Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   36 / 74

105K to 108K   out of 221K words

zata faru da bai ɗauke suba wallah da tuni yanzu suna cikin kwanciyar hankali batare da wata matsaba, shi yanzu ya zaiyi ya nemota gashi bayason haɗuwar sa da sameer baisan me zaifaruba dan ba ƙaramin aikin sa bane yasa hannun sa ajikin sa ba, yadaɗe agurin yakasa tayar da motar.......

________*SAM*

Unguwar maraba dake cikin abunjan suka dosa basu wani sha wahalar gane gurin ba suka isa har bakin gidan da kaka kwatan ta musu awaje sukayi parking daga dan nesa da gidan sannan suka fito gada dayan su suka nufi bakin gate din gidane tafkeken gaske da tundaga wake zaka gane ankashe masa kusɗi,

gate ɗin suka bubbuga amma ba abuɗe saida sukayi wajen sau uku sannan daga ciki akace wai waye ne,

shiru sukayi basu bashi amsaba sai suka ƙara bubbuga gate ɗin,

azafafe me gadin yabuɗe ƙofar yana cewa wai waye ne yake damun mutane ganin zaratan maza har uku yasashi yin ƙasa da murya,

yana binsu da kallo daya bayan ɗaya,

"waye kuke nema anan?

" bossay yace me gidan idan yana ciki kayi mana magana dashi,

saida yagama nazarin su tukunna yace baya nan,

baya nan kuma yace mana muzo cewar Sameer,

tunani yayi to kode da gaske suke amma de duk da haka baiyarda ba sai yace dasu to bari ina zuwa,

yafaɗa yana komawa ciki ai baigama rufe ƙofar ba bossay yayi saurin danna kai ciki yana shiga ya shaƙe mutumin baisake saba saida yaga ya sumar dashi sannan ya turasa dakin sa yaƙullo sa,

su Shettima ma da suka zama ƴan kallo suka bishi da ido kawai saida yagama sannan shettima yace me yasa kayi masa haka,

dan murmushi yayi yana sosa ƙeya yace ai wannan ɗan iskane muna fiki ne idan bahaka mukayi masa ba bazai bari mushiga ba bakuka ga irin kallon da yaringa yi mana ba da mun rabu dashi yashiga bazai fito ba dan idan yaje zai sanar dashi kunga shikuma tunda yasan bai haɗa appointment da kowa ba bazai fito ba zai iya cewa ace bama nan amma yanzu da nayi masa haka sai muje mugama binciken mu kami lafiya batare da wata matsala ba indai yana ciki bamu da wata fargaba,

yanzu de gaba ɗayan su saida suka jinjinawa ƙoƙarin sa da yayi dogon tunani a ɗan ƙanƙanen loƙaci da su basuyi ba sunji daɗi sosai da har saida sam yakasa ɓoyewa saida yace gaskiya kayi ƙoƙari gud thinking kace za muje dakai haka kake da zafin nama daman bansani ba,

sosai bossay yayi dariya jin ana yabonsa yace ai nafi haka kaima daga maka ƙafa kawai nake ne saboda.... sai kuma yayi shiru yana dariya,

shima sam ɗin yar ƙaramar dariya yayi sannan yace to shikenan zamu raba raini dakai daman rannan kace kafi ƙarfina ko to kabari duk san da komai ya daidaita zamu haɗa kwanji in koya maka hankali, haka suka cigaba da ɗan sa in sa akan batun ƙarfi kafin daga bisani shettima ya tunasar dasu abun da sukazo yi,

nutsuwa sukayi suka tunkari cikin gidan saɗaf saɗaf sukayi suka tura ƙofar falon suka shiga ciki sallama sukayi afalon amma sai sukaji shiru ba amsaba ɗakunan dake ƙasa suka shiga duddubawa amma basu ga kowa ba upstairs suka nufa da suke da tabbacin yana can ahankali suka shiga takawa har suka gama haurawa dakuna biyu ne asaman bakin ƙofar na farko sukaje suka tsaya sai sukaji kamar ba kowa ɗayan suka koma suka kara kunnen su sai sukaji kamar murya ƙasa ƙasa sosai suka ƙara manna kunnen su jikin ƙofar saida suka tabbatar da mutum aciki,

ɗagowa sukayi suka kalli juna shettima yayi musu alama da ido akan su afka kawai atake kwa suka tura ƙofar da ƙarfi Allah yasama ba muƙulli ajiki dan haka suna turata ta buɗu,

"zunbur sukayi daga kan gadon da suke akwan ce mace da namiji ne namijin ma magidan ci dan kana ganin sa kasan ya manyan ta dan harma yafara tsufa ita kuma macen budurwa ce dan zauna kusan haifar ta hakanne zaisa kagane ba matar sunna bace wannan duk yanda akayi suna kan gadon manne da juna suna morar loƙacin su sunade jin daɗin yanayin da suke ciki kawai sukaji turo ƙofa ankatse musu jin daɗin da suke ciki suna farantawa junan su,

namijin ne yafara tashi zaune san ganin wane isasshen da maine ya shigo masa gida kuma har cikin uwar ɗakin ya katse masa jin daɗin sa,

zaro ido yayi ganin zaratan maza agabansa, tunani yafara akan suwaye waɗan nan, daman Allah ya taimake shi jikin sa da gajeran wando ajikin sa dan haka yayi saurin saukowa yana shirin dauko rigar sa da sauri su sam sukayi kansa suka rufe sa da duka ta ko ina macen ce tafara ihu da kuka tabi ta tuƙuiƙuiye da zanen gadon tana faman sharɓar kuka tana basu haƙuri su rabu dashi amma basuma san tanayi ba,

saida suka tabbatar da yadaku sannan sukayi masa cali cali suka fita dashi ahaka suka fita dashi da gajeran wandon,

bayan sunkai shi mota acikin suka sakasa abaya suka ƙullo sanann suka dawo gidan suka hau bincike suka tarkato duk wasu takaddu da suka gani da kuma wayoyin sa harda laptop ɗinsa komai de ba abun da suka bari me amfani saida suka ɗauko sannan suka fito matar kwa harwaje tabiyo su tana yi musu magiya akan su rabu dashi bai turamata kuɗin da yayi mata alƙawari ba subari idan ya tura mata sai su tafi dashi wani kallon banza da sameer yayi mata ne yasa tayi shiru da maganar ta,

agurin suka barta suka ja motar su sukayi gaba sai kano ranau fari tass ganin sunyi nasara batare da sun sha wata wahala ba wajen ɗauko sa,

Suna tafiya suna hirar su cikin kwanciyar hankali da farin ciki ahaka har suka ƙaraso kano loƙacin da suka shiga garin kano biyar ta wuce direct inda suka kai mahaifin sumy nan suka kaishi shima saidai basu kaishi ɗakin da yake suka kaishi wani ɗakin daban batare da sunce masa komai ba suka ƙullo sa aciki suka fito,

saida sukaje sukayi sallar magriba sannan suka dawo gidan baban sumy sukaje suka fito dashi suka kaishi ɗakin da suka kai ɗayan da har yanzu baigama dawowa hayyacin sa ba,
"tambayar mahaifin sumy sukayi wanann shine mutumin nan ya tabbatar musu da cewa eh shine yana ɗan ɓoye fuskar sa saboda baya so yagane sa, saboda yasan da wuya ya gane sa a irin halin da yagansa yasan ba lalle yagane shi ba,

mayar da shi sukayi ɗakin sa sukace dashi yabari gobe zasu sallame sa yayi haƙuri zuwa gobe bayanda ya iya dole ya koma ɗakin yaci gaba da zama sukuma suka ƙara ficewa daga gidan saboda duk agajiye suke bazasu iya zama wani tattaunawa dasu ba yanzu dole sai sunke gida sun huta zuwa gobe sai su dawo,

mota suka koma suka shiga yanzu bossay ne yajasu zuwa gida suna kan hanya wayar sam tayi ƙara da bazai ɗaga ba sai kuma ya duba yaga momma ce ke kiran sa da sauri yaɗaga tare da kara wayar akunne daga kwancen da yake yayi saurin tashi zaune yace momma meke faruwa kisanar dani bansan me tace masa ba daga cen ɓangaren,
yace to shikenan gamunan munkusa ƙarasowa ma muna hanya ajiye wayar yayi shettima dake gaban mota ya juyo yace ya akayi ne lafiyade ko,
Sam yace wallahi bansan meke faruwa ba momma ce ta kirani tace wai gida ba lafiya komai nake nabari muje yanzu nan,
tofa Allah yasade lafiya cewar bossay,
sam yace anya kuwa lafiyar nan da sauƙi ka ƙara gudu de kawai muyi sauri muje tunda naji momma ta nemeni ni nasan ba ƙaramin abu bane zaisa momma kirana, Allah de ya taƙaita ta kawai koma meye yazo da sauƙi.....
"Ameen suka amsa masa dashi dagana kuma suka cigaba da tafiya batare da sun ƙara cewa komai ba........

motar su na shawo kwana shikuma Ammar tasa na fita daga layin dan haka basu haɗu ba,

shiga sukayi suka nufi parking space
suna gama daidaita parking sam yafara fitowa da sauri ya nufi part din momma suma su bossay da sauri suka fito suka rufa masa baya da sarsarfar su suka qarasa cikin falon ko sallam basuyiba suka afka ciki momma suka gani a tsaye sai faman zarya take a falon takasa zama tana ganin gabanta ya tsanan ta bugawa ganin bossay datayi dan ita duk atunanin ta shine yayan Ameesha shiyasa tafi jin kunyarsa,

momma lafiya meyake faruwa kince muyi sauri muzo gida ba lafiya kuma nibanga komai ba na tashin hankali meyake faruwa?
ajiyar zuciya ta sauke me nauyi da kyar ta iya cewa eh ai ganine ba ga masarauta ba amma inbada muwa mushiga daga ciki sai insanar dakai afuwan dan Allah tafada tana kallon su bossay saboda taja sam zuwa sama hannunta riqe da nasa tajasa har zuwa dakin ta saida suka shiga sannan ta sake sa shide binta kawai yake da kallo yana jiran jin abun da zatace masa dan shima hankalin sa yadan tashi ganin furgici a idon mahaifiyar tasa,
"Momma nifa duk kinbi kin saka ni araduni dan Allah kigaya min abun dake faruwa mana kin kawo ni nan kuma kintsaya bakice komai ba,

"Sameer takira sunansa
gabansa yaji ya fadi tunda yaji ta kirasa da ainahin sunan sa to hakanne yakara tabbatar masa da lalle ba lafiya ba dan ba qaramin abune kesa momma fadar sunan saba kai tsaye. batare da ta sakaya ba,

"momma ina sauraron ki me yake faruwa kisanar dani mana koma menene ,

sameer akwai damuwa sosai kuma akwai matsala narasa ma tayanda zan sanar dakai,

"kifada kawai momma i na sauraronki niduk kinbi kinsani arudani,

cikin sanyin murya tanaso tayi maganar amma tana qara jin nauyin fada masa,

shiru yayi tare da kafe ta da ido yana mamakin yanayin mahaifiyar tasa da dan tunda suka taso da ita inajin bai taba ganin taji nauyin fada masa wata magana ba sai yau hakan yasa yadan ji faduwar gaba da tsoron jin abun da zatace masa,

matsawa yayi kusa da ita tare da kamo hannuwan ta duka biyun yajata zuwa bakin gado ya zaunar da ita sannan ya fuskance ta da kyau yace momma plss calm down momma ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki sanar dani abun dake faruwa duk kinbi kin tada hankalinki nima kuma kina so kitayar min da nawa hankalin dan Allah kisanar dani damuwarki,

Memakon tabasa amsa saikawai tayi zunbur ta mike tana girgiza kai tace "sameer ina ni i na nutsuwa ai banga ta zamaba zama bai kamace niba ahalin yanzu bani da ikon zama hankalin bazai taba kwanciya ba,


ya ilahi sam ya fada afili tare da dafe kansa da yaji yana sara masa cike da gajiyawa yace momma nifa nagaji tundazu sai abu daya kike fada kinqi sanar dani yakike so inyine yana kaiwa nan ya mike tsaye ganin haryanzu batayi magana ba yasa shi nufar hanyar waje dan zuciyar sa tagama kaiwa karshe yaga inba haka yayi mata ba bazata fada zata cigaba da bata masa lokaci ne kawai,


ganin zaifita yasata da sauri cikin rawar murya tace sameer daman akan batun yarinyar da kukawoq jiya ne........sai kuma tayi shiru takasa qarasawa,

cak ya tsaya tate da juyowa asukwane yadawo da baya yazo gabanta,

WHAT...!!!?
yafada da qarfi yana kara matsowa kusa da ita,

"momma what u say yarinyar da muka kawo jiya kike magana akai me yasame ta me yafaru da ita wayataba ta?

tsorone yaqara kama momma ganin yanda duk ya rude lokaci daya sai faman tambayoyi yake jero mata,

shiru tayi bata basa amsaba, "momma kigaya min abun da yafaru da yar mutane,

"daman dazu da safe tunda suka tashi bayan sunkarya suka fita cikin gida suka gaiggaida mutane suka dawo sai ita ta kwanta bacci sukuma suka qara fita,

Sainaje dakin ingano lafiyar ta sai kawai na tarar da ita azaune tayi tagumi nake tambayarta abun dake damun ta take sanar dani cewa ai ta tashine bataga su Amra ba shiyasa tayi ta gumi nace tayi hakuri tazo nakaita gurin su shine muna fitowa ma sai mukayi karo dasu sun shigo da gudu sukace wai yaya Ammar yace taje yana son ganin ta da farko ma kin amince musu nayi sai da suka hadani da Allah da annabi sannan nace to suje basu dade ba da fita ba suka qara dawowa sukace yace wai sushirya zai kaisu shopping da murnar su suka shiga suka fara shiryawa.....
dan dakatawa tayi da maganar tana kallon sa ganin yanda ya zuba mata idanu yana kallon ta ko kiftawa bayayi,

hada ido sukayi dashi hakan yasa tayi shiru takasa cigaba tare da yin qasa da kanta,

hannu yasa yadago da ita suna facin din juna sannan yace momma me kikeson kice min kiyi maganar ki kai tsaye kigaya min abun da yafaru da ita kawai kibar duk wani bayani a yishi daga baya ina jinki accident sukayi ko kuma wani mugun abunne yasameta,

janye jikin ta tayi daga riqon da yayi mata sanan tace gaba daga inda ta tsaya batare da tabi tayanda yakeso din ba,

"tace dole inyi maka bayani ko kanaso ko bakaso,

shiru yayi tare da nade hannayen sa a kirjin sa yaci gaba da sauraron ta,

bayan sungama shirya suka fita to tunda suka fita basu dawo ba sai bayan sallar magariba dan har ina tunanin kiransu sai gasu sun shigo da gudu suna kuka natare su nace me yake faruwa suke sanar dani wai bayan sunshiga sungama yo shopping suka fito tare amma da suka shiga mota sai suka nemeta suka rasa sama ko qasa sun nemeta sun rasa.......

sun nemeta sun rasa sun nemeta sun rasa yafada yana jinjina kai momma me kikeso kice atakaice de kina nufin kice basu ganta ba tabata kenan ko me kike nufi,
"Eh" wallahi haka nima naji abun kamar amafarki wai basu ganta ba,

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a fili yace momma momma momma saida yakirata sau uku yakasa kuma cemata komai, idon sa har yafara canza kala,

da sauri tayi kansa tare da riqo hannun sa tace yanzu meye mafita nagaya maka dan kasamo mana mafita gashi kuma naga kai kana ma neman kafini shiga damuwar ni wallahi ma iyayen yarinyar nan nake ji ga wancen yayan nata ma dake waje bansan da wane ido zan kalle sa ba yaran nan sunso su tafi da ita jiya na hanasu suka hakura saboda bayanda zasuyi amma gashi kuma abun da yafaru yanzu meye abunyi,

daurewa kawai yayi tare da cewa ina su Ammar din suke,

"na korasu nace suje su lalobota kar wanda yasake shigowa inda nake inba tare da itaba gabadayan su na kora daga shi har su Amran wannan ai shirmene da shiririta ace kuna tare da mutum har yayi wani wajen baku kulaba koma dauke ta akai ai kamata yayi ace sunga wanda yazo daukan nata amma dake daga su har shidin bamai cikakken hankali sunje sundawo batare da ita ba kuma suka iya dawowa cikin gidan nan suka gaya min saboda tsabar sakarci,

"bawani zancen su koma nemota gwara ma kiyi musu waya sudawo kawai fitar suma baida amfani gwara sudawo kawai dan ba ganin ta zasuyi ba,

ina ganin ba laifin subane anshirya dauketa ne tun farkon fitar su shiyasa har akayi nasarar dauke ta batare da sanin suba,

idan Ammar din yadawo kice yazo ya sameni a part dina,

yana kawaiwa nan baijira cewar taba kawai yayi saurin barin wajen ya nufi hanyar fita yana jinta tana tsayar dashi amma baisaurare ta ba ya bude kofa ya fita tare da jan kofar abakin kofar ya tsaya tare da dafe kansa shikadai yansan abun da yakeji aransa duk wani tunanin sa nema yake ya tsaya yana tunanin sunkusa toshe wata hanyar gashi ankuma jawo musu wani aikin yanzu ta ina zata fara neman tama kuma yana da tabbacin wannan abun yana daya daga cikin shirin wadannan mutane su suka sace ta ko tantama babu, wani tunanin ne yaqara fado masa to idan sune meyasa basu sace ta tun lokacin da take hannun dadda ba lokacin ma da bawani tsaro da ake bata gashi taba zuwa makaran tama ita kadai duk tsawon lokacin da ta dauka awajen ta ba taba kokarin dauke taba amma sai gashi daga zuwan ta gidan su kwanan ta daya ansace ta shida yake tunanin ma ta dawo nan da zama gashi ba aje ko inama ba ansamu matsala abun da baitaba tunani ba,

yanzu tunanin da fargabar sa shine idan dadda taji labarin batan ta yasan bazata taba yarda dasuba bama ita kadai ba gaba dayansu har su bossay kunyar gaya musu yake ace wata matsalar daga gare sane tasanadin sa hakan yafaru shikam yau ina zaisa kansa taya zai sanar dasu wannan labarin marar dadin ji,

ya dauki lokaci me tsawo agun kafin ya daga kafafun su da kyar yajasu yatafi wajen su ransa fall tunani kala kala,

yana shiga falon duk sukayo kansa suna tambayar sa lafiya me yake faruwa amma bai iya basu amsaba,

abun da yafi basu mamaki ganin idonsa ya canza kala gashi kallo daya zakai masa ka fahimce halin da yake ciki basugana cika da mamaki ba

36 / 74