ba wani tafiya suka suka ƙarasa part ɗin kamar yanda yayi acan part ɗin haka yayi yanzu ma ya shiga kansa tsaye, ya kwa ci sa'a yana shiga ya tarar dasu gaba ɗayan su afalon waziri da matar sa saboda suma duk yaran sun fita kallo,
Ido biyu da waziri sai yaji girmansa aransa dan haka sai kawai yaɗan maze yayi sallama ciki ciki, yana ƙarasa shiga ciki,
Cike da murmushi shinfiɗe kan fuskar waziri dan har haƙoransa na bayya na yace "Ah ah ah kace banban baƙo ne yazo min to sannun ka da zuwa Bismillah ga guri zauna, ya nuna masa gefen sa, zama yayi tare da cewa "barka da safiya,
waziri yace "barkan mudai magaji mun kwana Lafiya ya kwana baƙunta ai daman yanzu nima nake shirrin zuwa can wajen ku ashema kana tafe,
Meer da duk yaji zaman gurin ya gundure sa ya gaji da surutun da yake masa, shiyasa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa "yauwa magana nazo muyi akan maganar maama Sabreena,
gyara zama waziri yayi yana fuskan tarsa da kyau sannan yace "to to madallah hakan yayi, nima daman jira nake inji yaya yayi maganar shiyasa ma banƙara yinta ba nabari zuwa wani loƙaci amma tunda yanzu kazo shikenan sai muyi,
Meer ya kalle sa sai kuma ya kawar da kai tare da mayar da fuskar sa yanda take tun farko sannan ya wani canza murya kamar bashine yanzu yagama magana cikin ruwan sanyi ba,
"Abu daya zuwa biyu nake son ji daga gare ka sauran duk kabarsa idan kafaɗan hakama kaɗai ya isa an hutar dakai kacire hannun ka zanji da komai,
Wani busashen yawu waziri ya haɗiya dan maganar Meer ba ƙaramin sosa masa rai tayi ba amma sai yayi saurin kawar da duk wata damuwa da take shirin wanzuwa aransa yace "ina jinka magaji saidai kuma wani hanzari ba gudu ba bazaka iya ba gwanda de kabari ataimaka maka saboda baka san kowa ba kuma baka san kan gidan ba dan haka bincike kai kaɗai ba ƙaramin wahala zai baka ba tsintaiya ɗaya bata shara, wannan abun yana buƙatar tsintaiyoyi da yawa, dole sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe kafin a cinma abun da ake so a cinma ina fatan ka fahimce ni,
Tunda ya fara magana Meer yake yi masa wani irin kallo ta ƙasan ido batare da shi wazirin ya fahimci hakan ba, saida ya bari yayi shiru ga mamakin waziri sai kawai yaji Meer yace "No needa nagama magana kuma baza canza ba, baijira cewar waziri ba, ya ɗora da cewa "tambayata ta farko agare ka shine kagaya min agun wanda kafara jin mutuwar ta sannan kuma agurin nan kace kana da dalilin da yasa ka yarda cewar itace kana da hujja to hujjar nake son ji idan ka gaya min waɗannan abubuwan shikenan ya wadatar dani ina sauron ka.......,
shiru waziri yayi na wasu ƴan loƙuta kafin ya gyara zama yace, azahirin gaskiya taƙa maimai bazan ce maka ga abakin wanda nafara jiba, ranar da abun ya faru bana gida ina dawowa natarar ana zancen mutuwar tundaga bakin gate ɗin, ni kuma a loƙacin ban yarda ba saboda tun adaren washe garin kafin ace ta rasu ɗin naje part ɗin ta sai na tarar bata nan sai mai aikin ta kawai ita kuma take sanar dani cewa ai bata nan ta fita unguwa nayi mamakin jin hakan ya za ayi tafita unguwa a irin wannan loƙacin ita kaɗai saboda kafin inje in sameta muna tare da yaya(papa) muna magana bayan mun gamane nace masa zane wajen mutuniyata saboda muna shiri da ita sosai, shiyasa abun ya ƙara ban mamaki da yasan bata nan ai da zai sanar dani tunda tare muka taho dashi ni nayi ɓangaren ta shikuma ya tafi wajen ɗayar,
a loƙacin nayi niyar inje insanar dashi sai kuma naga dare yayi sosai wataƙil ko ya sha'afane shiyasa bai sanar dani ba ko tayi tafiya me nisa ta kwana tunanin hakan shine yasa kawai na ɗan bar maganar zuwa safiya, da safe kuma sai kiran gaggawa ya same ni na fita daga gidan tun a subar fari ma nabar gidan, bandawo ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na safe ina dawowa kuma na riski mutuwar da na tambaya ya akai ta mutu kowa yake cewa hakannan aka tarar da ita ta mutu a ɗaki nace akaini wajen yaya akace ai baya cikin hayyacin sa yanzu haka yana ɗakin fulani a kwance, nan nashiga tashin hankali naje wajen mahaifiyar mu nace wai da gaske gimbiya sabreena ta mutu itama tana kuka tace min wai sunce da gaske ne amma itama bata yarda ba saboda loƙacin da za a fita da gawar hana kowa ganin ta akayi wasu ne suka yi mata wanka acewar fulani wai dangin tane sukazo tun asuba dan haka su sukayi mata wanka suka lullubeta kaf cikin gidan nan babu wanda yaga fuskar ta a haka aka fito da ita akayi mata sallah aka kaita maƙabar ta tunda nidai bana gidan aka kaita, da na tambayi ina dangin nata akace har sun koma ƙasar su nikuma a iya sanina nasan tunda aka kawota nan babu wani wanda ya taɓa takowa yazo nan daga cikin ƴan uwanta sai kuma ace ranar da ta mutu har suka zo kuma suka koma taya hankali zai ɗau wannan baya nin aloƙacin saida mukayi kaca kaca da fulani akan ƙarya ne babu wasu ƴan uwanta kuma banyarda ta mutu ba tadai faɗi inda ta kaita rigima mai ƙarfi taso ta tashi daga cikin gidan sai kuma daga baya aka samu masu yi mata aiki suka bada shaidar su sunga ta da idanun su kafin ayi mata wanka, duk da haka nace banyarda ba saida mahaifiyar mu(gwaggo)tace inbar zancen kar ta ƙara jin nayi wata magana haka inaji ina gani nayi shiru tun ba ake ko ina bama maganar ta watse aka manta da babun ta, ba a ƙara zancen taba kuma sai ranar da kuka zo aka ganta sannan kowa ya tuna da ita, yaro kam da ta tafi dashi daman ba zancen sa dan ko ni a loƙacin nama manta dashi banyi zancen sa ba, kuma wannan ba komai bane face asiri ina da tabbacin tun aloƙacin da abun ya faru an riga da an asirce kowa ne shiyasa babu wanda yayi jayayya akan maganar duk abun da aka faɗa sai mutum ya yarda saboda an batar wa da kowa tunanin su ta yanda ko maganar su ma babu wanda zaiyi, to kadai ji abun dake faruwa, sai an tashi tsaye gurin gano ko waye nasan yana cikin gidan nan abun dubawa ma shine idan akace baza a binciko su ba to dole zasu ci gaba da tayar mana da tozarma ba za ataɓa samun kwanciyar hankali ba sundun gayin dauki ɗaiɗai kenan tunda gashi naji labarin matar da kuka zo tare ba agan taba, kaga daga nan kuma ba asan kan wa zasu koma ba, bayama yanzu da suka ga dawowar ku cikin gidan dole suma su tashi tsaye saboda gudun kar akamasu, daka tawa yayi da maganar yana kallon Meer da yake taune bakin sa yana girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin waziri,
miƙewa tsaye yayi ya ɗanyi taku biyu zuwa uku a tsakiyar falon sannan yace "ina masu aikin nata da suka bada shaidar sun ganta kuma wacece wacce tace ƴan uwanta ne suka yi mata wankan gawa, waɗan nan suka kaɗai ake nema daga zarar ansame su to kamar ankama wanda ya ɓatar da itane,
Shima Waziri miƙewa yayi yace tabbas kamar ankama wanda yayi ne idan aka kamasa saidai kuma wani hanzari ba gudu ba tunda ga ranar banƙara ganin meye mata aikin ba tunda nasanta a fuska kuma hargidan su nasani saboda ni na kawota amma daga ƙarshe da na fara memanta hargidan nasu ma bansamu ba, sauran kuma bansan fuskokin suba amma ina da tabbacin suna cikin gidan nan sudai ba afita dasu ita kaɗai aka fita da ita da nayi bincike nagano hakan saidai kuma nakasa samun su kuma nayiwa fulani maganar loƙacin tana fushi dani taƙi tagaya min, amma yanzu dole mu ƙara tuntuɓar ta da maganar,
Meer yace "muƙullin amsar mu yana gurin ta, zata fito da wanda yasata ko tana so ko bata so, zanje na fito da ita yanzu nan yana kaiwa nan yayi alamar kamar zai fice daga cikin falon, Waziri yayi saurin dakatar dashi, daman yana sane ba fita zaiyi ba dan yaji ta bakin sane dan haka sai ya tsaya cak batare da ya juyo ba,
Waziri ya gyara tsayiwar sa da kyau tare da takowa zuwa gaban sa yana fuskan tarsa sannan yace "baka tunanin kuma bayan muƙullin amsar mu yana gurin ta itace ma amsar ina tunanin matar nan dole tasani inma bata saniba tasan wanda yasani saboda bata da gaskiya kwata kwata daga ita har ƙawar tata, gashi dukkan wani abu da zai fito daga gurin ta yake fitowa, bayan kuma ɗan da taje ta sato ta kawo sa amatsayin ɗa ai dole tasan shi zaizama sarkin shiyasa ta koreta ita kuma ta kawo nata in ba haka ba taya zata kawo wannan shawarar cewa tana da ciki ai sai tana da tabbacin barin waccen ɗin sannan zata ɗora nata akai,
Shiru Meer yayi yana nazari sai daga bisani ya ɗan numfasa sannan yace, "bana tunanin hakan iyakacin gaskiyar ta ta faɗa anawa tunanin kawai kamar ana amfani da ita ne wajen nuna kamar ita take aikatawa yanda duk abun da yafaru ita za azarga dan haka ni SAMEER ɗan SAMEER jikan SAMEER nacire fulani daga zargi yanzu nan ma za afito da ita, daga inda take kuma wanda zai shiga ba kowa bane face kai dan haka sai kasake shiri, kajira kirana, yayi maganar yana nunasa da yatsa cike da gargaɗi yana kaiwa nan kuma yaja ƙafarsa ya fice daga falon tare da banko musu ƙofar.....,
Saura kaɗan Waziri ya faɗi aƙasa dan ba ƙaramin buguwa zuciyarsa tayi ba dan tana daf da tarwatsewa ta fito waje kana ganin cikin idon sa zaka ga zallar tsoro atattare dashi,
Matar sa dake laɓe duk tagama jin maganganun su, ta fito daga inda take tana tafa hannu har ta ƙaraso inda yake bata daina tafawa ba saida ta tsaya agaban sa tana kallon sa ido cikin ido tace, "Bisa ga dukkan alamu zaki yazo farauta kuma ya farauci abun da yake so nidaman na daɗe da gane shirye shiryen ka idan nayi maka magana kace kar na dame ka to gashi nan yanzu ɗan cikin ka zai mayar dakai abun da yaga dama zai wulaƙan taka abainar jama'ar wallahi wallahi nayi da nasanin auren ka kaidai ba mutumin arziƙi bane munafuki mai fuska biyu Allah ya cigaba da tonar asirin ku acikin gidan nan ankama ka sai kasan ta yanda zaka kwaci kanka ai na godewa Allah da ya halicci wannan yaron a duniya dan yayi maganin irin ku gashi ka daɗe kana abu atunanin ka ba mai gane ka sai gashi a ɗan mintina yaro yayi wasa da tunanin ka ya nuna maka yafika iyawa, yanzu shawara ta rage game shiga rijiya ka kwana aciki kai ka ɗai ko kuma kajawo wasu ku kwana aciki kafi jin daɗin baccin domin mutuwar yawa kakace, wallahi idan baka faɗaba ma ni da kaina zanto na muku asiri dan masan duk abun da kuke shiryawa dakai da su...........
Bata ƙarasa ba yakai mata wata uwar shaƙa awuya yana ta fitar da numfashi idonsa sun kaɗa sunyi ja yama kasa magana ya shaƙeta kawai, ita kuma tana ta faman kakari zatayi amai tana ƙoƙarin ƙwatar kanta, amma ina ƙarfin su ba ɗaya ba, bai sake taba saida yaga ta daina numfashi sannan yasake ta, tafi luuuu ta faɗi a ƙasa mataciyyyya........✍️✍️
*Tammat bi hamdulillahh anan nakawo ƙarshen littafin nan akaro na biyu saida kuma muyi fatan shiga babi na uku, SARKI SAMMER DA ZaFI ZAFI yanzu za a fara wasan har yanzu dai da saura rina a ragaya, mujee zuwa......💃💃💃💃*
***********************
***********************
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)