Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   45 / 74

132K to 135K   out of 221K words

tayi ta kalle sa atake ita kuma ta tuna inda tasanshi amma sai tayi saurin girgiza kai tace a'a tana sunkuyar da kai yace oh sorry kamace kawai wataƙil yana faɗar haka yayi wucewar sa shettima dake tsaye  ya harɗe hannuwan sa ya kafeta da ido yana jiran sugama shi yama manta da ita sai yanzu da suka haɗu,

kwata kwata batasan da tsayiwar sa ba agun amma jin kamar ana kallon ta yasa ta ɗago kanta caraf idon su ya haɗe waje guda cikin duburbur cewa tayi saurin janye idon ta ta juya zata bar wajen yayi saurin riƙo hannun ta tsayawa tayi cak batare da tajuyo ba dawowa yayi gabanta tare da kallon fuskarta,

idon tane yayi rau rau ya taru da kwalla alamar zatayi kuka ganin hakan yasa kawai ya shiga janta suka fara tafiya batayi yunƙurin kwace hannun taba tace gaba da bin sa, part ɗin sam ya nufa da ita,

yana shiga ciki duk suna falo azaune kan kujera bai kalli kowa ba kuma baice da su komai ba ya wuce ɗaki da ita,

duk da kallon mamaki suka bishi ganin baice musu komai ba yasa suma sukayi shiru da bakin su suka zubawa sarautar Allah ido,

yana shiga da ita ya jefata ciki sannan ya juya  ya rufe ƙofar tare da saka mata key sannan ya juyo suna fuskantar juna kallon kallo suka shiga yiwa juna kafin daga bisani ya buɗi baki yace inajin ki kimin bayani shiru tayi ta sunkuyar da kanta tasan me yake nufi amma batasan ma ta ina zata fara yi masa bayanin ba ,

"magana nake miki kinyi shiru yayi maganar cikin ɗan ɗaga murya,

daman kiris take jira ta daɗe bataga wanda tasani ba akusa da ita dan haka akusa take kiris take jira a taɓata,

*dan haka daga wannan maganar sai kawai ta fashe mishi da kuka sosai tafara kuka duk wani baƙin ciki haɗuwa dashi yasa tafara tunanin halin da take ciki na damuwa,

mamakine yakamasa daga magana sai kuka to me yake damun ta haka tausayin tane ya kamasa sai kawai ya kamo hannun wanta yajata sukaje bakin gado ya zaunar da ita ita Kuma bata dena kukan ba jin kukan nata yayi har cikin ransa baisan loƙacin da yajawota jikin sa ya rungume ta alhakin da take ciki a yanzu bata da zaɓin da zata hanasa saboda itama tana buƙatar wanda zai rarrashe ta ahalin yanzu,

kamar zigata yayi tanajinta ajikin sa ta ƙara sakin wani kukan me tsuma zuciyar me sauraro sosai ya ƙara ƙanƙame ta ajikin sa daidai saitin kunnen ta yakai bakin sa ya shiga hura mata iska acikin yana cewa shiii yana ɗan shafa bayanta da ɗayan hannun sa ahankali duk de salon rarrashi shi yake mata,

tun tana kukan da karfi har ta fara yin low da muryarta shikuma yaci gaba da rarrashin ta sunkai wajen 20 minutes ahaka kafin daga baya tayi shiru tare da yin lamo ajikin sa sai kace wata ƴar baby.....,

saidaya tabbatar da ta samu nutsuwa sannan ya ɗagota daga jikin sa fuskar ta ya shiga kallo sai tayi saurin kawar da fuskar ta gefe saboda wata irin kunya taji ta kamata na kwanta masa ajiki da tayi,

hannu yasa ya juyo da fuskar tata sannan yaƙara saka ɗayan hannun hannuwa biyu yasa ya tallafo fuskar ta yana kallon cikin ƙwayar idon ta sannan,  in a slowly voice yace what happened? umhum "gaya min, yayi maganar cikin wani salo da saida tasa tsigar jikin ta tashi,

janye fuskar ta tayi daga hannun sa baihana ta ba yasake ta saboda yabata damar gaya masa abun dake faruwa,

shiru tayi takasa magana saida yaƙara tambayar ta sannan da ƙyarde ta shiga bashi labarin dalilin ta na zuwa gida har ɓatan mahaifin nata tun farko saida ta bashi labari da loƙacin da mutumin yaje yagaya musu inda yake sannan ta shirya tazo gidan amatsayin mabaraciya daga haka kuma har Ammah ta ganota amma bata ce mata komai ba bayan nan kuma ta dawo wajen fulani da zama komaide ta kwashe ta gaya masa amma banda son sameer da take da kuma dalilin suman da tayi rannan duk de abun da yashafi sameer bata gaya masa ba bayan shi kuma babu abun da ta boye masa kuma ta sanar dashi tunda tazo bata taɓa haɗuwa da mahaifin nata ba.....,✍️✍️

ayi haƙuri da wannan amma ba anan naso tsayawa ba amma ba dama saidai idan Allah yakaimu gobe da rai da lafiya.

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/5, 7:27 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 81

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

             
babu abun da ta boye masa kuma ta sanar dashi tunda tazo bata taɓa haɗuwa da mahaifin nata ba.....,✍️

  "yayi mamakin jin labarin data bashi baitaɓa tunanin abun da ake amasarautar har yakai haka ba,

cike da tausayawa ya riƙo hannun ta yana kallon ta yayi shiru yana rasa ta ina zai fara yi mata magana saida suka ƙara ɗaukan loƙaci ahaka batare da ya tanka mata ba,

har saida tayi tunanin ba abun da zaice mata tafara ƙoƙarin tashi daga gurin yayi saurin mayar da ita ta koma ta  zauna cikin ƙasa da murya yace sorry amma me yasa baki taɓa gaya min ba sai yanzu ai da kingaya min tun kafin kizo nan shigowar ki nan shima ai kinyi ganganci ke ahakan ki har kike tunanin zaki iya fita dashi daga cikin nan,

kamar zatayi kuka cikin muryar damuwa tace nima bansan kana da alaƙaba da nan ɗin ai da tuni nagaya maka sai washegarin ranan sa kukazo naganka amma bansani ba nima kuma banyi tunanin abun yakai har hakaba nazata zan haɗu dashi ta cikin sauƙi ashe abun is not easy yanzu dan Allah kataimaka min ko da mahaifina ne in haɗu wallahi inason ganin sa kuma haryau bangansa ba dan Allah kataimake ni,

kar ki damu in sha Allah zanhaɗaku amma idan na haɗaku zan fidda ke daga cikin gidan ki koma gida inyaso kibarmin komai zan dawo dashi amma sai anbi komai ahankali saboda nima da kika gani bawai ɗan gidan bane abokina ne tun na yarinta dan anan ma kusan nayi rayuwata amma duk da haka banda wani iko da zan iya zuwa kai tsaye in faɗi buƙatata ayi min ba bazai yiyu ba musanman irin wannan da sunriga da sun maidashi bawa da sarki da mahaifiyar sa baza su taɓa bari ya tafi ba saidai kawai yafita batare da sanin su to amma fitar ce abu me wahala amma de zansan yanda zanyi infito dashi batare da sanin kowa ba dan ko abokina ma ba lalle ingaya masa saboda idan nagaya masa bashi da haƙuri bazai yarda a fita dashi ba batare da kowa yasani ba sai ya ɗaga murya kowa ma yaji daga nan kuma azo asamu matsala anuna masa fin ƙarfi koma su canza masa wani gurin da bazamu taɓa ganin sa ba shiyasa zanyi komai ni kaɗai idan yaso daga baya sai ingaya masa,

wani irin daɗi taji ya ziyar ceta take tashiga yi masa godiya harda ɗan guntun kukanta saidai kuma a ƙasan zuciyar ta bataso yace wai zai fita da itaba dan tanason fita bata son fita dan wahala tana cin wahala agidan shiyasa take son tafi abun da kuma yasa bataso tafi saboda idan ta tafi shikenan bazata ƙara ganin abun sonta ba bazata ƙara sakashi a idon taba kai inna gaskiya bazata iya juraba gwanda kawai taci gaba da zaman gidan duk sanda suka haɗu tagansa tana jin daɗi aranta hankalin ta yana kwanciya,

"me kike tunani ya tambaye ta yana juyo da fuskar ta da sauri ta girgiza masa kai tace babu komai,

"Ok"  to yanzu inasao kishirya daga yau zuwa gobe koda yaushe ma zan iya sanar dake tafiyar mu tamu yakamata ki koma gida zamanki anan gangan cine idan suka riƙeki to wallahi har mutuwar ki babu inda zakije saidai afita da gawar ki bakisan halin mutanen ba daman da bakizo ba hakan ma ai yazo miki da sauƙi nayi mamaki ma da babu wata matsala har kikashigo kika zauna batare da wata matsala ba,

koda yake kinci sa'a hannun Amma kika faɗa amma da ace farkon shigowar ki kika haɗu da waccen matar da jikin ki yagaya miki dan baza ta taɓa yarda dake ba loƙaci ɗaya, ki godewa Allah da komai yazo miki da sauƙi,

nima kaina wallahi nayi mamaki saboda bansha wahala ba nashigo daman tun kafin ma nazo aranar da mutumin nan yaje yasanar damu nace zanzo yace kar nazo akwai matsala idan nazo amma nidai banjiba mama tayi tayi kar nazo harde muka lallaɓata nida yaya ta amince na taho kuma da nazo sainaga komai yazo min cikin sauƙi dan a ƴan mintina nasamu dama har na shigo ciki,

ɗan jinjina mata kai yayi sannan yace nima nayi mamaki,
"dan wallahi ranar da nafara ganin ki ranar ba ƙaramin mamaki nayi ba koda na haɗu da yayan ki naso muyi maganar dashi kuma bamu samu damar zama ba saboda nima ƴan kwanakin nan muna busy bana samun loƙaci shiyasa bamuyi ba amma yanzu tunda nasani bama sai namasa maganar ba kawai zan rabu dashi in mayar dake gida kawai,

"to kawai tace masa badan tana son tafiya ba saidan ba yanda zatayi,

hakade suka cigaba da ɗan tattaunawa kafin ta tashi zunbur tana wurga ido tunawa datayi da aikin da takeyi na mopping ɗin datake ashe bata gamaba ita tama manta sai yanzu ta tuna cike da tsoro ta kalle sa yace nagode sosai Allah yabar zumun ci bari inje inƙarasa aikin da nake Allah yasa bata fito ba ta nemeni,

  ganin duk tabi ta tsorata loƙaci ɗaya sai ta ƙara bashi tausayi hannu ya miƙa mata alamar ta tasoshi noƙi kafaɗa tayi sannan tace Allah fa ba kyau ana taɓa mutumin da ba muharramin kaba nidai kawai ka tashi da kanka inkuma in tafi in barka anan shikenan sai anjima tafaɗa tare da juyawa zata bar wajen caraf ya riƙo hannun tsayawa tayi batare da ta juyoba tafara jan hannun ta zata kwace shi kuma yaƙi saki yaƙara riƙeshi da kyau sannan ya yunƙura ya tashi abayan ta ya tsaya bazato ba tsammani kawai taji ya rungumo ta ta baya tare da ɗura kansa akan kafaɗar ta daidai kunne murya ƙasa ƙasa yace babu kyau ko kinsan babu kyau ɗin kika kwanta min ajiki ni bance miki ba kyau ba saike,

runtse idon ta tayi da ƙyar ta iya cewa dan Allah kasake ni intafi kuma ma ai bani na kwanta maka ajiki kai kajawo ni tayi maganar tana turo baki kuma bata buɗe idon ta ba,

shima cikin kwaikwayon irin muryar ta yace to da na jawoki meyasa kikazo bakice min ba kyau ɗin ba kuma nima ai da na jawoki bacewa nayi ki kwanta ba amma ki kwanta min akan ƙirjina gashi yanzu zafi yake min dan haka sai na rama indai kina so kifita daga ɗakin nan shima ya ƙarasa maganar yana turo baki kamar yanda tayi,

ji tayi kamar ta nitsi agurin saboda ta ƙaicin sa da yagama kamata,

uhm uhm uhm dan Allah kasake ni wai me nayi maka duk sanda muka haɗu sai ka raɓe ni bansan meyasaba kai hakan daɗi yake maka kana taɓa macen da ba maharramar kaba,

  "Uhm sosai ma inbantaɓa ki ba bana jin daɗi amma idan na taɓaki sai inji daɗi tunda haka kikace,

"barima inƙara yin abun da zaifin daɗi  dan naga alama iya taɓawa bazai gamsar dani ba gwara inƙara da yin wani abun ina ganin yin hakan sai yafi kema nasan zakiji daɗin ko yaƙarasa maganar tare da leƙo fuskar ta,

  da sauri ta ƙara rufe idon murya kamar zatayi kuka tace wayyo Allah  mama na,

dawowa yayi gabanta tare da ɗago haɓarta yana kallon ta ganin ya sakar mata hannu yasa ta faki idon sa ta kwasa aguje ta nufi wajen ƙofa tana zuwa da sauri ta murɗa key ɗin ƙofar na buɗuwa shikuma ya ƙaraso inda take da sauri yakai hannu zai riƙota itama tayi saurin ficewa daga ɗakin data fitama bata tsaya ako inama ko takan mutumin ta bata biba duk da taganshi da tafito amma bata tsaya ta fice daga falon bata daina guduba saida taganta agaban inda take mopping sannan ta zauna tana maida numfashi harda dafe ƙirjin ta afili tace lalle ma wannan mutumin shi ba a abun arziƙi dashi wallahi idan yana wani abun kai ka ɗauka na Allah ne amma sai ɗan iskan son taɓa mata ko kunyama bayaji oh Allah ya taimakeni da bansan abun da zai min ba aikwa da ya cuceni shiru tayi tana tunanin abun da yace mata sai kawai tasaki murmushi ta tashi tacigaba da mopping ɗin tanayi tana tuna moment ɗin su da yafaru yanzu,

aɓangaren sa kam tsaye yayi yana dariya yanda take gudun ba ƙaramar dariya ta bashi ba ita nan aganin ta gudan mishi tayi batasan rabuwa de kawai  yayi da ita ba shi kansa baisan me yasa yake mata hakaba idan suna tare kwata kwata controling ɗin kansa sai yaga yana tayin wasu abubuwan da baisaba ba kuma bayi yake ba sai akanta kawai yake jin hakan dagaskiyar ta tunda suka haɗu indai yaganta akusa dashi sai yaji yanaso yajita akusa dashi ba halinsa bane amma haɗuwar sa da ita tasa ya canza hali amma duk da haka a iya kanta yake iya hakan,

haka yai ta tunani shikaɗai a tsaye abokin ƙofa saida de yaga tunanin bayi masa zaiyi ba sannan ya fara takawa ahankali ya fito daga ɗakin zuwa falo inda ya tadda su sam azaune kamar yanda ya barsu,

  duk zuba masa ido sukayi suna jiran bayani amma sai ya wani basar ya nuna baisan sunayi ba kamar ma shi ba abun da yafaru guri yasamu kusa da Sameer ya zauna yana cewa to yanzu ya muke ciki ne meye mafita wani mugun kallo da sameer ya watsa masane yasa saura koris ya kwashe da dariya saboda yasan ma'anar kallon da yayi masa, 

cike da ƙara basarwa ya dake yace naga kana hararata daga magana nufa tambaya kawai nayi ba wata baƙar magana nafaɗa ba ko nayi kuskure ne a maganar danayi,

  "bossay ne yace haba bawan Allah kaima ai kasan me kayi ba sai anfaɗa ba nan duk kai muke jira,

"ni kuma to gani ai me yake wakana agaya min,

Sameer ne yakai masa duka akai yace wallahi ranka zai ɓaci waza ka mayar shashakai bamason rainin hankali,
kaja yarinyar mutane ɗaki kuma kafito kace zaka raina mana hankali uban me kayi mata harda sakawa ɗaki key,

"Bossay wacece waccan yarinyar?

ɗan shafa ƙeyarsa yayi sannan yace oh wai wannan maganar kuke nufi ai ni ban fahimta ba ƴar aikin kuce fa ai kai yakamata intambaya ko wacece nima bansan taba yau nafara ganin ta,

"Sameer ya ƙara harar sa yace "eh shiyasa naga kariƙo mata hannu ka kaita ɗaki sannan ka ƙulle ahakan shine baka santaba ko ɗan iska maƙaryaci dan tsabar rashin kunya ma bakaji kunyar muba zaka wuce da ita ta gabanmu kushiga ku daɗe duk acikin rashin sanine ko,

dariya yayi har haƙoransa na fitowa sannan yace to ba me aiki bace ai wani aiki makirata tayi mun ɗakin ka ta gyara ta wanke banɗaki shiyasa uaga mundaɗe amma bawani abu da yafaru bayan wannan dan haka ku kwantar da hankalin ku,

  "lalle ma yaron nan kasan Allah idan baka gaya min abun dake faruwa ba sainayi mugun ɓata maka rai me ka mayar damu mahaukata kaga Aliyu jeka kakiramin yarinyar cen da tafita in haɗasu dukan su inci mutuncin su arasa a inda za ayi sai aɗakina kuma karasa ma wacce zaka kaimin ɗaki sai ƴar aiki to wallahi daga kai har ita sai kunyi bayani sai kun faɗan abun da yahaɗaku,

hhhhhh shettima yasaka dariya sannan yace nine ma yaron naka wai kai ban girme kaba mutum sai ɗan iskan son girman bala'i, kai kuma bossay wallahi kar kasake ka kirata nan gurin magulmata kawai ina ruwan ku da abun da yafaru bazakuji komai ba to tsakanin na da ita sirri ne dan gwarama ku haƙura amma duk abun da kuke tunani ya faru to shiɗinne yafaru yaƙarasa maganar yama gyara zama yayi kwanciyar sa akan kujerar da yake kai,

acikisu babu wanda maganar bata ɗaure masa kaiba duk yagama rufe musu baki sunma rasa amsar da zasu bashi,

yagama kai sam ƙarshe da mamaki tunda suke baitaɓa ganin sa da mace ba kuma irin haka bata taɓa faruwa ba amma wai yau da me aiki ya shiga ɗaki kuma suna tambayar sa amma yaƙi yagaya musu yana faman raina masa hankali,

to kwa wallahi ba isaba bari shi yaje da kansa hakira yarinyar zasu cu ubansu dukan su dan bazai ɗagawa kowa kafa ba yana ayyana hakan yamiƙe tsaye da sauri zai fita waje wayar sa dake kan  center table ta fara ringing dawowa yayi ya ɗauki wayar sabuwar number yagani sai kawai ya maida wayar ya ajiye sai kuma yatuna  kode managen nanne yake kiran sa ko kuma wani ne daban kira me amfanine yana wannan tunanin har wayar ta katse  wani kiran ne yaƙara shigowa akaro na biyu hannu yakai ya ɗauki wayar sannan ya amsa kiran tare da saka wayar a speaker sai yayi shiru yana jiran yafara ji daga can,

kukan tane yafara dakar dodon kunnen sa atake yagane ko wacece me kiran sauri yayi yacire wayar daga speaker yasaka ta a kunne sa tare da saurin barin wajen ya nufi ɗakin sa,

yana tashi shettima yayi zunbur ya

45 / 74