ɗaure mata kaima shine taya yana tsoho dashi har yasamu ƙarfin da ya iya ɗaukan sa anya kuwa wannan mutumin mutum ɗin gaske ne baya tare da aljanu ko kuma shikansa ɗin aljanine yayi shigar mutane, ta manta da aiken ta yayi ta tsaya tana wani tunanin saida ya kuma yi mata magana sannan tayi sauri ta ƙarasa gurin hannun ta har yana karkarwa wajen miƙa masa robar saura kaɗan ma tasaki ruwan ya zube yayi saurin riƙe robar,
baice mata komai ba ya warware wani abu a takadda ya zubasa aciki ruwan yasa hannu ya jujjuya sannan ya ɗauko wani ganye yaringa ɗiba dashi yana watsa masa aduka jikin sa har saida ruwan yaƙare sannan ya zaro wani abu me kamar mai a kwalba ya buɗe sa yace da ita "matso, atsorace ta matso kusa dashi yace "kawo hannun ki miƙama sa tayi ya zuba mata aciki" yace "murtsuke shi a duka hannun ki,
nan ma batayi masa musuba ta murtsuke shi yanzu bata da wani zaɓi ko jayayya dashi dole tabi duk abun da yace mata, tana gama murzashi ahannun ta ɗan saci kallon sa tana jiran taji me zaice caraf kwa suka haɗa ido da sauri tayi ƙasa da nata,
"matso ki shafa masa shi afuska zuwa wajen wuyan sa gaba ɗaya, kasaƙe tayi tana kallon sa kamar bazatayi ba,
kallon ta yayi shima yace bazakiyi bane, idan bakiyi ba ke zakiyi asara dan sai kinfi kowa da nasani nan gaba, kiyi ki shafa masa in kuma sokike ya mutu to shi kenan intashi inyi tafiya ta,
"a'a yi haƙuri zanyi tafaɗa tare da ɗora hannun akan fuskar sa tana shafa masa ahankali kamar me tsoron taɓasa, ahaka har tagama shafa masa aduk inda yace ta shafa masa sannan ta cire hannun ta,
shi kuma yaƙarasa duk wani abu da yasan zai masa yasamu lafiya yagama komai ya mayar dasu cikin jakar yasaƙalata awuyan sa yamaidata mazaunin ta,
"kallon ta yayi yace taso ki zauna anan ya nuna mata gefen sa.,
Ahankali ta tashi daga inda take ta koma kusa dashi ta zauna inda ya nuna mata ɗin ta zauna tare sa sunkuyar da kai aƙasan zuciyar ta kuma tana jin tsoron sa Allah Allah take kawai ya tafi,
Hannun ta yakamo duka biyu ya riƙe anasa yana kallon ta, Itama ɗagowa tayi tana kallon sa sai kawai ya ƙara sakar mata murmushi, da sauri ta kawar da kanta,
Ganin hakan yasa yafara magana ahankali, kiyi haƙuri ni ba macuci bane ba kuma mugu bane dan haka ki kwantar da hankalin ki babu abun da zan miki duk abun da nake miki da wasa nake miki kawai tsokanar ki nake, Saboda naga kin tsorata ne da yawa shiyasa nayi miki haka. Kuma wannan bawan Allahn yana daf da tashi idan ya tashi kibashi kulawa sosai duk abun da ya buƙata kiyi ƙoƙari kiyi masa koda hakan zaimiki ba daɗi kinji ko?
Kai ta iya ɗaga masa kawai.
Sannan yaci gaba da cewa "bari ingaya miki wasu abubuwan da baki sani ba saboda ke yarinya ce ƙarama yakamata kiriƙe su tun yanzu kafin nan kafin zuwan wani loƙaci kina jina yayi maganar yana kallonta, yanzu ma ɗaga masa kan ta kumayi, Sai kawai ya girgiza kai ya ɗora da cewa...
"nasan kinsha gwagwarmayar rayuwa tun kina ƙarama kuma har yanzu kina kanshan ta kuma bazaki daina shantaba nan kusa, akwai wasu ƙalubalen da zasu sameki nan gaba, to amma inaso kiɗauki ƙaddarar ki hannu bibbiyu kiriƙeta amatsayin jarabawar rayuwar ki,
Nan gaba komai zai wuce zai zama kamar ba ayiba taurarin ki zasu cigaba da haskawa har bayan ranki keɗin watace anan gaba shiyasa zaki ringa ganin abubuwa kala kala na akasin farin ciki, ba tafa nake miki ba amma nasan akwai matsalolin da zaki fuskanta nan gaba fiya da waɗanda kika fuskanta abaya shawarar da zan baki itace kiriƙe addu'a safe da rana da dare ki yawaita ibada sosai fiye da wadda kike yi domin girma nazo miki ta nanne kaɗai zaki iya yaƙar maƙiyanku har kici nasara akansu,
kiriƙe abu ukunnan da zan faɗa miki.
Na ɗaya kinga wannan mutumin da yake kwance da shi kaɗai yakamata ki yarda shine kaɗai bazai taɓa cutar dake ba duk wani shawara idan zakiyi ko abu ya shige miki duhu kafin ki tunkari kowa da maganar kifara tunkarar sa koda bazai kulaki ba,
Na biyu daga yanzu kar ki ƙara yarda da kowa kar kibari kowa yaƙara sanin abun dake cikin ki ki yakice kowa daga cikin ranki hakan zai miki amfani nan gaba,
Na uku arayuwar nan kar kiga wai mutum yana miki wasa da dariya yana nuna so agareki akida yaushe kiyi tunanin shine masoyin ki to ba haka abun yake ba sai kiga wanda zai haɗe miki ran koda yaushe shine masoyin ki na haƙiƙa abun azuci yake wanda me iya fito da sirrin zuciya sai Allah sai kuma me ita idan yaso asani,
Hmm nasan duk yanda zanmiki bayani bazaki gane komai yanzu ba amma nan gaba zaki tuna da magana ta kuma zatayi miki amfani,
abu na ƙarshe kar kisanar da kowa abun da ya faru yau daga ciki harda haɗuwar mu sau ɗaya nake haɗuwa da mutum idan na barsa na barsa kenan amma ke kin zamar min dole zan ƙara waiwayar ki ko badaɗe ko bajima bari ingaya miki abun da bakisani ba yanzuma zuwana nan bawai sa'a kikaci muka haɗu ba a'a daman da shirin zuwan na fito saboda nadan halin da kike ciki shiyasa nazo dan na taimaka miki,
itadai tunda yafara magana take sauraron sa takasa tanka masa sai dalla dalla takewa maganganun sa wasu tagane wasu kuma tarasa in da suka dosa,
shima shiru yayi yana ƙara nazartar ta kafin daga bisani yace "KHADIJAH!
Da sauri ta ɗago ta kalle sa ita duk a surutun sama datake jinsu kamar faɗar su kawai yake baisan me yake cewa ba babu wacce ta ɗaga mata hankali fiye da kiran ainahin sunan ta da yayi,
Ganin yanda take kallon sa yasa shi sakin dariya harda sauti sannan yasakar mata hannu tare da miƙewa tsaye yace to ni loƙacin tafiya ta ya yi sai mun ƙara haɗuwa nayi farin cikin kasancewa dake yau ɗin nan sai nakejin dama kar natafi amma bazan iya kwana ako inaba batare da itaba da na zauna dake zuwa safiya,
Duk dake ɗinma kin cancanci hakan kina buƙatar zamana tare da ku amma tafiki buƙatar hakan dake da ita duk ɗaya kuke aguna saidai kuma kinfita gata ahakan,
da sauri itama Ameesha ta miƙe tana kallon sa, sai tace masa "wacece ita dan Allah kar katafi katsaya ka sanar dani waye kai kuma duk taya kasan abun da ya faru dani da kuma wanda zai faru dani kuma a ina kasan suna na dan Allah kar katafi kar barni da tunani kasanar dani waye kai?
Ɗan murmusawa tsohon yayi sannan ya ce "waɗannan tambayoyi ai sunyi min yawa dan haka bazaki samu amsa ko ɗaya ba yanzu kidai bari akwai loƙacin da yakamata kisani ba yanzu ba, Na miki alƙawarin zan dawo na bada jimawa ba ki tanadi tamyoyin ki dana yanzu da waɗanda zaki samo nan gaba duk sai ki haɗasu waje ɗaya idan nadawo zan baki amsar ko wanne,
kuka tasaka masa tace "dan Allah fa nace wallahi, zuciyata bazata taɓa kwanciya ba muddin baka gaya min ba,
"Zata kwanta mana indai kinso hakan Hadizatul kubra kisa aranki baki ma taɓa ganin naba ki goge haɗuwar da mukayi arayuwar ki kafin nan kafin wani loƙaci ki manta dani ki fuskanci abun dake gaban ki,
sannan abu da na manta bangaya miki ba kizama me dakakiyar zuciya duk wani abu dazai zo yafaru nan gaba kar kibari yayi tasiri a zuciyar bare har yayi miki illa akwai babban abun da zai taɓa miki zuciya nan gaba wanda baki taɓa jin irin taɓuwar ba to aduk loƙacin da hakan ta faru kituna da maganata ki saurin kawar dashi kar yayi tasiri a zuciyar ki in kwa bahaka ba ina mai tabbatar miki da zaki iya kamuwa da bugawar zuciya loƙaci ɗaya bari in baki wani abu...
Jakar sa ya zuge ya zaro wani ɗan baƙin abu me kama da awarwaro amma na robane hannun ta yakamo ya ɗaura mata shi sannan ya ɗauko wanima yace "shima ki saka masa amma ba yanzu ba sai nan gaba kidai adana sa duk sanda kika samu damar naɗa masa sai ki naɗa masa,
karɓa tayi tana jujjuya sa a hannu ta aranta tana tunanin ta ina zata iya saka masa a hannun wannan bauɗaɗɗan nutumin dandai baisan halin saba shiyasa yace haka,
"Kar ki damu akwai ranar da zai yarda kidai adana sa kawai.
Ɗagowa tayi ta kalle sa da mamaki ƙarara akan fuskar ta kardai yaji tunanin da takeyi anya kuwa wannan mutum ne to kodai bokane abun da take ta rayawa aranta kenan,
Sarai yagane tunanin da take bayaso ya ƙara rikita tane shiyasa yayi shiru kawai bai tanka mata ba sai kawai yace "to ni natafi Allah haɗamu da alkhairin sa ki kula dashi sannan kar kiji tsoron komai babu abun da zai sameki daga nan har waye war gari da yardar Allah,
Yana kaiwa ƙarshen zancen sa yayi gaba har yaje wajen ƙofa zai fita tayi saurin cewa bawan Allah baka gaya min sunan kaba saboda iringa tunawa dakai,
juyowa yayi yasakar mata wannan murmushin nasa da yazame masa jiki,
"Gashi nan kin faɗa shine sunana ai bawan Allah ne ni bani da kowa bani da komai dan haka sunan ma bandashi" ki kirani da bawan Allah ko kuma kice min mabaraci agurin Allah amma banda wani suna aduniyar nan ko kinga namiki kama da waɗan ake kiransu ni bana na haɗuwa da kowa bare aringa kirana idan naje kin gane? shikenan zan iya tafiya ko da kawai wata tambayar?
Ahankali ta shiga girgiza masa kai tana binsa da kallo, hannu ya ɗaga mata yana murmushi ya fice daga gidan tare da jawo mata ƙofar falon....,
Tunda ya fita take kallon ƙofar kamar shine awajen, Takai wajen mintina goma agun bata motsaba,
Ahankali tafara maida duban ta ga Meer maganar da ta faɗo mata itace wai duk wata magana da zanyi inyi ta da wannan mutumin mutumin da ko kallo baka isheshi ba taya zata fara tunkarar sa tagaya masa abun dake damunta wannan impossible abun da bazata ta ɓa iyawa ba kenan, Kuma meyasa zai ce mata wanda yafi kusanci da ita bashine mutumin kirki ba agurin ta, Taya kuma wanda yake cin zalinta ya tsane ta ƙiriri ace wai shine ba muguba duk da ance mugu baida kama amma baza ta taɓa yarda da cewa Meer ba mugu bane shine abokin shawarar ta kai gaskiya wannan mutumin baifaɗi gaskiya ba, da sake,
A fili tace duk ƙarya yazo yake faɗa mun bazan yarda da maganar ka ba ko ɗaya inma bokane kai babu ruwana tana ayyana haka ta zare abun da yasaka mata a hannu ta haɗa da na hannun ta ta watsar dasu gefe, tana watsarwa ta samu kujerar kusa da Meer tayi zaman ta tana faman sakin tsaki aranta tana ayya na wa duk abun da yace tayi baza ta yi ba abun da kuma yace kar tayi to kwa sai tayi baza ta ɗauki maganar saba ko guda ɗaya kamar yanda yace ta manta da shi to kwa zata manta dashi ɗin gaba ɗaya zatayi watsi da duk wasu ƙarairayin sa da ya yi mata, da sauri wata zuciyar tace to idan ƙarya yake taya akai yasan asalin sunan ki wata zuciyar tace to ba boka bane komai ma ai zai iya ganowa, da sauri wata kuma tace to koda bokanne ai zai iya gano koman ki na gaskiya shiyasa ya gano kuma ya faɗa miki dan haka yakamata kiduba maganar sa kar kiyi saurin yanke hukunci, da sauri ta miƙa tsaye tare da sakin tsaki tace ƙarya ne ƙarya yake ba zan taɓa yarda ba taya za ayi ma yace wai zan fuskan matsaloli nan gaba bayan kuma gashi yanzu ƙarshen komai yazo na samu dangina ina cikin su kuma meye zai zo yasame ne da ɗin ma dan banda kowa ne shiyasa na ɗan sha wahala amma yanzu komai yazo ƙarshe, zaka kawo min wata maganar banza, Wani tsakin ta ƙara ja a karo na biyu sannan ta ƙara miƙewa tsaye sai tana tashi sai taga kamar giftawar abu azubure ta juya sai kuma bataga komai ba maida dubanta tayi ga Meer ta ƙurawa fuskar sa ido sannan ta janye haka tayi zaune agaban sa tana jiran farka war sa, gaban ta taji yana tsanan ta faɗuwa ga kuma wani irin tsoron da tafara ji saboda ji take kamar da mutum acikin gidan,
kusa da Meer ta koma sosai ta riƙo hannun sa tare da kifa kanta a kan damtsan hannun sa, so take tayi bacci ko zata dai na jin tsoron sa take ji, amma duk da haka kamar ma daɗuwa yake,
Maganar tsohon ce ta ƙara faɗo mata loƙacin da yasaka mata abun hannun nan yace "kar ta cire zai taimake ta kuma babu abun da zai sameta daga nan har gobe da yardar Allah kar ta tsorata da zaman gidan da sauri ta tashi inda ta watsar dasu taje zata ɗauka sai taga baya gurin cike da mamaki ta shiga laliben inda ta jefar amma sama ko ƙasa ta rasa sa,
Ba ƙaramin mamaki tayi ba na rasa shin da tayi a bun kuma ya fara bata tsoro sosai, jiki a sanya ye ta tsugunna a gaban sa tama rasa wane irin tunani zatayi kwakwalwar ta, Ta kusan daina aiki gaba ɗaya koman ta ya tsaya tunda take bata taɓa haɗuwa da tashin hankali irin na yau ba,
Ɗaga kan da zatayi ta hango abubuwan hannun a wajen ƙarƙashin kuje ra da sauri ta tashi taje wajen tare da sa hannu ta ɗauko su sai yanzu hankalin ta yaɗan kwanta da ta gansu sai tayi tunanin daman itace bata lura da kyau ba wajen da ta jefar,
Mayar dashi tayi hannun ta ɗayan kuma ta kama hannun Meer zata saka masa ta tuna yace kar ta saka masa yanzu dan haka sai kawai ta fasa saka masa,
Koma wa tayi in da ta tashi ta kamo hannun sa ta kwanta akai tana kwanciya kuwa taji ta ɗan samu nutsuwa ta daina jin tsoron da take ji, bata daɗe da kwanciya ba wani nauyayyen bacci ya su lalo ya sureta.....,
Can cikin dare wajen ƙarfe huɗu da rabi Meer ya fara motsi da ƙafar sa daga can kuma sai ya fara motsa idanun sa da sukayi masa nauyi, A hankali ya shiga buɗe su dishi dishi yafara gani kafin daga bisani suka idasa washe wa gaba ɗaya, Tar ya buɗesu akan fankar dake juyawa, ɗan lumshe ƙyawawan idanun sa yayi sannan ya buɗe su duk a loƙaci ɗaya jin kamar mutum akan sa yasa shi saurin maida idon sa gun da yaji nauyin, A kan sumar kanta ya sauke idon sa tunanin ya shiga yi wai a ina ma yake da sauri kwakwalwar sa ta fara tariyo masa abun da yafaru tundaga farko har zuwa loƙacin da ya tuna sanadin tsayiwar sa a waje loƙacin ana ruwa da dukan da ruwa yayi masa har dai loƙacin da ya tsugunna agun yana karkarwa daga nan kuma bai ƙara sanin abun dake faruwa ba sai yanzu, tunanin ta ya a kai yazo nan ya shigayi bashi da mai basa amsa a halin yanzu dan haka ya kawar da tunanin ya ƙara kallon kanta tunawa da roƙon da ya ringayi mata ta buɗe ƙofar taƙi ya shiga tunawa wani irin ƙato ton a bune yazo masa rai ya tsaya masa tare da jin haushin ta da tsanar yarinyar shi kaɗai yasan halin da ya shiga a loƙacin amma saboda bata da hankali taƙi buɗewa,
da iya ƙarfin sa ya ɗaga hannun sa zai kai mata duka a kai sai yaji yakasa ɗaga sa hannun yayi masa wani irin nauyi da ya takurawa kansa ma wajen ɗagasa saida ƙashin sa ya bada sauti yace ƙas, saboda daɗewar da ya yi a kwance baya motsa su,
Rufe idon sa ya ƙarayi tare da buɗe su jikin sa yaji gaba ɗaya yana yi masa ciwo so yake ya tashi amma bai san ta in da zai fara ba ga hannun sa da ta danne masa shima ciwo yake masa, ba yanda zai yi dole ya haƙura ya tsaya da ƙoƙarin tashin da yake son yi,
Ahaka yaci gaba da zama loƙaci zuwa loƙaci yakan harare ta duk da baya kallon fuskar ta amma hakan bai hanasa ai ka mata da harara ba gashi ya manta sunan ta bare ma ya kirata ko zata tashi, kuma ya rasa da me zai kirata shiyasa kawai ya fasa yi mata magana,
Yana zaune agun yajiyo kiraye kirayen sallah a Masallatai zaro manyan idanun sa yayi waje saboda tsabar mamakin da yayi kenan ahaka ya kwana ya akai haka ta faru yarinyar nan ta barsa ya kwana anan aƙasa, wani tunanin ne yayi saurin faɗo masa rai ya akai yaji sauƙi haka har ya iya tashi da kanshi kuma yagan sa ba a cikin asibiti ba alhalin duk ranar da ruwa ya taɓa sa baya dawowa cikin hayya cin sa da wuri sai yafi sati a kwance, Duk da bai fi sau biyar hakan ta taɓa faruwa dashi ba shima kuma tun yana yaro ne da girman sa kuma sau ɗata yataɓa ritsawa dashi ranar kuma yafi sati biyu bai samu lafiya ba to amma yanzu ace a rana guda ya dawo cikin hayyacin sa harma yana tunawa da abun da ya faru haka cikin sauƙi ba wata matsala, to ya akai hakan ta kasance waye kuma ya shigo dashi cikin gidan bayan a waje abun ya faru, yasan dai ba ta yanda za ayi wannan yarinyar ta iya jawo sa, a fili yace "hakan bazai taɓa yiyu wa ba zata min bayani, yana gama faɗar haka ya maida duban sa gare ta da ɗan ƙarfi ya ɗan ɗaga murya yace "keee....., shiru ba bata motsaba saboda yanayin da yake ciki yasa duk da ya ɗaga muryar amma ba ta fitowa sosai saida yayi mata wajen sau uku sannan ta ɗan motsa kanta ta