gyara kwanciyar ta aƙasan capet ɗin ta ɗaga masa hannu, kamar tasan abun da yake so kenan ta ɗaga masa, Saidai kuma tana ɗagawar yaji hannun ma yafi da zafi ya sanƙame saboda daɗewar da tayi akai har yayi tsami sosai,
Oh my God! Ya faɗa cike da gaji yawa da halin da yake ciki ya rasa yanda zaiyi da ƙyar ya iya motsa ƙafar sa, amma hannun dai har yanzu yakasa motsa sa, gashi har antayar da sallah amma yana kwance wannan shi kaɗai ne abun da yafi ci masa rai kenan, ba ƙaramin abu ne ba yake hana sa zuwa sallahr asuba amma yau gashi abun da yaɗauka ba komai ba ya zame masa komai tunawa da ya yi cewar halin da ya shiga jiya ma ai da tuni yanzu haka baisan ma duniyar da yake ba kamata yayi ma ya godewa Allah da yakawo masa sauƙi da wuri....,
Haushi ne ya ishe shi ganin har yanzu tana kwance hankalin ta kwance yasa ya ƙara kiran ta da ƙarfi! juyi tayi fuskar ta ta dawo saitin sa suna facing ɗin juna saida ta fara yin miƙa saboda itama da ciwon jikin ta tashi saida ta gama miƙarta sannan ta shiga buɗe idanun ta a hankali har ta idasa buɗesu gaba ɗaya. Tana gama buɗewa suka sauka akan fuskar Meer maimakon ta janye idon ta, ta tashi sai kawai ta tsaya tana kallon shima itan yake kallo har saida yaga kallon nata yayi yawa sannan ya wurga mata harara tare da jan tsaki a hankali ya furta "mayya saidai kici kanki.
Hakan da yayi mata yasa ta saurin janye idon ta akan sa sannan ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune tana hamma tare da yin wata miƙar azaune tana duban garin yanda ya ɗan fara yin haske hakan kuma ya tabbatar mata da safiya har tayi daɗi sosai taji saboda tunawa dole ya tashi su tafi da zarar tayi sallah, tunani ta shiga yi to shi ne yake agun akwance har yanzu da alamar ma ko sallah baiyi ba ko uban me yake jira da bai tashi ba oho masa,
wani tsakin taji ya ƙara saki yana kawar da kansa gefe, da mamaki ta kalle sa a ranta tace masifaffe kayi ka gama kaci kanka ba kulaka zanyi ba, a fili kuma sai ta taɓi baki haɗi da miƙewa tsaye sanin bata da inda zata tayi alwala a ɗakunan yasa ta nufi kitchen direct taje can ta ɗibi ruwa sai ta fita ta ƙofar baya acan tayi fitsarin tayo alwalar ta dawo falon, Har yanzu yana inda ta barsa ko motsawa baiyi ba bata bi ta kansa ba ta fara tunanin da hijabin da zatayi sallahr,
Tsaye tayi taba ɗan dube dube ko zata samu amma bata ga komai ba sai mayafin da tazo dashi shi taje ta ɗauka akan kujera daman doguwar rigace a jikin ta kuma bata kamata sosai ba ga dogon hannu sai kawai ta yafa shi a kanta sannan ta hau kan Capet ɗin ta tayar da sallahr. Duk abun da take yana kallon ta yana jin taƙaici a ransa har ta idar tayi addu'ar ta ta ɗora da Azkar ɗin safiya ta ƙara yin wata addu'ar ta shafa, sai ta juya ta kalle sa tana juyawa suka haɗa ido maimakon yajanye saboda kamansan da tayi yana kallon ta sai kawai maze tare da harar irin ita yagani tana kallon sa,
Ɗan jinjina kai tayi kawai sannan tace tace "ina kwana, da sauri ya juyo yana kallon ta dan yayi mamakin wannan gaisuwar tata bai taɓa tunanin zata iya gaida shi ba,
Itama anata ɓangaren batayi tunanin zai amsa ba sai taji yace "lfy daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba"
So yake yace ta taimake sa amma ya kasa saboda yana gudun kar ta raina sa, da yayi mata maganar ta gwamma ce yaci gaba da zama a haka zuwa ɗan anjima ko zaiji sauƙin jikin sai ya tashi da kansa,
Abunne yafara bawa Ameesha mamaki ganin dai har yanzu bai motsa ba sai ta ɗan tsorata da hakan ta fara tunanin kodai yakasa tashi ne tuna hakan yasa ta ƙara maida duban ta gare sa, sai tace "Kayi sallah kuwa?
Ɗan juyowa yayi ya kalle ta baiyi magana ba har ta cire ran zai bata amsa ma sau taga ya girgiza mata kai alamar a'a,
Ta ɗanyi mamaki kaɗan amma sai ta danne tare da miƙewa tsaye ta matsa kusa dashi daf dashi ta tsugunna sannan tace "me yasa, ko ka kasa tashi ne?
Yanzu ma kan ya kuma ɗaga mata kamar wani ƙaramin yaro, Sai taji ya bata tausayi abun da zai hanasa tashi kuwa ai ba ƙarami bane adain iya sanin da tayi masa namiji ne mai dauriya amma tunda ya faɗi haka kuma har takai ga ya kasa tashi to ba ƙaramin abu bane yake damun sa dole ka tausaya masa,
Miƙewa ta tsaye ta kuma yi sai ta miƙa masa hannun ta,
Hannun ya shiga bi da kallo har zuwa kan fuskar ta yana tunanin me take shirin yi taya zata iya ɗaga sa tama mayar dashi ƙaramin yaro janye idon sa yayi batare da yace mata komai ba kuma bai miƙa hannun na saba,
Hannun tane ya fara ƙagewa da miƙa masan da take dan haka sai ta janye ta ƙara tsugunna wa a gaban sa tace katashi in taimaka ma kayi sallah,
A hankali taji yana magana dan bata ma jin abun da yake cewa kunnen ta taƙara matsar wa kusa dashi tace me kace?
"Baza ki iya ba nace"
"Wallahi zan iya ta basa amsa"
Shiru yayi baice da ita komai ba saida ya ɗauki loƙaci sannan yace "Bismillah ya faɗa tare da miƙa mata hannun riƙewa tayi tare da miƙewa tsaye ta shiga jansa amma ko motsi bayayi, in banda wata wahalar ma da take son ƙara masa babu abun da take da ta gaji sai ta saki hannun tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu, da yana dariya da babu abun da zai hanasa yi mata dariya yauɗin nan yanda take ta wani sauke numfashi ɗagasa kawai ɗaga warma da batayi ba amma wai ta gaji,
Kamar wacce aka tsikara tayi sauri ta miƙi tare da nufar kitchen binta yayi da kallo yana mamakin ƙarfin hali irin nata yarinya ƴar ƙarama da ita sai tsaurin idon masifa ita yanzu kallon mutum take wa kanta,
ta daɗe a kitchen ɗin baisan me take ba sai yaga ta fito ɗauke da roba a hannun ta yana kallon ta har ta ƙaraso inda yake ta ajiye robar da ke ta faman tiriri na ruwan zafin dake ciki, tana ajiyewa ta ƙara komawa sai ta fito da wani sabon towel da abayi amfani da shi ba, a gaban sa ta ƙara zama,
Duk yana kallon ta baice mata komai ba dan yagane me take shirin yi kuma ya jinjinawa kaifin tunanin ta dan yana da buƙatar hakan,
kamo hannun sa tayi ta ɗora akan cinyar ta sannan ta saka tsumman acikin ruwan zafin ta matse sai ta ɗaga hannun nasa tasaka shi akan tsinman ta fara ɗan mammatsa masa har zuwa wajen kafaɗar sa saida ta tabbatar da hannun ya gasu sannan ta koma ɗayan ma nan ma tayi masa ruwan yafara salan cewa dan haka ta ta shi taje ta ɗebo wani ta dawo taƙara yiwa ƙafafun su takan wandon jikin nasa take masa har wajen cinyo yin sa gaba ɗaya dai saida ta saka masa ruwan zafi a ko ina ta gasa masa har wajen wuyan sa sai da ta ɗan daddanna masa, sannan tasaka hannu ta ta ƙara ɗan daddanna masa wasu guraren, saidai kayan jikin sa duk sun jiƙi,
Ba ƙaramin daɗin jikin nasa ba kwa yaji dan a cikin kaso ɗari kaso saba'in ya ragu dan har ya motsa hannun da ta gajiyar masa dashi,
Hannun ta ya kamo da ɗayan hannun sa ɗayan kuma ya dafa kujerar da take gefen sa ya yun ƙura zai tashi amma sai yaji ya kasa, miƙewa tsaye tayi tasa iya ƙarfin ta da Allah yabata ga kuma shima yana ɗan ƙoƙarin tashin bai sakar mata duka nauyin saba a haka yasamu da ƙyar ya miƙe zaune,
Sannu tayi masa, ya ɗaga mata kai yana ƙara gyara zaman sa da kyau sai ya jin gina kansa da jikin kujerar,
'Robar ta ɗauke tare da towel ɗin ta ƙara komawa kitchen ɗin, sai taƙara fito da robar ɗayan hannun ta kuma ɗauke da wani jug, ta ƙaraso gurin sa ta ajeye masa robar agaban sa tace "bari in zuba maka kayi alwala,
hannun ya miƙa cikin robar ita kuma ta zuba masa ya fara wanke su kamar yanda akeyi dai idan za ayi alawala sannan ya wanke bakin sa hardai yagama duk wani abu da mutum zai yi idan zai yi alwala ya rage saura ƙafa sai ta dawo da robar wajen ƙafar tasa ta taimaka masa ya ɗaga ta wanke masa ƙafar sannan ta ajeye ta gefe ta ƙara ɗauko ɗayar ma tayi masa,
"Bayan ta gama ta ajiye robar a gefe daga can baya sannan tace "ɗakin ka abuɗe yake ta tambaye sa tana kallon sa, batare da ya kalle taba ya ɗaga kansa, tashi tayi da sauri tafara hawa upstairs ɗin ta nufi ɗakin nasa, tana zuwa ta buɗe ta shiga ciki tafara duddu ba inda zata ga jakar kayan sa bata gani ba dan haka sai ta nufi drowar ɗin dake ciki ta fara bubbaɗe su har tayi karo da wata jallabiyar tare da wando aciki, hannun tasa ta ɗauko sannan ta fito waje loƙacin da tafito yana ta ƙoƙarin jajjan hannu wansa dan yaji sun ƙara saki ko yaƙara jin ƙarfin jin nasa, kusa dashi ta ƙaraso sannan ta ajiye masa agefen sa tace ka canza kayan jikin naka kar wani sanyin yaƙara shigar ka,
'kai kawai ya ƙara ɗaga mata ita kuma ta ɗauke robar da jug ɗin ta nufi hanyar kitchen dan tabasa damar shirya wa,
tana tafiya yayi ƙoƙari yafara cire rigar sa ya saka jallabiyar sannan ya tashi ya zauna akan kujera ya cire wandon yasaka wanda ta kawo masa ya ajiye jiƙaƙƙun agefe,
saboda ƙwarin jikin nasa da yaji da azaune yayi niyar yin sallar amma da ya miƙe tsaye yaji shi ƙalau sai kawai ya tsaya da ƙafafun sa ya kalli gabasa ya tayar da sallahr,
tana shiga kitchen ɗin ta ɗora masa ruwan tea sannan ta fara tunanin abun da zata dafa musu, tunda akwai komai a kitchen ɗin gashi daman yunwa take ji jiya bata ci abinci ba ga kukan da tayi duk ya rarake mata ciki,
da ta rasa abun yi sai kawai ta ɗebo dankalin turawa daidai wanda tasan zasu iya cinye wa tafara ferewa bayan ta gama ta sauke shayin ta ɗora mai akan wuta, ta juye musu tea ɗin a wani ɗan ƙaramin flask, kafin ta gama manta yayi zafi sai ta hau suyar dankalin tana bata daɗe ba ta gama saboda baida yawa, tana gamawa ta juye shi a flate sannan ta soya musu kwai shima ta ɗora akai ta ɗauko wani flate ɗin ta rufe ta samu babban faranti ta jerasu akai maimakon ta saka cup biyu sai tasaka ɗaya acewar ta idan yagama sai taci nata ita kaɗai,
Yana zaune agun bayan ya idar da sallah har yayi Azkar baiga fitor ta ba yayi mamakin rashin fitowar tata da wuri duk da yana jin ɓurun ɓurun tunta kuma yana jin tashin ƙamshi amma haka baisa yayi tunanin ita take yin abun da yake ƙanshin ba yayi tunanin kodai na wani gidanne ya shigo ciki, saboda kallon da yake mata ko indome bazata iya dafawa ba, shiyasa baikawo abun da take a kitchen ɗin ba,
Yana gun yana tunane tunanen sa ta fito ɗauke da farantin a hannun ta, tunda tafito yake kallon ta da mamaki har ta ƙaraso gurin ta ajiye agaban sa ta ƙara miƙewa ta nufi wajen dinning taje ta ɗauko kayan shayi ta dawo ta zauna a gaban sa bata ce dashi komai ba, shima kuma baice da ita komai ba kawai yana binta da kallon mamaki,
Cup ɗin ta ɗago ta tsiyaya ruwan zafin aciki sannan tayi masa haɗi mai kauri bata cika masa siga da yawa ba saboda kartaje baya son zaƙi,
Tana gama haɗa masa ta miƙa masa kallon ta ya tsaya yi batare da ya karɓa ba, da haka zaice mata bazai shaba sai kuma yayi tunanin idan yayi haka bai kyauta mata ba kuma daman yana jin yunwa dan haka yasa hannu ya karɓa yafara sha a hankali, buɗe masa dankalin tayi ta tura masa gaban sa,
Ƙamshin da ya dake sane yasa sai yanzu ya yarda wai daman ƙamshin nan agidan yake, to ya akai yarinya ƙarama ta iya yin wannan aikin alhalin kuma inda ta taso ba wani babban gida bane bare ace ta koya anya kuwa zaiyi daɗi ba ƙazantar ta taje ta ƙwabo ba shayin ma dan a gaban sa ta haɗa masa amma da bazai shaba dan haka yanda ta turo masa haka shima ya tura mata shi gaban ta tare da cewa wannan ma ya isa kici kawai, yayi hakane dan kar tayi tunanin wani abun,
kallon sa tayi cike da sanyin murya tace "me yasa baza kaci ba......,
Ɗan ya tsuna fuska tayi yayi sannan yace "I'm not filling hungry"
kasaƙe tayi tana kallon sa har ya idasa maganar sa bataji daɗi ba dan haka tace "ka daure kaci ko kaɗanne zai maka amfani da yunwa ajikin ka kana buƙatar sa,
"Tom", yace kawai yaci gaba da shan shayin sa da baya jin zai iya ci kuma baya so su yi ta jan maganar shiyasa yace mata tom ɗin,
sunkuyar da kai tayi tana jira yayi ya gama taja sauran taci saboda yunwar tafara damun ta, kuma ba bata iya ci dashi ba tasan ma hakan daman bazai yi yu ba,
Har ya kusan shanye shayin bai kula dankalin ba da ta lura da hakan kuma tana kallon sa yana ɗan satar kallon dankalin amma bata san dalilin da ya hana sa ci ba ko bayar da da ita bane shiya sa bazai ci ba,
A hankali ta ɗago dara daran idanun ta ta sauke sa akan sa murya ƙasa ƙasa tace baza kaci ba saboda kana tunani zan cutar dakai ne ko me,
Batare da ya lalle ta yace "ko ɗaya" sai kuma yayi shiru,
Tashi tayi daga kusa dashi ta koma kan kujera ta zauna hakannan take jin haushin rashin cin da yaƙi yi kodan tana jiran sane yasa ta jin ba daɗi oho,
Har ya shanye shayin tas ya ajiye cup ɗin ya gyara zaman sa ya miƙar da ƙafafun sa ya ɗan kishin gyaɗa ta ƙasan ido ya hango ta kan kujera ta haɗe rai sai faman turo ɗan kucililin bakin ta take, shi abun mamaki ma yabasa dan yaƙi ci shine take jin haushi,
sun daɗe a haka babu wanda yaƙara cewa ƙala, tashi yayi daga kishin giɗar da yayi ya gyara zaman sa sannan ya jawo plate ɗin gaban sa yana kallo baya so tayi tunani marar kyau a kansa dan yaƙi ci kuma duba da yayi da ɗawainiyar da tayi dashi yau yakama yaci ko kaɗanne tunda har ta nuna son hakan,
Hannu sa ya saka a ciki ya ɗauko ƙwalli ɗaya tare da ɗan yagar dankalin yakai bakin sa, kamar me cin magani haka ya shiga tauna sa a hankali bayan ya cinye ya ƙara ɗauko wani maimakon ya ɗauki ɗaga yanzu sai ya ɗauko biyu saboda ya ɗan ji daɗin sa haka ya ringa ɗauka yana ci aransa niyar sa yaci ko guda biyar ne amma sai gashi ya ware yana ci yana taunasa cikin daɗin rai da kwanciyar hankali,
Tunda ya fara ci take satar kallon sa ta gefen ido bata bari ta kalle sa ba gidan kar taje su haɗa ido ya daina ci,
Shima kuma yana sane da ita yaƙi kallon ta yaci gaba da cin abun sa hankali kwance wasa wasa dai sai plate ya gani ya cinye tas batare da ya ankare da hakan ba, da yana cewa bazai ci ba gashi kuma ya cinye yanzu da wane idon zai kalle ta, Taɓe baki ya shiga yi yana ya tsina fuska kamar zai yi amai ɗagowa yayi da niyar yace mata me tasaka a ciki amai yake ji babu daɗi zuciyar sa sai tashi saboda kar tayi tunanin daɗi ne yasa ya cinye, saidai kuma yana ɗagowa da niyar faɗa mata sai kawai yaja burki da maganar tasa sakamakon hawayen da yagani kan fuskar ta ta sauko ƙasan kuje tare sai hawaye dake ziryar saukowa daga idon ta,
Ƙame wa yayi yana kallon ta da mamakin me kuma yasa ta kuka haka harda su sauko wa ƙasa shi baima san loƙacin da ta sauko ƙasa ba, Badai haushin ta yaƙi cin abin ci ba yanzu kuma gashi ya ci kuma tana kuka,
Tun tana hawaye kaɗai sai kuma ta fara fidda sauti harda su tura ƙafa gaba, mamaki bai gama kashe Meer ba saida yaga ta kifa kanta a ƙasa tana cigaba da kukan,
Tunani ya fara to kodai aljanu take shirin tayar wa in ba aljanu ba mutum yana zaune kawai yasaka kuka batare da anyi masa komai ba shi baitaɓa ganin inda akayi haka ba,
Daurewa yayi yace kee..! me ya same ki wani abunne ya cije ki komai, zaki sani a gaba kina min kuka ko na miki wani abu, tashi tayi zaune tana goge hawayen ta kalle sa da jajayen idanun ta da suka koma kalar na kuka ga majina da take taho mata tana mayar da ita,
Hannu ya sa ya dafe gefen fuskar sa yana kallon ta shi har yanzu abun mamaki yake basa, ƙara nana ta mata tambayar da yayi mata a farko ya yi amma still bata basa amsa ba saida ta ɗauki loƙaci tana shashsheƙar kuka sannan cikin kuna tace "yunwa nake ji kuma nasha wahala nayi mana kazo ka cinye gaba ɗaya, tana gama faɗar haka ta ƙara sakin wani kukan saboda baƙin cikin da ga kuma taso mata taso taci tunda tayi take haɗiyar yawu daman arayuwar tana son dankalin turawa da ƙwai idan