin nata murmushin da bata san tanayin sa ba,
shikuma hakanne yabashi damar zaro hanki din dake gefen kujerar ya lallaba yasakama ta a hanci kafin ta juyo ta kalle sa har ta sume luuu tayi zata fada jikin sa yayi saurin janyewa yana wani ya tsina fuska kamar yaga abun ƙyanƙyami haka ya kwantar da ita kan kujerar,
kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️
💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓
[6/2, 11:30 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*💖the talent troupe💖*
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿45&46
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️
Yana ƙarasawa bakin kwanar sai yaga baigansu ba hange hange yafarayi daga cikin motar amma baigansuba wani haushinne yaƙara kama shi tsaki yaja aransa yana tunanin kuma ina sukayi, cike da takaicin rashin ganin nasu yadauko wayarsa yakira shettima, ,,"kuna ina ne? yatambayesa bayan yaɗaga wayar,
bayan yabasa amsa kawai ya kashe wayar tare