bata basa amsaba saima fashewa da kuka datayi zaunar da ita tayi kan kuke ta suma sauran duk guri suka samu suka zauna suna jinyar jikin su,
itadai momy dariya take tayi aciki ciki bata bari ta fito ba daman abun da take gudar musu kenan suka ƙi ji,
sosai mom ta rarrashin ta ta samu ta ɗan tsagaita kukan sannan mom ta shiga tambayar su gaba ɗayan su amma har yanzu babu wanda ya iya bata amsa,
momy ce ta miƙe tace mom bari inbaki labarin abun da yafaru nan ta zayyano mata abun da yafaru tundaga farko har ƙarshe sannan ta ɗora da cewa mom wallahi yayi musu da sauƙi saida nagaya musu suka ƙi ji abun da yayi min babu wanda aka taɓa yiwa haka su ai amutun ce ya dake su nifa saida yayi min tsirara haihuwar uwata sannan ya dake ni kuma ya koro ni ahaka bainar jama'a ahaka,
babu wanda baiyi mamakin abun da ta faɗa mom tace ɗan gidan uban waye shi agarin nan a ina yake waye uban sa,
momy tace mom ba ɗan garin nan bane a Abuja yake ni banma san me yakawo sa nan ba,
mom ta miƙe tsaye tana zagaya falon tace aikwa ya taɓo tsuliyar dodo sai yasan bai daki banza ba dan bazan barsa ba koɗan gidan uban waye agarin nan sai na nemosa akan me zaisa hannu yadakar min ƴa to wallahi daga kanta bazai ƙara dukan wata ba tunda shi jaki ne da zai ringa kama ƴaƴan mutane yadaka kuma yazauna lafiya to yo ya taɓo me gata dan sai an rama mata abun da yayi mata wallahi bai daki banza ba sai yayi da nasanin dukan ta, tana magana tana faman huci wai ita ala dole taji haushi an dakar ƴa (to masu ƴa kizo wajena yaseen zan baki address ɗin sa idan kanki wuta yake nasa gobara yake hajiya halima shirgigeya)
momy najin maganganun da take aranta tace sai kin dawo Allah yabaki Sa'a wallahi bazana hanaki zuwa ba afili kuma tace wallahi mom yakamata dai anuna masa ya daki ƴar gidan gata yasan ko wa ya daka arama mata a wulaƙan tasa ya gane kuren sa,
tace "kar ki damu ai harke sai na ramawa yanda yayi miki tsirara sai anyi masa haka yaji inda daɗi sainasa ya kusan zagaye garin nan babu kaya ajikin sa sai anyi masa dukan mutuwa yanda sai yadawo jin tsoron duk wata mace bama kuba ke har uwar sama sai tagane kuren ta tunda yanayi bata dakatar dashi ba tabari yake wulaƙan ta ƴaƴan mutane sai sun gane kuren su gaba ɗaya sai na koya musu hankali......
sosai momy ta nuna jin daɗin ta harda murmushi amma fa murmushin da biyu take na mugun tane kawai take mata dan harta hasko yanda za ayi facali da ita da wannan ƙaton jikin nata, cigaba tayi da koɗata tana zugata akan kar ta rabu dashi gobe gobe zasu koma gurin ma zasu fara binciken inda yake za anemo har gidan da ya sauka,
da waɗannan maganganun suka sa su Rasheeda suka ɗanji dama dama har suka tashi da ƙwarin gwiwar su da taimakon su momy duk suka tashi suka kaisu ɗaki gaba ɗayan su.......✍️✍️
_🤣Woo gobe fa kowa ya shirya zamu taya su mom ɗin Rasheeda neman meer zamu ɗauki fansa🤣🤣🤣_
_gashi kuma gobe zamu tafi masarauta kai gobe dai da kallo da yawa_
I can't wait to see 💃💃💃💃💃💃
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 93
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
*_WASHE GARI_*
tunda sukayi sallar asuba babu wanda ya koma amma basu fito ba saida gari yafara yin haske sannan ummy ta fito tayi musu abun da zasu karya wajejen ƙarfe ta tara ta gama shirya musu komai akan dinning ɗin sannan taje tafara kiran maama tafito sannan ta haura sama taje ta kirawo meer da ƙyar ya fito acewar sa shi ta ƙoshi bayajin yunwa saida tayi masa dole sannan ya yarda ya fito,
saida taga fitowar sa sannan ta nufi ɗakin da Ameesha take, tana zuwa ta ƙwanƙwasa mata ƙofar tare da kiran ta tace zo kibuɗe ni kaɗai ce,
da sanɗa Ameesha tazo wajen ƙofar sannan tace Ummy dan Allah baya nan yana ɗakin sa dai ko?
"Eh, Ummu tace mata sannan ta buɗai ƙofar ta ɗan leƙo ta tabbatar da ita kaɗai sannan ta karasa buɗe ƙofar gaba ɗaya,
ummy ta kalle ta da towel aji kinta sai tace mata "yanaga baki saka kaya ba ko bakiyi wanka bane naganki ahaka,
ummy nayi kayan da zancanza ai suna motar banɗakko ba shi yasa danayi wankan na zauna ahaka saboda daman nifa ayau bazan fita ba ko abinci ma saidai inci anan indai ba barin gidan nan yayi ba bani fitowa wallahi,
ɗan murmushi ummy tayi sannan tace "da kinsan kina jin tsoron sa har haka shine kika cije sa,
bari insashi ya ɗauko miki kayan kisaka kifito babu abun da zai miki tunda har aka kwana baimiki komai ba to wataƙil ya manta ma shi bazai miki komai kidaina ɓuya ki kwantar da hankalin ki kifito muci abinci ke kaɗai muke jira kiyi sauri yanzu zan saka shi yakawo miki ,
a'a ummy wallahi indai shine bazan yarda in buɗe kofar nan ba nidai kawai dan Allah ummy akawo min abinci na nan ba sai na fito ba,
Ummy tace "Allah kar kidamu yariga da ya manta saboda shi baida riƙo kwata kwata indai kayi masa abu aloƙacin zai rama idan kwa ya wuce bai ramaba to ya barsa kenan,
dan haka kima daina wannan tunani bari inje idan ya ɗauko su amota sai ni in kawo miki nan sai kisaka mufita tare ina tare dake babu abun da zaimiki,
Ameesha tace "yauwa ummy to gwanda haka dai kikawo min da kanki sai mufata ɗin,
Ummu tace to shikenan bari inje sannan ta juya ita kuma ta koma ɗakin, ta rufe ƙofar bata saka muƙulli ba amma,
" tunda meer ya fito kuwa yake baza ido yaga ta inda yarinyar nan zata fito dan yayi alƙawarin sai ya rama abun da tayi masa tunjiya abun ya tsaya masa arai inbai rama ba bazai taɓa jin zuciyar sa daidai ba,
yana fitowa maama ta kalle sa sarai tagane kallon da yake yi dan haka tayi saurin kiran shi ta nuna masa gefen ta yazo ya zauna nan tafara jansa da hira suka gaisa da ita sannan ya juya ya gaida Abu banza Abu yayi dashi bai amsa ba dan har yanzu shima baisauko ba haushin shi yake jiki,
shikam ko ajikin sa sai ya ɗauko wayar sama yafara dannawa,
maama da ta lura da haka sai ta ɗan taɓasa da hannu yana ɗagowa ta nuna masa abu sa ido alamar abun da yayi bai kyauta ba shiru yayi baice komai ba,
ƙasa ƙasa tace kabashi haƙuri kayi laifi kallon ta yayi da mamaki haƙurin me kuma zai basa alhalin bai masa komai ba rashin amsa gaisuwar sa kuma ganin dama yayi shiyasa yaƙi amsawa kuma shidai yariga ya fita tunda ya gaidashi shine baiga damar amsawa ba to akan me zai basa haƙuri kuma,
girgiza masa kai tayi tace kayi abun da nace maka kawai inkanaso muzauna lafiya,
saida ya ɗauki loƙaci yana tunani ta inda zai fara bashi haƙuri batare da yayi masa komai ba saida ta ƙara taɓasa sannan dai ya daure batare da ya kalli inda Abu ɗin yake ba yace sorry shima can ƙasa ƙasa ya faɗa saboda bada son ransa yayi ba,
Abu yajisa amma yanzuma sai ya nuna baima san sunayi ba daga shi har maama,
maama zata ƙara magana kenan ummy ta ƙaraso wajen tana ɗan murmushi tace maama mutuniyar kifa taƙi fitowa saida ƙyar ta yarda zata fito amma ta manta kayan ta amota jiya tsokana tahanata ɗauko su saidai hayatee yaje ya ɗauko mata saboda har ta riga ta cire waɗan can tayi wanka nasauyawa take buƙata kawai ta fito,
dariya maama tayi tace ai nasan daman da ƙyar zata fito ai ya haƙura babu abun da zaiyi mata je ka ɗauko mata ka kai mata,
da sauri ummy tace a'a maama tace saidai ya ɗauko nikuma sai inkai mata idan tasaka sai mufito atare amma idan ba hakaba bazata fito ba dan haka yaje ya ɗauko yakawo min sai in kai mata,
Maama tace "to Shikenan hakan ma yayi yaje ya ɗauko ɗin yi sauri ka ɗauko danni ƴaƴan hanjina sun fara motsawa yunwa nake ji,
da farko ƙin yarda ya tashi yayi saboda yana ganin ta gama rainasa shine ma zaije ya ɗauko mata kayan da zata saka tabb tayi kaɗan kuwa saidaga baya kuma ko me ya tuna oho sai ya tashi ya nufi hanyar fita,
umm 87y kuma sai tafara saving ɗin maama ta zuba mata duk abun da take buƙata sannan ta koma wajen Abu da yaƙi kula kowa agun sai faman haɗe rai yake,
zuba mishi ta shigayi,
Meer na fita yaje ya buɗe motar yashiga duddubawa yagano jakar kayan nata ya ɗauko yana wani ya mutsa fuska kamar ya taɓa kashi ahaka ya riƙo jakar har ya ƙaraso wajen falon dake da ɗan tazara tsakanin falon da wajen dinning ɗin sai ya kalle su ya tabbatar da hankalin su baya wajen sai kawai yabi tagefe ya nufi ɗakin da yake da tabbacin tana ciki har yaƙarasa bakin ƙofar babu wanda yaga shigowar sa,
tunani ya ƙwanƙwa sa yayi sai kuma yafasa ya gwada murɗa hannun ƙofar yaji ko ba muƙilli aikam yana murɗawa yaji ta buɗu turawa yayi ya shiga tare da saka ƙafar sa guɗaya aciki sai kuma ya shiga gaba ɗayan sa dake ƙofar bata da ƙara kwata kwata bataji shigowar saba har ya rufe ƙofar bataji ba tana kwance akan gadon ɗakin tayi rigingine tanajiran shigowar ummy,
tsaye yayi a bakin ƙofar ya jingina jikin sa da ita yana kallon ta ganin har yanzu batasan da shigowar sa ba, sai ya ɗaga jakar hannun sa ya wulla mata ajiki azabure ta tashi zaune bata gama tsorata ba saida tayi ido huɗu dashi azubure ta miƙe tsaye tana muƙewa bata tsaya wata wataba ta kwasa aguje tayi hanyar banɗaki kafin yayi yunƙurin binta harta shige ciki ta saka muƙulli,
jinjina kai kawai yayi tare da yin ƙwafa yafice daga ɗakin dan shi ba ƙaramin yaro bane bazai biye mata suna guje guje ba zai rabu da ita har sai ranar da zatakawo kanta har inda yake zata gane kuren ta,
yana fita yasamu waje ya zauna inda ya tashi maama tace ina kayan,
"nakai mata kawai yace da ita sannan ya ɗauki tea 🍵 ɗin da ummy ta haɗa masa yafara sha,
kallon kallo ummy da maama sukayiwa juna ba wanda yace komai sai kawai ummy ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin tana zuwa taga ƙofar abuɗe shiga tayi taga ɗakin wayam ba kowa aciki kiran ta tashi ga yi, tana ƙarasa shiga cikin tsakiyar ɗakin,
daga cikin bathroom ɗn Ameesha ta amsa tare da buɗe ƙofar ta leƙo saida taga ita kaɗai ce sannan ta fito daga ciki tace ummy shine kika aiko sa badan nayi hanzarin ganin saba da tuni yayi min dukan mutuwa,
ummy tace "wallahi banma san yazo haka nace kawai yakawo min in kawo miki shine ya taho dan bansan ma loƙacin da yashigo ba har yashigo nan baidai yi miki komai ba ko,
"eh ummy Allah ya taimakeni bai kamani ba ai,
to yanzu yi sauri kisaka muje sai ɓata mana loƙaci kike tun ɗazu ke muke jira,
da ƙyar dai ta yarda ta shirya sannan suka fito tare, tana ta ɓuya abayan ummy har suka ƙaraso gurin can kusa da abu ta zauna tunda tasan idan tana kusa dashi ba lalle yayi mata wani abun ba,
saida ta zauna sannan duk ta gaida su amma bata gaida meer ba kuma babu wanda yayi mata magana dan basu lura bama amma shi yana sane da ƙin gaidashi ɗin da tayi,
ba ɓata loƙaci suka shiga cin abinci batare da kowa ya ƙara magana ba,
suna cikin ci wayar ummy tayi kara dubawa tayi sai taga number Ammi ce da ta karɓa jiya take kiran ra da sauri ta ɗaga tare da saka wayar a speaker tace hello daga can ma Ammi tace hello ina kwana dafatan kun tashi lafiya,
ummy ta amsa mata da lafiya lau,
sannan Ammi tace daman yanzu yaron gidan masarautar nan ya kira yace baida Number ku yace ku hanzarta kushir ya nan da ƙarfe goma za ayi wani taro acan kuma yanaso ayi agabanku saboda ansamu wata gagarumar matsala acan kuma yanaso ayi komai agaban ku dan haka yace kuyi gaggawar halattar taron,
ummy ta ɗago ta kalli maama sannan tace to shikenan gamunan sai kuma kushirya muna zuwa sai mu wuce yanzu zamu fito,
Ammi tace "to shikenan sai kun ƙaraso, daga nan sukayi sallama,
maama tace tofa me kuma yafaru haka da sassafe za ayi taro, ummy tace nimadai nayi mamakin hakan amma dai muyi sauri muje sai muji abun dake faruwa,
nandai sukayi shiru sukayi sauri suka ƙarasa cin abincin daman kowa yayi wanka dan haka basu wani ɓata loƙaci ba suka gama shiryawa suka fita daga gidan,
Meer da Abu agaba sai su maama abaya,
yanzudai bayi wannan mahaukacin gudun ba yana tafiya ahankali har suka iso gidan su bossay,
loƙacin da suka shiga suma duk sungama shiryawa su kaɗai suke jira,
Hajiyar shettima ma da shi kansa shettiman duk suna cikin gidan sun daɗe da zuwa saboda su zasuyi musu jagoran ci zuwa cikin gidan batare sa an tsayar dasu tamabayar su waye ba ko daga ina suke,
saboda kiran da sam yake tayi musu yasa basu wani tsaya gaisuwa mai yawa ba suka ƙara fitowa gaba ɗayan su harda dadyn bossay sai Ammi da bossay shettiman da hajiyar sa sai kuma dadda gaba ɗayan sudai haka sukayi mota mota wajen motoci haɗu sukayi suka nufi masarautar.........,
*******************************
________*masarauta*_________
:A daren jiya dai babu wanda yayi bacci me daɗi kowa ya kwana zuciyar sa babu daɗi wasuma basu samun damar rintsawa ba yanda suka ga rana haka suka ga dare kowa na tunanin me zai faru ba iya waɗan da abun ya shafa ba har sauran ma'aikatan gidan da akayi komai agaban idon su tun adaren kuwa labari ya karaɗe lungu da saƙon cikin masarautar babu wanda baiji ba dan magana ma harta fara fita waje kan cewar sarkin gari ba ɗan masarauta bane baida alaƙama da masarauta haka dai sukai ta yamaɗiɗi tare da ƙara gishiri da magi akan maganar dan tafi armashi saboda ba iya abun da yafarau ake faɗa ba sai anyi ƙari,
aranar yau kuma papa shima yadawo cikin hayyacin sa kuma shima Ammah tagaya masa abun dake faruwa ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba dan haka dan da nan yasa akafara sanar da duk wani wanda yake da alaƙa da masarauta akan ahallara ƙarfe goma daidai acikin fadar da kuma ƴan cikin fadar manya manya amma banda yara ƴan ƙananu iya iyaye da samarin gidan waɗanda suka mallaki hankalin kansu irin su sam kenan.....,
tun wajen ƙarfe tara akafara hallara acikin fada ɗaiɗai kune basu zoba kawai,
*_10:am_*
kowa ya hallara daga ciki sarki Salahudden ne karshen shigowa shi da Azeema suka shigo normal kayane ajikin sa dan ko hula baisakaba haka yataho kamar bashi ba tunda ya shigo papa dake zaune kan kujera ya ke binsa da kallo tunda ga sama har ƙasa ya kafe sa da ido bashi kaɗai ba sauran mutanen gurin ma duk kallon sa akeyi can ƙasa daga gefe babu kowa agun nan ya nufa ya zai zauna aƙasa papa yayi saurin dakatar dashi tare da cewa me yasa zaka zauna aƙasa kuma ina kayanka ka saka waɗannan kayan kuma ko hula baka saka ba akan wane dalili?
sunkuyar da kansa yayi tare da cewa aimin afuwa amma bazan iya kara saka kayan ba saboda badani yadace ba kujera ma kuma nagama zamanta koda ace hakan ba gaskiya bane bare ma kuma na tabbatar da bani da alaƙa da ita tuba nake mai martaba amma bazan iya bin umarnin ka ba akan sai nahau kujera koma nasaka wani abu da ya shafi sarauta yana gama faɗar haka ya zauna a inda yayi niya tun farko Azeema agefen sa ya zauna tare da hade gwiwowin sa ya kifa kansa akai bai ƙara kallon kowa ba har mahaifin sa dake gurin,
fulani kam yau itama ba kan kujera tana ƙasa kamar yanda kowa yake mutum biyu ne kawai akan kujera daga papa sai Ammah amma kowa na ƙasa, kujerar sarki kuma tana gurin itakaɗai ba kowa akanta,
wayar Azeema ce tayi ringing da sauri tasaka ta a silent tare da miƙewa tsaye ɗan ɗaga murya tayi tace agafar ceni zanje in shigo da mamana sun ƙaraso,
Ammah ce tace "to ki hanzarta ana ta ƙara ɓata loƙaci kowa ya hallara daman su muke jira,
da sauri ta fita daga cikin fadar,
papa ne yace "wai banga gwaggo ba ko ba asanar da itaba ne najita shiru har yanzu ko sai an ƙara kiranta,
Ammah tace " inagadai ko wani abunne ya riƙeta Ammar je ka kaƙara kiran ta,
da sauri ya miƙe tare da cewa to sannan ya fita,
yanama fita suka haɗu da ita tana daf da shigowa dan haka sai suka dawo atare suka shiga suna shiga ko sallama gwaggo batayi ba tace "nashiga uku ni ƴar nan me nake gani haka daman abun da ake faɗa min gaskiya ne suwa nake gani aƙasa sarki naga kanka haka ko hula kuma aƙasa azaune lalacewae har takai haka ina munafukar take hatsabibiyar almura amma dai