bar zazzaro idanun da take ba kana kallon fuskar ta bayan haukan da tayi sai idanun zaka gani da kyar jakadiya ta iya budar baki tace dd...an...Allah kuyi ha....kurrrrrrri taqara da wata irin murya wace kanaji kasan mutum yagama tsotara tana fada ta kulle idon ta rufff harda dorawa da tafikan hannun ta wajen rufesu bakomai yasata hakan ba sai washe bakin da Azeema tayi mata fararen hakoranta suka bayyana sai tasake canza kamanni gaba daya ko farin sani kayiwa Azeema ayaude kallo daya baze sa ka ganetaba saidai idan tsayawa kayi sosai ka qura mata ido shima da kyar zaka iya ganeta bare kuma wanda ba wani sanin taba yayi sosai kana ganin ta zakace wannan ba halittar bil adam bace saidai jinsin jinnu(aljanu)
abangaren Azeema kuwa sai da riyar taqe yi amma bata bari sauti ya fito ba dan ita saidaga baya ma tagane kwaliyar da tayine ya tsorata jakadiya shiyasa tana sane ta qara wangale mata haqora dan taqara firgita ta daman haushin ta tajeji saboda tun farkon ganinta ta nuna bata sonta ga abubuwan da take mata dan haka itama yanzu tasamu zata rama,
jakadiya na kyarma jikin ta gaba daya sai faman karkarwa takeyi gashi sotake tafita daga dakin amma takasa daga qarfata daga gurin ganin hakan yasa Azeema qarasowa inda take daf da ita ta tsaya sai tasa hannu tacire hannun jakafiyar data rufe fuska dashi jakadiya najin anriqe hannun ta taqara damqe idonta tana so tayi magana amma bakin ta sai karkarwa yake takasa budeshi Azeema sai faman dariya take tanaso tayi mata magana amma tasan tana bude baki dariyar da take zata fito ahakan ma saura qiris dariyar ta kwace mata ta fito fili sai kawai tayi saurin sakar mata hannun tare da juya baya tan sa hannu tana kunshe dariyar ta aciki,
jakadiya kam jin ansakar mata hannu yasata bude ido daya tana dan kyallowa aikwa tana kyallo bayan ta alamar ta juya baya yasata qarasa bude idon ta dan tabatarwa kanta abun da tagani datade ga da gaske ne ba kallon ta take ba sai kawai takwasa aguje ta bude qofa ta fita daga dakin tana gudu tana kiran nashiga uku wayyo Allah na tawa taqare yau nayi ido hudu da aljana tana cikin gudun tazo zata fita daga dakin kenan taji tayi karo da mutum qara rudewa tayi dan duk atunanin ta aljanar ce ta fito tasha gabanta wanu ihun tasaki tana neman hanyar fita taji andaka mata tsawa da cewa ke mahaukaciya inace baki da hankali daman wajen gudu ne da har zaki ture mutane saboda tsabar jahilace ke bakisan me yakamata ba nutsuwa tayi tare da zubewa awajen jikin ta na karkarwa tama kasa bashi hakuri hannu zai maketa yana cewa baki iyayuwa mutum laifiba kibashi hakuri kenan yakusa sauke mata lafiyayen mari kenan aka katseshi da cewa haba babana me yayi zafi haka ayi mata afuwa mana batasani ba kuma ka tsorata tane shiyasa takasa baka hakurin ranshi abace ya dago yana kallon papa da ya dakatar dashi da abun da yayi niya badanshi ba da baze dakata ba sai ya koya mata hankali papa na qarasowa gurin saiga Ammah ta qaraso falon tana cewa wai meke faruwane wa yataban na gaban goshin farin cikina tana fada tana gama qarasowa inda yake tare da ruqo hannun sa sai yanzuma idon ta ya sauka akan jakadiya dake durkushe agurin tana faman muzurai da idanu tare da hamdala aranta da Allah yakawo mata papa da ba abun da zai hanasa yayi mata dan isakan duka dan zuwa lokacin tsoron ganin aljana yabarta tsoron abun da zai matane akan gaba shine fargaban ta dan ba qaramin tsoranshi take ba hakannan ma inde yana gari bata son ko hada hanya suyi saboda dan qaramin abu zakai yahauka da masifa da duka bashida hakuri kwata kwata shiyasa ma mutane dayawa suke tsoron hada hanya dashi gudun matsala....
Ammah ce ta katseta da kiran sunan ta tace mari lafiya naganki anan me yafaru zatai magana kenan papa ya tareta da cewa bata saniba sukayi karo da shi shine zai kaimata duka na dakatar dashi shiyasa kika gansa haka itakuma takasa basa hakuri,
saboda ta tsorata kinsan mutumin naki bashida hakuri yafada yana barin wajen ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su,
Ammah tace ayya Allah sarki mari meyasa baki duba hanaya ba lokaci da kike tafiya da har yasa kika biheshi wannan ai gangancine yakamata idan kina abun kirin ga kallon gaban ki tana fada mata ta maida duban ta kan Sam tace dan lele na kayi hakuri karkasa damuwa aranka manta da ita zata kiyaye nan gaba tafada tana qara ruqosa sanan tace zo muje kaci abin ci dan naga cikin ka yana neman abinci Allah yasama kaci na dare be tanka Mata ba tasan halinsa daman yanda ransa dinan yabaci bazai kula taba dan haka kawai sai taja hannun sa da niyar kaisa kan dinning shettima dake bayansu yayi gyaran murya hakanne yasata juyowa ta kallesa sannan tace daman tare kuke shine kayi shiru ai ban kula dakai ba wallahi shima ita yake kallo yace daman ina zaki ganni hankalin ki yana kansa ni ai komawa ma zanyi inda ake nemana tundade in mutum yazo nan yar wariya ake nuna mishi ido ake rufewa anuna ma basan da halittar sa agunba wannan san kan fa yayi yawa aringa ragewa inba haka ba kuma nidai baza aqara ganin qafata awajen nan ba tunda ba a son ganin mu sai mujanye jikin mu ko yafada yana qoqrin juyawa yabar wajen yana juyawa kuwa yaji saukar dundu abayan sa tare da talle masa qeya sannan ta jawo rigar sa tabaya amma ko gezau beyiba to basamude mutum sai qarfin tsiya yanzu ji yanda na daddage na jawo ka amma kaki motsawa to juyo ka qara gaya min abun dakake fada dannasan basu qare ba shiyasa nayi maka shiru ka qarasa ki juyowa yayi yana sakin murmushi ta can bangaren shima daman ba fita zaiyi ba yasan dole ta dakatar dashi dan sunsaba haka da it,
gamin da yaqi juyowar yasata dan sassauta muraya tace kaifa kafiya matsala wallahi tuzuru kawai ina maka magana kayi qeqam sai kace tsohon soja da sauri ya jiyo yana kallon ta yace lallema tsohuwar nan ke har kina da bakin cewa wani tuzuru bayan ga qaton gardin tuzuru nan agaban ki kibari idan kika fara kawar dashi saiki cewa wani tuzuru koda yake ma wanna ai a tuzuran ma riqaqqe ne ya ruqa kamar dan yar kubewa kinsan kubewa ce idan ta riqe ko yankuwa ma batayi saidai a jefar dan bata da amfani to shima haka yake dan ko tsohuwar bazawara aka bata sadakar sa ma bazata karba ba saidai ko kinemo masa wata yar tsohuwara ahadata da Allah da kudade sannan tadan lallaba tayi maleji dashi dan sai tayi hakuri in kwa bahaka ba to saidai ya mutu ba aure, be ankara ba yaji saukar filo afuskar sa da qarfi zai dago kenan yaqara jin wani haka sameer da yabarsu agun tun dazu yakoma kusa da papa yazaun yana jinsu da bayi niyar tanka masa ba amma yaga abun nasa yayi yawa shiyasa ya dauki filulli kan yafara jifansa dashi saida yaga sun qare gaba daya sannan ya dakata,
Ammah ce ta daga hannuta itama tana kaima sa duka ta ko ina tare da cewa bakin ka ya sari danyan kashi saodai kagani akan ka amma bade akansa ba nan da watanni ma zaka gansa da zankadediyar budurwa kai kuma saidai ka qare a tsohuwar bazawarar daman dasu ka dace ba budurwar da zata kulaka inda tana da hankali saidai ko in makauniya ce bata gani sai acuceta ahadata dakai amma me lafiyade cikakkiyar me hankali bazata yarda ta aure ka tana fada tana dukan sa a qirji,
Shikam ko ajikinsa dukanta ko kadan bajinsa yake ba yana ta faman dariyar sa saida yaga dan kanta tagaji da dukan sa ta cire hannu tare da yin kwafa zata bar wajen yayi saurin ruqo hannun ta tare da kafeta da ido yana dan murmushi yace kema kinsan fade kike dan kinganni dan saurayi dani kinga kwa yanda 'yan mata suke rubibi akaina hmmm ba a magana zan kawo mikima kizaba min danni sunyi min yawa narasa wacce zan dauka aciki shima yagaya miki wace macen ce take sonshi duk wace ma yace yana so sai ta gudu tace bata son tsoho ita saurayi take so kamar ni fisge hannun ta tayi daga riqon da yayi mata tana galla masa harara sannan tajuya batare da tace masa komai ba saboda ya kaita qarahe bata da abun da zatace kuma tarama cin fuskar da yakewa sameer qarasawa tayi wajen sameer itama ta zauna shima shettima man yana dariya yabiyo bayan ta inda ta zauna ya zauna kusa da ita yace yana satar kallon ta sannan yace madam nifa yunwa nake ji kitashi ki bamu abinci musamman ma tuzurin ki ba inda zaije abashi abinci sai wajen ki nikam banda matsala yanzu ina nan ma idan na dau waya nayi kira nace akawo min ana rawar jiki za akawo min har inda nake Allah sarki shikuma saida taimakonki sai kun hada masa da li'ilafi wannan baqin jinin yayi yawa yana fada ya dubi inda sameer yake azaune ya hade rai kamar anyi mishi albishir da wuta ganinsa yayi yana nannade hannun rigar sa yana shirin tashi daga gurin alamar de zaiyo kansa yana ganin hakan yayi saurin tashi ya koma kusa da papa yana buya agefen sa yace papana kayi masa magana kar yatabani inzo in karyashi dan inya tabani ba barin sa zanyiba saboda ni ba sa'an sa bane nafisa qarfi dariya papa yayi yace to ai shikenan tunda kafishi qarfi kuma yasani ai rabudashi kawai yazo sai ka koya masa hankali ko a'a papa ai banason kuzo kuce naci zalinsa ne shiyasa bana son indake shi papa yace mun yarda ba komai mu sai mu bar muku ma wajen kudan dan batu kaga daga yau baze qara tunkarar ka da fada ba to nide a'a Ammah to ke kisa baki tunda papa yaqi ji itama tace bazan ba din nima nagoyi bayan sa to shikenan zaku gani tunda duk kunqi yimasa magana yana kaiwa nan sai yatashi yayi saurin komawa kusa da sameer akunne yarada masa yi hakuri nifa bada kai nake ba da waccan tsohuwar nake ture sa yayi daga kusa dashi yace to ni ina ruwana ko kaji tunda kafara nace wani abun yace a'a to amma meya nade hannu riga yace ganin dama yafada yana hararar sa tare da kada kai shi kadai yasan ta inda zai rama wannan abun da yayi masa shiyake cewa tuzuru zai kamasa ne nan gaba yanzu beda lokacin sa,
ganin kowa yayi shiru yasa Ammah tashi tace dan lelena rabuda shi bari inkawo maka abinci kai kadai shikuma yatafi wajen bazawarar tasa yaci tafada tana tafiya shettima ya bude baki kenan zaiyi magana sameer ya maka masa harara hakanne yasa shi yin shiru be tanka mata ba,
har takai bakin qofar kitchen din sai ta tuna da mari jiyowa tayi taga har yanzu ashe tana gurin takasa tashi daga gurin kiran ta tayi tace mari wai wai har yanzu baki tashiba ki tashi daga nan ba abun da zai miki miqewa tayi jiki babu kwari har ta nufi qofar dakin ta sai kuma ta tuna da aljanar dazu sa sauri tayo baya Ammah da bata qarasa shiga kitchen din ba ta juyo tace ke lafiyar ki qalau kuwa meye hakan kikeyi sunkuyar da kai tayi tace Allah taimakike Allah ya qaraja da ranki yake uwar dakina Allah......dakatar da ita tayi tace fadi maganar ki kai tsaye qara sada kanta qasa tayi tace daman abun da zan gaya miki wannan yarinyar da tazo wacce take dakin ashe ba mutum bace aljana ce da sauri Ammah tadawo kusa da ita tace aljana kuma kamar ya bangane ba nufin ki ta gudu taya ma kikasan aljanace inkawo mutum kiringa cemin aljana cikin rawar murya tace wlh aljana ce ni na ganta da idona bayan nagantane na gudo shiyasa har nayi karo dashi ban kula ba gaban Amma na faduwa tace amma bata nuna ba tace yanzu hakan tana cikin dakin tace mata eh tana ciki juyowa tayi tana kallon su papa da suma sunzuba ido suna jin abun da suke cewa Ammah tace kai kunji me tace wai aljana a cikin gidan papa ya mike ts aye yace kamar ya aljana taya akai ta shigo kuma hartabari aka ganta daman aljanun haka suke Ammah ce tace yarinyar fa danake baka labari dazu wai itace aljanar gaba dayan su suka miqe tsaye papa yace to muje mugani ko watakilma shirmeni irin nata me sunan baba muje gaba dayansu tsayawa sukayi sukaqi tafiya saida yasake yi musu magana sannan sameer yadan shafa kansa yace papa aljana fa akace kuma sai kace muje idan tayi mana wani abun fa nide bazan jeba kuje ku gano papa baki yasaki yace tofa kai yanzu qato dakai kace wai tsoro kake ji ko kunya baka jiba to kaifa ko kaima tsoron kake ji yafada yana kallon shettima shimade ba kunya yace eh papa aljani ai ba abun wasa bane dade mutum akace to koma waye zamu iya dashi amma banda mutan boye
papa kawai yanzu yanda za ayi mufita daga gidan gaba daya sai aje akirawo malami sai yazo ya duba yagani papa da mamaki yagama kashewa yace amma de kunban kunya wlh nibansan haka kukeba ashe duk matsorata na tara to wlh ba malamin da za akira kuma sai kunje idan aljanar ce inma wani abun zatayi muku ai da tun shigowarku zata yi muku kuwuce muta yafada yana turasa Ammah ma qarasowa tayi tace a'a bekamata kayi musu dole ba kabari kawai ayi yanda sukace aje akirawo malami hakan sai yafi duban ta papa yayi yace kinsan Allah na rantse kuma wlh sai munje kuma hardake dan haka kuwuce muje duk son bijerewar su amma papa yaqi ya dage akan sai sunje ba yansa suka iya haka sukayi hakuri suka tafi yasaka su agaba sai da sukaje daf da dakin sai kuma suka fara dawowa baya wannan yace wani yayi gaba wannan yace wani yayi gaba Ammah tace kunga kune maza kuyi gaba ni sai in zauna abaya shettima yace ai wlh kece agaba kinga ke kin tsufa daman kinkisa mutuwa mukuma kinga yanzu muke tasowa kinriga kin gama cin zamanin ki muma kibar muci namu tsohuwa kawai kiyi gaba yafada yana turata gaba dalla kadena turani daman angaya maka ita mutuwa zaba take duk da na tsufa sai kaga kai ka mutu kabarni yace eh na yarda amma de ai bata wannan hanyar ba da zamu mutu lokacin mu beyi ba papa ne yadaka musu tsawa yace banason shirme anan kuwuce yafada yana bude qofar dakin amma baigama budewa gaba daya ba sai yatsaya yace suzo su shige aikam kowa yaja burki daga inda yake shima kuma be shiga ba ashe shima aranshi yana danjin tsoron kawai dakewa yayi ganin sun tsaya yaqara yi musu magana wai baza ku wuce ba dan matsowa suka farayi ahankali Ammah ce agaba da shettima ya turota sai sai shi shima kuma sameer ne ya turosa sannan ya tsaya abayan su yana jiran yaga sungama shiga idan lafiya lau sai ya shiga idan kuma yaga sun dawo sai yajuya daga inda yake,
Azeema dake dakin tana zaune take jin murya sama sama kamar aqofar dakin yasata tashi tayo wajen qofar dataji anturo tasa hannu taqara budewa tana budewa sukayi ido hudu da papa,papa naganin ta yaja baya da sauri amma be bar wajen ba ya tsaya itama Amma sai ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda tagane yarinyar ce dai kawai kwaliya tayi ta lalata fuskarta tun ganin da sukayi papa yadan ja da baya ai basu tsayabama bare susan me za ace har sunjuya sun nufi hanyar waje aguje har suna 'yar rige rige wajen bude qofar qofa kuwa kamar tasan halin da suke ciki sai taki buduwa tsayawa sukayi suna kokarin janta Ammah da ta juya bayan ta zatace su kwan tar da hankalin su sai taga wayam babu kowa awajen maida dubanta tayi ga Azeema tace fito waje kinga ki tsorata min 'ya'ya wannan wace irin kwalliyace kikayi jin hakan yasa papa ajiyar zuciya danshima yafara tunanin ko aljanar ce dan shi betaba ganin anyi kwaliya irin wannan ba matsawa yayi yace nima ai ta kusan tsoratani ina wadannan matsoratan sukayi je kikirasu suzo suga abun da suke gudarwa 'yar qaramar dariya Ammah tayi tace lalle kam bari inkirasu tana fitowa daga dan lungun dakin ta hangosu zasu fita,
da qyar suka samu qofar ta budu ashe garin saurin su suka murda key din jiki basusan ta shiga luck ba suke ta faman janta ahaka suna murdawa ta budu zasu fita Ammah tayi saurin dakatar dasu tace ba aljana bace sai kudawo matsoratan banza kawai ni mace ma nafiku jarumta wallahi atare gaba dayan su suka juyo tare da sauke ajiyar zuciya sameer ne yace Ammah kunduba kuwa sosai kun tabbatar ba aljana bace tace musu wallahi ba ita bace jin harda rantsuwarta yasasu dawo wa cikin falon suka zauna suna sauke numfarfashi kamar wanda sukayi gudun tsere suna haka papa ya shigo falon tare da Azeema cikin falon kanta aqasa bata kalli kowa ba suka shigo dakin Ammah ce tace 'yata matso nan suganki kinga duk girman nan nasu tsoro ne dasu gaba dayan su yayyanki ne zo ku gaisa tafada tana jawo hannun ta kusa dasu dukan su zuba mata ido sukayi suna jiran ta dago suganta saida Ammah tace ki gaida su mana dago su ganki tana sane take so tadago suganta dan tasan dole su tsorata tunda ba saba ganin irin hakan sukayi ba itakuma daman tasan 'yan kauye suna irin haka shiyasa ma bata sha wahala ba ta ganeta ahankali Azeema ta shiga dago da fuskarta ai bata gama bude ido bama ta kalle su sam yayi zunbur zai gudu Ammah tayi saurin riqeshi tace kai wai wane irin matsoracine ancemaka