Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   48 / 74

141K to 144K   out of 221K words

tayi mata zuwa fitowar su har kawo yanzu da meer ya taimaketa ahannun mutanen nan,

gaba dayan su jikin sune yayi sanyi sun tausaya mata sosai maama kam harda kuka ummy ma saida ta zubar da hawayen tausayin ta yarinya karama da ita amma ta tashi cikin rashin gata,  tunda take ma ita bata taba jin labari irin wannan ba sosai labarin ya girgizata,

saida suka gama koke koken nasu sannan Abu yace ummy "a labarin da tabayar kamar sunyi kai daya da labarin da mutanen nan suka gaya min lokacin da suka kawo maama  suma sunce ai tare da yaro aka ganta mutumin da yakira su sukadauketa suka  kaita asibiti tundaga lokacin baisake dawowa ba, kunga kuma gashi itama haka tace labarin nasu kamar yayi daidai da hakan amma de kar mu yanke hukun ci maama ki fara bamu naki labarin muji,

maama da tunkan tagama bada labarin tasan ma dole wannan jikartace yaron da ake nema kuma danta kuma tagane babu wanda sukayi mata haka sai yan gidan su duk yanda akayi yanda aka koreta daga gidan shiyasa ake so akashe duk wani jinin ta sai yanzu take tunanin tun farko ma cikin ra da yaringa zubewa da sa hannun wani aciki saboda ba aso ta haihu da Allah kuma yayi sai ta haihun sai suka sace mata danta na farko da takara haihuwa kuma suka hada da ita da dan suka rabata daga cikin gidan tabbas bazata daga kowaba duk wanda yayi sanadin barin gidan mijin ta kuma ya rabata da yayan ta saitaga bayan koma waye,

Ummy ce ta kalli maama dataga gaba daya hankalin ta baya tare da su ta katseta da cewa "Maama muna sauraron ki kinyi shiru bakice komai ba,

kallon ta maama tayi sannan ta mike tsayi tare da harde hannuwan ta akan kirjin ta tana kallon su daya bayan daya said tagama kare musu kallo cike da dakakkiyar murya tace,

"Ni haifaffiyar garin Egypt ce kuma iyaye na ga a dayan su Allah yayi musu rasuwa tun ina yar karamata sukayi accident suka rasa rayukansu, a hannun kanin mahaifina na taso,
  aure ne yakawo ni nan na hadu da mahaifin su acan garin lokacin da yake karatu alaokacin da yanuna yana sona da aure kawu na yaki amincewa har saida iyayen su sukaje suka saka baki sannan ya amince ko shekara banyi ba da aure shima ciwon siga ya kasheshi matar sa bata da mutunci daman bata sona bata son zaman gidan danakeyi dan de bayanda zatayi ne yasa take zaune dani da ya mutu kuma tattara ita da ya yanta suka bar garin ma ni kaina yanzu bazan ce ga inda suke ba nima kuma banne mesuba tunda nasamu miji na yana kaunata muna zaman lafiya dashi babu wata matsala dake faruwa a tsakanin da shi hakama kuma mutanen gidan mana zaman mutunci da kowa ba wanda wani fada ya taba shiga tsakanin dasu,

mijina dan sarkin garin nanne lokacin kuma da za adaura mana aure tare da sarautar sa aka daura aranar aka bashi sarautar yazama sarki kasan cewar a al'adar su ba a zama da mata daya dan haka mubiyu aka daura auren mu atare rana guda,

bamu dadeba da aure na samu ciki saidai cikin baije ko ina ba ya zube nakara samun wani shima yazube tun ina hakuri har abun yafara ban mamaki na fara zargin wani abun amma kuma bansan wa yake aikata min hakan ba saboda kishiyata muna zaman lafiya da ita nasan bazata taba cutar dani ba daga baya kuma nama ajiye wannan tunanin naci gaba da rokon Allah yakara bani wani bayan kwanaki kuwa nakara samu saidai shi bai zube ba da taimakon Allah har lokacin haihuwa yayi na haifi da namiji aka saka masa sunan kakan sa sameer bayan suna da yan kwanaki na shiga wanka na barsa akan gado fitowar da zanyi naga babu shi bandamu dan duk azatona ko wanine ya shigo ya dauke sa saida na gama komai sannan nafito nake tambayar me aikina waye yazo ya dauke sa take cewa bata sani ba abu kamar wasa nashiga cigiyar sa amma kowa yace bai dauke saba sama ko kasa aka nemesa aka rasa haka nasha kukana mahaifinsa yana ban hakuri akan za ayi bincike ko sati biyu ba ayi ba aka watsar da maganar saidai nikadai inyi kukana in godewa Allah,

Tundaga nan ban kara samun ciki ba  ita kuma dayar matar bata haihuwa anje asibiti ance bazata haihu ba ganin hakan yasa mahaifiyar mijina tace yakara aure haka baya so yakara auren yar kanwar kishiyar ta,
bata dade da shigowa ba ta haifi yan biyu mata,

"suna da wajen shekara biyu da wani abun nima nakara samun wani cikin haka naita rainon cikin har Allah yakai ni lokacin haihuwa na haifeshi lafiya qalau ranar suna yaci sunan kakan sa sameer,

sameer yana da farin jini sosai yana da shiga rai saboda yana da fara'ar sa har yan biyunta suka fara girma kullum sai sunzo wajen sa tare suke wuni kuma muna zaman lafiya da kowa babu wani tashin hankali dake tashi atsakanin mu da yaran mu gaba daya,

bazan taba manta ranar wata lahadi tunda na tashi da safe nake fama da ciwon kai aranar ko fitowa ma ban iyayi ba kuma babu wanda yaje inda nake daga ni sai sameer yasakani agaba yana ta kuka ganin halin da nake ciki saboda sameer akwai tausayi koya yaga kashiga wani hali yaga baka mishi dariya zaisaka kuka yana rirrikeka to ranar ma haka yayi kwance ajikina yana kuka amma nakasa tashi inajin sa kuma nakasa rarrashin sa,

nayi mamakin ganin babu wanda yazo inda nake har dare yayi daman adakina sarki yake amma har dare yayi banga shigowar sa ba haka muka cigaba da kwanciya akan gado daga karshe de sameer yayi bacci yabarni ina ta fama da ciwon kai, dishi dishi nafara ganin a idona ina ganin abubuwa bibbiyu ina cikin wannan halin naji kawai ance taso nidai bazan iya tantance muryar da najiba saboda kamar de hankali na yafara barin jikina,

duk son danakeyi intashi ɗazu nakasa amma anacewa taso bansan loƙacin da na tashi aka kuma cewa dauko ɗanki nan ma na tsugunna na ɗaukesa inajin wani abu yanayi min yawo akai kamar sauraye kamar ƙudaje haka naji abun kamo hannu na akayi aka fara tafiya dani nidai bana sanin ina ake zuwa dani ammade inajin duk maganar da akayi min kuma inaji ina tafiya amma banma san a inda nakeba waɗannan abubuwan kawai nake iya tunawa,

ina jin loƙacin da aka sakani amota akaja aka fara tafiya bana iya gane hanya kuma bana gane mutanen da suke tafiya damu acikin motar duk da inajin muryoyin su amma sai inji kamar waƙa kamar ihu haka kawai nake jin muryoyin nasu bana tantance me suke cewa,

ji nayi andena tafiya sai aka buɗe motar kawai naji anturoni daga cikin motar aka ƙara turo Sameer dake ta bacci banma sani ba ko loƙacin bayama cikin hayyacin sa shima daga nan banƙara sanin inda nake ba saida gari yayi haske rana ta hasken idona tashi nayi sai naga sameer agabana yayi tagumi yana kallona gaskiya aloƙacin da na tashi bana iya tuna komai da kowa ammade ina ganin sameer amatsayin sa na sameer amma ni kaina bansan me mukeyi ba awajen ba kuma inaso inyi masa magana amma nakasa sai na buɗi baki zanyi magana sai inji kamar anɗaure min harshena haka natashi daga gurin gurin babu komai kamar ma daji kawai na ɗaukesa muka fara tafiya dashi bansan inda zamu ba kawaide tafiya muke har nazo wajen da naga mutane na ɗan wucewa wajen shine naje wajen wata bishiya nazauna nariƙe sameer akan cinyata kawai ina bin mutanen gurin da kallo har dare babu wanda ya kulamu gashi yunwa nakeji kuma ga kuma Sameer da shima yana tamin kukan yunwa amma nakasa buɗar bakima bare in rarrasheshi ahaka muka kwana baci ba sha sai da safe wani yabamu abinci amma sai nakasa ci kawai saidai inbashi shi yaci ina son ci amma yagagare ni,  ataƙaicedai bansan adadin kwanakin da nayi awajen ba,

inajin ranar da abun yafaru aka bigeni ina tunawa natashi daga barci na hango sameer can shida wani mutumi  kamar zai ɗaukesa nikuma na tashi da sauri dan inje inɗauko sa ina hawa kan titi naga wata mota duk da bana cikin hankalina sosai amma da naga motar sai naja dabaya ina kallon nacikin motar sai kawai naga yayi dariya tare da nufo inda nake duk da ba asaitin sa nake ba nikuma sai na tsaya naci gaba da kallon sa daga nan kuma bansan me yaƙara faruwa ba sai ranar da na farka awajenku..........✍️👍✍️

kuyi haƙuri da wannan ɗan Allah wallahi yau kwata kwata banajin daɗi, amma gobe in sha Allah zanyi ƙoƙarin yin me yawa.,


                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/7, 7:59 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 83

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

_______*sam*_______

    Adai adai ƙofar gidan su sumy yayi parking ɗin motar sa sannan ya fito daga cikin motar yana fitowa ya jingina da jikin motar wayarsa ya ƙara ɗaukowa ya gwada number ta amma still akashe yanzu ma bata shiga ba mayar da ita yayi cikin aljihu sannan ya ƙarasa bakin gate ɗin ya kwankwasa tsawon minti biyu yana gurin ba abuɗe ƙara bugawa yayi amma ba abuɗe ba saida yayi wajen minti goma da wani abun ba abuɗe ba da yagaji da tsayiwar sai ya koma cikin motar zuciyarsa duk babu daɗi kawai kukan tane yake masa yawo akai yana tuna marin da yaji anyi mata runtse idonsa yayi jin marin acikin kansa kamar yanzu akeyin sa haka yake jin ƙarar sautin sa, buɗe idonsa yayi da har sunfara canza kala damƙe hannun sa yayi tare da kaiwa stirring ɗin motar duka,

yana zaune acikin motar yakasa tafiya daga ƙarshe ma kifa kansa yayi akan stirring ɗin gaba ɗaya yakasa gane kansa ji yake bazai taɓa iya tafiya ba batare da yaganta ba,

ihunta yaki ya daki kunnen sa kamar daga sama da sauri ya ɗago dakan sa zuwa inda yajiyo sautin nata,

idonsa ne ya sauka akan ta anturota daga cikin gidan tare da watso mata kaya ajiki tashi ta ƙarayi daga faɗuwar da tayi ga ƙara nufar bakin ƙofar,

da sauri ya buɗe motar ya fito ya nufi wajen,

Wallahi sai kinbar gidan nan bazan iya cigaba da wahala dake ba kina lalatamin ƴaƴa ba tunda uban naki ya gudu yabarmu sai kikama gaban ki daman arziƙinsa kike ci tunda kwa yanzu baya nan dole kema kiyi gaba sai kije kicigaba da karuwan cin dakikeyi kamar ya da uwarki take sai kije ki tayata dama tasamu da ina hanaki bakiji to yanzu na buɗe miki ƙofa kije duk inda zaki ai ku abun kunya gaba yabaku ba baya ba shegiya matsiyaciyar ƴar gidan karuwar masu baƙin hali, sai faman cimata mutunci take awaje,

Ita kuma sai faman kuka tana roƙonta amma bata saurare taba tana gamawa ta koma ciki tare da banko ƙofar gate ɗin ta rufe,

bakin gate ɗin sumy taje ta tsugunna tan ƙara fashewa da matsanancin kuka ita yanzu idan ma ta tafi ina zata babu wanda ta sani bata da kowa,

duk abun da ke faruwa gaba ɗaya akan idon sam jin maganganun matar ya hanashi ƙarasawa wajen sai yanzu yafara takawa ahankali zuwa gurin ta zuciyarsa nayi masa wani irin suya tausayin tane yakama sa duk rashin tausayin sa yaude yaji wani irin mugun tausayi akanta,

tsayawa yayi abayanta tsawon ƴan mintina baice komai ba,

batare da yace komai ɗin ba yaɗan ranƙwafa kanta yasa hannu gaba ɗayan ta ya ɗago da ita ya tsayar da ita tsaye,

atsorace ta juyo dan ta tsorota saboda batasan da zuwan saba gurin suna haɗa ido dashi tagane sa ai tunkan ya buɗi bakima yayi magana ta faɗa kansa ta rirriƙe sa tasake fashewa da wani kukan da yafi na ɗazu ita kanta batasan dalilin yin irin wannan kukan da tayi ba yinsa kawai take ba ƙaƙƙautawa hannun sa ya ɗaga zai ɗora abayan ta sai kuma yafasa yayi hakan wajen sau uku yana kai hannu yana janyewa da ƙyar de ya rufe ido ya ɗora hannun sa akan bayanta shima ya rungumo ta atare suka sauke numfashi,

ahankali ya shiga bubbuga bayan ta alamar rarrashi baide ce mata komai ahaka suka cigaba da tsayiwa awajen ba wanda ya iya cewa komai,

ganin taƙi shirun ne yafara ƙoƙarin ɗago da ita daga jikinsa amma saita ƙara riƙeshi zuwan shi ba ƙaramin taimaka mata yayi ba daman tana son ganin sa sai gashi yazo adidai loƙacin da take buƙatar sa,

jin ta riƙeshi bai takura mataba wajen rabasa da jikin nasa ba ɗan ɗagata yayi kaɗan yarabata da jikin sa  ahaka tana jikin sa yafara takawa da ita ya nufi wajen motar sa da ita, yana zuwa ya buɗe gaban motar yasaka ta aciki sannan ya zagayo shima ya shiga yana shiga kuma baicemata komai ba haryanzu ya tayar da motar kawai yayi rivers yabar unguwar da ita.........

_____*shettima& Azeema*______

   cike da tsoro take binsa da kallo,

shikuma yana takowa wajen ta yana sakin murmushi ganin yanda ta tsure ta zazzaro ido sai abun yasa shi nishaɗi hannunwa a harɗe akan kirjin sa yake takawa zuwa wajen ta,

ganin yakusa zuwa inda take yasata fara ja da baya da baya shi kuma yaci gaba da binta ahaka suka cigaba yana binta tanayin baya har suka kai ƙarshen bango sannan ta dakata da tafiyar matsowa yayi jikin ta sosai har tana jin saukar nufashin sa akan fuskar ta,

  cikin wata irin murya da ita kanta batasan loƙacin da tayi taba tace "Please stop it tayi maganar can ƙasa ƙasa ƙurawa fuskar ta ido yayi yana kallon bakin ta da tayi maganar dashi wani abu yaji ya taso masa tundaga kan yatsan ƙafar sa har tsakiyar kansa ahankali ya lumshe idanun sa tare da buɗe su aloƙaci ɗaya ya saukesu akanta haɗa ido sukayi tayi saurin janye idon ta daga garesa ganin wasu abubuwa da suke fitowa daga idon sa suna shiga nata dan haka bazata iya jurar kallon nasaba,

raɓawa tayi ta gefen sa zata wuce yayi saurin tare ta ɗayan gefen ma ya tare da ɗayan hannun sa maganganun su sam me ya shiga dawo masa arai saurin kawar da tunanin yayi,

tagaji da abun da yake mata duk yabi yasakata awani hali ya hanata tafiya,

buɗar baki taƙara yi kamar yanda tayi magana ɗazu haka yanzuma ta ƙara yi cikin sanyin murya me kama da shagwaɓa tace "pls kabar ni intafi aiki fa nake na roƙeka plsssss,

yanda ta ƙara yin maganar tama fi ta ɗazu sakashi a wani halin,

"kinga yace da ita,

dagowa tayi tana kallon sa cikin marairacewa da murya yace nima plss sau ɗaya kawai da mamaki take kallon sa batare da tace komai ba me yake nufi da sau ɗaya kawai dan haka sai tayi shiru bata basa amsa ba ta juyar da kanta gefe,

hannu yasa ya juyo da fuskar tata suna fuskantar juna ya ƙura mata ido itama shiɗin take kallo yanzu bata janye ba,

da ƙyar ya buɗi bakin sa yace "kibani dama plsss ya faɗa yana lumshe ido yana buɗewa,

duk da batasan me yake nufi ba amma sai ta shiga girgiza masa kai..

wallahi ranki ya daɗe suna ciki yanzu nan fa yace infito daga ciki kuma ita baice ta fito ba shiyasa nayi gaggawar sanar dake saboda kizo ki kallewa idanun ki ganin ya kori ji,

atsorace Azeema ta kalle sa tace wayyo Allah na kajawo min masifa dan Allah kafita kar suzo sutarar damu ahaka,

ko gezau bayi ba saima ƙara matsawa dayayi jikin ta ya mannata da jikin sa,

kuka tashigayi masa tana roƙonsa tana ƙoƙarin kwace jikinta amma ya hanata damar yin hakan,

da ƙarfi fulani ta turo ƙofar ta shiga ciki,

kitchen ɗin ta shiga bi da kallo sai ta juyo ta kalli me aikin da alamar tambaya a cikin idon ta,

kafeta da ido Fulani tayi kafin tace ya banga kowaba kinsande babu abun da nafi tsana arayuwa ta kamar ƙarya baki tabbatar ba kikaje kika taso ni har inda nake

  girgiza kai tana cewa wallahi ba ƙarya nake ba ta faɗa tana  bin kitchen ɗin da kallo tana inda inda tace wallahi Allah anan nabarsu dakansa ya koreni daga ciki itama kuma tana ciki ya rufe ƙofar tayi maganar tana rarraba ido da tunanin to ina suka tafi sunsa taji kunya  ance ƙarya take,

wallahi saidai idan ɓuya sukayi amma suna cikin nan gurin ni nasan basu fita ba bari induba ko ina suna cikin nan ba inda sukaje,

"kin tabbata suna cikin nan?
"eh wallahi"

su Azeema dake laɓe abayan ƙofar store  ɗin kayan abinci dake kitchen ɗin tunda sukaji muryar su dab da shigowa cikin kitchen ɗin yayi sauri yajata suka shige suka ɓuya, Azeema jin batun za afara dubawa ta tsure saura kaɗan ta saki fitsari jikin taba ɗaya ya ɗauki ɓari,

  ahankali yace "ke ki nutsu babu abun da zai faru baza sugan muba,

"Wallahi sai sun ganmu gashinan fa zasutaho wallahi duk kai kajamin nashiga uku jin zata tona musu asiri yayi saurin toshe mata baki da hannun sa shi ba tsoro yake jiba kawaide yasan idan aka gansu abun akanta zai ƙare kuma ya ƙudartu niyar wallahi sai yaci uban matar nan da taje ta faɗa ma fulani gobe ma idan akace taje tayi munafurci bazata yiba ko aiken ta akayi bazata faɗa ba,

ɗan ɗaga murya Fulani tayi tace "tunkan ku wahalar dani wajen neman ku inkunsan kuna ciki

48 / 74