din,
momma dake saukowa daga step din stairs tun shigowarsu tana kallon su saboda itama tana falon abun da yafarune yasata tashi ta koma daki ba shiri yanzu kuma da taji komai yayi shiru yasata fitowa dan tambayar yan waje abun dake faruwa sai kuma tace karo dasu,
Qarasowa tayi tace rabu daita ya isa haka tafada tana kamo hannun ta tace zonan "yata rabu dasu daina kukan sai amaida ke gidan ko kai tadaga tare da dagowa tana kallon matar hakan nan taji bazata iyayiwa matar musuba sabosa kwarjinin da tayi mata sakin bossay tayi tare da komawa kusa da momma kamota momma tayi da kyau ta rungume ta lokaci guda Ameesha ta sauke ajiyar zuciya tare da tsayar da kukan da take bakajin kukanta saidai 'yar shashsheqar da takeyi kadan kadan momma bata saketaba har saida taji tayi lufff ajikin sannan ta dagota tana kallon ta yarinyar taji hakannan ta kwanta mata arai sai take ganin ta kamar su Amra,
"goge mata hawayen da suka bata mata fuska tayi sannan ta dawo da ita gefen ta tana kallon ta batayi mata magana ba sai ta maida dubanta ga su sam da duk sun tsaya suna kallon ikon Allah,
"wannan abunne ya tsora tata ko shettima ne yace eh wlh har suma ma tayi cike da alamun damuwa afuskarta tace ai dole ta suma wannan abu da babu dadin ji ai nima kaina nakusan suman dan na tsorata da wannan abun,
"Shettima yace momma ai inaga dama ba kya waje awaje yafi qara muna fitowa daga mota fa mukaji abun mamakin ma kiga yanda wajen yayi baki gaba daya abun abun maamaki wallahi,
"Momma tace nagani mana ai duhun gaba dayane dan har daki watakil ko gaba daya duniyar ce al amarin ubangiji kuma shikadai yabarwa kansa sanin manufar wannan abun,
"sam ne yace momma wanna fa a bun alamar tambaya dan iya cikin masarauta ne babu awaje yanzu na tambaya mukadai ne hakan tafaru damu,
da mamaki momma take kallon sa tace iya nan kuma? cike da tabbatarwa yace mata eh amma momma hakan be taba faruwa ba ko abaya cen? tace bai taba wallahi yau nafara jinsa amma bari intambayi papa inji ko hakan ya taba faruwa atarihin masarautar nan dan abun abun adubane,
"Sam yace gaskiya momma wanna fa babbar matsalace ni tunda nake bantaba jin irin wannan qarar ba qarin mamakin kuma ace gari da haske amma cikin nan yakoma duhu daga baya kuma yayi haske,
shettima ma yace nimade gaakiya abun ya tsorata ni harmafa da kururuwa kamar mutane kamar a horow film dannidai anan nataba jina makamancin irin wannan sai gashi kuma yafaru a gaske a gasken ma acikin gidan nana gaskiya da wani abun da yafaru acikin masarautar nan yakamata abincika,
momma tace maganar ka gaskiyace amma ai nasan tunda bamu kadai muka jiba nasan dole za ayi zama akan hakan tunda wannan ba abune da kasaba jiba gashi kuma kunce a iya nanne ni wallahi duk azatona gaba daya duniyar ce tayi haka,
hakade suka cigaba da tattaunawa akan wannan babban ala'amarin da yafaru dasu,
"Bossay dai baisaka musu baki ba tunda wannan abune na family be kanata ya tsoma musu baki ba duk da daman shi ransa fal yake da tambayoyin ganin wannan abun da baitaba gani ba yazata ko su sunsaba ko kuma sunsan dashi amma jin tattaunawar su yasamu amsar tambayoyin su saikawai yaja bakin sa yayi shiru bashida tacewa kawaidai yana mamakin hakan,
Ameesha ma bata saka nata ba amma de har yanzu a tsorace take jikin ta sai bari takeyi taciki so take ta tashi taje gurin bossay tace masa su tafi amma momma ta hanata damar hakan saboda suk maganar dasuke hannuta riqe yake da nata shiyasa baza ta iya tashiba kodan kwarjinin matar,
"bayan sungama maganar ne momma taqara dubansu "tace wanna fa daga ina tafada tana kallon ko qanwar wannance duk da shima de yau nafara ganinsa bansan ku tare ba taqarasa maganar tana nuna bossay sai lokacin bossay yadan sunkuyar dakai tare sa gaida ita amsawa tayi tare da cewa munhau wata hirar bamu gaisaba ko dan murmushi yayi kawai batare da yace komai ba,
"duk shiru sukayi saboda basusan ta inda zasu fara yimata bayani ba,
"saida taqara nanata musu tambayar sannan sam yace momma not enough time in mundawo zan miki bayani yanzu zata zauna daku zuwa dare zaizo su tafi tare,
"tace to shikenan Allah ya kaimu ai yanzuma su sweetheart zasu dawo daga makaranta taqarasa fada tana juyawa ta kalli Ameesha dake ta faman rarraba ido duk jinta take atakure takasa sakin jikin ta amma yanzu ta dena jin rawar da jikin ta yake mata,
tanaji tana gani sukayi sallama da momma suka fita jitake kamar ta bisu amma ba halin dole ta hakura ta zauna,
lokacin da suka fita,"cikin masarauta an cika dam da mutane kowa yafito Dan jin me yafaru yau amasarauta duk inda ka kalla mutanene a cure suna maida yanda akayi kowa nafadar albarka cin bakinsa,
ahaka suka ratsa ta suka shige mota duk da mutane sai kallon su suke suna Jira suji ko zasuce musu wani abun amma shiru har suka shiga motarsu suka fice suka barsu," sukuma suka cigaba daga inda suka tsaya,
"duk yanda momma taso Ameesha tasake da ita amma taqi saima qara nannadewa datakeyi ita kadai taqi sakin jiki da ita ko kallon tama batayi,
datagaji da ita taga bazata sake ba sai tayi tunanin ko saboda itane yasa taqi sakewa sai kawai tace ta tashi ba musu kwa tayi saurin tashi tsaye itma tashi tayi tare da kama hannun suka hau sama ta kaita dakin su amra again ta watakil tafi sakewa idan taga ita kadaice shiyasa ta kaita tare da cemata ta zauna bari akawo mata abun da zataci kafin su dawo kada mata kai kawai taga mata batare da tace komai ba guri tasamu ta zauna aqasan carpet dinsu bayan fitar momma tashi bin dakin da kallo dakin ya burgeta sosai ba wani tarkace Kuma wai Ahaka dakin Yara ne dama ace nata ne da tafi kowa farin ciki gadon su ta kalla sai ta tuna nasu dakin da katifar na kamar carpet din dakin nasu amma su ga qatuwar katifa gashi kuma harda gado tunawa tayi itakan tunds take inba gadon asibiti ba sai kuma ranar da ta kwana akan agidan su shettima dan jiyama qin kwana tayi akan gadon hajiya sai aqasa ta kwanta wai bazata iya kwana da itaba gado daya bayan ba ayi da itaba amma taqi haka aka rabu da ita ta kwana aqasa to bayan haka bata taba kwana akan gado ba Koda na qarfe ne hannun ta daga ta shafa gadon sai kawai ta saki murmushi komai ta tuna oho daya bayan daya taringa kallon komai na dakin tana cikin hakane wata tashigo dakin da try din abinci ahannuta tare da sakin fuska ta qaraso inda take tare da zama akusa da ita, kwanukan ta shiga budewa sannan ta tura mata gabanta kayan fruit ne aciki anyanyan ka mata su tace maza kici ba musu kwa domin kayan marmarin sun burgeta shiyasa ta ci Saida ta cinyesu tas sannan ta ture kwanan, kallon tayi cike da mamakin cinyewar da tayi,
"Aqaromiki? ta tambayeta "
kai ta girgiza mata tare da cewa a'a "
dan murmushi matar tayi sannan ta qara tura mata gasassun kaji da suka sha suya mai kyau har jajaja take tana shining indai ka ganta sai kaso kajita abakin ka yawun ka sai ya tsinke kamarde yanda na Ameesha yayi,
"aikam tana ganinsu tafara hadiyar yawu tare kaimata cafka ta danna abakin ta tafara yaga taunawa tashigo yi sobada dadin da yaziyarci kwanyar ta batasan likacin da ta lumshe Ido ba saboda tsabar dadi kunnen ta har motsawa saida sukai gashi daman tana mugun son kaza kaf duniya inka bata kaza to kabiyata(kamar de ni anan ammadai wannan bata burgeni ba😋) gashi kuma andade ba ahaduba shiyasa nanma ba kunya tazage taci abarta ta qoshi saidai Kuma duk sonta da ita takasa cinyeta dole ta hakura,
Itade tana zaune tana kallon ta har tagama ta kora da lemo mai sanyi sannan ta kwashe kwanikan tafita dasu bata dade ba taqara dawowa saboda momma tace ta zauna da ita dan haka ta dawo tacigaba da dan janta da hira dake matar tana da barkwanci harta fara sakewa da ita suna dan hira ammade ba sosai ba suna zaune agun aka turo qofar da qarfi,
tana shigowa ta jefar da school back dinta aqasa tare da cilli da takalmanta hamra ce ta shigo tana tafam fada tace kedai wallahi hankalin ki ragagge ne yanzu tagaban uban mutanen cen kishigo aguje kuma ahaka ba hijabi ko to wallahi sai nagayawa yaya,
lokacin datake wannan maganar Kam Amra harta shige toilet din taciki tace mata to ni ina ruwana da wasu mutanen ai ba hijabiba ko rigace babu ajikina sainabi ta gabansu wallahi ke angaya miki kashi qaryane to baya Jira idan yazo sai anyishi baya daga qafa saurafa kadan inyi awando ai wallahi da anqara second biyar ma sai nasakar muku shi amota shiru ta danyi da maganar tare da skin nishi sannan tace kai wallahi kashi duniya ne kinji yanda naji kamar ankwashe min wani mugun ciwon acikina...
"tsaki hamra taja tare da cewa banza qazama ko kunyar fadarsa haka gatsai babu ai da kindan sakaya kodan saboda bakuwa inma ni kinrainani tafada lokacin da take cire kayan jikinta yazamana daga ita sai riga da sket din na makaranta sannan ta qarasa kusa da Ameesha tana sakar mata murmushi duk da batasan ta ba kallon matar dakin tayi tace iya ladi wannan bakuwar fa daga ina? ta tambaya tana kallon Ameesha tana qara washe baki saboda ganinta sa'arta iya ladi na dariyar wautar Amra tace bakuwar momma ce yayyan kune suka zo da ita ayya Allah sarki sannu ko tafada tana mika mata hannu alamar sugaisa itama mika mata tayi fuskarta ba yabo ba fallasa asake saboda tunda suka shigo take kallon su taji sunburgeta tana son taga 'yan biyu especially na irin wadannan masu kamadin sosai......✍️✍️
[5/26, 9:09 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿37&38
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"my name is Hamra Abdullah Sameer nice to meet you,
Ameesha ce itama tace mata Khadijah Sameer zaki iya kirana da Ameesha.
"Wow nice name Ameesha taqara nanatawa tana qara wage baki dan taji dadin haduwa da ita gata sa'ar ta kallo daya taji jinin su yahadu cigaba tayi da surutu tana tambayar ta a unguwar da take gwanin sha 'awa inkagansu kai kace sun dade yanda tasakaki jikin ta itama haka ta saki jiki saidai ba yawan magana daga uhm sai uhm uhm,
Iya ladi dataga haka sai ta tashi tace to tunda kundawo ni bari intafi sai ku kula da ita bari innafiya sai insanar da momma kundawo ko kuma taga shigowar ku? taqarasa maganar tana kallon Hamra dake riqe da hannun Ameesha taƙi saki,
"a'a bamuhadu da itaba, tabata amsa.
"to shikenan zan sanar da ita ku kuma idan kunshirya sai kufito angama shirya muku abincin ku,
tana rufe baki Hamra "tace a'a iya ladi kawai kikawo mana nan muci da ƙawata. iya ladi"tace shikenan zan shiryo muku yanzunan kuyi sauri kuyi wanka to iya ladi yanzun nan zamu gama waccen banzarce taqi fitowa tundazu sai kace mecanza fata,
"iya ladi dariya kawai tayi tace Allah ya kyauta inkikayi hakuri yanzu zata fito ai basu gama maganar ba suna cikin yi ta turo qofar,
"maida dubansu sukayi ga Amra data fito daga banɗaki jikin ta sanye da towel da kyar take iya qafarta har ta qaraso kan gadon tana zuwa tafada batare da ta saka kayaba ruf da ciki tayi tana sauke numfashi jikin ta duk ya mutu saboda rudewar da cikin ta yayi hartakaita da yin gudawa shiyasa duk take jinta asama sama jikin yayi sanyi ba kuzari,
"murya qasa qasa kamar ba Amra ba tace bakuwa ina zuwa bari jikina yadawo daidai kibani 3 minutes zanzo ki ganni in ganki zamu gana,
"Shiru Ameesha tayi saidai tadanyi mata murmushi,
"Hamra ce tace Allah yaqara bake bakyajin magana ba kullum ciye ciye kici wannan kici wancen ba dole kitafaman shiga banɗaki banza me rubebben ciki Allah qara wallahi zantayi miki kuma sai nagayawa momma abun kikeyi a school,
"banza tayi mata tare da kawar da kanta gefe hartayi shiru sai kuma taji bazata iyaba sai kawai tayi tsaki tace malama ni yanzu bani da lokacin ki kibari nan da yan mintina sai inzo ki maimaita abun da kikace yanzu ta kaina nake,
"mtsww tsoron ki nake jine dazan kasa maimaita wa ne banza marar kunya kawai tafada tana kallon ta da ta juya mata baya bata tanka mata ba,
Miqewa tayi tace my qawa bari inyi wanka infito ko ta tashi karki kula wannan yarinyar zata rainaki dan raina mutane baya mata wuya,
" yar ƙaramar dariya Ameesha tayi sannan tace ai ta girmeni wane raini kuma saidai ma ai kice kar ba rainata,
"waya gaya miki kingirmeta inma baki girmeta ba to kin girmeta da hankali dan ita bata dashi domin jariri ma wataran yafita lissafi bare kuma ke da kike ahaka Nana san zaki girmeta,
" wallahi Hamra kifita daga idona inbaki daina cewa bani da hankali ba wallahi sai na nuna miki danyan haukan ina gaya miki banaso amma kinqi kidaina ko abun har yakai agaban mutane to wallahi Allah yabaki sa'a da rabon jikinki yayi tsami ,
rai abace Hamra tabar qoqarin cire rigarta datake tajuyo tana ta kalleta tace ni kike gayawa haka ni zaki daka to Bismillah dan halak ka fasa angaya miki din mahaukaciya kiyi abun da zaki inkin isa hannun ki yatabani idan kincika marar kunya mahaukaciya kawai tafada makawa bayanta harara qinkulata tayi hakan yasa taqara quluwa jitake kamar taje ta shaqota daga kan gadon tayi mata duka amma ba hali dan anhanasu dukan junansu idan kwa hakan tafaru ko kaine da gaskiya kai za ahukunta musamman ma da ta tuna yayansu yana nan shiyasa kawai tarabu da ita tare da yin kwafa ta wuce bathroom tana tafaman bambami itakaiadai,
"kulawa yabawa ancewa jaka adama cewar Amra tanatabe baki tare da yunqurawa ta tashi zaune,
"itade Ameesha na zaune ta zuba musu ido ita abun nasuma dariya yabata dan bataga abun fada ba anan amma ta lura Hamra taji haushi ita da gaske ta dau abun,
"bayan Amra ta tashi wajen wardrobe dinsu taje ta ɗauko doguwar riga marar nauyi tasaka sannan ta dawo gurin da Ameesha take zaune,
itama zama tayi daf da ita tace bakuwa ganin nazo nidai sunana Amra yayar waccen yarinyar da tashiga banɗaki,kallon ta Ameesha tayi tace kuna twins amma har akwai wani yaya da qanin,
Amra tace"eh mana amma ba rana ɗaya akahaifemu ni aka fara haifa ita kuma bayan kwana biyu aka haifeta kigakwa ai narigata zuwa duniya koda minti ɗaya na girme ta na girmeta bare kuma har kwana biyu,
"Wallahi ƙarya take miki rana ɗaya aka haifemu kuma ni nafara zuwa duniya kafin tazo cewar Hamra da ta fito daga wanka,
"harararta Amra tayi tace kinga rabu da ita ido ba muduba ai yasan kima kema ai kinga alamar nice babba ko? tafada tana kallon Ameesha,
"daga mata kai tayi tace eh naga alamar itace babba duk wanda yace shine to bashi bane kemeyasa kike son shekaru haka,
"Amra tace au hakama zakice to shikenan ba ruwana dake tunda kema ƙaryata ni zaki tafada tana ƙoƙarin miƙewa daga gurinbarin wajen kamota Ameesha tayi tace yi hakuri na yarda kece babba ni inkina soma sai inƙara miki da nawa shekarun dan murmushi Amra tayi sannan tace Allah ya taimake ki kinyarda amma da nikadai nasan zaman dazanyi dake saboda ƙaryatanin da kikayi to ai shikenan yanzude komai ya wuce tunda nayarda,
hamra dake jinsu tana saka kaya bata yanka musuba ta juyo tace ƙawata kema kirabu da ita kike kiyi wankan kafin akawo mana abincin ba musu ta ce to tare da miƙewa daga gurin Amra ce tayi saurin tashi tace zo kikarbi towel tafada tana nufar inda suke a sakale ɗaukowa tayi ta bata tana karba bata cire kayan agun ba ta tashiga ahaka da kayan jikinta bata daɗe ba tafito bayan tayi wankan sai ta maida kayan jikin ta tan fito duk suka bita da kallo Amra tace naga kin mayar da kayan da kika cire kinga fa waɗanda na ɗauko miki kallon kayan Ameesha tayi sannan ta qara kallon ta tace "a'a Nagode wannan is ok ai dazan fito nasaka dan hade rai tayi tace Allah sai kinsaka su,
hamra ce ta karaso wajen da take itama ɗauke da kaya ahannun ta tace dallacan ko zata sakama naki zata saka to nawa zata saka ungo dan Allah kicire waɗannan kisaka wannan Amra ce ta fusge kayan tace Allah nawa zata saka inbanda neman fada ma bani nafara bata nawa ba itama hamra tace nata za asaka itade ta zuba musu ido sunatayi kowa yaqi hakura suna cikin haka momma tashigo dakin tsayawa tayi tana kallon abun da sukeyi Amra ce tafara ganinta sai tace yauwa momma gwara da kika shigo kizo kiyiwa hamra magana tabari tasaka kayana mifa nafara bata nawa shine itama wai saidai tasaka nata kuma wallahi momma na rigata qaraaowa tayi sai ta karbi kayan gaba daya sai ta dauki ɗaya tabawa Ameesha tace saka wannan kuyi sauri nace baza akawo muku nan ba kufita muci gaba dayan mu,
"gwalo Amra tayiwa hamra saboda kayanta momma ta karba tabawa Ameesha,
ita kuma Hamra haushi taji ta hade rai daman tasan hakan zata faru tunda taga shigowar momma tasan shikenan momma na Amra zata bata,
Momma da ta lura da fushin da hamra take da harzata shareta sai kuma tafasa kawai sai tace ke kiyi hakuri tunda kece babba kuma ba ga ta nanba sai inroqi abarta tunda