Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   6 / 74

15K to 18K   out of 221K words

tajawo wanann abun gashi ita tabata musu lokaci azuciye yayi kanta da nufun ya kaimata mugun dukan da zaisa ta farka har yakai hannu sai kuma yadakata ko me yatuna kuma oho saikawai ya yaye abun rufar gaba daya sannan yasa hannunsa duka biyu tare da dan rankwafawa kanta zai dauketa kenan
kawai sai ta bude idon ta ahankali tana budesu ta saukesu akansa qara waro ido tayi ganin shi dab da ita shikuma duk da yaga ta bude idon amma be daga daga rankwafawar da yayi ba saima qara ynuqurin da yayi zai dauketan sai kawai ta matsa daga kusa dashi sannan tayi saurin ja baya tana hade rai hadi da turo dan mitsitsin bakin ta gaba ashe tun farkon shigowar sa ta farka daga bacci kawai likimo tayi amma duk abun da sukecewa tana jinsu tayi shiru saboda bata son tafiyar amma kalaman bossay ba qaramin tsaya mata arai yayi ba wai miji shi zai aureta abun dabata taba tunani daga garesa ba wai aure sai maimaitawa take aranta kenan daman tunfarko bossay sonta yake bata sani ba ko kuma yanzune yafara bata da wanda zai bata amsa ganin hakan yasakata murginawa dayan bangaren na gadon tare sa zura qafafunta qasa sannan ta miqe batare da ta kalli kowaba ko kuma tayiwa wani magana ba saboda duk haushinsu takeji gaba dayan su hakan nan taji harshi ma bossayn  haushinshi take ji duk datasan kowa ita yake jira amma sai ta wuce wajen qofa kawai ta bude ta fita daga dakin,
Sukam kamar wadanda aka kafa agurin duk suna kasa motsawa kawai sunbita da idanu harta qarasa ficewa daga dakin ta bacema ganinsu sannan bossay yayi saurin bin bayan ta daga bisani ma shima shettima yabi bayan su shikam yana gun atsaye kamar gunki saboda tsabar mamakin da yagama kasheshi shi wannan yarinyar zatayiwa haka har yazo zai dauketa amma ta maida su 'yan iska ta tashi tayi ficewar ta karkada kai yayi tare da furta lalle sai na koya miki hankali kwafa yayi kawai sannan shima ya fice daga dakin yana zuwa yaga duk bama sa falon har sun fita daga ciki sunyi waje saboda tana fitowa bata tankawa kowa ba ta nufi waje taje wajen motar ta tsaya tana ciccin magani saikace wacce akayiwa wani abun sai cika take tana batsewa su hajiya kuma daman sun gaji da tsayiwa dan haka suma suna ganin ta fita ba wanda ya dakatar da ita sai ma binta da sukayi abaya sunsan de tunda tafito yanzu suma mazan zasu fito basu kai ga qarasawa wajen ba bossay yabiyo su yana kiran Ameesha amma ko kallon inda yake batayi ba saima juyar dakai da tayi da dan mamaki yaje binta da kallo meyasa ta juyar masa da kai kuma ya kira ta tayi masa shiru leka fuskarta yayi yace baby meesha ya akayi ne bakison tafiya ko kiyi hakiri anfi qarfinane nima bada son raina zaki tafi ba amma kar kidamu koda yaushe zan ringa zuwa inda kike kwanciya ce kawai zata ringa rabamu dake zuwa wani lokaci kuma zan daukeki gaba daya,
Ammi ce ta doke masa qeya tace dalla malam rufewa mutane baki banason shashancin banza kadauketa kakai ta gidan uwarka meyasa kai baka jin maganane me kake so kazama dan hade rai yayi yace Ammi ba nan zan kawota ba gidana zankaita ana gama wannan bincikin idan komai ya daidaita za ku aura min ita muje can muyi rayuwar mu mukadai watakil ma mubar muku qasar gaba daya saidai muringakawo muku ziyara  ko baby meesha yafada yana kallon ta kawar dakai tayi batace masa komai ba,
riqe baki Ammi tayi zatai magana kenan su sameer suka qaraso wajen yana zuwa kuma ya bude motar yashiga yasa suma sauran duk sukayi saurin shiga amma banda Ameesha da bossay ya riqawa hannu lokacin da take qoqarin shiga motar inda hajiya ta shige bayan motar itama kuma nan zata shiga kamarde ayanda sukazo kallonta yayi sannan ya matso daf da ita yanda bama kowa zai iya jin abin da zece ba sannan  yace ki kulamin da kanki nabaki amanar kanki gobe zanzo tunda safe kai kawai ta daga masa amma bata samu damar basa amsaba zaicigaba da magana Ammi ta daka masa tsawa tace wai kai wani irin yarone sai batawa mutane lokaci kake kasake ta ko kwa sai na saba maka anan gurin nibansan yaushe ka canza ba kazama haka to wallahi inbakai wasaba sai na hana ka zuwa wajen nata kaci gaba dayin abun da kakeyi karkafasa Ammi me nayi to ni banga wani abu da na aikaya ko nafada da baidace ba yafada cin qunan rai tare da sakin Ameesha ya juya yayi tafiyarsa batare da yaqara kallon ta ba kuma tunda yatafi be jiyo ba itama kuma sai takasa shiga motar ta tsaya tana bin bayansa da kallo saitaji duk ba dadi jitake kamar ta kirashi tace yadawo karyatafi amma ba halin yin hakan ba yanda ta iya dole ta hakura tayar da motar da shettima yayi ne yasa ta dawowa cikin hayyacin ta sannan ta shiga motar dadda dake tsaye takasa magana tama zama wani sakaka da ita jikinta duk ya mutu itama bata son tafiyar tata shiyasa ma takasa yimata magana saboda idan tayi zata qara karyar mata da zuciyar ta itakam Ameesha batama kalli inda take saboda gaba daya hankalin ta nakan bossay tana shiga Ammi ta rufe mata murfin motar sannan Ammi ta shiga yimusu Allah kiyaye hanya hajiyace kawai ta amsa mata sannan sukayi sallama yatayar da motar tare da janta baya sai lokacin Ameesha ta dagi kai suka hada ido da dadda jitayi zuciyarta wani iri ganin yanda dadda ta koma kamar zatayi kuka  suna hada ido dadda ta saukar da kanta qasa duk yanda taso dadda ta dago su hada ido amma hakan besamu ba har shettima ya juyar da kan mota suka nufi wajen gate suna zuwa gate man ya bude musu suka fita daga gidan saida su Ammi suka ga fitarsu sannan suka juya suka koma cikin gidan,
su shettima suna hawa kan titi Ameesha ta saki wani marayan kuka sosai tasakar musu kuka acikin motar cikin bacin rai Sam yadaka mata tsawa da yasata san yin shiru hajiya ce face aa babana ya isa haka karkasake yimata  same kakeso taji ai dole tayi saboda kewansu gashi anrabata dasu zataje inda batasani ba bata saba zama acan ba kaga dole kwa saitaji ba dadi taqarasa fada tare da  qara jawo Ameesha jikin ta tana rarrashinta da bata baki ahakade akaci sa'a da kyar tayi shiru sai daman shashshekar kukan take tare da sauke ajiyan zuciya atare atare runda yayi shiru kuma motar sai ta dauki shiru ba wanda yakara magana ahaka suka cigaba da tafiya sunzo daidai wani super market hajiya tace wait.. kaga kutsata adan yimata siyayya ai tana rufe baki Sam yace hajiya da kinrabu da ita muje kawai zuwa gobe  sai ko shine sai ya kaita tace to shikenan nan ma shirunne ya biyo baya basu dau loqaci ba suka qarasa gidan bayan yayi horn me gadi ya bude musu sun shiga ya daidaita parking sannan suka firfito sam be fito ba yace wa shettima su wuce asibiti kawai basai sun shiga cikin gidan ba OK  yace masa bayan sungama fita hajiya da Ameesha har sunkai bakin qofama sannan shettima yace hajiya zamu wuce hospital sai mundawo ta dan juyo ta kallesa sannan tace to shikenan sai kundawo Allah ya kiyaye hanya sannan ya shiga cikin motar yaqara tayarwa suka bar gidan.......✍

*kuyi hakuri da wannan daga yaude angama yin typin kadan kadan nadawo gida daga tafiyar danayi in sha Allah zuwa gobe zanyi me yawa*


     
Assalamu alaikum,

kutsaya ku karanta kar ku wuce yana da matuqar muhimmaci agareku.

*ILIMI HASKEN RAYUWA*

Ina matan aure harma da 'yan mata wadanda basu samu damar yin makarantar islamiya ba ko kuma wadan da sunyi amma yanayi rayuwa yasa sun manmanta da wasu abubuwan to ga dama tasamu akwai mata dayawa wadan da suke cikin wannan halin suna bukatar ilimi kuma wasu suna so amma basusan ta inda zasu fara ba wasu kuma hidimar gida da iyalai bazasu samu damar fita su nema ba,
To amma fa kusani hakan ba hujja bace awajen Allah domin acikin wani hadisi ance azaba ta tabbata gawanda be nemi yasani ba kuma ko kasani ma idan baka aiki dashi nan ma azaba zata tabbata agaresa dan haka kutashi kunemi ilimi kar kuzauna da duhun kai ko girman kai ilimi ba ai masa girman kai kitsaya ki fadada iliminki musamman bangaren akdari mata dayawa suna da qarancin ilimi akai,

Duba da hakan yasa muka kawo muku hanya mafi sauqi na online class kina zaune a cikin gidan adakin ki azaune ko akwance ma zaki samu duk wani ilimi da kikeso dai dai iyawarki,

yar uwa awa nawa kike batawa akan wayarki batare da ki qaru da ita baki koyi komai ba aciki awa nawa kike batawa akan karatun littattafen novel da kalle kalle da basu da amfani,

zamu bude group iya mata zamu kawo muku littattafan addini sannan kuma zamu ringa qarin alqur'ani me girma duk surar da baka iya ba za akoya maka duk daga inda kake so zaka koya zamu koya muku baki kodaga alifunne baka iyaba za a koya maka kuma da yardar Allah zaka iya,
Ga abubuwan dazamu ringayi kamar haka👇
1_ALQUR'ANI
2,HADISI
3,AKDARI
4,ARABIYYA,
5,SIRATUL NABIYYI
6,NURANIYYA
DA dai sauran su duk waddannan abubuwan zaku samesu agarabasa me sauki naira dari ukun ka ta baka ilimi kuma idan kabiya ka ta samu kenan baza ataba cemaka wata yayi ba biya kudi ko shekara nawa zakai saidai idan kai kagaji da nema kace ya isheka domin karin bayani sai ku tuntubemu ta wannan number 08124226526

Pls duk wanda ya karanta yatayamu da share dinsa zuwa group group domin inkai baka ra ayi watakil wani yana da ra,ayi akai kuma be ganiba plss share it
[5/9, 11:32 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526
'Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*

                         🅿11&12

Bismilah.......✍

Suna qarasawa asibitin kowa ya nufi nashi office din dan gabatar da abun da sukazo yi sam na shiga nasa office din ya wuce dakin sa kai tsaye saida yafara shiga bandakin ciki yayo wanka sanan yafito ya canza kayan da yake ajiyewa aciki sannan yadan bude frige yadakko fresh milk me sanyi ya sha yaji yadan samu nutsuwa sannan yaje wani guri kawai naga yadaga wani labile saiga qofa agurin budeta yayi ya shiga dakine haka dan qararrami ba anan yake ajiye duk wani mahimman abubuwansa dan ba kowa ma yasan da dakin ba gaban wani board dake jikin bango nan yake yadauki makar yafara rubuce rubce ajiki yana yi yana tunani saida yagama rubce duk wani suna da yaji dadda tafa in kuma bata fadi sunan ba to zai rubuta abun da yafaru da kuma abun da akeso agano agun saida ya gama rubuce shi tass da danni wani wani abunma bansan me yarubuta ba shikadai yasan yanda yayi lissafinsa inba ayi maka ma bayani ba cazakayi hauka ya rubuta agurin saida ya tabbatar komai yayi daidai yanda yakeso sannan yafito daga dakin yamaida qofar yarufe kan gadonsa yadawo ya kwanta fuskarsa tana kallon sama yana ta sake nazarin maganganun dadda yana musu dalla dalla sosai ya shiga kogin tunani kamar kuma wanda aka tsikara da allura haka ya tashi zunbur jikin sa yaqara gyarawa sannan yafito daga dakin wayarsa da yabri a office yadauka yakira shettima yace yazo su tafi yana fadar haka yayanke wayar sannan ya fito daga office din yana fitowa suka hadu da shettima tare suka qara fita suka shiga mota suka bar asibitin suna fitowa shettima ya kallesa yace ina mukayi yace gida dan haka direct masarauta suka nufa lokacin da sukaje anfara kiraye kirayen sallah sai kawai suka fara shiga masallaci sukayi sallah kafin suka shiga cikin gidan suna part din momma suka fara shiga suka gasheta sanna suka fito suka nufi part din fulani da sukaje basu sameta ba dan haka kawai sai suka wuce wajen Ammah........


____________*AZEEMA*

tana zaune adakin bata fita daga qarsjede bacci ne ya salallabo ya sureta bata farka ba sai wajen magriba shima jakadiya ce ta tasheta ta watsa mata wasu kaya sannan tace gashinan idan kinyi salla kizo tana nemanki tana kaiwa nan ta qara fita bata jira amsarta ba daukar jakar gana must go tayi ta bude sai taga kayan sawa ne da hijabai harda mayafai yawancin kayan ma duk dogayan rigunane irin na larabawan nan da mayafan su sai riga da sket shima kananu ne harda takalmi da jaka tana kalla tana ta faman sakin murmushi saboda ba qaramin dadin kayan taji ba kuma tun a ido sun matukar burgeta tasan zasuyi mata kyau tunda take daman bata saba saka kaya irin wadannan ba masu tsada da tagama dubawa sai ta tashi tsaye saboda murna harda tsalle tashiga yi adakin saida tagama tsalle tsallen sannan tasamu waje tazauna tame jin dadi aranta dan harta matsumu tagansu ajikinta,
agurin tabar kayan ta shige bandaki ta cire kayan jikin ta tafara wanka sannan ta dauro alwala
ta fito jikin ta daure da zanin wankan da ta shiga dashi kayan ta kuma yiwa dai dai sannan tafara gwadawa haka taitayi idan ta gwada wannan saita kalli wani taga kamar shi zai finata kyau sai tacire ta qara gwada wani ahaka jakadiyar ta qara shigowa dakin kallon ta ta shiga yi tundaga sama har qasa saida tagama qare mata kallo sannan ta girgiza kai batare da tace mata komai ta wuce bathroom din bata jima ba ta dawo cikin dakin fuskarta da danshin ruwa alamar de itama alwala tayo salaya ta shinfida ta tayar da sallah,

shi go war jakadiyane yasata tsaida gwajegwajen da takeyi ta dauki daya kawai tasaka da hartasaka ta daidai yanda akeyi tayi rolling da mayafin sai kuma ta tuna ashefa bawai amatsayin wayayyirta zata zauna ba sai kawai tayi saurin kunce daurin datayi rigarma sai ta cireta gaba daya sai ta dau wata rigar marar ado sosai brown color sai dan wani ado da akayi aqarshen rigar da qarshen hannu sai wuyan ma duk akayi ado da coffee sai mayafin ta shima brown amma sai ta ajiye dan kwalin rigar ta dauki na wata rigar amma shi yellow ne itakanta saida tabawa kanta dariya ganin irin hadin ganbizar datayi kawai sai ta daura shi kamar dan kwali ta dauko red din hijabi ta sake daurawa akai kuma bekai mata har qasa ba kana kallonta zaka ga kalar rigar da kuma kalar dan kwalin da ta daura ga kuma jan hijabi sai ta fito das abinta kamar jakar kauye daga kanta tayi ta kalli wani dan tebur dayake cikin dakin an dan jere abubuwa akai qarasawa tayi tana zuwa kuwa taga wata hoda akai sai kwalli taso tasamu janbaki akai amma babu shi sai kawai hoda da kwalli kuma hodar ba mudubi ajiki bata damu daganin madubiba kawai ta hau shafa hodar ahaka tasan ta isa amma sai ta qara gogo wata ta qara dan barawa tanasane ta ringa shawafa har kan hijabin da kuma kan yellow dan kwalin data daura hmm abun ba acewa komai dan bazakace ga da hallitar datayi kamaba gaba daya ta canza kamanni kwalin ta zaro taqara ranbadawa akan idon ta harda yin jagira tajata atsaye kamar dogon yaro idan baka qura ido bama zakayi zaton bata raba girar ba saboda saura kadan ta hadesu bangama tsorata da itaba saida naga space din data bari na jagirar sai taja fashin goshi agurin(wannan abun da wasu sukeyi yanda ake zanen bille shima haka akeyinsa akan goshi wasuma tunda ga farkon gashin su ake jamusu shi har zuwa tsinin hancin su zakugansa an tsgawa mutum shi to itama irinshi tayi da kwalli),
tana gama zanawa sai kawai ta dawo kan bakin ta nanma ta zana amma saboda ba kallon madubi take ba saikawai tazana ya kusan cike mata duka leban nasama da naqasa bayan tagama nan kuma sai kawai ta dawo kan kuma tunta taqara jan bille awajen dayan bangaren kumatun kuma sai taja abu guda biyu amma atsaye suke kuma ba wanda ya hade da wani guda dai dai ne saidai rashin kallon madubi yasa daya yafi daya tsawo taso tayi miyau miyau(uku uku nagefen baki da akeyi)
amma tana tunanin bazata iyaba saboda zata iya cike fuskarta da baqi gaba daya shiyasa kawai tabarshi tanayi tanawa kanta dariya aciki ciki saboda kar jakadiya tajita tsayawa tayi tana tunani kuma me zata qara sakawa dazaisa de asan itafa yar qauye ce bata san komai ba bata da gata kuma ba kallon madubi take ba batasan tayi ba yanda kowa zai qara yarda da ita kuma bata yanda wani zai zargeta saboda shirmen dazata ringayi musu tsawar da jakadiyar ta daka matane yasata katse tunanin datake ubanwa yace kitaba min kayana waya baki izini tafada tana tunkaro inda take itakam takasa motsawa daga gurin bare tayi tunanin tashi duk dataji tahowarta kusa da ita bata gama tunanin ba taji matar tasa hannu ta tayar da ita tsaye tare da juyo da ita suna facing din juna hannu ta dafa zata kaiwa fuskarta mari amma sai ta dakata sakamakon tozali da tayi da fuskarta asukwane ta saketa tare da sakin dan qaramin ihu tana ja da baya baqaramin firgita tayi ba da ganin fuskarta ba gashi dama tubarkallah tana da idanu gasu farare tas kuma sai ta qara waro su akanta tana kallon ta da mamkin abun da yasata shiga wannan tashin hankalin harhaka batasan kuma zaro idon datakeyi matane yasa ta qara tsorata da itaba jakadiya na ja da baya itama tana qara binta hakan yasa jakadiya qara rudewa ganin tana qara tunkarota gashi bata

6 / 74