Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   41 / 74

120K to 123K   out of 221K words

din suka fito gaba dayan su suka shiga ciki inda suka nemi ayi musu iso ga managen gurin ba bata lokaci kuwa aka kaisu har office din sa sameer da bossay ne da shettima kadai suka shiga sukuma suka tsaya daga bakin kofar,

bayan sun shiga sun gaggaisa da managen suke sanar dashi abun da ya kawo su atake shima hankalinsa ya tashi yashiga basu hakuri sannan akace aduba cctv camera din na jiya ko za aga wata alama nan ya shiga duba computer din dake gabansa bincike ya shigayi da ido sameer yayi wa bossay alamar yaje ya duba shima bossay ya zagaya ta bayan sa yana ganin dubawara da yake yi daga bayama gaba dayan sune sukaje suka tsaya suna kallon videon tundaga safe har zuwa yamma aka nuno lokacin da suka shigo gurin aikam suna tsayawa da motar su sai ga wata motar ta tsaya daga bayan su,

anan sam yasa aka saka pause sannan akace su Ammar su shigo suna shogowa aka nunawa Amra akace itace motar da sauri tace eh wallahi itace kuma itace dazu ta fito daga gida wallahi nagane ta itace,

play aka saka videon da suke kalla yaci gaba da tafiya saida babu wanda yafito daga motar...

cigaba da kalla sukayi har lokacin da su hamra suka fito tabbas tare suka fito saidai kuma abun mamakin suna fitowa kuma sai camera din ta dauke gaba daya ashe tundafa lokacin ma bata kara aiki ba har sai washe gari taci gaba da aiki,

gaba dayan su dagowa sukayi aka shiga kallon kallo gaba dayan su sun kasa magana,

managen gurin ne yayi karfin halin cewa to kungade abun da yafaru ni kaina ma bansan da hakan ba bansan ya akai hakan ta faru ba amma de kuyi hakuri kuje zuwa gobe insha Allah zan bincika ahankali har ingano inda aka samu matsar bazai yiyi muyi yanzu ba saboda idan nace za ayi to za aja hankalin customers kuma baza asamu ma'aikata ba dole sai zuwa dare zan tara su gaba daya sai aduba daga ina matsar take kuyi hakuri amma in Allah ya yarda kar kudamu zanyi kokarin gano muku zan kira wani abokina shi zaifi dubamin abun dake faruwa dan zai iya sawa ma gurin haske aga koma menen awajen kar kudamu da wannan,

Sai yanzu duk suka samu bakin magana kowa na tofa albarkacin bakin sa game lamarin amma basu tashi hankalin suba tunawa da inda Amra tace taga motar sunsan bazasu sha wahalar bainceke ba da zarar sunje gida suna ganin komai ya daidaita,

dan haka ba bata lokaci suka kara kwasar jiki suka nufi hanyar gida suna tafiya suna hirar jefi jefi ahaka har suka karasa unguwar suka nufi masarauta suna shiga gate na farko da yake abude koda yaushe sun nufi gate nabiyu da zai sadaka da cikin masarautar bossay dake tuke yayi saurin taka burki da mamaki duk suke kallon sa shettima yace ya akai lafiya de ko da hannun yayi musu alamar bakin gate din masarautar kallon sa yayi yace me fa yafada cike da rashin fahimta,

bossay ne ya dafa kai yace akwai matsalafa kunsan me nagani duk suka ce aa suna duban bakin gate din da yake nuna musu sude sunga wata mata abakin gate din kuma bisa ga dukkan alamu fada akeyi da ita watakil ko hanata shiga akayi,

da kyar bossay ya ce abun da muke gudu ya faru shikenan dan haka kowa yasamo abun cewa saboda tsohuwa ta bayyana kowa ya tanadi abun cewa,

Sameer ne yace wai me kake nufine sai faman zance kake mana bamu fahimce kaba,

Cike da tashin hankali bossay yace dadda ce kakar Ameesha wallahi itace waccen ake rigima da ita,

cike da tashin hankali har suna hada baki wajen cewa dadda fa kace..........🙆‍♀️


barkan ku da sallah fatan kowa yayi Salla lafiya........


                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/1, 9:32 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️75&76

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

             
  
       "cike da tashin hankali har suna hada baki wajen cewa dadda fa kace..........🙆‍♀️

"kwarai kuwa wallahi itace waccen yanzu yazamuyi,

"Sameer me yace anya ba juyawa zamuyi mubari idan ta tafi sai mushiga yanzu idan ta saka mu agaba fa me zamuce mata kumsande wannan matar ba ita kaɗai bace yanzu tana ganin mu zata nemi ta tara mana mutane anan gurin kaɗan daga cikin aikin ta dan haka wallahi masalaha shine mujuya kawai mujira tafiyar ta,

bossay yasaki murmushin yaƙe dan shi kaɗai yasan halin da yake ciki saboda duk yafisu sanin wacece dadda idan ta kafe akan abu ɗan juyowa yayi ya kalle sa yace wallahi bakasan halin ta bane shiyasa kace mujuya ai indai ba in muka juya to daga nan bazamu dawoba har abada dan wannan matar da kake gani zafin kanta yawuce tunanin ka ai tunda ta riga tasaka ƙafarta ta fito daga can gidan kuma har tazo nan tofa wallahi babu wanda ya isa yasa ta koma sai tayi abun da yakawota koda kuwa zata sha wahala to idan tasa abu gaba saitaga tasamu zata bar wajen, yanzu da kuka ganta acan ko tofa babu inda zataje sai tashiga gidan nan dan hakama ka canza wata shawarar amma banda wannan,

sosai suka ƙara mamakin irin wanann halin na dadda,

Sude su Ammar sunyi jigum jigum suna sauraron hirar su suna jin jinawa me wannan halin koma wacece saboda basu santa ba,

shettima ne " yayi gyaran murya yace nifa inaga kunsan me za ayi "duk suka ce a'a" sannan yace kawai muje musame ta inyaso sai mu lallaɓata ta koma gida muce kuma yarinyar tana wajen Hajiya daman kuma tasan ai ba anan aka ajiye taba tana cen gidan kunga idan ta ƙara nacewa sai taje canɗin mukuma sai muyi tayi mata  yawo da hankali da haka har ta haƙura mumaida ita gidan da ta baro ko ya kukace,

"Bossay yace Hmmm lalle baka san taba ne shiyasa kake wannan zancen itace zata yarda har kayi mata yawo da hankali kuma kurabu lafiya da sake Maganar nan taka,

sameer da duk kansa ya ƙulle akan dadda saida yaɗau loƙaci kafin yayi magana da ƙyar ya iya cewa muje kawai ni nasan yanda zanyi da ita,

jinjina kai kawai bossay yayi yana ayyana abubuwan da zasu faru idan sun haɗa da dadda shide gabansa sai dukan uku uku yake baice komai ba ya tayar da motar suka nufi inda daddar take,

**Wallahi baka isaba sai na shiga gidan nan ko kuma kaje kayo min magana da sarkin gidan inma baza kubari inshiga ba uban me zan ɗauka acikin gidan ni yarinyata nazo ƙarɓa tun ɗazu nake tsaye agunnan ina fahimtar dakai amma baka fahimta nabika ta lallami nabika ta salama amma kaƙi ji ko to wallahi zan ture ka inshiga cikin gidan nan kabar ganin ka gabjeje wallahi ba wahala zakayi min ba wajen ture ka dan kaga ina ɗaga maka ƙafa to ko shi sarkin ya isa yayi min abun da kayi min to wallahi duk bakin cikin ka sai na shiga sai anfito mun da jikata acikin gidan kafin a zauna lafiya inkwa ba a fito min da itaba wallahi sai na ɗagawa kowa hankali cikin gidannan sai na daga hankalin kowa da kowa,

shide me gadi yabi ya garƙame ƙofar dan shi duk atunanin sa mahaukaciya tazo zata shiga dan gaba ɗaya bayanin ta datakyi baiga meye amfanin su ba dan shi duk a shirme da shiririta yake ɗaukan zancenna ta,

  dadda da tagade da gaske me gadin baida niyar bari ta shiga yasa  ta aro duka ƙarfin ta  zata ture shi taji an riƙe mata hannun,

  cak ta tsaya tare da ɗagowa  dan ganin ko waye tana ɗagowa tozali da fuskar bossay saurin wara idanun ta,

ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da kallo dan suma duk sun fito waje kawaide bossay ne yarigasu saurin zuwa saboda ganin abun da take shirin yiwa me gadi,

Kamar wacce aka tsikarawa haka tayi saurin kwace hannun ta Sannan ta shiga tafa hannu da yiwa Allah godiya tana cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Allah na gode maka daka haɗani da waɗannnan mayaudaran munafukan Allah ta'ala nazo har inda kuke kuzo mushiga ku fito min da jikata ko ku haɗani da sarki idan bakuji maganar tawa b ai zakuji ta Sarkin ku ai ku muje yanzunnan mu je gabansa yaraba mana faɗa dan banyarda daku ba gaba ɗaya ku baku da gaskiya idan kuma kunsan kuna da ita to akaini duk inda take yanzunnan dan ba inda zan ƙara zuwa batare danaje ko inaba ƙafarta ƙafata eheee......,

bossay ne yace dadda wai meye hakane kike yi dan Allah kidena irin wannan abun bashida amfani  kinsan kwa a inda kike wannan maganar  duk maganar da tazo bakin ki faɗar ta kike kai tsaye gashi kina ai bantamu da wani laifi taya kike tunanin zamu cutar da yarinyar da nayi niyar cutar da ita daba tuni na cutar da ita ba tun kwanakin baya da wataran ma idan mun haɗu baki saniba saunawa zamu haɗu batare da sanin kiba kuma duk loƙacin banyi yunƙurin cutar da ita akan me kuma zan cutar da ita yanzu alaƙocin da tafi buƙatar taimakon kowa duk nan da kika ganmu kullum burinu mu muga munnemo mahaifan yarinyar tunda kika bamu labari kowa ya katse uzurin gaban sa mun dawo muna nata safe rana dare koman mu akan ta yake ko loƙacin kanmu bamu dashi isasshe sai nata amma ke duk abun da ake bakya gani to baza akaiki in taken ba kiyi duk abun da zakiyi duk tunanin da kikeyi akan munyi mata wani to hakanne munyi mata duk abun da kike tunani sannan kuma mun kasheta bade haka kike so kijiba to mun kasheta muma kizo ki kashemu ko kisaka akashemu yana kaiwa nan cikin fushi yayi fuuuuu ya koma cikin mota yashiga saboda har ga Allah abun da takeyi yafara isarsa duk da biyu yayi maya haka yayi mata saboda yaɓata masa rai kuma yayi mata haka saboda yasan hakanne kawai zaisa tadena maganganun datake yi idan baifito mata ta bayan gida ba zata shiga hankalin ta ba amma yanzu yasan ya kashe bakin magana dole tabi yanda suke so....,

guri dadda tasamu tayi zaman dirshen aƙasa tare da nannaɗe kafafunta tayi zaman musulunci sai kuka hawayene kawai yake wanke kwaranyowa daga idon ta yana saukowa ta rasa bakin magana kuka kawai takeyi abun da bossay yayi mata ba ƙaramin tsaya mata arai yayi ba,

da su shettima suma har zasu juya subarta agun sai kawai sukaji ta basu tausayi sameer ne ya tsugunnna agabanta tare da cewa kiyi haƙuri ta shi mushiga amma de ita bata nan tana cen gidan wajen Hajiya kamar yanda muka gaya miki idan kuma baki yarda damu ba ai zaki yarda da hajiya bari akira miki ita sai ki tambaye ta kiji  jikarki tana cikin ƙoshin lafiya babu abun da yasameta mude bazamu taɓa cutar da itaba amma tunda baki yarda ba yanzu kitashi ki koma gida ni da kaina zan kawo miki ita har gida nayi miki alƙawari daga nan zuwa dare zan kawota kinji yaƙarasa maganar yana kafe ta idanun sa,

zunbur tayi ta miƙe tsaye tare da cewa ƙarya kuke wallahi ƙarya kuke har ni za azo ana tsarawa to aheer ɗin ku kunyi kaɗan inbiku yanda kuke so ni banason daɗin baki ai abu mafi masalaha anan shine kode akawo min ita yanzu nan ko kuma akaini inda take amma inbahaka ba kuma  ba gidan dazan koma ni kaɗai dan haka sai kusan yanda zakuyi dani idan kuma bahaka ba wallahi zan shiga in sanar da sarki idan shima ya kasa zan kaiku wajen ƴan sanda dole kufito da yanda kukayi da ita dan ni Wallahi jikina yabani baku da gaskiya akanta da abun da kukayi mata in kuma ƙaryane inganta mana yanzu tare daku ammade kace ai tana awancen gidan kuma ga motar ku indai da gaskene mushiga kawai mutafi cen ɗin,

dafe kansa Sameer yayi azuciyar sa yana jinjina irin wannan taurin kan da kafiya akan abu to shidai baisan yanda zaiyi da itaba dan haka sai kawai yace to muje gidan ya faɗa mata tare da muƙewa kamar gaske gidan zaikaita,

binsa ta shiga yi abaya tana tafiya ta na ƙara yin maganganu har sukaje wajen motar baya ta buɗe zata shiga sai taga ƴan biyu aciki dakatawa tayi sannan ta juyo ta kalli sameer dake gefen ta gira ya ɗage mata suna haɗa ido sannan yace kishiga kawai,,,

ina shiga ina zan zauna ko akansu kake so in zauna Ammar ne yayi saurin buɗe ɗayan barin ya fito sanaan yace ta shiga bari shi yaƙarasa ciki aƙafa shiga tayi ta zauna tana ta faman cika tana batsewa tunda ta shiga take makawa bossay harara Sarai yaganta amma sai yanuna baima san tanayi ba yanzu Sameer ne yajasu zuwa cikin masarautar zuciyarsa cike da tarin damuwa yanzu kuma ina zaikaita da yaɗauketa wata zuciyar ce kawai tace kugaya mata gaskiyar abun dake faruwa wata zuciyar kuma tayi saurin kwaɓar sa akan karya kuskura Yahaya mata idan kwa tasani abun nata sai yafi haka dan haka gwara ma yakaita wajen momma ta riƙe mata ita ahanata fitowa sukuma sai su fito suci gaba da aikin su da wannan shawarar ta zuciyarsa ya samu kwarin gwiwar ƙarasawa cikin gidan...

_______hamza

Yaron nan wai me yake damun ka a yan kwanakin nan duk kabi kazama wani iri baba ne yakewa hamza magana dake kwance kan yayi ruf da ciki kamar me bacci,

dagowa yayi tare da tashi zaune yana fuskantar baba sannan yace baba ciwon sone yake damuna kataimaka kaje kayo min bikon yarinyar nan wallahi ta shiga raina ta zauna amma duk sanda zamu hadu duk maganar da zan mata bata kula ni narasa ya zanyi da ita amma gaskiya ina sonta baba yazanyi da sonta,

baba ne yayi dariya irin tasu ta manya sannan yace hamza kenan bakajin magana yanzu duk iya tsarin naka da dauriya irin taka amma kake son mace ta canzaka ai bai kamata kana jin shakkarta ba kawai kaje gadan gadan kasame ta ka gaya mata abun dake ranka idan taga zata amince dakai to idan kuma bata amince ba sai ka hakura ai ba awa mutum dole akan soyayya,

baba wallahi masifaffiya ce kuma ina ganin kamar tainani tayi shiyasa taki kulani saboda na lura kamar ba baiwa bace saboda jikin ta bai nuna wata wahala ba ranar fa dana fara shan gabanta zan mata magana saura kiris ta kwashe ni da mari nayi saurin matsawa amma badan hakaba sai ta mareni saboda na tari gabanta kawai sannan ta gargadeni akan ko a hanya naganta kar nasake na kara yimata magana amma ni bana ji sonta ya rufe min ido duk sanda naganta sai na kuma yi mata magana baba wallahi kai kadai zaka iya taimakamin,

dariya baba yayi sosai dan har hakuran sa saida suka fito cikin yar dariyar yace ni kuma dame zan iya taimaka maka da girmana ina ni ina yiwa yarinya magana akan soyayya wanna yakin kai kadai zakayi shi ba ruwana aciki,

to wallahi baba indai baza ka taimakamin ba zansan yanda nayi na sace yarinyar nan in boye ta inta kallon ta ina yimata abubuwan da dole sai ta soni,

"Au daman anayiwa mutum dole akan so taya zaka ta soka bayan ka saceta to wai ta inama zaka saceta kuma ka kaita ina idan kasace ta din?

"kai baka jin tsoron akamaka wane irin hukun ci za ayi maka idan ka aikata hakan,

Baba tsorofa kace ai wallahi cikin gidan nan babu wanda ya isa yasa inji tsoron sa kaf cikin gidan nan baba nifa ko fita nayi niya babu wanda ya isa ya hanani kawaide saboda inma nafita bansan inda zani ba kuma anan din ina samun yanda nake so amma bana zaman gidan nan saboda wani dan haka ka ajiye maganar tsoro ma agefe ni hamza bana tsoro saidai inbada tsoro,

"eh baka jin tsoron mutane amma ai ga mace nan zata saka ka agaba tunda hartayi yunkurin marin ka ka kasa komai kaga kwa ai kasamu wanda kakejin tsoro din,

Dan shafa kansa yayi sannan yace baba itama ai dan ina sonta ne shiyasa na daga mata kafa amma badan haka ba kaikasan bata isa ta mareni ba ko niyar da tayi ma sai na koya mata hankali amma dake sonta nake nakasa yi mata komai kuma ahaka naci gaba da son nata,

yana gama maganar ya kara gyara zama sannan yace baba nifa taimako daya zaka min muje tare kawai sai kace mata kai mahaifinane kana neman min auren ta tayi maka magana da manyan ta nasan de kai babbane baza tayi maka abun da take yi min ba,

daga nan nikuma nasamu dama sai in kuma tsarata har ta amince dani ka yarda baba,

baba yace nidai ba inda zani da girmana kasa yarinya ta dena ganin mutun cina idan wani abun ya hada tunda tace bata sonka to bata sonka din ka hakura da ita kawai,

"Wllahi baba bazan iya hakura da ita ba kawai kayi hakuri muje tare ni inaji ajikina idan mukaje tare Allah zata amin ce idan taga da gaske nake de sonta nake kuma auren ta sai tafi yarda dani,

  "nifa ba inda zani kaje can kai kaɗai amma babu ruwana,

baba wai yanzu haka zamuyi dakai tunda muke bantaɓa neman wata alfarma ba awajen ka amma yau ɗaya na nema amma kaƙi amincewa shikenan baba nagode,

yana gama faɗar haka

41 / 74