Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   55 / 74

162K to 165K   out of 221K words

yakai bakin sa yace wai ya banga kana farin ciki ba kamata yayi kaima ka shiga cikin su nanfa duk ƴan uwanka ne wacen sojan ma dakukayi dambe ashe faɗan ƴan uwantakane,

gabansa yaji ya faɗi yace wai kana nufin wannan labarin da masarautar mu yafaru wannan matar papa ce,
bossay yace eh mana kai alabarin bama ka fahimci inda ake nufiba kenan kamanta loƙacin da muka haɗu dasu har na cemuku suna kama da Ameesha kace zaka tambayar mana kakan ka ko yasan ta ashema matar sace da ka tambaye da kaji me zaice,

Shettima yace "kai to ai koni ban fahimci komai ba sai yanzu daka faɗa kumafa ka kallesa ka kallesu sai yanzu naga suna kama da wancen yafaɗa yana kallon inda Meer yake caraf suka haɗa ido ashe duk abun da suke idon sa akan su shi da yariga yasan komai akansu yasan ƴan uwane amma baijin zai iya karɓarsu amatsayin ƴan uwa dan har yanzu haushin sam yakeji da yasa ta dalilin sa mahaifin sa yayi masa abun da yafi tsana aduniya mari dan haka sai yarama akansa zaiji daɗi aransa kuma bazai taɓa kallon sa amatsayin ɗan uwaba,

suna haɗa ido da shettima Meer yace"uban me kuke cewa anan kun haɗa kai kuna munafurcin mutane harda magana ƙasa ƙasa munafukai kawai sai nayi maganin ku dukan ku duk ɗagowa sukayi suka kalle harda su maama kallon sa sukayi saidai kuma idan ka kalli bakinsa sai ka rantse bashi yayi maganar ba saboda yana gama faɗar abun da zaice yamayar da bakinsa yanda yake,

maama ce ta girgiza kai bata yi masa magana ba kawai ta mayar dakanta kan su sam da hannu tayi masa alamar yazo,

jiki babu kwari yatashi yafara takawa har zuwa inda take zai tsugunna agabanta kenan tayi saurin saka hannu ta ɗagosa tare da rungume sa tace kasan ko ni wacece shine yanzu ma bazaka gaida niba  ni daman nasan taurin kan nan ba abanzaba na gwaggwo ne shiyasa ranar tun kan naga kamannin ka nagane halayen ka shiyasa ma na tsawatar maka danaga zaka yimin rashin kunya,

"kai ɗan waye acikin gidan dan nasandai ba kai ba ɗan sarki Muhammadu bane, saidai jika,

kansa asunkuye dan gaba ɗaya jikin sa yagama mutuwa kunya da nauyin matar duk sun mamaye sa yayi dana sanin abun da yayi musu ahanya baisan haka abun zaije yadawo ba gashi yanzu shike da kunyar abun,

ahankali yace "eh ni jikan sane kuma jikan ɗa ga munbiya itace mahaifiyata,

Masha Allah kai jikan Sa'adatu ne kenan Allah sarki matar nan akwai mutunci munyi zaman amana da ita  tana nan lafiya dai ko,

"Eh" kawai ya iya ce mata

ita kuma taƙara ce masa ina maryama itama tana nan ko,

Eh yace maimakon ya kalli ta sai kawai ya gun da dadda take duk da halin da yake ciki saura kaɗan yasaki murmushi sannan yace ai da itama sukayi faɗa da wannan tsohuwar ya nuna dadda,

kai kai maryaman ce take faɗa da wani ammadai to saidai idan ƙarshe ta kaita matar da take da haƙuri tunda muke bantaɓa jin ta ɗaga murya ga wani ba gaskiya saida idan ƙarshe aka kaita,

ai kafin ma sameer yabata amsa dadda tayi saurin karɓe maganar da cewa wanna shegiyar matar ce ba ruwan ta to kwa saidai idan sanin da kikayi mata dan nidai akamannin ta banga haƙuri akan fuskarta ba ko kaɗan baya dashi da wani kanta kamar murhun giya,

wai daman inda naje ne nanne masarautar da kuke magana akai ai bansani ba sai yanzu muna da alaƙa da cikin gidan ai zama bai kama muba yakamata kutaso yanzu muje gidan ko,

maama ce ta ɗanyi murmushi sannan tace a'a bayan zuba sai mun fara bincike domin mugayen acikin gidan suke kuma bamu san suwaye ba dan haka muke so sai mun fara samun hujjoji tukun zamu je yanda muna zuwa muna da hujjar da zamu kama duk me hannu aciki yanzu daman waɗannan muke jira suzo su gaya mana abinciken da suka fara me suka gano tafaɗa tana kallo sam da yake zaune agaban ta,

kai kai waɗannan mutanen saidai Allah yasaka muku dan sunriga da suncuce ku saidai muce   Allah ya isa tsakanin mu dasu mugaye azzalumai in Allah ya yarda sai Allah ya toni asirin su kuma ba wani ɗaga ƙafa da za'ayi wai sa anfara bincike wannan maganar ma ku manta da ita dole daga yau zuwa gobe ahaɗu amasarautar idan kuna nan taya zaku gane mugayen ai zuwan musu za ayi kai tsaye inyaso daga baya ayi binciken acikin gidan wannan shine babbar masalaha dan wallahi muna nan bata yanda za ayi agano su waye saboda ba ƙaramin shiri sukai ba ƙananun mugaye bane tsaf yanzu kina nan ke baki gano suwaye ba su su ganoki suƙara rabaki da gidan ko su salwantar da rayuwar ku gaba ɗaya tunda har suka koreku daga gidan baza su taɓa bari ku koma cikin gidan Indai suka gano kuna raye nidai anawa ganin gwanda kawai aje musu zuwan bazata atayar musu da hankali mukuma anan zamu zuba ido akan kowa mugane take taken marassa gaskiya sai mu maida hankalin mu kansu duk wani motsinsu yazamana akan idon mu zasuna gudanar dashi daganan har loƙacin da zamu kama mutum dumu dumu sai mukamasa da hujja ina ganin hakan sai yafi mana sauƙi kuma tahakane zamuyi saurin gano su,

"Good thinking 👍,

suka jiyo muryar Meer yace,

sai yanzu ya matso kusa dasu sannan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya tare da cewa "wannan tunani ne me kyau hakan yakamata ayi idan kun ɗauki shawarar tafa amma idan ma kuma baku ɗauka ba da banyi niyar sanar daku ba amma yanzu zan gaya muku ko bakujeba ko ninikaɗai me sai naje kuma ayu ɗinnan dan bazan iya barin abun araina ba ace anzalin ce ku kuma kunsan ko su suwaye kuma kunsan har cikin gidan da abun yafaru shekara da shekaru maama ba kya cikin gidan kuma ace ayanzu kindawo hayyacin ki kindawo cikin garin kuma zaki wani zauna aɓoye awani wajen inkikai hakan kina tsoron suma ai tun yanzu yakamata ayi duk abun da za ayi dan banga amfanin yin wani bincike wai abayan idon su abun da wannan matar ta faɗa shine gaskiya nafaɗa muku hakan bawai dan dole sai kunjeba amma nidai yazamemun dole inje kuma inna je zan iyayin abun da ba daidai ba dan zan kama duk wanda yazo hannu na da mai gaskiya da marar gaskiya sannan kuma zan sanar dasu ko ni wane agurin su.......

maama ce ta shiga tafa hannun tace maganar ku gaskiya ce nima na goyi bayan hakan amma ba yau za ajeba mubari sai gobe sai muhaɗu gaba ɗayan mu muje kaima kayi haƙuri kar kace zakaje yau kabari muje tare gobe gaba ɗayan mu,



maƙe kafaɗar sa yayi tare da taɓe baki irin duk yanda kukayi tundaga nan bai ƙara cewa komai ba nan dai suka cigaba da tattaunawa atsakanin su daga ƙarshe su maama sukace zasu koma gida inyaso gobe idan za atafi sai ahaɗu har su Ammi aje gaba ɗaya,
gaba ɗaya sukayi na'am da wannan shawarar akan goben za ahaɗu,


amma fa da jikata zamu tafi dan bazan iya tafiya inbarta ba, tayi maganar tana kiran Ameesha tazo zuwa tayi gabanta sannan ta riƙo hannun ta tace ai zaki bini ko..?

kai ta ɗaga mata tana murmushi,

dadda tayi saurin cewa au yau baya za anuna min shalele na tafiya zakiyi kibarni bayan kinsan nima na daɗai banganki ba ina buƙatar ki kusa dani na daɗe banji ɗumin kiba akusa dani kizauna tare dani tunda gobe zaku haɗu kinji,

Ameesha ce ta kalle ta tace dadda kefa mundaɗe tare dake ita kuma fa yau muka fara haɗuwa dan haka nidai ita zanbi ida kuma baza ki iyaba sai kizo mutafi tare kawai muje can mukwana amma ni bazan zauna ba anan ai komai yana son canji dan haka na canzaki kema tayi maganar tana yiwa dadda gwalo,

dadda ta riƙe baki tace au haka kikace ko to jiki adawo lafiya tsohuwar zuma ai da ita ake magani zaki dawo kisame nine duk inda kikaje, loƙacin kuma nima na daɗai da canzawa zan canza jika ne danma jikan todai bari inyi shiru dana ce wani abu amma dai shirun yafimin alkhairi,

dariya wasu suka sa mata saboda sun gano ta jikan da take nufi Meer ne shikuma bataga fuska ba shiyasa tayi wannan furucin,

Ameesha ma tagane ta dan haka tayi dariya itama sannan tace duk inda zakije ki ɗauko baza ki taɓa jin daɗin zama dashi ba, au🤭 namanta ashefa baki faɗi jikan namiji ne ko mace bamu san wanda kike nufi ba,

harar ta dadda tayi sannan tace abar maganar ni ba wanda zan canza amma fa kema bazan karɓe kiba idan kindawo idan kika tafi kintafi kenan dadda tayi hakane saboda abar maganar meer dan taga alamar wasu sun ɓaro jirgin ta...,

hakadai suka cigaba da wasa da dariya kamar babu abun da yafaru dasu (daman ance duk halin da kaka tsinci kanka kar kabari karasa farin ciki kayi ƙoƙari ko murmushi ne kasanyawa fuskar ka hakan zai rage maka wani raraɗaɗin dake cinka amma ace kullum dan abu yasameka ka tsaya kai ta sanyawa kanka damuwa abanza zaka cuci kanka wallahi kayi ƙoƙarin yakicesa gefe kayi rayuwar ka idan loƙacin damuwar ta tashi sai kayita aloƙacin sannan kaƙara kawar da ita)

ataƙaicedai basu suka bar gidan nan ba sai bayan sallar magrib sannan suka tafi kowa yayi nasa guri sai kuma haɗuwar gobe me ban mamaki,
acikin su ba wanda baya jiran goben nan tayi (daga ciki kuwa harda ni dan na matsu inga me zai faru gobennan Allah dai yakaimu da rai da lafiya daman ance inda ranka kasha kallo aduniya)

amma duk wannan farin cikin da sukeyi banda sam dan gabansa har faɗuwa yake dan baisan me zaije yadawo ba gobe agidan su yana tsoron jin wani abun daban da baishirya jin saba ji yake kamar yaje ya sanar dasu kafin goben amma ba halin yin hakan shima dole yajira goben yaga abun da zai faru.......,


*************************
*MASARAUTA*

_____*Fulani*

"
Fulani tunda su dadda suka fita itama anata bangaren take tayi tata masifar ita kadai bata da wanda zata sauke bala'inta akan sa tadade afalon guri guda takasa tashi daga gurin sai faman lissafo abun da zatayi wa matar nan duk inda take saitasa an lalubo mata ita dan bazata taba rabuwa da ita ta tafi hakannan taci galaba akanta tazo har inda take har cikin masarautar ta tagaya mata magana kuna ta tafi batare da andau kwakkwaran mataki akan taba ta dau lokaci me tsawo agurin kafin ta yunkura tana niyar barin wajen sai kawai taji turo kofa dakatawa tayi daga tafiyar datake tare da juyowa idon tane suka sauka akan hamza zaro ido tayi waje watakon wannan yaron bazai daina shigo mata guri kai tsaye ba kenan,

da farko ta tsorata da ganin sa amma tunawa da magan ganun hajiya sarah yasa ta cire tsoran sa aran ta cike da masifa tace uban me yakawo ka kuma kashigo min guri batare da izinina ba wai kai dan gidan uban waye agarin nan,

duk wannan abun da take masa ko ajikin sa sai murmushi ma da yasakar mata wanda yayi mata ciwo arai,

ciki yatako kuma yanzu ma bai cire takalmin ba ya shigo har ciki yakaraso gabanta yana binta da wani banzan kallo sannan yace akwai abun da zakiyi ne anshigo din idan zaki fidda ni kuma sai kifitar dani dan na fahimce kin manta kashe din danayi miki dazu shiyasa har kika samu damar magana to kiyi duk abun da kika dama nima zanyi nawa muzuba mugani wanda yaji tsoro ya bari,

haka kace ko haka kace ko to kwa zaka gani sai kasan yau wacece ni naga har yanzu baka san wacece niba labarina kake ji ko,

nikwa nasan ko wacece ke saidai ki nunawa wanda baisan kiba ko wanda yake jin tsoron ki yafada yana galla mata harara sannan ya matsa daga kusa da ita tare da daga murya yace budurwata babyna kina ina haka yai ta kwalawa Azeema kira tunda baisan sunan taba daman dan haka yake ta kiranta da hakan,

Azeema dake daki sarai tajiyo sa tun lokacin da yafara kiran ta kuma tagane muryar sa dan haka sai tayi banza dashi,

itadai fulani ta zuba masa ido tana kallon sarautar Allah tanaso ta nuna dakewar ta amma takasa saboda idan ta kalli idonsa saitaji tabbas wannan yasan wani abun akanta saboda zakewar sa tayi yawa babu yanda za ayi ace yana irin wadannan abubuwan batare da yataki wani abun ba inagadai hajiya sarah bata fahimci maganar da tayimata ba da kyau bata gane zancen taba kodan bataga yaron ba amma wannan yaron akalaman sa ba wani bugun ciki dole yasan wani abun ammadai zata kara tuntubar ta takara gayama ta abun dake faruwa ko zata fahimce ta, wannan tunanin da takeyi ne yasa takasa tanka masa ta rabu dashi yagama abun da yake ya fice mata daga gurin,

juyowa hamza yayi ya kalle ta sai kawai yace dan Allah dan kiramin ita najita shiru idan bacci kuna take kar ki tasheta kinji uwar masarautar su, yayi magana yana kara sakin murmushi,

banza tayi dashi tasan so yake ya kunna ta daga baya kuma ya yabamata maganar da yaga dama yatafi yabarta dan haka kawai ta watsa masa mugun kallo me kama da gargadi sannan ta juya tabarsa agun ranta kamar zai fasa kirjin ta yafito saboda halin da take jin kanta ayau, yau abu biyu sun hadar mata ta rasa mafita dole taje takira hajiya sarah,

binta yayi da kallo sannan ya girgiza kai tare da cewa "kadan ma kika gani wallahi sai nasa kin tsani kanki sai nasa duk sanda kika ganni sai nasaka miki faduwar gaba sai kin tsani ganina,

har yana niyar juyawa yafita saiga Azeema ta fito tsayawa yayi yana kallon ta itama shi take kallo bata kalle sa da yawaba ta dauke kanta daga gare sa tana takowa zuwa inda yake saboda itama daman tana so suyi magana dashi akan wane irin sirri ne da matar nan take boyewa,

dan haka sai kawai ta sakar masa murmushi, murmushin da ya kusa sa hamza zaucewa baigama cika da mamaki ba sai da yaji tace yi hakuri inajin kiranka ban fito ba ina shiryawa ne nayi wanka I'm sorry muje ko tafada tana nuna masa hanyar fita,

ba karamin mamaki tabashi ba baitaba tunanin haka daga gareta ba ko kusa dan harma yacire rai da fitowar ta dan yasan baza ta fito ba idan taji muryar sa amma saigashi ta fito harda murmushi da bashi hakuri shikam yau ina zaisa kansa da farin ciki,

hartaje wajen kofa bai iya motsawa ba saida tajuyo takara yi masa magana sannan yafara daga kafarsa yana takawa kamar wanda baida laka ajikin sa haka yake tafiya har yakarasa gabanta ita tafara fita sannan yabita abaya kamar rakumi da akala haka suke tafiya,

suna fitowa waje ta tsaya shima ya tsaya kallon sa tayi tana jiran taji ta bakin sa amma shi saboda tsabar mamaki ya kasa magana saida tace inajin ka me yake tafe dakai, duk tana yi masa hakane dan tasamu sudan saba daganan sai tayi masa maganar fulanin dan yanzu bazai yiyu ace daga haduwar suba tafara yi masa maganar ba lalle bama ya kulata amma idan suka saba tasan wannan normal ne zata iya yimasa maganar kanta tsaye,

zai bude baki yayi mata magana kenan sai tayi saurin dakatar dashi sannan tace "nan gurin da mutane da tawa na wucewa muje wani gurin ina ganin sai ya fi mana safe,

"wai dan Allah da gaske kike wannan batun anya kuwa kece?

Azeema tace da gaske nemana inkuma inkoma to sai intafi idan kagama mamakin sai kakirani,

da sauri yace "a'a dan Allah karkitafi muje to saima in hadaki da baban nawa daman nace zan kai mashi ke dan yau cewa yayi bazai biyo niba,

"Allah sarki ba komai muje ai yayi kokarima saboda nasan daga ji kai ka takura masa bayin kansa bane,

dan murmushi yayi sannan yace " ya akai kika gane Wallahi kamar kinsani amma dan Allah kada kice a'a bazaki ba,

akan me zance a'a nima ai zanso inje in gaida surikina,

juyowa yayi da sauri ya kalle ta dan yakara tabbar wa wai itadain ce kuwa da gaske kokuwa watace adai daban dan baitaba tunanin tana magana ba haka kuma maganar ma dashi takeyin ta harda cewa sirikin ta ita ko kunyar sama batajiba to kodai daman tana sonsa itama tunda yace yana sonta itama take sonsa kawai taki nunawa ne saboda jan aji irin na mata,

ganin yatafi tunani ya s a ta dan daga hannun ta tana cewa "hy"

da sauri ya dawo hayyacin sa ,

tunannin me kake ne haka tun adazu ina ta magana,

tunanin ki nake wallah ai ni kullumma cikin tunanin ki nake tunda naganki har yau bansake jina daidai ba sai yau ada naganki gani gaki hakan bakaramin farin ciki bane agare ni bazan taba mantawa da wannan ranar ba yaudin ta musamman ce agareni babbar rana dan tunda na hadu dake ranar farko nake wannan mafarkin inaso in kasance dake akoda yaushe Allah yasa yanda nakejin ki araina kema kiji koda rabin yanda nakejine zanyi farin ciki da hakan dan Allah ki taimakawa rayuwata yayi maganar yana kafeta da ido shiru tayi takasa basa amsa,

ganin hakan yasa jikin shi yin sanyi dan haka sai kawai yayi shiru baikara cewa komai ba yafara tafiya,

ta fahimci halin da yake ciki sai taji kamar bata kyau tamasa,

atsanake tafara magana yanzu haduwar muce tafarko dan haka bazaiyiyu kace duk wata tambaya sai na baka amsaba kabari zuwa wani lokacin sannan nagama karantar hakayen ka dan haka karkasawa kanka damuwa akan naki cewa komai game da baya nan dakake min ina fatan ka fahimce ni,

yaji dadin bayanin da tayi mishi dan haka sai kawai yace babu komai wallahi nikoda iya kulawar da kika yiminne ma kadai ta wadatar dani babu abun da zance miki sai godiya,

ahaka suka ringa tafiya sauna hirarsu kamar daman tuncan sun daade da sanin juna saida suna tafiya wasu

55 / 74