Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   14 / 74

39K to 42K   out of 221K words

yaje amma bazai yarda yabisa ba gudun kar yaqara mazgesa a hanya
cikin lallami da lamana yafara yimasa magana kaga nifa ba dukanka zanyiba kawai katashi kaje inda tace din ni nabarka lafiya yafada yana saurin barin wajen gudun karma yayi masa wani jawabi tashi baba yayi yace ni bari intafi yaro kai kuma kaje inda yace maka din kar ka kuna jawowa kanka matsala tashi yayi shima yace baba muje ba inda zani inta isa tazo ta jani ta kaini wallahi matar inba bata bini ahankali ba sai na koya mata hankali(🤔uwar masarutar guda zaka koyawa hankali lalle wanga mutum akwai tsaurin ido yaseen nidai ba ruwana🤐 idan tajika),

babane ya kalle sa yace a'a karkace haka kaje kawai ni wlh banason karinga yimata wannan abun kai ko tsoronta ma naga bakaji bakasan tasa ayi maka wani mummunan abun kallon baba yayi kawai yadanyi murmushi me cike da ma'noni kalakala sannan yace kar kadamu dani baba muje ba abun dazai sameni dan nafi qarfin ta wallahi bata isa tayi min wani abun ba yaqarasa fada yanayin gaba baba de da kallon mamakin irin qarfin halinsa yake sannan shima yabi bayansa yana dan jin dadin ganin shima ba ayi masa wani hukuncin ba lokacin da ya isa dakin su yatar da Hamza har yacire rigar jikin sa yayi kwanciyar sa hankalin sa a kwance baba ya kalle sa ya kar kada kai yace Allah ya shiryeka amma nide wlh inajiye maka abun dakanje yadawo nide wallahi ka barmin daki karkaja min kaga ahakama batasan guri daya muke kwanba da bansan wane danyen aikin zata kuma yimana ba dan Allah ka rufamin asiri ka rufawa kanka kazo ka tafi wajenan kaji yafada yana zama kusa dashi tare da zuba masa idanu yana jiran yaga ya tashi,

tashi yayi zaune baba yama dauka tafiyar zaiyi hat yafara jin dadi aransa sai kawai yaga ya koma yaqara kwanciya yace baba nifa banason mita tunda nace bazani tofa ba wanda ya isa yasani inje ko itace tazo da kanta saidai idan daukata zatayi takaini in kwa ba haka ba saidai ta rabu dani yafada yana rufe idanun sa alamar bacci zaiyi,
karkada kai baba yayi kawai batare da yaqara cemasa ko uffan ba yaja bakin shi yayi shiru daga bisani kuma yatashi ya shige bandaki,

Kwan kwan kwan hamza yaji ana buga qofar bude idon sa yayi tare da jan tsaki ya kuma juyawa ya koma ya kwanta jin anqara bugawane akaro na biyu yasa shi miqewa afusace ya fito dan zabgawa koma waye masifa,
yana bude qofar zai fara zazzaga masifar sai kawai bakin sa ya makale masifar ta koma ciki yakasa furta ko kalma daya sakama kon tozali da idanunwansa sukayi masa da ita cak ya tsaya yana binta da kallo itama shi take kallo...................✍️

tofa wa hamza yagani da yasahi kasa magana kode matar da yake cika bakine tazo da kanta abun da baitaba tunani ba shiyasa yakasa magana ko kuma watace daban saidai gobe maji ko wacece wannan da tasa sashi yin shiru muje zuwa.................✍️
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿25&26

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️





Kwan kwan kwan hamza yaji ana buga qofar bude idon sa yayi tare da jan tsaki ya kuma juyawa ya koma ya kwanta jin anqara bugawane akaro na biyu yasa shi miqewa afusace ya fito dan zabgawa koma waye masifa,
yana bude qofar zai fara zazzaga masifar sai kawai bakin sa ya makale masifar ta koma ciki yakasa furta ko kalma daya sakama kon tozali da idanunwansa sukayi masa da ita cak ya tsaya yana binta da kallo itama shi take kallo...................


"ita tafara kawar da idonta gefe tare da sunkuyar dakai sannan murya can qasan makoshi tace kaine Hamza?

saida ya hadiyi yawu tare da abun da ya makale masa awuya sannan ya kuma dubanta tundaga sama har qasa kana daga bisani yace "eh"

Sannan tace uwar masarautace take some ganin ka yanzu nan tace mutafi tare tana wajen gurin nan tana jiranka agun, "wani kallo ya watsa mata sannan yace ita me ya hanata zuwa da kanta kije kice idan ta isa tazo da kanta...yana gama fadar haka ya rufe qofar sa yakoma yayi kwanciyarsa,

da mamaki Azeema tabi qofar da kallo tana tunanin wannan waye shikuma da har akace anakiran sa amma wai bazezo ba tazo da kanta amma koma waye yajawowa kamsabala'i dan bega ayanda tazo wajen take nemansa ba da baifara cewa ajen ace bazai zo ba yanda fuskarta take ahade nan kana gani kasan ba sauqi da fushinta ta taho wajenasa Amma shikuma ga abun da yace tabb babbar magana saida tagama tunanin nata sannan tayi gaba abunta,

" tana zuwa wajen ta ta sunkuyar da kai tace ranki yadade nasanar dashi amma sai yace wai inje gashinan zuwa danace masa kince mutafi tare sai yace ba yanzu zaizo ba sai yayi wanka zaizo yasameki a sashenki wai kiyi hakuri yanzu zaizo tafa qarasa fada tana kifkifta ido dan itade ko hauka take bazata iya gaya mata abun da yace ba sai taga kamar ita tayi rashin kunyar da hakan be dace yafada ba to amma ita tayiwa zancen nasa kwaskwarima

da dan mamaki fulani take kallonta a iya sanin ta da yaron baitaba bata hakuriba amma shine da kansa yanzu yace tayi hakuri lalle wannan abun abun mamakine agareta
shiyasa daman da akazo akacemata hamaza yace baza adakesaba kuma bazaije gidan qasan da taceba akaisa ba yama yi tafiyarsa daki dataji hakan shine kawai tace bari tazo da kanta sai ta taho da sabuwar baiwarta Azeema dan takiramata shi ya fitoyasameta awajen,

duk da taso yafito din amma jin ance harma hakuri yabata kuma zaizo yasameta shiyasa kawai taji ranta yadan kwanta har sukayi gaba ta tafi part dinta da niyar jiran sa yaqarasa.....

(Tab nace kam zaki bushe kwa dazaman jiran sa dan ko qyeyarsa ba zakigani ba aradu)


baba ne yafito daga bandakin da sauri ya qaraso wajen yace yarona murya wa naji kaidawaye?
"dabansa Hamza yayi sannan yace wata yarinyace wai an aikota tazo ta kirani, "kaikuma me kace mata cewar baba,"nace mata bani zuwa " dafe kai baba yayi yace amma kaide wlh matsalace dakai yanzu har tazo da kanta kace bazaka ba"Hamza yace wallahi baaba baza niba saidai tarabu dani in kuma zata iya shigo wa sai ta shigo "baba yace ohh sai yanzu na fahimceka dan kasan bazata iya shigowa sashen muba ko shiyasa kake cika baki to wallahi idan bakai ahankali ba saboda kai zata iya karya dokarta nakin shiga sashen masu aiki ta shigo tazo wajen ka,"dan murmushi Hamza yayi me qayatarwa sannan yace to mutuncin waye yazube nata ne ai banawa ba ita zata ji kunya kuma daga lokacin zan qara dena ganin mutuncin ta kai bama nikadai ba duk wanda yaji abun da tayi sai ya kalli abun ta wata siga daban saboda a tarihin gidan nan sarakai da matan su basa zuwa sashen ma'aikata kai harma 'ya'ya yansu basa zuwa inda muke saboda girman kai da suka dauka suka dorawa kansu aganin su idan sukazo wajen mu kar sun qasqantar da kansu sai kace mu ba mutane bane, ni wallahi Allah yasa tsautsayi ya kawota nan har video sai nayi mata in watsawa mutane sai qarshen haukan nata.
da mamaki baba yake kallon sa yace lalle ne wuyanka ya isa yanka wallahi sai yanzu naqara yarda ka raina matar nan kai kowa na tsoron ta amma kai ko dar bakaji aranka to da wacce wayar zakayi mata? nidai bantaba ganin ka da waya ba!

"tashi zaune yayi sannan yace tana ajiye ne bana amfani da ita saboda bata dameni ba banma san abun da zanyi da ita ba agidan nan amma akanta zan daukota addu'a ta shine Allah yasa tazo taga yanda ake aiki da cikawa, "zama baba ya gyara sannan yace nikam inyi maka tambaya ta bakin nata me ka takame da kake ji da kanka har haka dole da abun da kake takama dashi shiyasa ka banbanta da sauran ma'aikata me yasa kake mata haka? "murmushin gefen baki yayi sannan ya mike batare da yace masa komai ba ya nufi hanyar toilet sai yakai bakin qofa sannan yace nataka abubuwa da yawa amma de sirrine asannu kowama zaisan abun da nataka acikin gidan nan saura kiris ta fashe kaida baba ka zuba ido kasha kallo, nan gaba ma sai na fitar da kai daga gidan nan lokaci kawai nake jira.
yana kaiwa nan ya wuce cikin bandakin bai saurari cewa baba ba ya shege tare da rufar qofar,

Shide baba shiru yayi yana daukar maganar sa duk ashirme da shiririta irin tasa dan gani yake ba wani abu da yataka kawai dai rashin jin tsoro ne kuma ya lura ajinin sa yake baya shakkar kowa shiyasa har yake neman ya gagari kowa tunda gashi ko masu yin hukun ci agidan yasaka musu tsoran sa babu me tunkarar sa yayi masa wani abun koda gimbiya uwar masarau ta tasaka su suyi masa sukuma baza suyi ba shiya sa yaqara samun damar yin abun da yaga dama yi batare da fargaba ba.
yana zaune agun yana tunane tunane Hamza ya fito jikin sa duk ajiqe alamar de wanka yayi tunda yafito baba yake binsa da kallo Amma shi kam ko takan sa bebiba duk da yaji ajikinsa baba na kallon sa amma sa ya basar ko kallon inda yake ma beyiba yaqarasa gurin da kayan sa suke shidaman baifiya saka kayan da akabashi na ma'aikata ba duk abun da yaga damar sakawa sakawa yakeyi yanzu ma wasu riga da wando ya dauko kananu yasaka saidai basu kamashi ba kamar ba daidan sa ba haka yasaka su saida yagama shiryawa tsaf sannan ya dubi baba yace baba nayi komai yayi daidai yace kar naje taki kulani,

da baba beyi niyar kulasaba amma jin abun da yace yadago yana kallon sa ga mamaki sannan yace wace zata ganka tace baki daidai ba uwar masarautar ko wa??

"dan bata fuska yayi yace haba baba waccen tsohuwar banzar zanyiwa kwalliya mata tafa nake nufi gurin ta zani yafada yana sakin murmushi da kana ganin sa kasan daga cikin zuciyar sa yake direct,

"cike da mamaki baba yace daman kana da aure shine amma baka taba gayamin ba a ina matar take baba yafada cike da zumudin jin ta bakinsa ,
"dariya hamza yayi har kana iya ganin fararen haqoransa sannan yace baba naga har ka qagu kaji ko to nibanda aure kuma bantaba yiba yanzu de nakeson inje infara farautar samowa duk da bansan ina zangan taba amma koda tana wajen waccen wahalalliyar ne sai naje na nemota wauyar ta in fita amma ina fita zansan komai akanta " baba yace bakasan taba ma shine kakecewa matar ka a ina ka taba ganin ta? da har kake kiran ta da matarka?
" tsayuwa ya gyara sannan yace baba kasan ance so gamon jini akwai wanda kuna haduwa zaka ji ya kwanta maka to nima hakance ta faru dani, "kallo daya bisa qa ida naimata zuciyata sai ta kamu "
Wacce nace maka dazu tazo nemana tsohuwa ta aikota to ita zanje nema yarinyar tamin gashi kuma naga alamar ma bakuwace saboda bantaba ganinta ba sai yau kaga kwa dole inje injiyo news akanta,
saboda mamaki kwa baba yakasa cewa dashi komai saidaga baya "yace to Allah yabada sa'a nide ba ruwana aciki idan ka dawo kanufi dakin ka kar inji kar ingani sai komai ya daidaita ka rage neman fitina sai kadawo,

murmushi hamza yaqara saki tare da fadada fara'ar fuskarsa "yace baba wallahi ba inda zan koma ina nan idan nagama ganota ma harnan dakin zankawo ta itama daga qarshe innema mata 'yancin kanta tadena bautawa waccen matar,
"baba yace dawa zaku zauna saidai idan ni zanbarmuku dakin amma bada niba aciki,"kai baba wallahi kafiya tsoro kai da kake dani kuma meyasa zaka ringa tsoro ko yatsa wani yanuna maka saina karya masa yatsa dan haka kadena tada hankalin ka ka kwantar da hankalin ka kamar kayi bako ya mutu "kaga ni ka isheni da surutu tafi kaban wajen Allah ya tsare dan Allah tafi cewar baba yana magana yana nuna masa qofa,

kafada ya daga sama sanna yace ai ko baka koreni ba yanzu zantafi yafada yana nufar qofar fita tare da fara yin waqa.........

*Dakece zanyi wuff, zanyi wuff.....
Dakece zanyi wuuf zanyi wuuuf...
zanyi wuf.......
"Kece tawa innda rai da raboo... amanar zuciya kedamketa....*


Ahaka yayitayin waqarsa yana tafiya har yafice daga sashen su ya nufi cikin masarautar kai tsaye da shi kansa besan ta inda zai faraba neman taba.....😜😜😜😜🫣🫣,(Allah kutayani da addu'a kar mukai wajen shekara bamu gama ba, wlh yanzu banason yin typing ina farawa sai inji nagaji😂 bansan me yasaba yaseen gaba daya sai ahankali) pray for me ko zanringaji inayi dayawa batare da nagaji ba
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿27&28

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

    *__Bossay__*

    "bayan ya fito daga gida yashiga mota yabar gidan ransa yana danyi masa zafi saboda maganar auren nan da akayima sa shikadai yasan abun da yakeji,
aransa yana ayyaba irin abun da zaiyiwa wannan yarinyar bade tanace sai ta aure shiba kuma ta shiga tsakanin sa da mahaifinsa shine zata biyo masa ta wannan hanyaryasan halin mahaifinsa indai yace sai yayi abu to ba wanda ya isa yacanza masa ra'ayi dan haka. bashida wani abun cewa dole yayi hakuri yakarbi auren ta amatsayin qaddarar sa jiyake kamar yayi hauka afili ya furta duk ni najama kaina da tunfarko bance inason ta ba da shikenan amma yanzu gashi nan tazo ta zamemin qarfan qaya ana korarta tana qara naniqemin sai kace mayya mtsww ya buga tsaki kamar tana gurin,
ahaka yayi ta tafiya saida yaje wajen wata kwana bayan ya shiga layin sai yasamu gefen titi yayi parking a gefen hanyar sannan ya dauko wayarsa yayi kira ana dagawa yace yawwa na shigo layin ina zanyi ko intsaya kafito,
bansan me akace masa ba daga can bangaren kawaidai naji yace tom shikenan ganin nan zuwa kashe wayar yayi yana qara jan tsaki afili yake cewa yanzu dan rashin mutunci muyi wayar dakai zanzo amma ka wani ce min kuntafi asibiti cike da takaicin maganar da shettima ya gaya masa,
kwafa yayi  tare da tayar da  motar sa yayi rivers yaja motar sa ya nufi hospital din kai tsaye dan bazai iya hakuri ba tunda ya fito dan yaganta dole sai yaga hasken idanusa  zaiji dadi..

bewani bata lokaci ba ahanya sakamakon gudun da yake kwararawa adan qanqanen lokaci yaqarasa bayan yayi horn me gadi ya bude masa yashiha yayi parking a parking lot sannan ya fito ya shiga ciki kaitsaye ya nufi office din shettima tunda daman yasani kuma yana kyautata zaton dole suna can shiyasa be qara kiranshi ba ya nufi gurin,
"nocking yayi daga ciki akace masa "Come in" turawa yayi yashiga da sallama abakin sa, "amsa masa shettima yayi shikuma yaqarasa shiga ya zauna akan kujerar da take facing din shettima tare da miqa masa hannu suka gaisa yadan fara dube dube yana neman Ameesha dan murmushi shettima yayi yace neman ta kake ko dan sosa kai bossay yayi alamar yaji wani iri sakamakon kamansan da yayi,

"tana ciki bacci take cewar shettima "
joyowa yayi ya kalle sa "yace bacci kuma at this time?

"shettima yace eh mana ai ita yanzu   kasan ba daidai take da sauran mutane ba kwakwalwar ta tana bukatar hutu akoda yaushe anfiso ta ringa bacci yanda zatafi samun sauqi da wuri idan tension yayi mata yawa zata iya samun matsala wani lokutan taringa yin abubuwa kamar ba mai cikakken hankali ba,

"cike da gamsuwa da bayanin sa yadan jinjina kai yace ayya Allah sarki Allah ya qara mata lafiya wadanda kuma sukayi mata haka Allah yasaka mata Allah ya toni asirin su,
"shettima yace Ameen thumma Ameen yauwa bari na in tabo sam ingaya masa kana nan kaga sai mufara ma maganar yanzu tunda duk mun hadu sai asan abun yi yafada yana qoqarin dauko wayar sa yana danna wa sameer kira,
"bossay yace gaskiya de nima abun da nakeso ayi kenan wallahi naji shiru be nemeni ba har yanzu,

"shettima dake qoqarin kiran sam yadan dakata ya dago yana kallon bossay shima shi yake kallo,
   "Shettima yace ai inba kiransa nayi ba bazai taba kiranka ba bakasan me kayi masa ba ko ai sa'a ma kaci da yabarka haka ai kabata masa rai duk da kafi bata min raima amma ni nawa me sauqi ne shi sai yafini jin haushi saboda shi beda hakuri ko kadan nayima mamaki da har yayi wannan dadewar awajen batare da yataba lafiyar jikin ka ba,
dariya bossay yayi yace ai naga alama wayagaya maka be tabani ba saida yabani ajiyar mari ai tundaga nan nadan qara tsorata dashi ni nasan ma watakil ba wani girmemin yayi ba amma wai har yadaga hannu ya kwasheni da mari duk girman nan nawa Allah ma yaso ni babyna bata gani da tuni yasani jin kuyarta wallahi wallahi kufara bashi ruwan buta yarage wannan zafi ran dan wallahi idan baidai na wannan halin ba. bazai samu matar aure ba, ba iyayen da zasu dauki yarsu su bashi dan wallahi wataran sai ya baballa musu ita ya cuce su kuma ya kora musu

14 / 74