Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   69 / 74

204K to 207K   out of 221K words

da janta har yakaita cikin falon yana shiga ya jefata ciki ta faďi qasa saura kaďan kanta ya bugu da center table  dake tsakiyar falon Allah ya tsagaita mata wahala ya kareta bata kai ga buguwa ba yasa ka hannu ta dafesa,

loqacin da suka shigo anfara kiraye kirayen sallahr isha'i  dan haka sai babi ta kanta ba ya juya zai fita har ya kai bakin qofa sai kuma ya tsaya haďe da juyowa ya wurga mata wani banzan kallo sannan yace "ko da wasa kikayi kuskuren fitowa na lahira sai yafiki jin daďi yana kaiwa nan yayi fice abunsa,

ko kallon sa batayi ba saida ta tabbatar da yafita tayi saurin tashi zaune tinanin yanda zata samu mafita ta shiga yi yanda zata kare kanta daga haďuwa dashi,

jitayi kamar tafiya tayi tunanin ko shine ya dawo aguje ta miqe har ra doshi ďakin da ta kwana tana zuwa tajisa arufe arikice ta juyo ta qara nufar ďayar kofar nanma takasa buďewa babu qofar da  bata gwada buďewa ba amma duk sunqi buďuwa,

qofar shigowar taqara kalla tajidai har yanzu bai shigowa sai kai tayi sauri taqarasa gurin qofar taci sa'a kuwa kye ďin yana jikin qofar,

sai kawai tayi sauri ta rufe qofar ta kulle harda su zira saqata ajiki sannan tabar muqullin ajiki saboda koda ya zira wani bazai buďu ba,

duk da atsorace take da zaman itakaďai amma ta gwammace ta zauna ita kaďai akandai yadawo yasameta aciki, dan tunanin tama kawai wuqar ya tafi ya ďauko kasheta zaiyi shiyasa ta rufe ta koma kan kujera ta zauna cike da tsoro da fargaba jikin ta sai rawar sanyi yake abunne ma yahaďar mata biyu ga tsoro ga sanyin garin shiyasa take rawar ďari,

tana zaune agun har tsawan loqaci bataji dawowar saba wani tunanin ne yafaďo mata kodai tafiya yayi yabar ta ita kaďai tunanin hakan yasa ta tashi da sauri ta taje wajen  window ta yaye labulen ta leqa waje sai ta hango motar agun ajiyar zuciya ta sauke ganin bai tafi ba tana niyar barin wajen kenan ta hango shigowar sa da sauri ta saki labulen ta koma inda tame ta zauna gabanta na qara faďuwa tafara addu'ar Allah kawo mata ďauki Allah yasa dadda tazo ta taimaketa..........,

bugun zuciyar ta ne ya ƙaro loƙacin da tajisa kusa da ƙofar yana murɗawa alamar zai buɗe ƙara ƙanƙame jikinta tayi ajikin kujera jikin ta nacigaba da ɓari,

ba ƙaramin mamaki yayi ba ganin ƙofar arufe da alama rufeta akayi ransa yaji yaƙara ɓaci ga sauran muƙullan suna cikin falon har muƙullin motar yana ciki ya ajiyesu loƙacin da zaiyi alwala,

buga ƙofar ya shigayi da ƙarfi kamar zai ɓalle ta,

cikin ɗaga murya yace "ki buɗe ƙofar nan wallahi kika bari na shigo sai ranki yayi mummunan ɓaci ki buɗe,

tana jinsa amma ki motsawa batayi ba  haka yai ta bugun ƙofar nan taƙi buɗewa, haƙura yayi ya nufi wajen motar sa yajata ko zata buɗu amma yajita arufendai da yabar ta taƙaicine ya isheshi yarasa samun mafita,

dawowa yaƙara gurin yaƙara bugawa bata buɗe ya koma wajen window ɗin suma arufe suke ta ciki tashin hankali wanda ba asamishi rana yau wannan ƴar kucililiyar yarinyar ce ta rufe masa ƙofa rainin har yakai yana mata magana tanajin sa tayi masa banza idan kwa yakamata ta shiga uku sai ya kusan karya ta wallahi abun da baiyi niyar yi mata ba tajawa kanta sai yayi mata abun da bata taɓa tunani ba aidai dole ta buɗe tunda ba aciki zata kwana ba,

samun wani ɗan guri yayi ya zauna yana jiran buɗewar ta acewar sa idan tagaji da zama ita kaɗai zata buɗe,

gugugu gari yaɗauki kukan hadari loƙaci ɗaya ya turniƙe da haɗowar wani gagarumin hadari,

zunbur ya miƙe daga gurin cike da tashin hankali da fargaba da ruwan samane kawai yake haddasa masa tsoro da fargaba saboda ko ɗigon ruwa ba ya bari ya taɓasa indai ya taɓasa har suma yana iyayi baya son ruwan sama ya taɓasa saboda akwaisa da jin sanyin aɗan ƙanƙanan loƙaci sanyi yakesawa ya fita daga hayyacin sa inda kagansa hankali kwance ana ruwa to yana ɗaki aduƙunƙume aciki bargo yana bacci shine kaɗai kwanciyar hankalin sa,

asukwane yaƙara zuwa kusa da ƙofar yayi mata wani irin mahaukacin bugu wai ko zataji tsoro ta buɗe amma taƙi buɗewa,

cike da raunin murya da yasan bashida wata hanya da ta wuce wannan yace "pls ki buɗe I promise you bazan miki komai ba kibuɗe hadarine agarin kar ruwa ya sauko,

kamar tana gabansa ta maƙe kafaɗa alamar bazata buɗe ba haka yayi tayi mata daɗin baki ta buɗe amma taƙi buɗewa acewar ta wayo zaiyi mata shiyasa yabiyo ta wannan hanyar dan ta buɗe yasamu damar cin uwar ta,

daga ƙarshe ma da tagaji da bugun da take sai kawai ta tashi da ƙyar taje ta kunna T.V tare da ƙure vollum yanda bazataji saba kuma hakan zai rage mata tsoron da takeji saboda daman bataji ƙarar hadarin ba dan haka koda ruwan ma akafara ba lalle tajisa ba,

dafa kansa yayi ajikin ƙofar yana ɗan mammatse jikinsa saboda sanyin da yafara kamasa tunani yayi kodai yafita daga gidan yaje koda wani restaurant ɗin ko kuma yatafi masallaci sai kuma ta tuna ai sun rufe masallacin yanzu saidai kawai ya fita ko zai samu wata mafakar awaje gashi ɗakin me gadi ma arufe yake bare ya shiga,

har ya juya zai tafi sai kuma tunanin ta ya faɗo masa in bazai mantaba ranar da suka haɗu da aka fara ruwa wataƙil tsoro ne yasa ta dawo kusa dashi ta kwanta dan ya fahimci hakan to gashi kuma yanzu ita kaɗai aciki yasan bata yarda dashi ba da yace mata hadarine agarin tunda gashi yanajiyo sautin tvn da ta kunna alamaun batajin ma abun dake faruwa, to idan yatafi yabarta kuma ta ankare wane irin hali zata shiga wata zuciyar tayi saurin bashi amsa da cewa ta shigama duk halin da zata shiga tunda ita ta zaɓi hakan ta mutuma ina ruwanka,

da wannan tunani yayi na'am dashi da hakan ya ɗage kafaɗa tare da ɗan taɓe bakin sa ya ɗaga ƙafa zatafi aikwa kamar ɗaga ƙafarsa ake jira ruwa ya fara saukowa da sauri yayi baya kusa da ƙofar saboda wajen gurin ya ɗan rankwafo amma ba sosaiba babu abun da zai hana ruwa ya taɓaka, saidai bakamar kana tsakiyar saba kunsa koya guri yake idan kaji ruwa neman ɓuya kake agun,

shima haka ya koma jikin motar ya manne da ita yana ƙara buga ƙofar duk da yasan bazataji saba saboda ƙarar vollum ɗin, duk addu'ar da tazo bakinsa yinta yake tun ruwa na taɓasa kaɗan kaɗan har yadawo sauko masa da yawa take kwa yafara fita hayyacin sa nufashin sa nayin sama sama kamar zai ɗauke agun ya sulale ya tsugunna yana dafa ƙirjin sa loƙaci ɗaya idanun sa suka fara kakkafewa takurewa yayi guri ɗaya ya jingina da ƙofar jikinsa sai karkarwa yake haƙoransa har kaf kaf suke dana juna wajen rawar baki da yake, ƙafarsama nema take takasa ɗaukar sa haka yayi zaman dirshen agun ya haɗa kai da gwaiwa ya matse jikin sa, tun yana motsawa har yadaina motsi agun da alamun dai kamar ya ƙame agun sanyin ya ƙamar dashi ko numfashi ma bayayi,

a kai wajen awa ɗaya ana keta ruwa yana sauka akan bawan Allahn nan da yana cikin wani yanayi matacce ko rayayye babu wanda yasan halin da yake ciki,

aɓangaren Ameesha jinsa kamar ma baya bubbuga ƙofar yasa ta ɗan rage vollum ɗn tare da yin sanɗa ta matso kusa da ƙofar ta kara kunnen ta dan taji yana gurin ko ya tafi shiru taji alamun babu kowa agun gurin windown ta ƙara komawa ta buɗe labulen ta leƙa wajen motar sa taga tana nan, anan take ganin ruwan da yake sauka kaɗan kaɗan,

mamaki ne yakamata daman da gaske yake hadarine agarin gashi ruwa har ya fara sauka to ina yayi Allah yasadai bata fiya yayi ba, da sauri ta dawo wajen ƙofar ta murɗa Kye ɗin tare da jan ƙofar dan ta duba inda yake,

tana buɗewa taji abu me nauyi akan ƙafar ta kamar anjefosa cike da tashin hankali takai dubanta kan ƙafar idon ta sukayi mata tozali dashi,

wata iriyar ƙara tasaki cike da firgici ta tsugunna agaban sa tare da fara taɓasa ganindai da gaske baya motsi  yasa ta janye ƙafar ta da ƙyar tafara jijjigashi tana taɓa saitin hancin sa taji babu numfashi,

Inna lillahi wa inna illaihi raji'un, inna lillahi wa inna illaihi raji'un, inna lillahi wa inna illaihi raji'un, itace kalmar da take ta nanatawa cike da tashin hankali da bata taɓa tsintar kanta ba a ciki ba,

da gudu taje wajen kitchen duk tabi ta duburbur ce ta rasa ina zatayi saitayi wajen kitchen ɗin sai tadawo da ƙyar dai ta iya buɗe ƙofar ta shiga ta ɗebo ruwa a kofi cikin sauri ta dawo wajen kafin tazo ma ruwan duk yagama zubewa baifi rabin kofi ba yarage saboda tsabar saurin da take,

tana zuwa ta yayyafa masa a fuskar sa amma kamar ta watsawa bango, daga tsayen da take ta saki kofin ya faɗi ƙasa ya fashe,

hankalin ta da jinta gaba ɗaya sungama gushewa bata son loƙacin da itama tabi kofin tayi daɓas aƙasa hawaye na rige rigen saukowa yayin da ta kafesa da ido tana kallon sa agaban ta tana yimasa kallon gawa,

tashin hankalin ta shine idan ta tuna loƙacin da yake roƙon ta ta buɗe babu abun da zaiyi mata taƙi buɗewa gashi ta sanadin ta ya rasa ransa, yanzu kamar ita ta kasheshi kenan tunda itace sila,

ahankali ta furta kisan kai ni na kasheshi sai kuma ta shiga girgiza kai tace "a'a, a'a, a'a bani bace wallahi bani bace bani na kashe shi ba, bai mutu ba ni nasan bai mutuba da ransa haka takama sanbatu awajen kamar zararriya sai kuma tayi saurin miƙewa taƙara natsawa kusa dashi, ta shiga girgiza sa da iya ƙarfin ta tana jijjigasa tana cewa ka tashi dan Allah katashi kar ka mutu ka tashi Inga baka mutuba kar wani yazo yaganka ahaka kayi haƙuri ka tashi dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan ƙara rufewa ba katashi kayi min duk abun da zakayi min na yarda ma ni ka kasheni da duka bazan ƙara guduwa ba,  tanayi tana jijjigasa amma ko motsi bayayi kuma bata fasa jijjigasa ba tana sanbatu wasu abubuwan ma batasan tana  faɗa ba saboda bata cikin hankalin ta gaba ɗaya,

kuka kam harda su majina dataga dai da gaske baida niyar tashi sai ta fara jansa wai ta matsara dashi daga bakin ƙofar amma sai takasa, ɗaga ƙafar ta da zatayi saikwa ta sauketa akan kwalbar kofin da fasa take jini yafara zuba daga ƙafar ta sakin sa tayi,

sannan tayi saurin zama agunta riƙo ƙafar tana kuka tanaso ta cire amma zafi ya hanata sai kuka take ga tsoron ta jinin da taga yana fita, kwance tayi agun tana sakin wani kukan azabar tana juyi zata tashi taƙara ɗora hannun ta akai shima kwalba tashiga da sauri ta tashi zaune tana yarfa hannu dake ta hannun bata kai ta ƙafarfa saita damƙe idonta ta zare kwalbar da ƙyar,

gudun karta ƙara taɓawa yasa tasaka hannu again tafara tattare kwalbar waje ɗaya aikwa tasamu rabonta dan Saida wasu ƙana nun suka ƙara shige mata hannu haka ta zauna tana kuka tana ciresu hannun ta duk ya farfashe,

kallon ta ta mayar kansa har yanzu yana nan yanda yake a sanƙame, wani tunanin ne ya faɗo mata bata san loƙacin da ta miƙe tsaye ba tana takawa kuma kwalbar ta ƙara shige mata runtse idon ta tayi sosai sannan ta ƙara buɗesu duk da azabar da takeji haka ta daure ta cije ta shiga takawa ahankali, ko ɗan kwali babu akanta haka ta fito daga cikin falon halin da take ciki yasa batabi takan kwalbar dake ƙafar taba duk da zafin kwa da takeji haka ta daure take ɗingisa ƙafar tana taka inda ba kwalbar, da ƙyar take takawa har ta ƙaraso bakin gate ɗin ga ruwa da akeyi amma ba mai yawaba yayyafi ne shima ba sosai ba, buɗe ƙofar tayi ta fito wajen titin tsayawa tayi tana duban garin yayi tsit bakajin motsin komai kuma kan titin ma babu kowa ba mota ko ɗaya,

duk irin tsoron Ameesha yau ta dake batajin tsoron saboda zuciyar ta tabushe kawai burin ta ta haɗu da wani yakaita gida taje ta faɗi halin da ake ciki, da atunanin ta ko zata iya zuwa gida aƙasa amma sai ta tuna batama san hanyar da zata dosa ba,

ta daɗe agun bataga giftawar kowa ba har tana tunanin ta juya kawai sai taji wata ƙara na ruɓeɓɓen mashin ta bayan ta da sauri ta juya tana kallon hanyar da yake tahowa ko fitila babu ajiki haka mashin ɗin yake tafiya matsawa tayi gefe tana jiran ƙarasowar sa gun,

tun kan ya ƙaraso take ɗaga masa hannu tana cewa wait wait pls help me, amma mashin ɗin yana zuwa sai yayi wucewar sa, har ɗan binsa tayi tana kiran yatsaya ya taimake ta amma yaƙi kamar tayi kuka haka ta haƙura ta juya zata koma har taje wajen gate ɗin sai kuma taƙara jin ƙarar mashin ɗin..... ɗan juyowa kawai tayi tana kallon sa bata ƙara gigin tsaidashi ba tayi tunanin yanzuma wucewar sa zaiyi shiyasa batayi tunanin dakatar dashi ba,

sai kawai taga ya nufo inda take, take taji wani irin daɗi ya ziyarce ta,

agabanta yayi parking ɗin mashin ɗin nasa tare da kasheshi sannan ya sauko daga kai, tsoho ne sosai jikin sa kuma yana sanye da wasu irin kaya kamar na fata ga wata jakar arataye a wuyan sa kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci mafarauci ne,

da tagama kallon sa tsorata tayi dan aduhune batagan sa sosai ba, ita bata taɓa ganin ma mutum da irin wannan shigar tasa ba tunani tafara kodai aljanine, ko kuma ɗan daba,

tunanin hakan yasa tafara yin baya baya, kallon ta yayi tundaga sama har ƙasa sai kawai yasaki murmushi yace "da kinsan kina jin tsoron kika tsaida ni me yafito dake a cikin daren nan akuma rin wannan yanayin bakya tsoron wani abun ya cutar dake ko mugayen mutane?

shiru tayi tana kallon sa takasa cewa komai saboda har yanzu a tsorace take dashi,

wani murmushin tsohon yasaki yace yarinya karkiji tsoron komai sanar dani buƙatar ki yanzu nan inbiya miki ni ba macuci bane, saboda irinku nake zagayawa daman inda mai neman taimako in taimaka masa,

sai yanzu ta ɗanji sanyi aranta ganin yanayin sa yasa taji kawai ta yarda dashi kuma tasan zai iya taimaka mata ɗin kamar yanda tace,

ahankali ta shiga bashi labarin abun dake faruwa tundaga A har Z, yana gama jinta yace muje ciki to in dubasa,

gaba ta fara yi yana binta abaya ganin tana ɗingisa ƙafar da ƙyar yayi saurin dakatar da ita tsayawa tayi tare da juyowa, tana kallon sa wata ƴar ƙaramar fitila ya ɗauko sannan ya tsugunnna agaban ƙafar ta yace muga ƙafar ɗan ɗaga masa tayi yagani sai yace ta zauna, ya cire mata,

batayi musuba ta zauna ɗin, shi kuma ya kamo ƙafar saida tayi kuka wajen cire mata sannan yasaka mata wani magani da yazaro ajakar sa, bayan nan ya taimaka mata ta shi tsaye da ɗan ɗingishin suka karasa cikin gidan har sukazo ƙofar falon inda ta barsa haka tazo ta same sa,

ita tafara shiga ciki sannan tsohon ya shiga idonsa aka Meer dake yashe aƙasa kamar gawa,

ganin irin kallon da tsohon yake yiwa Meer yasa Ameesha ƙara tsorata murya cike da rauni da take shirin fashewa da wani kukan, ta kalli tsohon tace "ya mutu ko....?

kallon sa yamayar kanta sosai ya zuba mata ido yana kallon ta kamar me son  gano wani abu ajikin hakan kuma harsaida ya haddasa mata faɗuwar  gaba tare da tsoro ganin irin kallon da yake mata ko ƙiftawa bayayi ga wani uban kwalli da yasaka da sai yanzu ta ankara dashi,

bata gama furgitaba saida taga yana canza kalar fuskar sa ya haɗe ta tam ta koma wani iri tare da zaro mata idanu yafara nufar inda take,

ganin hakan yasa tafara ja da baya tana karkarwa yayin da idanun ta suka cika taf da hawaye tana tafiya muryarta na rawa tace "dan Allah kayi haƙuri kar ka cutar dani dan Allah dan Annabi,

duk magiyar da take masa baida na binta ba saida yakaita kusa da bango sai ya tsaya agaban yana sake kallon ta yanda take kuka kamar ranta zaifita,

saida yaƙara ɗaure fuska sannan yace "me yasa kika kashe shi duk maganar da kikayi ban yarda dake ba ƙarya kike ke kika kashe shi. shine zakizo ki shirya min ƙarya ai na ganoki kuma yanzu zan kirawo miki ƴan sanda suzo su kamaki ko kuma ni inkamaki in tafi dake, wanne kika fiso ni ko ƴan sanda?

da sauri ta shiga girgiza masa kai tare da haɗa hannu wanta guri guda tashiga yi masa rantse rantse wallahi ba ita bace,

girgiza kai kawai yayi tare da sakar mata murmushi har haƙoransa na fitowa waje,

baice mata komai ba kuma sai ya matsa daga kusa da ita ya koma wajen Meer jakar sa ya ciro daga wuyan sa sannan ya zauna akusa dashi yafara ɗan tattaɓa sa, juyawa yayi ya kalleta tana inda yabarta bata daina kukan ba,

"zo ki ɗauko min roba ki zubo ruwa aciki sannan kidaina wannan kukan,

da sauri tasa hannu ta goge hawayen saboda ba ƙaramin tsoron sa takeji ba, cikin sanɗa tafara tafiya ta nufi ƙofar kitchen da kallo yabi bayan ta yaga yanda take tafiya, sai kawai yayi murmushi yana ɗan kaɗa kai yana sane dan yaga ya zatayi ya ɗan canza murya tare da ɗaga murya da ƴar ƙaramar tsawa yace "kee...!! bazakiyi sauri ba ne.,

Allah sarki daman kwa a tsorace taken sai kawai ta kwasa aguje tama manta da ciwon dake ƙafar ta ta takesa saboda tsoro, tana shiga kitchen bata daɗe ba ta fito da wata ƴar babba babbar roba da ruwan aciki kamar yanda yace mata tana fitowa taga har ya maidashi tsakiyar falon ya ɗorasa akan Capet mamaki ne yakamata ganin har ya maida shi kafin ta shiga ta fito kuma abun da yafi

69 / 74