dayi bazaka faɗi gaskiya ba to kai zaka sha wahala gaka ga su zasu ɗora maka daga inda suka tsaya ne ba ruwan mu saboda haka katai maki kanka kayi abun da yakamata dan tsiratar da ranka in kuma zakaci gaba da rufawa wani asiri to kaine aruwa dan abanza zasu kashe ka kuma sun kashe banza sai ka zaɓa idan sirrin su yafi ranka to in kuma ranka yafi sirrin su yarage naka.....,
ai ba shiri ya tashi zaune yana gyara zaman sa yanda zaiji daɗi saboda jikin sa duk amace yake yayi tsami,
saida ya taro nutsuwar sa sannan yafara magana cikin sunkuyar da kai yace "zan faɗi duk abun da nasani kuma iyaka gaskiya ta,
amma dai kamar yanda nace muku bansan shiba ban taɓa ganin saba to hakanne saidai zan baku number wanda muke communication dashi ta waya dan koni yaƙi bari insan shi ko in haɗu dashi bamu taɓa haɗuwa ba saidai ya ɗorani ne akai duk ranar da wani abun yafaru insanar dashi......,
maganar gaskiya office ɗin da kuka je bashine ainahin office ɗin ba wannan office ɗin kawai anyi shine saboda irin haka kuma an umarci kowa da kowa indai anzo neman office ɗin director ɗin to anuna masa wannan office ɗin shiyasa ma aka gyara sa kamar normal office ɗin wancen ɗin ma amma awajen directors ɗinma basu san da zaman wannan office ɗin ba shima kamar office ɗin kowa yake awajen su sai ka shiga cikine kawai zaka gane yana da bambam ci da sauran sannan kuma yawancin waɗanda ake ɗora akai basu da wani alaƙa da wajen kawai suyosu ake daga waje a ɗorasu akai.....
ni kaɗaine kawai wanda ke da alaƙa da gurin nawane office ɗin, ina zaune aka kirani da sabuwar number akace ana son magana dani, nace "inaji na gyara kara zama, sai kuma aka kashe wayar sai kawai naji alart ina dubawa naga maƙudan kuɗi aciki da sukai matuƙar furgita ni dan aƙala kuɗin sunfi million ɗari aka turo min bangama mamaki ba aka ƙara kirana akace naga alart nace"eh" cike da furgice abakina sai mutumin kawai ya kwashe da dariya yace "ai wannan bakaga komai ba kada ɗan wannan kuɗin yaɗaga maka hankali, nan gaba zaka samu fiye da haka indai ka bamu haɗin kai kagama arziƙi dan ba abun da zaka nema karasa arayuwar nan duk abun da kakeso zan baka,
sai na tambaye sa nace wane irin haɗin kai kuke buƙata daga gareni sai yace "akwai wani mutum zamu kawo sa nan gidan da zummar zai zauna muna so kasan yanda zakayi ka kaɓi case ɗin batare da kowa yasan da shigowar saba sannan kuma ko nima bazan gansaba zadai ayi komai a ɓoye kuma za ashigo dashi gidan amma na ƴan kwanaki za aɗauke sa kawaida ana buƙatar saka hannun na wajen shigo dashi gidan zanyi musu jagora har ashigo dashi,
sai nace musu ai dole sai na kai file ɗin sa can wajen su sannan sai alƙalai sun saka hannu sai yace "kar in damu da wannan su zasuyi komai sudai ɗaki kawai suke buƙata in bar musu komai a hannun su......
duk da wannan batun nasa banyar da dashi ba kuma na nuna masa bana son kuɗin daga nan sai ya kashe wayar baiƙara nemana ba sai bayan kwana uku sanann yakirani da duk daha ban amin ce ba dan ina tunanin idan aka kamani dole asirina zai iya tonuwa duk ranar da akazo dubasu akaci karo dashifa za asamu matsala haka yaita kwantar min da hankali har yaja ra'ayina na yarda,
bayan kwana biyu saiga wani daga cikin ma'aikatan gidan yakawon file ɗin sannan akace insaka hannu kuma kar inbar gurin aikin yau zuwa dare zasu shigo dashi na karɓa nayi signing na basu bansan dai inda suka kai file ɗin ba,
haka naita zama har bayan sallar magariba sanann aka ƙara kirana akace in fito inyiwa mai gadi magana zasu shiga ina gurin me gadin ma bamu gama magana dashi ba naga har sun shigo sun wuce dake na gayawa wanda ya mawo min file ɗin inda zasu ajesa dan haka basu jira iso naba sukayi wucewar su ciki nabisu da kallo sannan nabi bayansu zanbi hanyar da suka bi sai wani yatare ni yace kar inje sunce ya jira yanzu zasu fito sai kawai nace masa "to"
daga nanma ban tsayaba na koma office ɗina dan in harhaɗa kayana intafi gida fitowata ke da wuya na nemesu na rasa ban damu ba tunda daman nasan harkace ta rashin gaskiya sai kawai nayi tafiyata gida,
washe gari da na dawo naje ɗakin da na kwantanta musu sukaishi dan inyi magana da mutumin, saidai ina zuwa naga ɗakin wayam babu kowa aciki da ba ƙaramin mamaki abun yaban ba nadaɗe aci ina alajabi ni kaɗai sannan nafito na koma office ɗina na ɗauki wayata nakira number da ake kirana da ita amma sai taƙi shiga haka nai ta gwanda wa bata shiga har na haƙura ina daf da tashi saiga kiransa yaƙara shigowa na ɗaga tun kafin ma inyi magana yayi saurin katse ni da cewa kar kace komai nasan kaje baka gansaba ko kar kasa kanka tunani ka gama yimana naka aikin dan ba anan muka ajiye saba mun canza masa guri saboda tsaro bamu san kowa yasan shi daga ciki kuma har dakai shiyasa muka canza masa waje batare da sanin kaba mungode da haɗin kanka yanzu zakaji alart mungama dakai....,
daga nan ya kashe wayar baijira nace komai ba dan haka ya turo min wasu kuɗaɗen, daga nan kuma ban ƙara jin ɗuriyar sa ba tun ina mamakin abun har na daina naci gaba da sabgar gabana har na fara kashe kuɗaɗen da suka bani da kaɗan da kaɗan,
saida akayi kwanaki da yawa dan nama manta da batunsu yaƙa kirana bayan na ɗaga mun gaisa......, sannan yaƙara bijiro min da buƙata office ɗina nace wannan kuma bazan iyaba suyi haƙuri su nema awani wajen tunda bani kaɗai nake da office ba, sai yace yasan da haka nawa kaɗai ake buƙara abun da suke so in kawai shine za abada kuɗi agyara office ɗin batare da sanin manyan mu ba, daga nan kuma zasu kawo wanda zai ringa kula dashi nikuma inje duk inda nake so sannan in ɗan ringa shigowa gurin ina ɗan zagayawa sai intafi aikina kawai inleƙo in koma su zasu ci gaba da kula da komai,
nace masa hakan ai bazata taɓa yiyuwa ba abani office ɗin amatsayina na ma'aikaci kuma ace wai wanine daban zai ringa kula da gurin taya hakan zata taɓa faruwa batare da sanin kowa ba sai kace gidan yarin mahaukata a ina ya taɓa jin anyi irin haka inbanda shirme,
sai kawai yace ba ataɓa yin haka ba kuma za ayi yanzu dole in amince ko ina so ko bana so idan kuma ba hakaba sai sunsa anyi min abun da bantaɓa tunani ba sai nayi da nasanin rashin amincewar da nayi dan sharrin da zasu ƙullamin bazan taɓa cire kaina daga ciki ba,
na tsorata da maganar sa sai kawai nace masa na amin ce amma da sharaɗi yafara faɗa min daliin da yasa yake so sai wani ya shigo office ɗin sai yace basai naji ba sudai buƙatar su kenan akwai aikin da zasu sa ayi musune aciki duk yanda naso yagaya min yaƙi ba yanda zanyi dole na haƙura na amin ce,
bayan na amin ce mungama magana sai washe gari yace yafasa kawo kowa nida kaina zanje in ɗauko wani in ɗora nidai na rasa gane kan wannan abun nasa nan ma nace masa na amice naje na lalubo musu wanda zasu ɗora akai sukayi magana dashi sannan muka fara aiki mu biyu aguri ɗaya batare da sanin kowa ba,
ataƙaicedai munyi haka da wajen mutum biyar idan wani yazo sai suce ya tafi wani ma yaƙara zuwa na biyar ɗin shine wannan ya nuna baban sumy sannan yace loƙacin da zan kawo sa sai suka ce suna buƙatar idan na kawo sa inbar komai a hannun sa in haƙura da zaman office ɗin ma gaba ɗaya in faɗi duk abun da nake so zasuyi min bayan kuma kuɗaɗen da suke turo min akoda yaushe daman kuma gaskiyar magana inada son kuɗi su suka nake amince wa da duk wata buƙatar su haka na ƙara amincewa da wannan buƙatar tasa,
dake ina da hanyoyi agurin sai kawai nace ni zanyi resigning daga aiki amma ina neman alfarma ga wani ɗan uwana da aɗora akai ban sha wahaba kuwa aka amince na kawo sa to shikaɗai ne dai yake zaune da sanin kowa ta baya kuma yana min aiki domin bama tare dashi amma kullum duk abun dake faruwa sai yakirani ya sanar dani,
ranar kuma da kukaje wajen sa tun kafin ma ya kirani yagaya min, wancen mutumin yakirani yagaya min cewar za azo office ɗin kuma dan haka inkira wancen ince masa kar yasake yafaɗa musu inda nake saboda ni zasuzo nema yayi musu yawo da hankali kawai da haka har su tafi,
sai kuma aka samu matsala basu tafi ba suka gano sa,
duk maganar da sukayi najisu dan haka nayi saurin kiran wancen nagaya masa abun dake faruwa sai yace "in rabu dasu idan kungama komai inkira ku ingargaɗe ku akan maganar nemana da kuke indai tsoratar daku kuma innuna muku cewar nasan komai game da wanda kuke nema sannan kuma ince nasan inda kuke kucire hannunku daga cikin case ɗin in bahaka ba kuma zanyi maganin ku, shiyasa aranar na kiraku nayi muku barazana amma wallahi bansan kuba bansan komai ba baya ga wannan abun da nafaɗa muku wallahi tallahi iyakacin abun da nasani kenan,
kowa shiru yayi yana nazarin tunanin da zaiyi game da wannan labarin da mutumin nan yabayar shin maganar sa gaskiya ce ko kuwa amma dai duba da yanda yake rantse rantse kamar da ƙanshin gaskiya aciki,
sam ne ya tsugunna agaban sa sannan yace file ɗin kuma da akace kaje kana nema fa ido rufe har kana mishi barazanar cutar dashi idan baifito da shi ba yayi masa tambayar yana kakkafe sa da ido,
dogon tunanin yashiga saida sam ya daka masa tsawa sannan yace ba magana nake maka ba,
sai loƙacin ya dawo daga tunanin da yake sannan yace wannan ba file ɗinsa bane case ɗin wanine ya taso za ayi shari'a dashi kuma ni akabawa file ɗin loƙacin da abun ya taso aka kirani akace inbayar ko in faɗi indai yake ba agansa ba shine nakira nace masa ya laluboshi yace min baigansa ba nazo da kaina na duddu ba nima bangasaba shine hankali na ya tashi saboda nasan ƙarshen zancen idan nake nace ba agansa ba raina ne zai ɓaci shiyasa nace ya nemo sa amma ba abun da ya shafi wannan maganar bace,
miƙewa sam yayi tare da yarfar da hannun yana dafe kansa dan wannan abubuwan da suke faruwa nema suke su tarwatsa masa ƙwaƙwalwa sai ana tunanin ansamu mafita za afara warwarewa sai kuma aga akasin haka wai sai yaushe komai zai zama normal ne abun yayi yawa daga wannan sai wancan,
A fusace meer yazo gaban yana binsa da wani irin matsiyacin kallo sannan yace kawo number mutumin da yake kiran ka, dan Meer akwai karantar mutum yagama karantar sa kuma ya yarda da duk abun da yafaɗa shiyasa ma baiƙara kai masa mazgaba,
kai mutumin ya girgiza yace watar tana can gidana na abuja basu bari nataho da ita ba,
sam yace "mundauko ta ai tana office, saidai aje can aɗauko yanzu,
Papa da tun ɗazu yakasa magana sa yanzu ya samu damar cewa "basai kunje yanzu ba kubari agama komai zuwa anjima sai kuje, da "to" sam ya amsa tare da samun guri yazauna,
shiru gurin ya ɗauka kafin daga baya papa yace za a iya mayar da su inda aka ɗauko su sannan suje suyi sallar la'asr,
kamar baban sumayya zaiyi kuka haka ya durƙusa aƙasa yace dan Allah tund dai banda laifi kutai maka ku barni intafi gida dan Allah kusake ni intafi yayi maganar sada kansa ƙasa hana addu'ar Allah yasa su barsa ya matsu yaje yaga ƴar sa,
buɗar bakin papa kam yace ba matsala zaka iya tafiya amma koda yaushe idan wani abun yafaru da ya shafeshi zai iya jin kira ya zauna cikin shiri,
cike da murna da farin ciki yace "ya amince koda yaushe ake buƙatar sa zaizo,
saida aka ƙara gargaɗin sa da ja masa kunne haɗi da ƴar ƙaramar nashiha akan yaguji abun duniya komai zaiyi ya tsaya iya gaskiyar sa yanzu gashi yajawo kansa duka da kwana wani wajen batare da sanin iyalan saba ya kiyayi cin hanci ko nan gaba domin hakan ba inda zaikaisa saidai ya kaisa yabaro sa,
sosai jikinsa yayi sanyj yayi da nasani daman tun ba yauba tun ranar da sam ya dake sa agaban ƴar sa yake nadama, dan haka yayi masu godiya yayi wa kowa sallama harda wanda aka kamosu tare da yake ji kamar ya bisa, bayan yayi musu sallama sannan ya miƙe tsaye yajuya zai fita har yakai bakin ƙofar zai buɗe sai kawai yaji ance RABI'U......cak yaja yatsaye sakamakon jin muryar wanda bai taɓa tunanin jintaba a irin wannan loƙacin batare da ya juyo ba yafara ko kwanton anya kuwa muryar da yaji daidai kunnuwan sa suka jiyo masa amma kuma yana da tabbacin ko amafarki yajita yasan ta wace dan bazai taɓa mance taba,
ahankali yashiga juyowa har yagama juyiwa gaba ɗaya yanda ya zuba musu ido haka suma ƴan ciki suke kallon sa,
ɗaya bayan ɗaya yafara binsu da kallo dan yaga ta inda mai muryar zai fito yaji muryar sa amma kuma gashi baigan sa,
Abu ne ya miƙe tsaye sannan yafara takowa ahankali har zuwa gaban sa yakafe sa da ido kallon kallo suka shiga yiwa juna,
saura kaɗan baban sumayya ya faɗi ƙasa yayi saurin dafa bango yana zaro ido tsawon minti biyar yakasa magana shima kuma abu bai masa magana,
sai da ƙyar baban sumayya ya iya ɗaga hannun sa ya shiga nuna sa da yatsa yana mamar mamar da baki yanaso yayi magana amma yakasa da ƙyar dai ya daure bakin nasa ya buɗu yace "umaru ru......,
na'am Abu ya amsa masa yana kallon sa tare da harɗe hannun sa aka ƙirjin sa, yana sake ƙare masa kallo,
abun mamaki sai kawai hawaye suka fara sauka daga idon sa cikin hawaye yace "daman kana duniya daman zan sake ganin ka arayuwa ta babu irin neman da banmaka ba umaru nayi neman har nagaji har garin Lagos naje bansame kaba daga ƙar she nahaƙura ashe da rabon sake haɗuwar mu aduniya ashe bazan mutu da zunubin ka ba dan Allah ka yafe min abubuwan da nayi maka abaya da abun da mahaifiyata tayi maka na roƙeka ka yafe mata dan ta cutar dakai arayuwa yaƙara sa maganar yana zubewa aƙasa yana dafa ƙafar Abu hawayen sa har yana ɗiga kan ƙafar sa,
Abu baisan loƙacin da shima yaji hawaye na zubowa da sauri yasaka hannu ya share hawayen tare da tsugunna yasa hannu biyu yaɗan bubbuga kafaɗun sa sannan ya ɗagosa ya miƙar dashi tsaye tare da rungume sa rungume juna sukayi,
kowadai na falon sun zuba ido suna mamakin wannan sanayyar da tasu a ina suka san juna haka, har da su kuma,
Abu ne yaraba su sannan ya kamo hannu sa suka dawo ciki, ba tare da ya zauna ba yakalli su Abu da suka tsare su da ido suna jiran ƙarin bayani,
kallon su yayi sannan yace "wannan bawan Allahn da kuke gani ƙani nane koma ince kusan sa'ani muke dashi agidan da nafara tasowa na tsinci kaina kafin daga bisani kuma muka rabu sai yau Allah ya haɗa mu,
bayan yagama gaya musu kafin ma yayi magana ya maida dubansa ga baban sumy sannan yace "Rabi'u ai kaman ta da komai yafiya kuma babu abun da kukayi min nima na daɗe ina cigiyar ku bansa meku ba tunda natafi da na dawo akacemin kun tashi haka na koma naci gaba da rayuwa ta ni kaɗai nakama kasuwan cina har Allah yayi min arziƙi nama bar ƙasar naje nayi aure har bayan na dawo ma na kuma bada cigiyar ku gidan radio amma shiru tun ina neman ku har na haƙura zan cen da nake maka yanzu haka bandaɗe da sanin ma ba mahaifin mu ɗaya ba dakai sai kwana biyu da suka wuce nasan hakan, sakamakon haɗuwa da mahaifiyata ta gaskiya da mahaifina ga kuma dangina babu abun da zance sai godiya ga mahallici na,
yanzu waɗan nan dakake gani iyayena ne wannan itace mahaifiyata wannan kuma mahaifina ga ɗana kuma wanda kuma ake tuhumar ku akan ɓatansa kuma shima ɗan uwana ne ƙanine agare ni,
dan haka ni banda wata damuwa yanzu daman damuwata ɗaya ce ta inda zan sameku dan innuna farin cikin riƙe nin da mahaifinka yayi sai gaka kuma Allah ya haɗa mu nayi murnar ganin ka sosai, domin ko mai kukayi min arayuwa bazan taɓa mantawa dakuba saboda kun gama yimin komai ko ince mahaifin ka yagama yimin komai arayuwa tunda har ya ɗauke ni aloƙacin da bansan kowaba banda komai har ya raineni na mallaki have ankalin kaina kafin ƙaddara tazo ta rabamu, idan ban yafewa iyalen aba ai bancika ɗan halak ba banyiwa kaina adalciba zan kasance ɗata daga cikin masu yin butulci nikuma ba butulu bane....ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yaɗan yi murmushi tare da kara kamo hannun sa yace "Rabi'u ina so kamanta da komai kabar tuna baya kasa ma kamar babu wani abu da yataɓa faruwa tsakanina da kai na rashin jituwa da makaman cinsu komai ya wuce yanzu ka zauna anan idan muka gama komai zamu je dakai kaini wajen baffa inganshi harma da Inne itama inason ganin ta da sauran ƙanne na ina fatan duk kowa yana nan lafiya da ransa da lafiyar sa dai ko? yaƙarasa maganar tare da faɗaɗa fara'ar fuskar sa,
shiru Rabi'u yayi yakasa cewa komai saboda abun al'ajabin da yagama kasheshi wai wanda suke ɗauka abanza suke wulaƙan tawa da cin mutuncin sa da zarafi ashe yafi su matsayi shiɗin wani ne yafisu zaiso kwa haɗuwar sa da mahaifiyar sa da har yanzu tana nan yanda take taƙi