ita gida dan bazai iya hakurin halin mata ba nidai wallahi shawara nake baku kusamu ruwan buta abashi yasha ko bedena ba zai rage,
"tunda yafara maganar shettima ke faman yin dariya saida yaji yayi shiru sannan yace to shikenan zan gaya masa kace abashi ruwan buta zaidena masifar da yake ko,
"zaro ido bossay yayi sannan yace la rufamin asiri dan Allah karkagaya masa kaqara jamin yadena kulani tunda daman haushina yake ji"
"shettima yace ai badaina kulaka zaiyiba wasu marukan zai baka kasan shifa yafi bawa mari muhimmanci fiye da komai "bossay yace ai naga alama tunda yayi min da yasa naga wuta ta wuce ta gefen idona amma de ba haka yakeyiwa mata ba iya maza yake mara "shettima yace har sumana saidai inbasuyi masa laifiba amma sunayi zai mare su kaamar yanda zai mari namiji haka suma zaimusu dan idan ransa yabaci ba ya bambamce mace da namiji kowa ma daya yake daukansa,
"jinjina kai bossay yayi yace amma iya kannen sa dan wallahi idan kamari mace sai ancika tara duk mari daya dubu biyar bare shi nashi na dabanne saidai yabiya dubu goma dan Allah indai irin marin da yayi min ne wata macen saita bakunci lahira ko kuma ya canza mata kamanni hallitar da Allah yayi mata,
shettima yace wayagaya maka zai biya ai ba wanda ya isa yasashi yabiya "bossay yace Allah nidai ina uban yarinya ya marar min 'ya sai ya biyani dan bazan rabu dashi ko yabiya ko in rama mata "shettima yace da kwa kaima kasha marin "bossay yace kasan Allah sai na rama mata kai nifa yanzuma idan yaqara dukana sai inda qarfina yaqare dan sai na nuna mishi nawa dantsen yafi nashi nifa ranar ma da ya mareni bansan meya hanani ramawa ba amma yayi nafarko yayi naqarshe kana ganin shi hakan nan ni ajikina inajin idan zamu danbatu sai nayi qasaqasa dashi dan nimafa ina da qarfin nan hmmm yafada yana cije baki irin zan kamashi dinnan ya dora da cewa Allah ya hadamu idan ya hadamu kar yaraba sai nasa yadena marin kowa aduniyar nan bare kuma mace danni su zan daukarwa ma fansar marin da yake musu dan dakatawa yayi da maganar.....,
"sosai shettima yake dariya saida yadan tsagaita sannan yace to shikenan yanzu muje filin dambe tunda gaka gashi sai kuraba raini nidai ina gefe duk wanda yayi winning zan mishi kyauta me tsoka "bossay yace fadi nawa zaka bayar kai nikuma ko beyi niya sai naje har inda yake nakira shi yanazuwa zanfara nannaushin shi idan yaji zafi sai yarama kaga daga nan sai mufara fadan rabaraini ko ya kace hakan ai yayi fadi nawa zaka bayar?
"shettima yace ko nawa kake so zan baka kai bama nikadai ba shi kansa idan yaga kagi shi qarfi zai qaramaka wasu kudaden dan haka gaka gashi kawai farawa zakuyi basai kaje wahalar nemansa ba,
cike da rashin fahimta bossay yace dan Allah zai biyani dagaske? "Shettima yace kwarai ma kuwa zai biyaka adadin kudaden da kakeso ma zai iya baka.
cike da jin dadi bossay yace to shikenan angana yanzu de kaje kirashi,
"shettima yace ai basai najeba shiyazo farawa kawai yarage muku yaqarasa fada yana riqe dariyar da takeson kwace masa,
"bossay yace nifa bazanje office dinsaba kaje kai kakirawo sa yana zuwa zan fara aiwatar da nawa aikin amma fa kafin kafita duk wani abu dakasan yanada amfani ka dauke shi kar muyi maka asara,
"shettima yace to shikenan ba matsala bari infita in baku guri yafada yana miqewa daga kan kujerar yace to bari inje intaya Ameesha zama adaki kar mujikun turo mana qofa kuma bana ma so ku tashe ta yana kaiwa nan ya juya zai shiga daki "bossay yace to ya kuma zaka shige baka kirashi ba nifa bazan iya kiranshiba saboda bana son yagane wani abun yaji tsoro yaqi biyoni shiyasa nakeso kai kaje
"dan juyowa shettima yayi yana mishi murmushi me qayatar wa sannan yace wai a ina zan kirashi bayan gashi ga ka ai baka da matsala basai ka wahalar da kanka wake zuwa wajen saba tunda duk yaji tattaunawar tamu gashinan yafada yana nuna masa bayansa da da hannu alamar ya kalli bayansa,
dasauri yajiyo dan ganin da gaske yake yana juyawa sukayi ido hudu da sam dake tsaye ajikin qofa a harde hannayensa guda biyu a kan qirjin sa ya zuba musu ido yana kallon su basu dade da fara zancen ba ya shigo dake beyi nocking ba kuma qofar ba qarane da ita ba shiyasa basu ji shigowar sa ba shima shettima sai daga baya yagansa saboda yana facing dimshi shiyasa ya gansa amma bossay baisan da zuwan saba shiyasa yazauna yana ta uwar zuba arashin sani,
"da sauri yayi qasa da kansa tare da miqewa tsaye yana kallon shettima irin meyasa baka gaya min ba shikam shettima daiyar sa yake yace to bismillah let me caunt three 1yafada yana kallon bossay yanda yayi tsuru tsuru da idanu kamar jikaken bera "shettima yaqara cewa 2 ai kafin yayi na ukun bega tahowar mutum ba sai jin mutum yayi abayansa yana boyewa murya qasa qasa yace nifa ban shirya ba kace masa yatafi idan na shirya ni da kaina zanje insame shi "juyowa yayi yace au hakama kace to shikenan yace ka taho wai kuyi anan yafada yana kallon sam da yayi tsaye kamar gunki ko yatsansa yaqi motsawa kawai ya kafesu da idanu tare da qara hade fuska, "saida yagama shan qamshinsa sannan cikin takunsa na isa da qasaita yafara takawa zuwa cikin office din,"bossay naganin haka yana nufowa inda suke yafara juye juye yana neman gurin buya qofar da shettima yanuna masa dazu yace Ameesha na ciki tana bacci yatuna dan haka ya nufeta da sauri ya bude qofar ya turata zai shiga arashin sani Ameesha da tashin ta daga bacci kenan tazo wajen qofar zata bude shikuma ya turata da qarafi kafin tayi yunqurin matsawa yature ta tafadi qasa,
qara tasakai tana dafe kanta saboda jin zafin da ya ratsata, da sauri yayi kanta tare da dagota shettima ma da sauri yaqarasa gurinsu yana cewa subhanallahi ya akai haka yaqarasa fada lokacin da yakai ga tsugunnawa agabansu cikin rikidewa yaqara dagota sosai yana kiran sunan ta amma bata amsaba kuma bata bide idon taba tsorata yaqarayi yace dan miko ruwa insaka mata shettima na qoqarin tashi yadauko sai kawai sam yamiqo musu karba shettima yayi ya shiga yayya famata amma nanma shiru bata motsaba shettima ne yace mayar da ita kan kujerar cen adubata da sauri ya sureta ya kaita kai ya kwantar da ita nande shettima yashi ga duddubata gashi ansaka mata ruwa amma taqi farfadowa yana kanta yana tunanin abun da zaiyi mata sam ya qaraso gurin tare da dan rankwafowa kanta yayiwa shettima alama da ido ya matsa tashi yayi yabasa guri shikuma sai ya tsugunnan agabanta yaqara diban ruwa atafin hannun sa ya shafa mata afuska yagade taqi bude ido daman kuma yasan hakan zata iya faruwa yanzu watakil faduwar ta taba mata kwakwalwa bossay ya matso ya riqe hannun ta yana dan jijjigata dan Allah kiyi hakuri baby wlh bansan kina wajen ba dan Allah kitashi sai faman surutu yake shikadai saida sam yace malam ka ishemu da surutun banza kafita daga nan yace gaskiya kayi hakuri amma qafata qafarta ba inda zani duk abun da zakayi mata kayi mata ina gun tunda ai ni mijin tane yakamata dukma abun da za'ayi ayi agabana ko "wani kallo sam ya watsa masa da yasashi yin shiru
" sannan yadan sosa qeya yace kaifa matsala ta dakai kenan to maida wuqar ni bada fada nayi maganata ba kawai kawai de sai kuma yayi shiru
"shettima dake bayansu yayi dan murmushi yace mutum de yadena cika baki da kurun banza inbahaka ba kuma jiki yayi tsami,
bossay yasan dashi yake sai yayi masa shiru yana maida hankalin sa ga Ameesha maida dubansa kanta sai kawai ya zaro ido cike da mamaki ganin abun da sameer yake shirin yiwa Ameesha..........✍️✍️✍️✍️
Ba yawa ayi hakuri da wannan👏
Assalamu alaikum,
kutsaya ku karanta kar ku wuce yana da matuqar muhimmaci agareku.
*ILIMI HASKEN RAYUWA*
Ina matan aure harma da 'yan mata wadanda basu samu damar yin makarantar islamiya ba ko kuma wadan da sunyi amma yanayi rayuwa yasa sun manmanta da wasu abubuwan to ga dama tasamu akwai mata dayawa wadan da suke cikin wannan halin suna bukatar ilimi kuma wasu suna so amma basusan ta inda zasu fara ba wasu kuma hidimar gida da iyalai bazasu samu damar fita su nema ba,
To amma fa kusani hakan ba hujja bace awajen Allah domin acikin wani hadisi ance azaba ta tabbata gawanda be nemi yasani ba kuma ko kasani ma idan baka aiki dashi nan ma azaba zata tabbata agaresa dan haka kutashi kunemi ilimi kar kuzauna da duhun kai ko girman kai ilimi ba ai masa girman kai kitsaya ki fadada iliminki musamman bangaren akdari mata dayawa suna da qarancin ilimi akai,
Duba da hakan yasa muka kawo muku hanya mafi sauqi na online class kina zaune a cikin gidan adakin ki azaune ko akwance ma zaki samu duk wani ilimi da kikeso dai dai iyawarki,
yar uwa awa nawa kike batawa akan wayarki batare da ki qaru da ita baki koyi komai ba aciki awa nawa kike batawa akan karatun littattafen novel da kalle kalle da basu da amfani,
zamu bude group iya mata zamu kawo muku littattafan addini sannan kuma zamu ringa qarin alqur'ani me girma duk surar da baka iya ba za akoya maka duk daga inda kake so zaka koya zamu koya muku baki kodaga alifunne baka iyaba za a koya maka kuma da yardar Allah zaka iya,
Ga abubuwan dazamu ringayi kamar haka👇
1_ALQUR'ANI
2,HADISI
3,AKDARI
4,ARABIYYA,
5,SIRATUL NABIYYI
6,NURANIYYA
DA dai sauran su duk waddannan abubuwan zaku samesu agarabasa me sauki naira dari ukun ka ta baka ilimi kuma idan kabiya ka ta samu kenan baza ataba cemaka wata yayi ba biya kudi ko shekara nawa zakai saidai idan kai kagaji da nema kace ya isheka domin karin bayani sai ku tuntubemu ta wannan number 08124226526
Pls duk wanda ya karanta yatayamu da share dinsa zuwa group group domin inkai baka ra ayi watakil wani yana da ra,ayi akai kuma be ganiba plss share it
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿29&30
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
bossay yasan dashi yake sai yayi masa shiru yana maida hankalin sa ga Ameesha maida dubansa kanta sai kawai ya zaro ido cike da mamaki ganin abun da sameer yake shirin yiwa Ameesha.........✍
"hannu ya sam yasaka ya riqe mata hanci tare da matsa bakin ta,
jin anriqe nata hanci kuma taji zafi yasata saurin bude idon ta tare da cewa wayyo dadda ta kasakar min hanci kasheni zakayi taqarasa fada tana qoqarin tashi zaune "
sakin ta yayi yabita da kallon mamaki gaba dayansu ma ba wanda beye mamakin jin muryarta radauba,
Qarasa zama tayi da kyau tana fuskantar su daya bayan daya saida tagama kallon su kawai sai tasaka dariya tare da cewa ashede zan iya acting din film yanzu duk kwarewar ku ba wanda ya iya ganoni to lafyata qalau inajin ku nayi shiru saida naji ana niyar kasheni taqarasa maganar da qarayin wata dariyar,
duk ido suka zuba mata suna kallon ta sai da qyar bossay ya iya tsugunnawa agabanta yace haba baby meyasa zakiyi haka bayan kinsan hankalin zai tashi kidena irin wannan wasan ni wlh banaso kinji yanda nakeji idan wani abun yasameki amma kikazo kikayi mana haka plsss karkiqara kinji ni yafada yana bin beauty face dinta da kallo "
itama shi take kallo saida yagama maganar sa sannan tace to yayana nadena daga yau bazan sake ba,
yace yauwa babyna haka nake sonji yanzu babu wani abun da yake damun ki?
kai ta daga masa alamar babu komai yace to shikenan haka akeso Allah yaqara miki lafiya,
"Ameen tace masa taqara jan bakinta tayi shiru"
tundazu nazo na dade anan ma akace kina bacci tace ai da katasheni "yace a'a ai ba aso anatashinki inkina bacci tace to ai kaine kuma ni lafiyata qalau danasani da tun dazu nafito dan nama dan jima da tashi kawai de fitowar ce banyi ba yace ai shikenan yanzude ai gashi munhadu ko?kai ta kuma daga masa sannan tace jiya nayi missing dinku nikadai sai naji duk ba dadi da ba dadda akusa dani tafada tana dan marairaice fuska irin abar tausayin nan,
bossay yace ayya kiyi hakuri zakisaba kinga ai kwananki daya amma nasan kinadanyi kwana biyu zaki saba dasu gashima kuma dayan yayanki zairinga zuwa dake nan kina gani mutane yafada yana nuna mata shettima "dake tsaye yana binsu da kallo sai yaji sun burgesa sai yakejin dama ace qanwarsace wacce suke uwa daya uba daya da tasha gata shide arayuwar sa yana son qanwa mace shiyasa ko gidan su sam yaje haka yake kula dasu gashi kamar qannen sa haka yake son qannen sameer"
dagowar da tayi suka hada ido tasakar masa murmushi shima saitaji dama batace gidan ba dadi ba kar shima yaji ba dadi aransa, shima murmushin yamayar mata dashi kawar da idon ta tayi ta qara maida dubanta ga bossay,
dorawa yayi da cewa nima kuma zan ringa zuwa muna fita yawo ai zakije ko dan murmushi tayi masa batare da tace komai ba tashi yayi yazauna akusa da ita yana kallon ta da kyau zai qarayin magana,
Sameer da ya koma kan wata kujerar daban yana daddana wayarsa ya katse musu hirar da cewa malamai kun ishemu surutu kutashi muje muyi abun da yakamata yafada yana mikewa tsaye suma ba wanda yace masa komai bossay ya miqe daman shettima shi yana tsaye be zauna ba,
itama ganin duk suna tsaye yasata tatashi tsaye itama tana dan hararar sam ta gefen ido saboda batason tashi tafiso suzauna ita da yayanta suyi ta hirar su sai tafi jin dadin hakan amma kawai ya wani zo yakatse su idan bayason ji shi basai yafita ba kowani yace nasa dole sai yazauna agun ita haushi na yake bata batason taga sun zauna guri daya dashi bata samun sakewa saboda haushin da yake bata,
kamo hunnu ta dataji anyi ne yasa ta katse tunanin da takeyi tare da kallon bossay da shima itan yake kallo suna hada ido ya daga nata gira daya yace yade me yake damun qanwata tunanin me kikeyi ne haka har sun fita sunbarmu,"kallon dakin tayi taga basa ciki bata bashi amsaba kawai tace mutafi ba komai,
"beta kurata sai tagaya masa ba kawai shima yajata suka fita daga dakin lokacin su sam harsun bar office din suma suna fita suka hangosu dan haka sai suka nufi inda suka gansu da dan sauri har suka kamosu tare suka qarasa wajen parking lot din "shettima ne ya kalli sam yace wacce motar zamu shiga yace muje awace yanuna masa motar shi nan yaje suna duk suka qarasa shettima yana driver seat sam kuma ya shiga gefe Ameesha da bossay kuma suka shiga baya tayar da motar yayi rivers tare da saita motar yaja suka qarasa bakin gate me gadi ya bude musu suka fita daga asibitin saida suka hau kantiti sannan shettima yace ina muka dosa?
Sam yace masa tudun maliki prison,
"dan juyowa yayi yana kallon sa alamar yana jiran qarin bayani jin yayi shiru be da niyar qara cemasa komai yasa shi cewa kunyi magana da itane yace masa eh naje da safe ai mungama magana da ita yanzu can zamu fara zuwa tagaya min sunan shi da inda ta taba zuwa taganshi komaide na rubuta direct zamuje ne dady yakira yasanar da zuwan namu bazamu samu wata matsalaba kawai zuwa zamuyi(dady mahaifinsa kenan saboda babban lauyane kuma sananne shiyasa bema fiya zaman gidan sarauta ba dan mutane da yawa ma basu san shi dan gidan bane saboda bema fiye aiki anan ba jefi jefi ake daukan sa wataran yazo yayi shari'a shiyasa ba kowa yasan asalin sa ba ande sanshi akan aikin sa, to wannama shiyasa sam ya roqesa akan yakira can prison din tunda yana da hanyar da zai iya nema musu alfarmar shiga kai tsaye ba bata lokaci kuwa kuma batare da ya tambayesa dalilin zuwan nasaba kawai ya amsa masa tare da gaya masa yana da aboki agidan dan haka zasuyi waya yaje kawai to kunji dalilin da yasa zasuje kai tsaye tasanadin dady mahaifin sam)
jinjina kai shettima yayi yace kace tazo mana da sauqi ma kaga ko shari'ar ma za ayi sai dady yatsaya mana kawai basai munsha wata wahalar nemo lauya ba sam yace nima abun da nake tunani kenan amma da kyar dady ya yarda dan zai iya hadamu da wani yace zai tsaya mana yanzu kuma duniya ba amana watakil shi wanda yake tunanin zai yi da gaske azo abashi cin hanci daga qarshe azo asamu matsala amma de zan lallaba shi ko insa papa yayi masa magana nasan watakil ya amince,
dan numfasawa shettima yayi sannan yace ai bayani zamuyi masa inyaji labarin kaga dole zai yarda ya tsaya mana bazai qiba ko yakace yafada yana dan juyowa ya kalli gefen da sam yake azaune sannan ya mayar da hankalin sa tuqin da yakeyi,
shiru sam yayi kamar ma bazai bashi amsaba sannan yace Allah yasa yauwa kafin nan inason mu fara biya gida zan dauki abu daga nan kuma a ajiye yarinyar nan saboda ba da ita zamu ba in mundawo sai kadauketa ku tafi, "ok" shettima yace masa sannan suka cigaba da tafiya batare da kowa yaqara magana,
amma qasa qasa kanajin surutun su Ameesha da bossay saboda suma tasu hirar suke dan bama sajin abun da suke cewa kasancewar shi gogan bawani daga murya yake ba ahankali yake yi hadi kuma da surutun da sukeyi sai yazamana basu jin zancen da sukeyi,
da qarfi Ameesha tace dan Allah yaya