akayi agidan su Rasheeda har guziri take ta tafi dashi gida saboda son da take masa shiyasa ma da ta rasa abun yi ta yi musu shi ko ɗanɗa nawa bata yiba saboda batason tajiyo daɗin sa tun kan tazo ci saboda tasan bacci zaiyi da yawa idan yagama sai ta cinye gaba ɗaya to kuma gashi yanzu ya ɓata mata bojet tana ji tana gani a gaban ta ya cinye bai bar mata ko ɗaya ba,
Tunda tayi maganar yakasa motsawa daga gun ido kwa bai yarda sun haɗa ido ba saboda wata irin kunya ce ta kamasa wai abincin mutum biyu ya cinye shi kaɗai tabb akwai matsala yanzu bai san ma yanda zai yi da ita ba,
Sai yaji ta basa tausayi kuma ta basa dariya da tasan bata ciba ta kawo masa kuma harda jin haushi dan baici ba yanzu kuma yaci tazo tana masa tijara,
kukan natane ya ishe shi sai ya kalle ta yace "me yasa baki gaya min ba, da kin gaya min ni ko ci ma ba zan yi ba, daman ni ai banyi niyar ci ba kece kika takura min naci abun ma da ko daɗi babu kinzo kinsa zuciya ta sai tashi take ni banyi kukan ba sai ke to wallahi ki min shiru tun kan ranki ya ɓaci a gunnan ni nace kibani, sai kiyi haƙuri kisha tea kawai ko kuma kije kiƙara yin wani bada akwai ba, yayi maganar yana haɗe rai waishi a dole kar ta kawo masa wani raini a ciki idan ba haka ya yi mata yasan baza su zauna lafiya ba dan ta fahimci yarinyar a kwai tijara yanzu sai tasaka masa ciwon kai,
Jin maganar da yake mata kawai ta koma ta kwanta aƙasa taci gaba da kukan taƙaici biyu ya haɗar mata maimakon ya bata haƙuri amma shine zai rufe ta da faɗa duk abun da tayi masa bai gani ba ba sannu bare na gode saidai ma ya ƙara mata da wani laifin kuma ya hauta da masifa saboda shi ya kawo faɗa duniya,
Duk yanda yaso ta tsoratar da ita tayi shiru amma taƙi yi, uzuri yayi mata saboda yarinya ce kuma yasan shine da laifi kowa akayi wa haka bazaiji daɗi duk da ba da sanan saba ya yi hakan,
Abun da bai taɓa ba yau shi zaiyi tashi yayi da kansa ya nufi kitchen ɗin dan yi mata wani yasan duk abun da zai mata bazatayi shiru ba kuma yanzu halin da take ciki bazai iya dukan ta ba idan ma ya dake ta kukan sai yafi haka kuma babu yanda zai yi da ita ga bazai iya driven yanzu ba shiyasa amma da ɗaukan ta zaiyi su tafi gida shiyasa gwara ya bi da ita a hankali su rabu lafiya,
Tunda ya shiga kitchen ɗin yake faman sakin tsaki yake tunani yafara yi yama ake yin dankalin yasan tunawa yayi ashe fa sai an fere da sannan a soya tab zai iya kuwa, ji yayi ina bazai ɓatawa kansa loƙaci ba wajen yi juya yayi ya fice daga kitchen ɗin yana fita yaƙara hango ta har yanzu kukan take wani tsakin ya kuma ja sannan ya juya ya koma idan ma baiyi ba ransa zai ta ɓaci gwara yayi mata ya hutawa ransa,
Da sauri yaje ya ɗebo dankalin tare knife ya fara fere sa yana ajiye wa akan drowar saida yafere wajen guda biyar da ya ajiye ya samu wani ɗan benci dake gefe ya zauna ya huta sannan ya tashi ya cigaba wajen guda ashirin ya fere sannan ya yayyan ka su yana yi yana zama ya huta agurin yankan kuwa saida ya ɗan yanke a hannun amma wuƙar bata shiga sosai ba, daman man da ta gama suyar dashi yana kan gas ɗin bata ɗauke ba dan haka sai ya kunna kawai baijira ya ɗau zafi ba ya antaya duka dankalin aciki ya koma kan bencin ya zauna yana jiran ya soyu ɗan jimawa kaɗan ya tashi yaje ya jujjuya sa yaga har yanzu bai fara soyuwa ba kuma baya tafasa, komawa yayi yaƙara zama bai daɗi ba ya ƙara dubawa still dai yana nan yanda yake,
Wajen mituna goma yaga dai yagaji da zaman sai ya tashi ya leƙa ta yagan ta a zaune ta haɗa kai da gwiwa tana abun da take,
komawa tayi gurin da yaga yana ta motsi sosai yana ta motsawa alamar zai soyu shikuma daman yaga ji da yaga haka sai kawai yayi tunanin ai yama gama soyuwa plate ya ɗauko ya fara kwaso shi daga cikin mai yana zuba shi direct akan plate ɗin ba wani jiran tsanewar sa kawai da man da komai yake zuba wa a kai, yana gama kwashe wa yakashe gas ɗin yaɗauki plate ɗin dankalin har zai fita sai kuma ya tuna ashe fa da egg ake cin sa a jiye wa yayi sannan ya nufi inda yaga crades ɗin suke yaje ya kwaso guda biyar yazo ya farfasa su ya zuba su a kwana nan da yaga ta yi amfani dashi, sai ya ɗauki maggi har guda uku ya zuba a ciki ya samu gishiri shima ya zuba da ɗan yawa ba laifi daidai misali amma a wajen sa albasa kuwa yama manta da batun ta ko ince ina jin baima san ana sakawa ba, ya kaɗa abun da gwanin kyau a ido yanda yake kaɗawa kai kace wani ƙwararren kukunne ga wani gumi da ya fara tsatstsafo masa na wahala, man da ya soya dankalin ko ince ya gasa dankalin baiyi tunanin ya juye saba ko kuma yarage a'a kawai shaka ya watsa kwan duka a ciki bayan ya zuba yayi kwance aƙasan man sannan ya kunna gas ɗin, ya zuba masa ido yana jiran ya fara tafasa ya soyu kamar dankalin abun da ya basa mamaki sai yaga wai har ya fara tafasa bai ba kamar yanda dankalin ya ɗauki loƙaci ba, daɗi ne yakama sa da yaga yana ta ƙara kunburowa mai na shirin zubowa yana ganin haka yayi saurin kashe gas ɗin sai da ya jira man ya ɗan lafa sannan yasaka ludayin ya fara ɗibo sa sai yayi mamaki gani duk ya dagar gaje bai haɗe jikin sa ba ba kamar yanda ta kawo masa ba, sai yabar hakan kawai azin soyuwa yayi da yawa shiyasa ya dagargaje tsamosa yayi tsaf gaba ɗaya ya ɗora sa akan dankalin sannan ya ɗauki plate ɗin ya nufi hanyar fita dashi, saida yaje bakin ƙofar sai ya tsaya yana ƙarewa abun kallo yadai san shidai a ido ba kamar haka yaci ba ɗazu amma yana da tabbacin dai haka ake, ƙara kallon sa yayi sai yaji wani irin daɗi ya ziyar ce sa wai shi yayi wannan gaskiya yayi namijin ƙoƙari saidai bayajin zai iya ci saboda ya dafa sai yaji duk ya haumasa kai(hmm daman idan ƙwaraiwa tayi ƙwaraiwa ai mutum baya iya cin abincin da ya girka musamman idan yayi kwaɓa irin taka, gaskiya Meer kaban kunya duk wannan iyayin ba a iya komai a kitchen ba daman,🤔😁😁)
A hankali ya shiga takawa cikin falon ya doshi inda take har yaƙarasa gaban ta sannan ya tsaya, bata ɗago ba tana kan gwiwar ta bataji zuwan saba sai wani nannaɗaɗɗen ƙarni da ya nannaɗe yashiga ya lallaɓa ta ƙasa ƙafar ta ya dakar mata hanci da ƙarfi, hakanne yasaka ta ɗagowa da sauri ba shiri dan ganin abun da yake neman saka ta amai......,
Ido biyu tayi da dankalin da yake miƙo mata, sannan tabi hannun sa da kallo har zuwa kan fuskar sa sannan ta ƙara mayar da kallon dankalin da a ido ma baida kyaun gani kana gani kaga ɗanyan abu babu alamar soyuwa ko ɗaya,
Gajiya yayi da tsayiwar har yake jin kamar ya ajiye mata amma ganin kallon da takewa abun sai yayi tunani ko burgeta yayi tayi tunanin ƙoƙarin da yayi,
Hannu tasa kamar zata karɓa sai kawai ta fasa ta miƙi tsaye tana kallon sa tace meye wannan?
Da mamakin rainin hankalin tambayear da tayi masa haɗe rai yayi sosai sannan yace "Idon ki me yagane miki,
Ta manta da kukan da take bata san loƙacin da ta tuntsure da dariya ba ai saikwa ta hau ƙyalƙyala dariya tana kallon sa waishi nan da gaske dankali ya soya tana kalla sai ta ƙara fashe wa da wata dariyar kamar sabon kamu, hannu takai zata karɓa ya janye haushi ya kamasa tama mayar dashi mahaukaci ya sha walaha yayi mata abu kuma tazo tasa shi agaba tana masa dariya ko taga wani abun na dariya ajikin sa, ko kuma abun da yayi ne yabata dariya oho mata,
Ameeaha fa sai an kawo ɗauki ta tafi sai dariya take harda su riƙe ciki ita ƙwanne ma yafi bata dariya yanda yayi wani wara wara kuma tana kalla ta fahimci acikin mai ya zuba sa, shiyafi komai bata dariya ashe duk burgar tasa bai iya girki ba sai iya dukan mutane,
Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska...........✍️✍️✍️
tofa team ɗin Meer a kawo taimakon gaggawa a koyawa Meer girki kar raini ya shiga tsakanin sa da Ameesha dan naga alamar bazata ɗaga masa ƙafa ba wajen dariyar nan tata,
To fa ga kuma bawan Allah ko waye wannan tsohon da yazo gurin Ameesha taya akai yasan ta haka to kodai bokanne kamar yanda Ameesha take zato, Amma dai muje zuwa muji shi kuma dame yazo,
*_to ya kuka ga wannan page ɗin da aringayin irin sa da kuma aringayi kullum duk ƙanƙantar sa wane kuka fi so???????_*
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 99
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
____Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska...........,
___Ɗif tayi da dariyar da take masa ta fara ƙif ƙif da ido gudun kar ya shigar mata ido, take fuskar ta tayi dama dama da mai kamar a fuskar a ka soya ƙwan, duk da taji ƙarni kuma taji haushin kifa matan da yayi a fuska, amma itama dan ta ƙara masa wani baƙin cikin sai kawai tasake fashewa da dariyar ta ciga ba da yi masa dariyar,
Hannu ya ɗaga zai kai mata duka tayi saurin gocewa ya daki iska, ƙwafa yayi cike da ta ƙaici yana hararar ta yana kallon dankalin dake zube a ƙasa yana ƙara jin wani irin haushi na taso masa yanzu yarinyar nan dan ta gama ci masa mutun ci ya sha wahala ya dage ya taƙaƙƙare ya zuba basirar sa yayi mata amma yanzu shine zube a ƙasa gashi kuma taso tasa shi gaba tana masa dariya, dan tagama rainasa to kwa wallahi bata isa ba sai ta cinye sa tas duk da ya zuɓe a ƙasa sai taci sa da haka dan bazai yi wahala aban za ba,
Tana tsaye daga ɗan nesa dashi tana dariyar ta tana toshe baki bata ankara ba taji ya fisgota ta faɗa kansa saura kaɗan ta faɗi tayi saurin rirriƙe shi, hannu yasa ya ƙara riƙota da kyau kamar abun arziƙi a haka ya rungumo ta suka zauna a ƙasan gurin sannan ya rabata da jikin sa ya zaunar da ita agaban sa, Yunƙurin tashi ta fara yi yayi saurin riƙe ta ya miƙar da ƙafafun ta sannan ya ɗora nasa a kai ya danne su, sannan ya haɗa hannu wanta gaba ɗaya biyun ya riƙe su da hannu ɗaya ya matso da ita gaban sa sosai yanda ba yanda zata tayi ta tashi sannan yasa ɗayan hannun sa ya ɗebo dankalin tare da ƙwan ya matso dashi wajen bakin ta,
Cike da zaro ido ta fara girgiza masa kai tare da rufe bakin ƙam yanda bazai iya saka mata, dodana mata shi ya shigayi a bakin amma yaƙi shiga saboda ta rufe bakin ƙam,
haɗe rai yayi ya harare ta yace wallahi idan baki buɗe ba ranki zai ɓaci ba yunwa kike jiba nace kije kiyi kinƙi saurara ta kuma yanzu kinsa naje nasha wahala nayi kice bazaki ci ba wallahi baki isaba sai ki cinye sa,
Kuka tafara yi tana girgiza kai aranta tana ayyana taya zata iya cin ɗanyan dankali ita bana rashin soyuwar ne ma yafi damun ta ba ƙarnin ƙwan shi yafi ɗaga mata hankali, gashi tana so ta buɗe baki ta bashi haƙuri kuma tana tsoron kar ta buɗe ya danna mata shi,
Duk yanda yaso ya da tura mata taƙi buɗewa sai kokawa suke tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, da yaga dai abun nata ba easy sai kawai ya ajiye dankalin a ƙasa ya sakar mata hannu,
Nan tasamu damar buɗe bakin ta ta shiga basa haƙuri da yi masa magiya amma ko kallon ta baiyi ba sai ya ɗauko mayafin ta ya ƙara haɗa hannun nata duka biyu ya ƙulle mata hannu wan dashi sosai ya ƙulle yanda bazata iya kuncewa ba, saboda zafin da taji harda hawaye,
Ƙara jawo ta yayi yasa hannun sa ɗaya ga matsa mata bakin har saida ya buɗu sannan ya sa ɗayan hannun ya ɗebo dankalin dan mugun ta ciki hannun sa yayi dashi ya nufi bakin ta dashi,
Duk yanda taso ya kwacewa shigar dankalin bakin amma hakan ya gagara saidaya danna mata shi abaki, ƙin taunawa tayi, yace wallahi ko ta tauna ko yasa ta haɗiye shi ta dole,
Ba yanda ta iya haka tafara taunasa garas garas saikace ɗanye tana taunawa tana jera masa Allah ya isa tafi cikin kwando kuma tayi alwashin wallahi bashi yaci dan sai ta rama, inda Allah ya taimake ta ma bai haɗa mata da ƙwanba iya dankalin ne, tana hawaye saida ta gama taunesa tsaf, sannan yaƙara ɗebo mata wani yanzu kam har da ƙwan ga haɗo mata ƙwan ma kuma yafi yawa haka shima ya danna mata shi yace "oya cinyesa yanzu nan ai baima gama maganar sa ba tayi saurin furzar dashi tana kallon tace "wallahi bazan iya ciba dan Allah ka rabu dani ba cikina bane me yasa kake son yi min dole inci abun da kwata kwata babu daɗi kuma wanna kwan gishiri da maggi yayi yawa wallahi bazan iya ciba, kuma kaci gaji ga uban ƙarni da yake baka sa albasa ba Allah kuwa bazan iya ciba saidai ka kashe ni........,
Bam taji a bakin ta yasa hannu ya buge mata baki, Saida tasaki ƴar karamar ƙara sakamakon zafin da taji ga ya ƙulle mata hannu bare ta shafa wajen,
Bai dadda raba ya ƙara ɗebowa ya cusa mata shi a baki ta ƙarfin tsiya sannan ya toshe mata bakin ta yanda bazata iya fito dashi ba,
Maggi ne da yaji suka zagaya mata baki take taji zuciyar ta ta hargitse amai ya taho mata duk yanda taso ta riƙe sa abun ya gagara saboda yazo mata wuya, yana sakin bakin kuwa tashiga kwarara amai, yanda yayi ɗaiɗai da ƙafarsa ya danne ta haka aman nan ya wanke masa jiki gaba ɗaya akan rigar sa ta kwararo sa agaba ɗaya rigar jikin sa,
Damƙe idon sa yayi jin zubar amai ajikin, aransa kuwa nanata kalan man anan yake "amai amai ajiki na tabbb wannan yarinyar ta tagama dashi shida ko jin ana amai ma baya so yau shi akayiwa amai ajiki,
tana gamawa ta fara maida numfashi bazato ba tsammani taji ya ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari har guda biyu, take jinra da ganin ta suka ɗauke saboda aman da tayi da kuma ƙarnin da yaje samun ta taje taji wani irin zazzaɓi ya fara ziyar tatta da kwa yaƙara mata da mari take ta sume awajen, tayi gefe zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta sai kuma yaji tayi nauyi jikin ta ya saki gaba ɗaya, tsaki yana yasake ta saboda ya gane sume masa tayi,
tashi yayi yana me ƙenƙamin jikin sa ji yake kamar ya cire duk jikin sa, haka yake ji duk ya tsani kansa, Tsaye ya miƙe yana so ya cire rigar amma yana tunanin ta inda zai fara saboda idan ya ɗaga ta zai taɓa masa fuska shikam bazai iya jurar hakan ba, da yarasa yanda zaiyi kawai sai ya ɓalle bottel ɗin jallabiyar ya kama tsakiyar ta da iya ƙarfin sa yajata Ya yaga Tsakiyar ta tunda ga sama har ƙasa ya keta ta ya cire yayi wulli da ita gefe,sannan ya zare dogon wandon ma ya rage daga shi sai gajeran wando shima na ciki skintight irin na maza da suke sakawa ta ciki kafin su ɗora gajeran wando,
wajen fridge yaje ya ɗauko ruwa me sanyi, yazo ya yayyafa mata kaɗan bata motsaba, saida ya sharara matasa bakin robar sannan ta kawo numfashi me nauyi, a zabure ta miƙe zaune saidai idon ta nayin ido biyu da santaleliyar surar jikin sa ba kaya, take ta haɗiye wani yawu me zafi da ya haddasa mata wani suman batare da ta shirya hakan ba ta tafi luuuu ta koma inda ta taso,
Mamaki ne ya kamasa ganin ta ƙara sumewa yana tunanin anya kuwa lafiyar ta ƙalau ita abun suma baya mata wahala, tsaki yaja tare da wucewa upstairs yaje ɗakin sa ya ɗauko wasu kayan ya saka ya fito yana tafiya yana sakin tsaki,
saida yazo daf da ita ya ɓalla mata wata uwar harara yaje inda ya