yake kuma yana so ya kalle sa dan yayi masa gargaɗi amma yaƙi bari su haɗa ido da yagama maganar ma sai ya matsa daga kusa dashi,
"yi haƙuri yanzu zamu tafi cewar maama..
ina jinka kai ɗan inane ko ɗan nan garin abujar ne,
"A'a ba anan nake ba ni ɗan garin kano ne,
kano wacce unguwa? tasake jefa masa tambaya gabaɗayan su babu wanda beyi mamakin jin irin tambayoyin da take masa ba,
shiru yayi kafin daga bisani ya daure yace mata unguwar laraba cikin masarautar sarki Salahuddenu Muhammad sameer anan nake ko zaki sa akamani ne to ga address ɗin nan nabaki idan kinshiga cikin kano duk wanda kika tambaya gidan sarki Salahuddenu Muhammad sameer za akaiki,
wani irin abu taji yataso mata tundaga ƙafarta har tsakiyar kanta gaba ɗaya jikin yaɗau ɓari taciki loƙaci guda taji wasu zafafan hawaye nasan zubo mata tayi saurin tare su ta mayar da su gudun kar su zuba agaban su,
ɗan murmushin yaƙe ta ƙaƙaro tayi tana so tayi magana amma tana tsoron idan ta buɗi baki tayi magana hawayen da take riƙewa zasu iya zubowa,
juyawa tayi yazamana ta juya musu baya basa kallon fuskarta cikin rawar murya ta buɗi baki da ƙyar tace idan kaje ka gaida Muhammad sameer ɗin tana kaiwa nan tabar gurin da sauri saboda kukan da taji yataho mata gadan gadan.... tana zuwa ta buɗe motar ta shiga baya,
duk mutuwar tsaye sukayi agun kowa na mamakin halin da suka ga ta shiga kowa da kalar tunanin da yakeyi su sam suna tunanin to tasan kakan sane itaɗin wacece saboda wanda tace agaida bama Sarkin ba baban sarkin kakansu kenen tabbas kwa yabi bayanta yaji ko itaɗin wacece?
sukuma su ummy suna tunanin meyasa tayi hakan kode sune ƴan uwannata datake nema dole akwai wani abu da tasani akan wanann yaron da kuma labarin inda yaron yagaya mata,
duk a ƴan minti na sukayi wannan tunani saboda yanda tayinne loƙaci ɗaya babu wanda yataɓa kawo hakan zai faru,
atare suka bi bayanta gaba ɗaya suna zuwa suka shiga tambayar me yasata kuka kawai hawayen ta ta goge sannan ta girgiza musu da ƙyar tace mutafi dan Allah tafaɗa batare da alamar wasa a fuskar ta ba yanda tayi maganar dole yasaka duk wanda yaji yayi abun da tafaɗa batare da sun ƙara tanka mata ba kowa ya shiga inda yake suka rufe ƙofar, daidai loƙacin kuma sam yaƙaraso gaban motar tasu suna ganin sa tacikin glass ɗin amma sai maama tace muje kawai karku saurare sa daman meer haushin shi yake ji dan haka yatayar da motar yajata da ƙarfi badan sam yayi saurin matsawa ba da ta kansa zaibi.... tsaye yayi agun yakasa motsawa yana faman bin motar da kallo har ta ɓace ma ganin sa...
sannan yadawo hankalin sa dasauri yakoma wajen su shettima da suka zama ƴan kallo agun,
da sauri ya buɗe gaban motar yashiga sannan yace kuyi sauri binsu zamuyi kar mubari su ɓace mana da sauri suma suka shiga shettima nacewa amma kasan zamu bisun ka tsaya har suka bace bai saurare sa ba suna shiga yana motar a 360 yabi inda yaga sunyi addu'a yake kawai Allah yasa yakamosu to mumade zamu tayaka da addu'ar dan kamosu saidai addu'ar amma da kamar wuya.......✍️✍️✍️✍️
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
[6/20, 7:46 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️61&62
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
suna shiga yaja motar a 360 yabi inda yaga sunyi addu'a yake kawai Allah yasa yakamosu to mumade zamu tayaka da addu'ar dan kamosu saidai addu'ar amma da kamar wuya.......
anan muka tsaya yanzu kuwa zamu ci gaba sunana Ahmad isah shirin nan dakan ilimantar ya nishaɗantar da masu sauraro😂😂😂😂😂😂😜raidangi goro sabon shirinmu na radio📻 (ina masu jin rai dangin goro ga wata Ahmad isah ɗin💃💃😜😂)
"sosai yake kwarara gudu dan ganin yakamo su sai yanzu yake tajin haushin tsayiwar da yayi da yabisu tun aloƙacin da basu ɓace masa amma yanzu da wuya ya tadda su sai faman sakin tsaki yake yana dukan stirring ɗin yana cigaba da gudu dan bai karaya ba tundade yasan gurin babu kwana dole miƙewa sukayi dan haka shima ya miƙeɗin yayi wajen 15 minutes yana tafiya be gansuba dan sun riga da sunyi masa nisa,
Shettima ya dubesa yace yakamata mu haƙura dan ba ganin su zamuyi dan naga muna shirin barin garin ma gaba ɗaya gwara mukoma muyi abun da ya kawo mu inyaso sai mufara nemansu anan tunda daga gani kamar anan suke da zama kaga sai mu faɗaɗa bincike ko Allah zaisa da rabon muƙara haɗuwa dan ko ni zanso muƙara haɗuwa da matar nan dan ina ɗan hasaso wani abu game da ita amma kuma bansan meyasa tayi mana hakaba indai hartasan inda aka bata labari harda cewa kuma agaida papa daga nan kuma tayi tafiyar ta batare da tagaya mana a inda ta sanshiba gashi kuma bisa ga dukkan alamu inajin ko akwai abun da ya taɓa haɗata da papa ko kuma gidan ku tunda in ka lura fa tunda kagaya mata inda kake yanayin ta ya canza sannan kuma saida ta juya mana baya kafin tafaɗi agaidashi ɗin cikin rawar murya,
shide duk wannan jawabin da yake masa jinsa kawai yake dan baida niyar juyawa shima tunanin sa yana wajen dan ba komai ma yakeji ba, shikaɗai kawai yake surutun sa,
bossay dake baya duk yanajin abun da Shettiman yake cewa saidai shima abun da yatsaya masa arai yasa yakasa tanka masa har saida yaji yayi shiru sannan shima ya buɗi baki domin fito abun dake ransa tun tsayiwarsu agun,
""nikam wai dan Allah bakuga abun da nagani ba ko nikaɗai nake ganin hakan? cewar bossay,
shettima ne yaɗan juyo ya kalle sa sannan yace me kakegani?
wallahi ni wannan tsohuwar matar nan tunda tafito nifa ido na nakanta nake kallon ta sai kuma yayi shiru,
"me tayi ?" cewar Shettima yafaɗa tare da juyowa gabaɗayan sa yana kallon bossay danjin me zaice,
"wallahi sai naga kamar suna kama da baby kai bama kamar ba sunyi kama sosai kodanni nafi zama da ita amma akwai abubuwan da tayi da yawa agun sai inga kamar baby ce ta girma,
cike da ɗan rashin fahimtar wacce yake nufi yace wake nan wace kuma baby dan baikawo kowa komai ba da yace masa baby sai yasa yatafi tunanin wace baby shiyasa baigane me yake nufi ba,
"AMEESHA!!" mana
wani wawan burki sam yaja sakamakon jin numfashinsa nasarƙewa stirring ɗin nashirin barin hannun sa shiyasa yayi saurin taka burki da gaba ɗayan su saida sukayi gaba suka dawo dan Shettima dake gaban motar sai da kansa yaɗan bugu da jikin motar,
hakan yahanasa bawa bossay amsar maganar da yayi,
har suna haɗa baki wajen tambayar sa lafiya yayi irin wannan taka burkin yana shirin kaisu lahira ,
jiyayi yawun bakin sa ya daskare gaba ɗaya yana son yin magana amma ya kasa sai zazzare ido kawai yake yana kallon Shettima dake gefen sa,
kai lafiyar ka ƙalau kwa? cewar Shettima,
bossay ne yafara fahimtar halin da yashiga saboda abun da yafaɗa ne yasashi shiga wannan yanayin tunda inzai tuna yana faɗar sunan baby ya taka wannan burkin, ruwan gora dake gefen sa ya ɗauka ya miƙawa sam tare da buɗe masa murfin robar sannan yabasa,
ba ɓata loƙaci kuwa sam ya karɓe saboda daman shi yake buƙata ahalin yanzu yana karɓa ya kafa kai bai sauke ba saida ya shanye duka sannan ya sauke robar numfashi ya shiga saukewa saida ya tabbatar da nutsuwar sa ta dawo jikin sa yadawo hayyacin sa,....
sannu suka shiga yi masa batare da ya amsa ba yace yarinyar da nakai gidan mu ita kake magana akai ko yafaɗa yana kallon bossay,
bossay yace eh ita wallahi ni sosai naga suna min kama ko ido nane,
shettima yayi saurin cewa wallahi ba idon ka bane saida kafaɗa kuma nake ta hango kamannin su,
da ƙarfi sam yace no wonder wallahi tunda naganta nima kawai nake mata kallon sani amma na rasa a inda nasan ta tabbas suna kama yazama dole mune mo matar nan duk inda ta shiga shiru yayi na wasu ƴan daƙiƙu yana nazari.... kafin daga bisani ya gyara zama yana fuskantar su da kyau sannan yace to amma me yahaɗa yarinyar da wannan matar da kana ganin tama kasan ba ƴar nan bace ita dan ko dangi ma bazaiyiyu su haɗa ba saboda kowa inda ya fito da ban to amma abun da yaban mamaki shine wannan maganar da matar nan tayi ta in gaida papa amaganar ta kuma da yanayin ta ya nuna tasanshi to taya tasanshi a ina tasanshi me yakaita kano kuma ni da ace bata nuna ko wata alama ba game da papa to da kamannin ta da yarinyar nan bazai dame niba saboda ana haka daman some times kana iya haɗuwa da irin hakan kaga wani yana kama da wani kuma batare da sun haɗa dangi ba to amma wannan maganar da tayi yasa gaba ɗaya na shiga ruɗani nama rasa wane kallar tunani zanyi akai amma koma meye ina zuwa zan tambayi papa sannan in faɗa masa saƙon ta sai inkwatan ta masa kammanin ta ko zai ganeta ta haka kawai zai sa tunanin ya tsaya waje guda,
shettima yace hakane nima wallahi lamarin yaban mamaki yakamata musan ko wacece wanann matar dan amsoshin tambayoyin mu suna gurin ta ita zata warware mana tunanin mu tagaya mana inda tasan papa da kuma dalilin da yasa ta canza ana batar sunan sa wannan shikaɗai muke buƙata dan maganar kamanni da Ameesha ma a ajiye shi gefe kamace kawai daman hakan tana faruwa aduniya kowa akwai me kamannin sa aduniya dan haka wannan ba abun damuwa bane,
caraf bossay yakarbe shi da cewa a'a wallahi wannan ba kamace kawai ba nidai anawa ganin kamar da akwai alaƙar jini a tsakanin su dan wannan kamanni yayi yawa har maganar kusan iri ɗayace da yanayin karya harshen su nifa tunda muka fito a kanta nake saida nagana ƙare mata kallo tass tunda ga sama har ƙasa kuma in baku manta ba a labarin da dadda ta bamu ai ba asan inda dangin mahaifin ta suke ba kunga kwa ai a ko ina ma zamu iya haɗuwa danginta mahaifin ta to nide aganina akwai dangantaka atsakanin su me ƙarfi ma kuwa,
"eh maganar ka kusan gaskiya ce saidai kuma inde suna da alaƙa da wannan yarinyar to kuma taya akai tasan papa kuma har yanayin ta ya canza ni gaskiya bana tunanin suna da alaƙa kawaide kasan papa ba anan yayi karatu ba dan yataɓa bani labarin loƙacin da nima aka fita dani karatu naƙi yarda yake gaya min shima ai ba anan yayi karatu acan yafi to wataƙil zai iyayiyuwa ko sunyi makaran ta ɗaya dashi dan naga gaskiya wannan ba ƴar nan bace ko kuma de wani abun ya taɓa shiga tsakanin su shiyasa da taji sunan yasa ta shiga damuwa,
shettima ma yace zancen kenan nima nafi tunani ko haɗuwar wani gurin ce abu yashiga tsakanin su da yasa ta riƙeshi ko kuma soyayya kasan papa akwai ɗaukar wanka ga kyau inajin ko ya yaudare tane kode makaman ci haka,
"hararar sa sam yayi yace me kake nufi kenan kakan nawa kake cewa mayaudari to kwa kamar a kunne sa kafaɗa dan sai nagaya masa,
"ɗan murmusawa shettima yayi yace to ai ba ƙarya nayi ba wallahi indai kaga mace tayi kuka ko ta shiga wani yanayi idan aka ambaci mutum to ya yaudare tane ko kuma tasoshi shikuma be sota ba tayi son maso wani daga baya kuma harta haƙura ta auri wani to sai kaga idan suka haɗu dashi ko kuma ƴaƴan sa kode wani abun da ya tuna musu dashi sai kaga sun tsinci kansu cikin wannan halin....
"Sameer yace to nide bansanu ba zan tambaye sa inji idan yasanta zai gaya mana inda take daga nan kuma sai munemi yanda zamuyi idan tana da amfani sai mune meta idan kuma munga ba abun da muke tunani bane akanta kawai sai murabu da ita kawai muyi focusing ɗin abun da ke gaban mu,
bossay dake baya yace to yanzu meye abun yi danni yanzu hankalina ma gaba ɗaya ya tafi kan waccen matar dan gaba ɗaya tafara canzan tunani
yakamata muyi nazari akanta sosai wannan abun yana buƙatar tunani da dogon nazari amma de Ubangiji shi yabarwa kansa sani shiyasa ya haɗamu da su kuma muka rabu dasu akwai abun dazai faru watakil rabuwar ce mafi alkhairi shiyasa muka rabu batare da munji wani ƙarin bayani ba sai yazamana kamar ansaka mu cikin duhu da wani tunani amma de kuma idan muka ƙara nazarin faruwar wannan abun da haɗuwar tamu zamu fahimci kamar wani ƙarin haske ne Allah ya nuna mana a binciken da zamuyi ina ganin ayanzu idan muka samu matar nan akusa damu zamu samo bakin zaren wani abun, ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yace ko ya kukace maganata abar dubawace kuyi tunani akai sosai zaku gane abun da nake nufi amma fa ni anawa ganin kenan da kuma hasashen da nakeyi wannan matar itace muƙullin wata ƙofar tamu wanda saida ita zamu shiga wani wajen.... shiru yayi yana jiran jin ra'ayoyinsu game da bayanin da yayi musu,
"shiru motar ta ɗauka gaba ɗaya kamar babu kowa acikin motar,
sam ne ya katse musu shirun da cewa "zamu duba maganar ka amma sai mun samu loƙaci sai muƙara tattaunawa akai amma saima na tambayi papa abun da yace duk saimu tattara maganganun muga inda kuma yakamata mu dosa....
shettima yace hakan yayi kaga loƙacin komai zai fara tafiya bayan munɗauko wannan mutumin shima kuma awajen sa zamu samu ƙarin baya ni duk sai mu haɗa su waje ɗaya,
to hakan ma da kukace yayi Allah ya dafamana ya shige mana gaba akan abun da mukasa gaba Allah ya taimakekum da tai makon sa yabamu ikon cika alkawarin da muka daukar wa kanmu,
"Ameen!"
suka amsa masa dashi gabaɗayan su.,
daga nan ba wanda yaƙara magana Sameer ya tayar da motar suka juya saboda daman banan hanyar zasuyo ba unguwar da mahaifin sumy ya kwanta ta musu suka nufa tunda suka fara tafiya bawanda yaƙara magana saidai kowa yana tasa maganar da zuciyar sa kowa na saƙa da warwara shi kaɗai.............,
*maama*
"dan Allah maama kiyi haƙuri kiyi shiru wallahi muma zaki iya saka mu kukan ummy ce me maganar muryarta cike da damuwa take bawa maama haƙuri da tunda suka baro wajen ta fashe musu da kuka kuma tambayar duniya sunyi mata akan tafaɗa musu dalilin kukan nata amma taƙi buɗa bakin ta sai kuka kawai harda me sauti take duk tabi tasaka su a damuwa(daman idan babba yana kuka ai kaima dole kaji kamar kayi kukan nidai saida nayi ma😭, wallahi koya kaga nagaba da kai na kuka saikaji jikinka duk yayi sanyi😢😢)
"da ƙyar suka samu ta ɗan tsagaita kukan nata baya fita sosai yanzu ahaka suka ciga ba da tafiya ba wanda yaƙara magana suna so su tambayeta amma suna tsoron kar su tsokano ta taci ga ba daga inda ta tsaya shiyasa kawai suka rabu da ita suka bari idan sun sauka ta dawo daidai sai su ƙara tambayar ta........
************************
*Masarauta*
__________cikin fada.
Sarki ne akan ƙasaitacciyar kujerar sa ta mulki wacce aka ƙawata ta da ado kala kala na sarauta ajiki kana kani kasan ba ƙaramin kuɗi aka kashe mata ba wajen ƙawatata iya adon ma da aka yi ado dashi wasu maƙudan kuɗaɗen aka kashe mata ba,
gefen kujerar sa kuma Fulani ce itama a hakinmce akan tata kujerar sai wata kujerar daga can gefen ta papa ne da Ammah a azaune suma atasu kujerar da batakai ta fulani ƙawatatuwa ba,
ƙasa kuma su waziri ne da galadi ma da sauran de duk wanda yadace nakusa kusa de duk de ajali ne awajen amma banda yara dan ko su momma babu su aciki iya manyane kawai agun,
waziri ne ya fara ɓude taro da addu'a dayiwa annabi salati kamar yanda yake a addinan ce idan za ayi taro ya wuce mutum biyu zuwa sama anaso kafin afara maganar sai abuɗe zaman da addu'a,
"bayan sunyi addu'ar ne"
"fulani ta gyara zama tare da bin kowa da ido saida ta gama shan ƙamshinta kamar yanda ta saba aduk loƙacin da taga kowa cewar ta yake jira to fa anan ƴan mulkin suke motsawa saitagama ja muku aji da ƙara ɓata muku rai sannan zata faɗa muku buƙatar ta, yanzu made hakan take bata canza zani ba saida tayi musu haka sannan ta fara magana,
"ƙara gyara zama tayi sannan tace tom duk danasan kowa yasan shine dalilin taruwar mu anan maganar da tasa nace kowa ya hallara anan kenan ina fatan kowa yana da