Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   73 / 74

216K to 219K   out of 221K words

ajiye muƙllin motar ya nufi hanyar waje har yaje bakin ƙofa ya tuna idan ya koma gida ba ita yasan dole sai an tuhume sa akan hakan, tunanin hakan yasa shi dawowa da baya ya ƙara ɗaukan ruwan ya watsa mata a fuska wani sanyayyen numfashi ta sauke saidai taƙi buɗe idon ta dan tana farkawa taje surar jikin sa ta sake faɗo mata duk da ta rufe ido amma bata daina hango ta ba a idon ta ƙara ƙanƙame idon ta tayi tana so ta manta da abun da tagani amma hakan ya gagara, 

Har ɗan leƙen fuskar ta yake yana mamakin abun da take shi tsoro ma ta ɗan basa har yafara tunanin to kodai aljanune da ita, ɗan dakewa yayi, sannan yayi gyaran murya, yace "ke meye haken kike kitashi mutafi ko inyi tafiya ta,

"wallahi bazan buɗe ba bana son ganin ka ahaka Please dan Allah katafi ka matsa daga kusa dani, tana faɗa tana sake rufe ido tana girgiza kai,

wani dogon tsaki yaja jin batun da take sai yanzu yagane dalilin suman nata tab aikwa tana ruwa zata mutu watarn kenan idan taga me duka lol 😂 injini fa ba inji saba ah to,

Haushi da taƙaici yasa yarasa mema zai ce mata, dan ta bashi haushi, wani tunanin ne ya faɗo masa to kodai shatin alulun sane shiyasa ta tsorata saboda skintight ɗin babu abun da baya fito dashi, tuna hakan yasa yaji yafara jin haushin kansa me yasama tun wuri baiyi wannan tunanin ba bai saka kaya ba ya tashe ta, gashi yanzu taga girman sa shikenan wataƙil ta samu damar rainasa, ji yake kamar yayi hauka ya akai yabari haka ta faru, cije bakin sa yayi tare da furzar da iska me huci sannan ya sa hannun ya fara shafa sumar kansa yana me ƙara jin wani taƙaicin, tsaki ya kuma ja cikin sarsarfa ya juya mata baya sannan yace "idan kinga dama ki kwana anan banda loƙacin ki yana kaiwa nan ya ƙara gaba ya fice,

A hankali ta buɗe idon ta suka sauka abayan sa loƙacin yana daf da fita daga cikin falon,

da sauri ta miƙe zaune ganin da kaya ajikin sa yasa tayi saurin tashi tsaye, saida ta bari yagama fita daga ciki sannan ta biyo bayan sa loƙacin da ta fito har yaje bakin motar yana ƙoƙarin buɗewa, sauri ta ƙara gudan kar taje ya tafi ya barta shiyasa ta fara sauri harda ɗan gudu gudun ta, yana shiga ciki itama ta buɗe baya ta shiga,

yana jinta amma bai ce mata komai ba kawai ya kaɗa kansa tare sa tayar da motar yajata zuwa bakin gate ɗin sannan ya fito, ya buɗe ya fitar da motar ya ƙara fitowa yaje ya zuge gate ɗin sannan ya shiga ya tayar suka ci gaba da tafiya....,

Tunda suka fara tafiya ba wanda yayi magana acikin su kowa da abun da yake tunani,

Sun ɗan fara nisa da tafiyar batare da ya juyo ya kalle ta ba, ta cikin madubi ya kalle ta yaga yanda fuskar ta take maiƙo gaba ɗaya tayi dama dama mamaki yayi ita ko damun tama bayayi, murya can ƙasa ƙasa yace "ki samu abu ki goge fuskar nan kuma wallahi idan mukaje kika faɗi abu ɗaya ma zaki yanda zanyi dake,

tajisa sarai amma saita murguɗa baki tare da basarwa irin bataji me yace ba, jinta shirua yasashi ƙara maimai tawa yace "ko baki ji me nace, sai tayi sauri ta ɗago tace "wai magana kake, girgiza kai kawai yayi saida suka ɗan ƙara tafiya sannan ya ƙara maimaita mata, sai kawai tace ina ruwanka ko fuskar kace yanda ka watsa min ahaka zanje gida innunawa maama kuma ince kayi min dukan tsiya, sai tayi ƙasa da murya yanda bazai ji taba tace kuma ince baka iya girki ba kayi  kwaɓa da jagwalgwalon ka ka turamin shi abaki dan mugunta,

Allah ya taimake ta baiji abun da tace ba da ya sassama ta amotar yadai ji tana magana amma baiji me take cewa ba,

girgiza kai kawai yayi yaci gaba da yafiyar sa kamar ma bazai bata amsa ba sai can dai yace "mu zuba mugani dan kinga bantaɓa ki ba ko tara ki nake wallahi na kamaki sai kin gwanmmace dama baki san wanda yassanni ba bare kuma ni harkiyi min abun da kikaga dama yanzu dai kinci sa'a na ɗaga miki ƙafa amma ki kiyayi haɗuwar nan gaba, am telling you that kiriƙe wannan, tundaga nan yayi shiru bai ƙara magana ba, duk da yana jinta tana ƙara wasu maganganun ƙasa ƙasa amma bai kula taba suka ci gaba da tafiya, har suka ƙaraso masarauta, suka shiga ciki loƙacin da suka dawo gida goma na safe saura, dan haka yana tsayawa da motar ko parking bai gama daidai tawa ta buɗe motar ta fita tare da kwasa aguje ta nufi part ɗin maama,

da kallo kawai yabita yana jinjina irin wannan halin nata na yarinta zallah, shima buɗewa yayi yabi bayanta cikin takun sa na kamala da kwarjini duk wanda ya haɗu dashi a hanya sai ya zube ƙasa ya gaida shi tare da yi masa kirari shikam baso yake ba dan haka babu wanda ya iya amsawa har ya ƙarasa cikin falon baiyi sallama ba ya faɗa ciki kansa tsaye, tundaga bakin ƙofa yake jiyo sautin kukan ta, yana shiga yaganta jikin ummy tana ta kuka,

Ummy ce tace zo nan tafa ɗa tana kallon sa ƙarasawa yayi kujerar gefen ta ya zauna, yana hararar Ameesha ta ƙasan ido,

Ummy tace "ka kyauta abun da kayi me kayi mata, kallon ummy yayi ya maƙe kafaɗa yace "babu"

Ummy tace ƙarya kake ba abun da kayi mata naga fuskar ta haka gashi takasa magana sai kuka take meye ma dalilin ka na ɗaukar ta katafi da ita kuma kabar wayoyin ka anan sannan kuma kaƙi dawowa gidan, kuma yanzu ana tambayarka zaka wani ce ba komai,

ransa ne ya fara ɓaci bare da ta kalli taɓa yace to idan nayi mata wani abun ai gata nan kitambaye ta mana, rashin dawowa kuma kinsan dai ana ruwa bazan taɓa fitowa a wannan loƙacin ba, yana faɗar ransa yana ƙara yi masa suya tunawa da halin da tasa ya shiga jiya har ruwa yayi masa duka awaje gashi kuma yazo gida ana neman yi masa faɗa ta ƙaicine ya ishe shi kawai ya miƙe daga gurin ya nufi ɗakin sa yana ji ummy tana yi masa magana amma yaƙi dakatawa saboda halin da yafara tsintar kansa komai ma zai iya faruwa idan bai nesa dasu ba,

Ameesha ƙasa ƙasa ta fara yi da kukan nata jin abun da yace saitaji yabata tausayi gashi bai faɗi gaskiyar abun da ya faru ba idan hakane ma ai ita ya rufawa asiri ashe su baya a son ruwa ita da kuma ga abun da tayi masa tasana din tama da tuni ya rasa ransa badan ta wannan tsohon ya taimake shi ta ba,

A hankali ta shiga goge hawayen ta sannan ta miƙe daga kan ummy tana shirin barin wajen ummy ta ƙara riƙo ta tana tambayar ta tagaya mata abun da yayi mata sai kawai itama tace mata ba komai, tana faɗar haka itama ta wuce ɗakin su ita da dadda,

Da kallon mamaki ummy ta shiga binta tana tunani me take nufi to da ba komai tasan dole yayi mata wani abun tunda har tashigo tana kuka, gashi kuma taƙi faɗa to meke faruwa ne dasu gaba ɗayan su dan ta fahimci dole akwai wani abun da yafaru tunda taga shima ransa a ɓace har tana masa magana ya shareta tasan ba ƙaramin abu bane zaisa shi yi mata haka, tana zaune agun tana tunane tunane maama ta shigo falon da sauri,

Miƙewa ummy tayi tana kallon ta tace maama lafiya dai ko an samu inda take,

cike da damuwa maama tace a'a wallahi babu inda ba aduba ba kuma me gadi yace baiga fitar taba, abun ya mugun ban mamaki wallahi,

ummy tace tofa gaskiya abun dole ayi mamaki kai kai abun yayi yafara yin yawa daga wannan matsalar ta lafa sai kuma wata ta kunno kai gaskiya da sake yakamata asan abunyi, ga waɗan can yaran ma sun shigo yanzu,

Maama tace sai yanzu suka dawo lafiya dai ko ba abun da yayi mata, me ya hanasu dawowa?

ummy ta ɗan kwaɓe fuska alamar damuwa atare da ita tace wallahi dai gasunan sun shigo shi ransa aɓace ita kuma tana kuka kuma duk na tambaye su me yafaru kowa yayi cemin ba komai sun shige sun barni a wajen,

Maama tace to Allah ya kyauta Allah yasadai lafiya, yanzu dai kar ki bari yarinyar nan tasan kakar ta bata nan abari zuwa anjima idan ba aganta ba sai asanar da ita, ki bata kulawa yanzu dai mai martaba ya ƙara sawa a bincika,

Da to ummy ta amsa mata sannan ta samu waje ta zauna tana me mamakin ɓatan dadda abu kamar almara lafiya suka tashi amma ace aɗan loƙaci ƙanƙani anrasa inda ta shiga sai kace allura,

Fita maama ta ƙarayi waje dan takasa zaune takasa tsaye,

Meer ne ya ƙaraso falon kusa da ummy yazo ya samu waje ya zauna murya can ƙasa yace ummy waye ya ɓata,

Ummy ta kalle sa cike da damuwa tace wallahi dadda ce muna zaune anan gaba ɗayan mu tace bari ta ɗan shiga cikin gidan shiru shiru muka ga bata dawo ba shine fa aka hau neman ta tode yanzu zancen da nake maka anne me ta anrasa acikin gidan nan kuma me gadi yace baiga fitar ta ba,

Ɗan taɓe baki yayi baice komai ba batare da yaji ɗigon damuwa aransa ba, ya daɗe agurin a zaune kafin daga baya ya tashi ya fice daga, cikin falon wajen masarautar ya fito tare da harɗe ƙafafun sa ya nade hannun sa akan ƙirjin sa tare da cije bakin sa leben ƙasa yana karkaɗa kai, ya daɗe agurin yana ta bin mutane gurin da kallo ɗaya bayan ɗaya, wani dogari ne yazo wucewa, sai ya ɗaga hannun ɗaya yayi masa alamar yazo,

Da sauri dogarin ya ƙaraso gurin sa tare da zuɓewa agun yana gaida shi sai ya ɗaga masa hannu, batare da ya kalle saba yace inason kasamo min kujera ka kawo min nan gurin sannan kacewa kowa da kowa yazo ina son ganin sa,

Da sauri ya miƙe yace angama ranka ya daɗe maganar ka kamar yankan raiza ce, ko mutanen garin kake son gani yanzu zaka gansu agaban ka.....

Wani wawan kallo ya watsa masa da yasa yayi saurin haɗeye maganar sa yajuya ba jimawa sai gashi ya kawo masa wata kujerar ƙarfe me kyau, sannan ya ƙara komawa kan kace me gurin yafara cika da mutane wasu kodan su gansa sazo musamman matan gidan, dan da yawa ya tafi da imanin su, wasu tun daga nesa suka mayar dashi tvn su har suka karaso gaba suka zauna,

Dai dai da me gadi ba abari ba saida aka kirasa kowa ya hallara agun, duk yawansu kuwa gurin ya yi tsit baka jin motsin komai kowa ya kama kansa gudun jawa kai bala'i dan sunji labarin sa baya ɗaukan raini, yanzu zai canza maka kamanni da duka,

duk abun da ake yaje kunnen papa dake part ɗin Ammah dan haka bai dakatar dashi ba duk abun da zai yi yasan bazaiyi ba daidai ba, ba papa kaɗai bama har su ummy da maama ba wanda baiji ba kuma babu wanda yayi yunƙurin da katar da shi ko tambayar sa dalilin sa na haɗa wannan taron, su Amra ma anfito kallo Azeema taje ta kirawo Ameesha suka samu waje daga ɗan gefe suka zauna suna kallon sa musamman ma mutuniyar tasa Amra da har ta manta da haushin nasa da take ji na jiya, kowa dai yana gurin yara da manya maza da mata, su waziri ne da matayayen su kaɗai basa gun, manyan dai gidan, sune basa gun,



Saida Meer yagama ƙare musu kallo gaba ɗayan su sannan ya gyara zama tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sannan yace tsofaffi su ware gefe tsofaffi mata da maza su ware gefe takan su zai fara, da sauri kowanne su ya tashi suka koma inda ta nuna musu kowanne zuciyar sa cike da zullumin abun da zaiyi musu suna tunanin laifin da suka aikata,

Dorinar hannun wani dogari yace abasa har guda biyu ya karɓa ya haɗa su waje guda,


Miƙewa tayi daga inda yake ya taka yake gaban tsofaffin ya shiga zagaye su yana karkaɗa bulalar a hannun sa sai ya yi kamar zai ɗagata ya sauke akan wani sai ya fasa, saida yagama ruɗasu duk suka sha jinin jikin su tunkan aje ko ina, ga mamakin su sai kawai ya shiga binsu da ita yana sauke ta akan kowa duk wanda ya samu zuba masa yake saidai ba wani dukan su yayi sosai ba ya dakata, sannan ya kalle su yace wannan ɗan tuni nayi muku ba wai hukunci ba, abun da nake so daku shine kafin inje indawo kowa yagama haɗo min labarin abun da yasani game da cikin gidan nan saboda kune manya nasan kundaɗe a cikin ta kuma kunsan komai dan haka nake gargaɗin kada wanda ya sake yayi min ƙarya kuma game da matar da ta ɓata ɗazuna nan shima inason jin wani abun daga gare ku, ina mai baku shawara mutum ya faɗi gaskiya ya zauna lafiya, yana gama faɗar haka ya juya gurin sauran, yace a rakani part ɗin waziri take kowa ya miƙe zai rakasa ya daka musu tsawa da cewa baku da hankali ne da zaku miƙe dukan ku, dukan su komawa sukayi suka zauna,

Sai ya nuna wani namiji me ɗan jiki yace "muje, da sauri ya miƙe yayi gaba shikuma yabi bayan sa, har yafara tafiya ya juyo yace "kar wanda yabar gurin nan kuma kar wanda yayi magana daga nan har naje na dawo, yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya.........✍️✍️

          ***********************

  
                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                     *The last of book 2*

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️


Sai ya nuna wani namiji me ɗan jiki yace "muje, da sauri ya miƙe yayi gaba shikuma yabi bayan sa, har yafara tafiya ya juyo yace "kar wanda yabar gurin nan kuma kar wanda yayi magana daga nan har naje na dawo, yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya........,

Har part ɗin suka ƙarasa loƙacin da suka ƙarasa bai wani jira cewar abada izinin shigaba ya canza fuska ya haɗe girar sama da ta ƙasa sannan ya danna kai ciki direct, yana shiga babu manya a falon sai wata yarinya tana ganin sa ta shiga wage baki tana nufowa inda yake ba yanda ya iya dole ya ɗan sasauta fuskar sa ya miƙa mata hannu ya riƙe nata sannan yajata suka zauna akan kujera surutu ta shiga yi masa yana biye mata wani abunma baya gane me take cewa saidaga baya cikin wasa yace mata mamanta tace masa tana ɗaki yace to jeki kira min ita, da gudu ta sauka daga kan kujerar ta nufi ɗakin mahaifiyar tata bata wani jima ba suka fito tare yarinyar akwai surutu,

mahaifiyar tata na fitowa tana ganin sa ta saki fuska fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙarasa kujerar gefen sa ta zauna tana kallon sa, shikam inbanda haɗe rai da ya ƙarayi babu wata alamar raha a fuskar sa, murya adake yace ina me gidan ki?

mamaki ne yakamata sosai amma kuma ta wani fanni sai ta ajiye mamakin ta saboda itama taji labarin sa ance baida mutunci amma bata san har su rashin mutuncin nasa yake ba, sai gashi yayi mata ko girman ta bai duba ba ba gaisuwa ba komai sai tambayar me gida, katse mata tunanin ta yayi tare da cewa bana maimaita magana,

Ɗan murmushin yaƙe tasaki tare da cewa ayya yi haƙuri baya nan amma nasan ba nisa yayi ba yana ɗayan part ɗin matar sa mu biyu ne,

Kafin ma ta idasa maganar ta ya miƙe tsaye sannan ya kalle ido cikin ido yace waya gaya miki mutuwar Sabreena, gaban ta taji ya faɗi jin sunan da ya amta itafa koda akace ta dawo bataje ta ganta ba ganin take kamar fatalwa zataje ta gani dan bata gama gasgata hakan ba shiyasa taƙi fita taje ta ganta,

Saurin daidaita nutsuwar ta tayi tare da kama kanta sannan ta shiga tunanin waye ma ya sanar da ita tabb nan ake yinta wallahi ta manta bazatace ga bakin da ta fara jin mutuwar nan ba,

"Kin matane in tuna miki ta tsinkayi muryar sa,

Ɗan kallon sa tayi da har zatace eh ta manta sai kuma loƙacin ya dawo mata a ƙwaƙwalwa ta tuna tabbas waziri ne yagaya matatake kwa ta sanar dashi, yana jin haka baice mata komai ba ya fice daga ciki, da kallon mamaki tabishi yanda taji labarin sa ashe ya wuce haka,karkata kai tayi aranta tana ƙissima abubuwa da dama sannan taja hannun yarinyar da take ta ƙoƙarin bin Meer da ko kulata bai ƙara yiba tunda suka fito har ya fice kuma yama manta da babanta, kamar tai kuka haka tabi ta suka koma ɗaki gaba ran matar waziri duk adagule babu daɗi....,

Meer na fita yasanar da ɗan rakiyar tasa inda yake son zuwa nan suka juya akalar tafiyar tasu zuwa ɗayan ɓangaren,

73 / 74