kuyi gaggawar fitowa ku amsa laifin ku idan kuma ba hakaba kuka bari na nemoku da kaina to bazakuji da daɗi ba nagaya muku,
sosai Azeema ta ƙara tsurewa ƙafafun ta har suna karkarwa zasu kasa ɗaukan ta sanin halin ta kuma tasan tabbas aka duba sai ankama su,kuma abun da tafaɗa sai ta tabbatar dashi musamman ita dan tasan ba lalle shi a hukuntashi ba kamar yanda za a hukun tata,
dan haka tunkan ake ga nemosun ta yanke shawarar tayi magana kawai aji inda suke wataƙil idan tayi haka hukuncin yazo mata da sauƙi kamar yanda taji fulanin ta faɗa,
dan haka ta buɗe baki zatayi magana tunkan ta idasa buɗe bakin shettima da ya fuskanci abun da take shirin yi,shima atsorace yayi saurin ɗora bakin sa akan nata dan ya hanata damar yin maganar...
zaro ido tayi aranta tana ayyana lalle wannan mutumin bashida saiti su da suke cikin wannan halin na tsaka me wuya amma yakeso yaƙara jawo musu wani laifin yanzu idan aka gansu ahaka da da wane ido zata kalli mutane,
ƙoƙarin ƙwace kanta tafarayi ya riƙeta sosai gudun kar ta tona musu asiri shi kansa zaiji kunya idan hakan ta faru.......,
me aikin ce ta fara takawa taje ta leƙa wani lungu dake gefe can kitchen ɗin sannan ta leƙa ta ƙofar waje ko zata gansu amma bata gansu ba,
Fulani kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......😜😜😜
Kai wannan page ɗin akwai yawa nasan kowa saida yagaji da karanwa 😬 ku jinjina min
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[7/8, 9:24 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 84
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
____HAMZA___
tun loƙacin da yataho ruwa na dukansa ya ƙarasa ɓangaren su ɗakin su yashiga yana shiga ya tadda baba azaune wajen sa yaje ya tsugunna duk da kayansa sunjiƙe amma hakan baidamesa ba burinsa kawai ya bawa baba labari,
gyara zama yayi yana washe baki kamar gonar auduga yace "baba albashirin ka?
baba shima yana kallon sa da ƴar fara'ar sa akan fuskart yace "goro"
"baba yau munyi magana da ita har waje tafito wannan ruwanne ya hanamu yin soyayya amma de nace mata zan koma idan ya ɗauke kuma tace to sannan kuma na sanar mata dakai zaku gaisa ɗin anjima ta amince,
sosai baba yanuna masa jin daɗin sa akan nasarar da yayi yau,
,"gaskiya nataya ka murna Allah yasanya alkhairi Allah yasa matar kace yanda kake sonta Allah yasa itama tasoka,
"Ameen' Ameen" baba Allah ya amsa ,
ince dai ba dole kayi mata ba ya akai ma ta amince dakai yanzu bayan kace koda yaushe wulaƙantaka take?
hmmm baba bawa ai ba a cewa komai kaide kawai kacigaba da tayani addu'a amma yau ai har marin da ba ayi min ranar nanba shi aka sauke min yau,
"mari fa Allah dagaske kake wai mace ce ta mareka lalle so ba abun da bayasawa nikam dole inga wannan yarinyar da takeyi maka abun da kaga dama kuma karabu da ita lalle ta ciri tuta jarumi guda irin ka ta ɗaga hannu ta mare ka?
"hmmm baba abar maganar kawai nidai yanzu ka shirya anjima da yamma zamu ƙara komawa,
"to Allah yakaimu ammade wannan abu yaban mamaki wallahi mari tabb,
"baba dan Allah kabar maganar nan wai sai nanatawa kake ni banɗauke sa komai ba dan ko zafima banji ba,
burina kawai ta kulani kuma ta kulani naji daɗi kuma anjima ma zata kulani,
bai basa labarin yanda sukayi da fulani ba,
"baba yace "natayaka murna sosai Allah yakaimu jimawar da rai da lafiya,
"yauwa baba Ameen abun da nakeso inji kace kenan,
tashi yayi daga gurin ya hau cire kayan jikin sa sannan ya canza wasu busassun yayi kwanciyar sa yana ta tunanin yanda sukayi da fulani shikenan yasan yanzu duk sanda yake buƙatar ta zai ganta akoda yaushe wayyo daɗi zai ringa kasancewa da ita koda yaushe,
baba na kallon sa duk abun da yakeyi amma saidai kawai yayi murmushi yana jinjina irin son nan da yakewa yarinyar nan abun har mamaki yake basa........
'Fulani kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......✍️
da sauri me aikin nata ta taho dan itama ta leƙa saidai cikin rashin kula tabi ta wajen sa Azeema take wanke wanke kuma ta zubar da ruwa agun dan haka tana takawa ta ta zame ta faɗi ji kake timmm ƙatuwar mata aƙasa ta faɗi da bombom ɗin ta tayi zaman dirshen agun, ihu tasaki me ƙara sakamakon zafin da taji abombom ɗin nata,
hakan da tayi ya dakatar da fulani daga ƙoƙarin shiga store ɗin datake ta juyo dan ganin abun da ke faruwa,
azaune ta ganta tayi zaman dirshen tana wurwur ga ido kamar na mujiya,
fulani tace "me yasameki kikewa mutane irin wannan ihun? haba murja sai kace wata ƙaramar yarinyar... kinsan dai bana son haniya da yawa bare kuma aringayi min ihu aguri,
"fɗuwa nayi nataho da sauri ban kula da ruwan ba na zame,
fulani tace to ai sai kitashi tunda ba wani ya yarda keba gobe idan kin taho sai kiringa kallon gabank......
bata ƙarasa ba sakamakon jin ringing ɗin wayar ta dake hannun ta yasata katse maganar da takeyi,
duba wayar tayi dan ganin me kira da sauri ta ɗaga kiran saboda daman shi take jiran tsammani tunɗazu,
tana ɗagawa tayi saurin ficewa daga kitchen ɗin har tana haɗawa da ƴar sarsarfar ta gurin yin sauri,
taƙaicine ya ishi murja yanzu ta faɗi maimakon tayi mata sannu amma saima faɗa da zata hauta dashi sannan kuma tayi ficewar ta saboda bata da tausayi, da ƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe tsayi azaba tasama ta manta da waɗanda take nema daman ta gama girkin da takeyi jerasu yarage dan haka kawai itama tafita daga kitchen ɗin dan sai taje tayi jinya kafin ta iya ci-gaba da aikin.....
duk abun dake faruwa akan kunnen su Azeema dan haka suna jin fitar su Azeema tafara ƙoƙarin ƙwace kanta sakin ta yayi yana kallon ta itama shi take kallo sai tayi saurin janyewa saboda hakannan sai tafara jin kunyar abun da yayi mata yana ganin haka yasaki kayataccen murmushi sannan yace ,"matsoraciya kawai daman haka kike da tsoro to wallahi ki rage tsoro,
bata ce masa komai ba ta ɗago ido ta hararesa tare da cewa ni matsamin in wuce wallahi kar ka ƙara zuwa inda nake bazakajamin bala'i ba ina zaman zamana inji da abun da yake damuna ma basai ka ƙara da naka ba,
"au hakama zakice ko danma kinsamu na taimakeki shine kuma yanzu zaki min rashin kunya to wallahi inbaki bini ahankali ba sai in ƙara wani yanzu kuma inbari har sai kowa yazo ya ganmu ahaka ana tambaya kuma ince ke kika jawo ni,
"inbaka fasaba dake su basu da hankali sai su yarda dani najawo ka ƙarfinka nafi da zan iya jawo ka kuma ka biyo ni ai duk wanda ma kagayawa wannan abun babu wanda zai yarda dakai saboda wannan ai maganace da ba wanda zai yarda,
"haka kika ce to bari inyi sai mugani,
"wai me zaka ƙara yi?
kashe mata ido ɗaya yayi yace "shan sweet sweet ɗin nan akwai daɗi yafaɗa yana ɗora hannun sa akan lip ɗin na ƙasa yaɗan shafa shi,
wani irin yam taji jikin ta yayi mata da sauri ta kai masa duka a hannun tanaso tayi magana amma takasa sai faman hararar sa take kamar idon ta zai faɗo,
dariya yayi kawai tare da cewa "kinaso kina kaiwa kasuwa ko to shikenan zo ki wuce kar na ɗora ki akan network dan naga kina niyar hawa,
matsama ta yayi batayi wata wata ba tabi ta gefen sa ta fita kuma bata gane ma network ɗin da yake nufi ba kawai itade burin ta ta fice daga gurin,
tana fitowa shima yafito akusan tare suka fito,
tayi wajen wanke wanken ta tana Allah Allah tayi sauri tagama kar fulani ta dawo ta ganta a kitchen ɗin,
da har zai ƙara zuwa ya takura mata sai kuma ya tuna any time fulani zata iya dawowa kuma baisan hakan ta faru dan haka sai yayi saurin fita daga kitchen ɗin yana daf da fita daga falon saiga murja ta fito daga ɗakin su caraf kwa idon ta ya sauka akan sa shi baiganta saboda yajuya baya kuma har yafita bai san da itaba da yazo yayi mata gargarɗi,
tana ganin fitar sa ta girgiza kai tare da saurin nufar kitchen dan taga Azeema na ciki tana leƙawa kuwa ta ganta a tsaye tana wanke wanke ƙarasa shiga tayi har gaban ta sannan tace "ke munafakar ina ce ina kuka shige daman nasan kuna ciki ɓuya kukayi ke ƴar iska ce ban saniba daman daga kallon idon ki nagane fitsararriya ce ke bada abun kima har kinkai matsayin da zaki kula ɗan masu gida ke asuwa to wallahi sai na sanar da ita anɗau ƙwaƙƙwaron mataki akanki zama masarautar nan sai ya gagareki daman duk wani take taken ki akan idona kikeyin sa kuma ina nan tara ki nakeyi akwai ranar ƙin dillanci kicigaba daga inda kika tsaya kar kifasa,
duk wannan abun da take ko ɗaga ido ta kalle ta Azeema batayi ba tacigaba da aikin da take har tagama murja na gurin tana surfa mata maganganun jin taƙi kulata yasata taita fusata tanajin haushin abun da tsanar yarinyar.........,,
ita kwa Azeema tana gama wanke wanken ta daman ta kusa gamawa basu abu uku ne suka rage mata tana gamawa tayi ficewar ta tabatar da luguden laɓe a kitchen ɗin,.......
Fulani can uwar ɗaki ta shige gudun kada wani yaji wayar da take,
cike da damuwa akan fuskarta tace Hajiya sarah kinsan tunyaushe nake neman layin ki yaƙi shiga sai ɗazu dana gwada naga ya shiga ke kuma baki ɗaga ba,
daga can ɓangaren Hajiya sarah tace gode yanzu bagashi na kiraki ba gaya min me yake faruwa kike nemana haka, kinsan tun ranar da nazo gidan ki washegari nabar ƙasar sai shekaran jiya nadawo,
ajiyar zuciya Fulani ta sauke sannan tace gode yanzu duk ba wannan ba ina cikin tashin hankalina ga ɗaya baya jikina akwai matsala fa,
ina jinki ai daman tun ranar danazo nasan za asamu matsala tunda saida nagaya miki tunwuri ki gaggauta korar wannan mutumin danagani amma kika ƙi matsala kwa ai yanzu kika fara gani muddun yana cikin gidan nan,
"nifa ba wannan ne matsalar ba bana ta wannan danni ba matsalar da na fuskanta daga gare sa,
"to meye matsalar? Hajiya sarah ta tambayeta,
gefen gado fulani tasamu ta zauna sannan tace matsala ta wani yaro ne da acikin masarautar nan kuma bawa ne tun yana ƙarami yake cikin masarautar nan loƙacin da yazo kamar almajiri wani tsoho yakawowa sarki shi yace ya taimaka masa asamawa yaron aiki bashida kowa shine fa sarki ya karɓesa yazama bawa,
amma yaron nan tunda yafara girma na fahimci yaron taurin kaine dashi baya nuna tsoro ga kowa haka yaron yake to daga baya kuma rashin mutuncin nasa ya wuce kan kowa har yafara dawowa kaina idan nayi magana bayajin maganata idan hukunci nasa ayi masa sai tsoratar da masu hukunci idan dukane baza adake saba idan wani hukuncin ne sai yayi tafiyar da yace bazaiba har da kaina naje inda suke nayi kiran yaronnan amma yaƙi zuwa abun idan nazauna ina mamaki sosai me yaron nan yake taƙama dashi da yake min irin waɗannan abubuwan abun na damuna narasa yanda zanyi dashi yafi ƙarfin kowa,
to babban abun da yayi min na ƙarshe ɗazu ɗazunan shi yafi komai tsaya min arai ya firgita ni sosai ina cikin nan nida wata me aiki sai ya shigo ciki kansa tsaye ko sallama babu kuma da takalmi yatako har inda muke sai ya tsaya wai yanason magana da mai aikin abun yaban mamaki sosai natsaya inga iya gudun ruwansa dana ga abun nasa yayi yawa natashi tsaye zan maresa sai yariƙe min hannu,
"ataƙaicedai hajiya sarah da na takurawa yaron nan nayi masa barazana ai sai ya dawo min da tasa barazanar da ta taka tawa ninkin baninkin,
"tofa lalle wannan yaron da abun da yataka amma de kaini ƙarshen labarin.... hajiya sarah keyin wannan maganar,
"hmmm fulani tace kedai bari ai bangama kaiki ba,
"kinsan me yace min,
"a'a"
wai duk abun danake atafin hannun sa idan nayi wasa sai ya fasa siriina kowa yaji abun da nake ɓoyewa tsawon loƙuta, dan haka kar nasake ɗaga masa yatsa ko in ɗaga masa murya abuɗe yaringa gayamin yana gamawa ya fice abunsa babu ko ɗar,
abun ya mugun ɗaure min kai shin shiɗin waye dan ina tunanin ma loƙacin da abunnan yafaru wataƙil ko haifar da ba ayiba inma an haifeshi to bashi da wayo ƙarewa ma kuma baizo nan gidan ba to a ina yaji waya basa labari, wannan sirrin dai nasan daga ni sai ke sai mutum ɗaya shima kuma yanzu baya raye to ta ina maganar nan tafito abun ya ɗaure min kaifa sosai,
dariya Hajiya sarah tasaka mata wanda har tana jiyo sautin ta da mamaki take bin wayar da kallo kamar Hajiya sarahn ce agabanta,
saida tabari ta tsagaita dariyar dan kanta sannan tace "lafiyar ki ƙalau kuwa yaza ayi ina gaya miki damuwata amma kina min dariya kuma......
hhhhhh Hajiya maryama ai dole inyi dariya wallahi kinban dariya sosai yanzu banda abunki dan Allah ina tunanin ki yatafi yanzu wannan ɗan abunne zai sakaki adamuwa kinajin maganarsa ai kinsan kawai barazanace ba gaskiya ba ta ina zai sani kawai bugar cikin ki yayi saboda ɗan duniya ne yayi miki haka dan yagane lagonki kuma yagane kinyi ganganci da kika nuna masa kinji tsoron sa yayi galaba akanki ko kinji yace ga abun da kike ɓoyewa?
"A'a kawaidai ca yayi zai tona min asiri ni kuma nasan inada sirrin shiyasa nayi tunanin ko shi yake nufi,
"to gaskiya kinyi kuskure har ɗan yaro yafiki wayo yasan yanda zaibi ya tsoratar dake, to wallahi tun wuri ma kisan yanda zaki ɓullo masa ki nuna masa asalin kalar ki, ki dakatar dashi daga abun da yakeyi ko kuma abu me sauƙi ma kifata daga harkar sa kar kishiga harkar sa bare har yasamu dama yaci gaba da tsoratar dake tunda de fitinanne ne zai iya jawo miki wata matsalar nan gaba tunda kika nuna masa kin tsorata akwai sirrin kenan kinga daga nan zai fara ƙoƙarin bincike akanki har ya tabbatar da abun da kike ɓoyewa ɗin kuma yana sani tofa ba shakka kowa sai yasan abunnan gwara jini dashi ku rabu lafiya da dayanda zakiyi ma da kinsa an fitar dashi daga gidan dan wannan zama dashi haɗari ne dan sai yayi abun da baki taɓa tunanin ba,
sai yanzu fulani ta ɗanji dama dama aranta duk atunanin ta yaron nan da gaske yasan sirirrin ta ashe duniyan ci kawai ya nuna mata,
"to yanzu ya kike gani zanyi dashi inbarsa yaci gaba da zama bakya ganin idan na Kore shi zai iya yimin wani sharrin ma ko kuma yayi wani abun da zai cutar dani bakiga fa yaron ba wallahi bayajin magana zai iyayin komai tunda kikaga kaf cikin masarautar nan kowa na tsorona amma banda shi ai kina kwa banga wanda zaiji tsoro ba suma kansu ƴan gidan tsoron sa sukeji dan wani daga cikin su ya taɓa ban labarin dukan da yayi musu shiyasa suke shakkar sa kuma wallahi duk daga baya ya tsiro da waɗannan abubuwan da ba yayi ammafa ina tunanin anya ba wannan tsohon da kika ce in kora bane yake zugashi saboda kullum suna tare yanda ba ataɓasa haka yakafa ya tsare babu wanda ya isa ya taɓa tsohon nan,
"afff bana gaya miki ba kince ai shi baida matsala zancen kenan ki koresa shine abu mafi sauƙi shikuma yaron kawai kibarsa yaci gaba da zamansa amma karkiringa takura masa da zaisa ya fusata yaje yayi muku wani abun kawai kurabu dashi kifita daga harkarsa,
"to shikenan nagode da shawarar ki har kinsa na ɗanji sassauci amma wallahi da gaba ɗaya hankalina ya tashi amma yanzu kin kwantar min dashi shiyasa akullum nake sonki akusa dani saboda kinfini tunani me kyau ina ƙara godiya sosai sai kinji alart dan wannan shawarar dole inbaki tukwicin ta,
"ba komai wallahi ai kinfi ƙarfin haka agurina wannan ba komai bane Allah ya tsare nan gaba nagode noma sai najiki,
"in sha Allah kwa yanzunnan zakijini,
daga nan sukayi sallama kowa ya kashe wayar,
atake ta tura mata maƙuden kuɗaɗe ta account ɗin ta sannan ta tashi zuciyar ta fess bawani taƙaici ta faɗa bathroom saboda futsarin da take taji tunɗazu tashin hankali ya hanata yi...,
*Sam*
tunda suka fara tafiya babu wanda yasamu damar yin magana kowa da abun da yake tunani har suka ƙaraso wani babban gida horn yayi me gadi ya buɗe suka shiga ciki a parking lot yayi parking sannan ya buɗe ya fito daga motar yayi sauri yazagaya ta inda take yasa hannu da kansa ya buɗe mata ƙofar tare da miƙa mata hannu, nata ta ɗora akai yakamota yafito da ita daga cikin motar,
hannun sa riƙe da nata suka nufi cikin gidan bayan sunyi sallama aka amsa musu suka shiga cikin falon gidan, saida suka shiga ya sakar mata hannun,
wata mata nagani a hakimce akan kujera hannun ta riƙe da waya tana lallatsawa ba tsohuwa bace kuma baza kace mata yarinya ba kanade ganin ta kasan ta manyan ta sosai,
jin murayar sa yasata ɗagowa tana ganin shine ta faɗaɗa fara'ar fuskarta tana miƙewa tsayi tare da cewa oyo oyo wata sabon gani kode ɓatan hanya kayi baka saniba shima fuska aɗan sake yace inajin dai nayi