Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   26 / 74

75K to 78K   out of 221K words

bin fuskarsa da kallo tare da ƙara nazarin sa,

duk da wannan bayanin nasa shifa haryanzu bai yarda dashi yasan dole akwai abun da yake boyewa saboda shi yana da baiwar saurin gane marar gaskiya wani tunanin ne yafado masa arai dan haka sai kawai ya sassauta murya tare da zama agabansa suna kallon juna sannan yafara magana yace nasan kasani dan ko rantsuwa nayi bazata cini ba naga rashin gaskiya a idon ka kuma wannan abun daka ga inayi maka akwai dalili  dan haka  karkamin ƙarya kar ka boyemin duk abun dakasani domin hakanne  kadai zaisa kabar gidan nan daga kai har ita din dan saina musguna muku kamar yanda kake shirin yimana Yakamata kakama kanka ka kama girman ka bazan ƙara taɓaka ba saboda ƴarka kasan inda dare yama kacire hannun akan wannan case din dan baƙaramin case bane bakasan komai ba bakasan kowaye mutumin nan ba bakasan labarin sa ba kawai andoraka akai kaikuma ka hau ka zauna zaka dauki alhakin sa dan haka ina gargadin ka da kacire hannun ka tun kafin lokaci yaƙure maka tun kan kafara da nasani abune hawa hawa shima da mukace kagaya mana bashi muke nema ba kawaidai ta sandin sa zamu iya gano wanda muke nema,
kawai  zallar mugunta akayi masa aka rufe sa ba tare da ya aikata komai ba kuma sun hana kowa saboda wani ƙudurin su da yake kansa Ni yanzu bazan iya baka labari ba amma inason ko nawa yake baka ni kuma zan ninkamaka sau uku kagayaman duk wani abu da kasani akan wannan case din,

    "sosai jikin sa yayi sanyi shiga daman kawai mayan kudine shiyasa yaƙi gaya musu saboda kar yarasa wancen kudin da za abasa amma yanzu tunda yaji za aninka masa to ba abun dazai hanasa fada mishi,

   saida ya gyara zama da kyau yana fuskantar sa har zaiyi magana sai kuma yayi shiru,

ganin hakan yasa sameer cemasa inajinka kafadi duk abun dake ranka,

   dan numfasawa yayi sannan yace "zan gaya maka iya abun da nasani amma fa kafara min alkawarin tura min kudina saboda nasan wannanne ƙarshen aiki na aƙarƙashin sa dan haka dole ina buƙatar kudin da zan samu incigaba da juyawa yaƙarasa maganar yana kawar da idon sa gefe yanajiran jin amsarsa....

"baka da matsala karkadamu da wannan cewar sam,

    "agaskiyar magana wannan case din naku bansan komai ba akai kamar yanda kasani kuma bansan mutumin da kuke magana akaiba ƙarewa ma ni bantaɓa ganin saba,
iya abun da nasani shine wannan mutumin da kaji nayi waya dashi shine ya sauka daga kai kuma shi laluboni intaƙaice maka bayani ma bawannan fannin nakaran taba hakannan yasame ni da maganar abokin wani makocinane tun ada amma yanzu yama tashi daga unguwar alokacin yasameni yace yanaso yaban aiki gidan yari zaiban office dinsa nace masa nifa bawani karatune da ni me ƙarfiba da har za abani aikin office sai yace wannan ba matsala bane indai zanyi yanda yakeso shikenan shi zaji da komai ba ɓata loƙaci na amince masa saboda shine babba agurin kuma yagama siye kowa agun ba wanda baya bin umarnin sa sai abun da yace akeyi agidan nan shiyasa ma hukuma batasan me akeyi aciki ba koda anzo dubamu yana kafawa kowa abun dazaiyi baza ataba zuwa akamasa da wani laifi ba shiyasa ma yaɗorani akai saboda yana da muhimmin wani abun da yakeyi amma loƙaci zuwa loƙaci yana kawo mana ziyara sannan yana kiran waya yaji duk halin da ake ciki shiyasa tunda nafara nima ba ataba samun wata matsalaba ina aiki batare da gwamnati tasan dani ba,

wata rana yazo yana neman wani file hankalin sa yayi matuƙar tashi da baigansa ba aloƙacin ya rufe ni da faɗa akan innemoshi duk inda yake inbahaka ba sai ya kasheni duk inda nasan nakaisa ma infito dashi,
nima ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba jin abun da yace nan ya fita yabarni na hau bincike gabadaya office din Saida na hargitsashi ina neman sa amma bangansa ba haka na kira bagaya masa bansan inda yake ba,
ƙara dawowa yayi shima ya duba dakansa amma baigansaba dayaga haka sai kawai ya yanke shawarar yace ko watakil yatafi dashi zaije ya duba amma nima intabbatar na ƙara dubawa, na amsa masa da yo,

har zai tafi sai nace masa wane irin suna zangani ajiki sannan kuma wane irin case ne,
nan yake cemin wani case ne daɗaɗɗe kuma wanda ake case din akansa anriga anfita dashi baya cikin prison din file din sane kawai aciki shima kuma za afita da shi yaɗora min da cewa ko ba dade ko najima yasan za azo memansa dan haka kar masake ma fadi wani abu ince bansan komai ba saidai akira wanda case din ke hannun sa tunda mukayi maganar kusan kullum sai yakira yaji batun ganin sa amma ince bangansa ba,

bansan kuma ya akayi ba kawai yadena kira yatambaya ko ganin sa yayi oho baigaya min ba,

ni kuma aloƙacin ne nafara binciken ko waye tunda naji abun da yace nafara zarginsa akan baida gaskiya akan wannan case din yaza ayi ace anfita da mutum daga ciki ba tare da angama bincike ba kuma har ana neman file dinsa wanna case din da alamar tambaya akansa,

nan nafara tambayar wani tsoho ko yasan case din yace min eh yasan dashi a kawo sane kuma anƙi barin kowa yagansa sai wani mutum kuma ba afito dashi daga daki kamar sauran ƴan gidan kullum yana ɗaki kuma shi kadai babu wanda yasan me ya aikata saboda komansa ba irin na sauran bane,
yataba bani labarin akwai wata mata datake zuwa wajen tana neman sa amma ance mata baya nan kullum sai tazo dayagade tanace da zuwa sai ya taimaka mata har inda yake yayi mata hanya aɓoye ta shiga tagansa tayi wajen zuwa biyar kuma sai akayi masa rasuwa mahaifin sane ya rasu dayatafi kuma sai matarsa ma tafara rashin lafiya aƙallade yakai wajen wata biyu baidawo ba da yadawo kuma sai yadaina ganin ta baima dadeba kuma sai shika sa wancen mutumin da take zuwa gurin sa sai akafita dashi daga gidan ma gabadaya tundaga nande bai ƙara samun labarin saba dagashi har matar datake zuwa wajensa bata ƙara dawowa ba abun da yasani kenan shima,

"harzuwa loƙacin dana fara aiki,
tunda ga laƙacin na ƙarfafa bincike gurin nagano inda file din yake amma shiru bangasaba har yanzu da nake maka magana,
"tunda mukayi maganar wataran kwatsam ya kirani cewar yaga file din sannan yaƙara jaddadamin akan duk loƙacin da akazo neman sa  inyi saurin sanar dashi nace masa to,
duk bayan sati daya sati biyu yakan kira yaji ko anzo nemansa amma ince a'a"aranar da mahaifinka yakirani na sanar dashi cewa wani yakirani akan zakuzo akan maganar mutumin nan da kuke magana shine yace kar nasake magaya muku inda yake kuma idan nayi hakan zai ƙara min kudi akan albashina kaji dalilin da yasa naƙi gaya muku iyakacin abun danasani kenan,
yaƙarasa maganar yana dan kallon sa,

  "miƙewa sameer yayi yafara zagaya dakin ransa na wani irin zafi yayi wajen minti biyu batare da yace komai ba saida yagama zagayan sa sannan ya juyo yana kallon sa sannan yace "a wace unguwar yake da zama kasan gidan sa?

    "eh nasani nataɓa kaimasa saƙo har gidan sa da yake da zama,
Shikaɗai yake zaune ko tare yake da iyalen sa?
   shikaɗai yake zama ko aure ma baitaba yiba,
      
"zaka iya yimin kwatancen gidan da unguwar?
     nan ma eh yaƙara cemasa,
good 👍 ina jinka kwatan tamin,
nande yabasa address din inda yake sannan yadora da rokon sa akan dan Allah karyagaya masa shi yagaya masa dan zai iya daukan mataki idan yaji koda akan iyalen sane shikuma bayason abun da zai shafi ahalinsa yafiso koma me za'ayi ayi masa iya shikaɗai,

    nan yace babu abun dazai sameka muna nan daga ranar da yazo hannun mu to yagama yawo komansa yazo ƙarshe,
nan yaji dadi sai yanzuma yake ta danasanin ƙingaya musun da yayi gashi yazo yasha najaki abanza,

    "zakaci gaba da zama anan har zuwa loƙacin da zamu kamo sa,
kamar aradu yaji maganar tasa shi duk atunanin sa tunda yafaɗa musu shikenan zasu rabu dashi kawai yabashi kuɗin shi yaƙara gaba bashi ba komawa aikin gidan yari watakil ma ya haɗa iyalansa subar garin amma sau yaji wannan zancen nasa da bai taɓa tunani ba,

    sameer ne ya katse masa tunanin sa da cewa kaji de abun da nace ko saboda tsaro badan tsoro ba dole mu cigaba da riƙeka idan komai ya kammala sai mu sakeka katafi amma bazai taba yiyuwa nasake ba batare dashi yazo hannun muba idan mukai haka munyi kuskure,

   "to amma ba na riga nagaya maka ba nikuma meye nawa aciki kaga dan Allah kabarni natafi duk abun da nagaya maka gaskiya nagaya maka kuma bazan yaidare kaba tsakanina da Allah nagaya maka kurabu damu mutafi katuramin kudina kuma,

     bazai taba yiyuwa ba kama dena bata bakin ka zande mayar da ƴarka gida amma kaidai bqzan sakekaba sai gobe idan mun kamoshi sannan kai kuma in sallameka dan haka kamadena wahalar da kanka dan nariga dana gama magana,
yana kaiwa nan ya fita yabarsa adakin,

    "Yana fitowa yayi karo da sumy abakin ƙofar ta haɗa kai da gwiwa tana tafaman shashsheƙar kuka,   "tana jin bude ƙoafar tayi saurin ɗagowa ta kallesa kawar da kansa yayi gefe,
kulle dakin yayi sa key,

   da har yajuaya zaunar gurin batare da ya kulataba har yayi taku biyu sai kuma ya tsaya juyowa yayi yakalle ta ganin yanda fuskarta tayi gaje gaje da hawaye gashi tayi jaa idon ta duk sun kunkubura saboda kukan da tasha,
hakan nan yaji ta ɗan basa tausayi maganar gaskiya maganganun ta sun dan tabashi yasan baiyi mata adalciba baikamata yadaki mahaifinta agaban taba gashi itama batasan hawa ba bare sauka yaje ya daukota yakawo ta nan sannan yadaki mahaifinta agaban ta itama kuma ya mareta kuma yarabata da mahaifinta,
tuna maganar da tayi masa nacewa kai yanzu wani yadaki mahaifin ka agaban ka wane irin mataki nema baza ka dauka ba saboda ni macece shiyasa to kai da Allah in Allah ya yarda sai kasamu wanda zaimaka fiye da yanda kayi mana,
tabas maganar ta gaskiya ne uba baifi uba ba bawanda za ayiwa haka ya ƙyale dan shi aganin sama idan wani yayi kuskuren aikata wata maganar ma da baigamshe sa ba sai ya canza masa kamanni sai inda ƙarfin sa yaƙare bare kuma takai ga agaban sa wani yadaki mahaifin sa ai inajin sai ya iya raba mutum da numfashin sa jikin sa yaji yayi sanyi ahankali ya shiga takawa har zuwa gabanta tsayawa yayi sai kuma ya rasa me zaice mata....
miƙamata hannu yayi batare da yace mata komai ba alamar takawo nata hannun,

     "jin tsayuwar mutum akanta yasata dago kai karo tayi da hannun sa,
hannun ta tsaya kalla sannan ta shiga bin hannun nasa da kallo har zuwa kan fuskarsa suna haɗa ido da ita ya gallamata harara tare da hade fuska,
kasaƙe tayi tana kallon sa ganin hararar da yayi mata batasan loƙacin da itama ta mayar masa da harar ba tare da sakin dan siririn tsaki ta kawar da kanta,
   sarai yaji tsakin da tayi masa kawaide ya rabuda itane saboda tausayin ta da yake ji idan yace zai biye mata zasu bata loƙaci ita rashin kunya shikuma bazai daukaba dukan ta zai tayi kuma ita zatasha wuya shiyasa kawai ya rabu da ita kawai yanzu baida loƙacin ta,
janye hannunsa yayi daga miƙamatan da yayi ahankali tace tashi mutafi ko motsawa batayi ba bare yasa ran zata tashi ƙara maimaita mata yayi,

  "amma still de bata motsa ba, tsugunnawa yayi agabanta yace bakiji me mace miki bane yafaɗa yana leken fuskarta afusace ta juyi itama ta hade ran tare da doka masa harara sannan cike da tsiwa tace naji din banzan tashin ba ba inda zani batare da nahaifina ba mugu kawai marar tausayi,
kafeta yayi da ido baya ko ƙiftawa hakanne yasata hadeye sauran maganar da take shirin yi itama batasan lokacin da tasaki jiki takama kallon ƙwayar idonsa ba kallon juna suka shigayi batare da kowa yasan dalin kallon ba.........✍️✍️✍️



               💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(mrs bmb)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
           
[6/6, 9:40 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

               💖NEW TEAM💖
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️49&50

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

kafeta yayi da ido baya ko ƙiftawa hakanne yasata hadeye sauran maganar da take shirin yi itama batasan lokacin da tasaki jiki takama kallon ƙwayar idonsa ba kallon juna suka shigayi batare da kowa yasan dalin kallon ba.........✍️

   "ita tafara kawar da idon ta daga garesa tana ƙara tamke fuska,
  sai loƙacin shima yadawo cikin hayyacinsa dan sosa kai yama rasa yazaiyi da ita ya fuskanci inyaci gaba da biye mata rainasa zatayi gashi kuma sai ƙara bata masa loƙaci takeyi tunanin hakan yasashi baiƙara yimata magana ba bazato ba tsammani kawai taji ya miƙar da ita tsaye tare da kamo hannun ta zai fara tafiya da ita aikwa tayi saurin sakar masa kuka tana kwace hannun ta "kasakeni nace maka ba inda zani batare da mahaifina ba"ko kallon ta baiyi ba yaci gaba da janta suna dab da fita, "taƙara jan burki cikin sanyin da ita kanta bata san loƙacin da tayi ba, shima kuma sanadin hakan yasashi dakatawa da tafiyar da yake yi,
  "dan Allah dan Allah fa nace taya kake tunanin zan iya tafiya inbar mahaifina anan acikin irin wannan halin kataimakawa rayuwata idan ma natafi nabar nan bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba ko bacci bazan iyaba mahaifina shin uwata shine ubana shine gatana banida kowa aduniyar nan sama dashi taya kake expecting din zan iya tafiya inbarsa kasan radadin da nakeji acikin zuciya aduk loƙacin da naganka amatsayin wanda yadakar min uba agabana ubafa mahaifina ka daga hannu kadake shi agabana akan idona akan abun da bai taka kara yakarya ba meyasa meyasa zakamin haka bayan ka yaudareni kaje hargida ina kwance cikin kwanciyar hankali kaje  ka yaudareni nashiga motar,har abada bazan taɓa yafemaka ba Allah ya isa tsakanin na dakai taƙarasa maganar tare da ƙara fashewa da wani irin kuka kai kanajin kukan kasan cike yake da ƙunci da tsantsar ɓacin rai jitake kamar tashaƙeshi sai taga yadena nunfashi tukunna tasakeshi"

"tana kaiwa nan da ƙarfi ta kwace hannun ta daga riƙon da yayi mata da sauri ta juya zata bar wajen yayi saurin riƙota tare da jawota tafaɗa kan ƙirjinsa, "jin haka ba ƙaramin tsorata tayi ba hakan yasata sakar masa kuka awajen saitin kunnen sa,
damƙe idon sa yayi ƙam batare da yasan me yake ba ya rungume ta tare da tallafo bayan ta da duka hannu biyu atare suka sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ahankali yashiga dan bubbuga bayan ta alamar de kamar zai rarrasheta yanaso yace wani abu amma yakasa bude bakin sa saboda nauyin da yaji yayi masa, yafa fara kasa gane kansa tunda ya hadu da yarinyar nan sai sawa take yana yin wasu irin abubuwan da baitaɓa yiba amma yabar hakan kawai da tausayin ta dayake watakil shiyasa yake mata haka,

kokarin miqewa takara yi amma ya hanata yaqara riqeta tayanda baza ta iya kwace kantaba,

harcikin ransa yakejin kukan nata yanaso yace tayi hakuri amma yana jin bazai iyaba yasan baikyauta mata ba kuma saidai tayi hakuri dan bazai iya barin ta anan wajen ba kuma bazai iya sakin baban ta ba batare da sungama bincikensu ba dole sai sun riqeshi saboda har yanzu baigana yarda dashi ba yasan idan yasankeshi watakil yakira wancen din yagaya masa shikenan ya ruguza musu shirin sa shiyasa bazai sakeshi,

Amma gashi ita kuma tasakanshi agaba sai faman rigima take masa kuma yarasa ta yanda zai fahimtar da ita,

sai mutsumutsu take masa ajiki sanadiyar hakan kuma ya haifar masa da wani irin yanayi da be gama tantance na meye ba cikin qasa qasa da murya yafara yimata magana niba zan qarayiwa mahaifinki komai ba ki muje inmayar dake gida shima zuwa gobe da kaina zan kawosa har gida nayi miki alqawari bandauko mahaifin ki da wata manufa ba dan na cutar dashi nadauko shine da dalili wanda ko ke kika tsincin kanki a irin halin dole ki kama koma waye mahaifinki yayi wani kuskure ne ya boye gaskiya ne akan wani case da akeyi mu kuma muna son yagaya mana gaskiya ne shiyasa muka dauko sa kema kuma bamu dauko ki dan muyi miki wani abuba mundauko kine kawai dan muyi masa barazana dake yagaya mana gaskiya kuma gashi burinmu ya cika yagaya mana abun da nuke bukata amma dole sai mun kamo wancen zuwa gobe sai musakeshi,

Amma daga yanzu babu abun da zai qara tabashi zanma saka azo adubasa abasshi kulawa, "kiyi hakuri kikoma gida zaman ki anan bazai yiyuba kinji?

   Shiru tayi bata bashi amsaba saidai tadan rage kukan datake yi yazamana hawayene kawai yake zuba a daga idon ta,
tawani fanni ta danji dadin bayanin da yayi mata ta wani bangaren kuma har yanzu inta tuna lokacin da yake dukan mahaifin ta sai taji wani irin haushin shi yazo mata wuya,

   "bakice komai ba ya katse mata tunanin da take,
still de shirun tayi masa bata tanka masa ba
  jin shirun nata yasa yaqarajin ba dadi aransa yasan daman ba lalle ta fahimce sa ba zata dauka kawai shi mugune ya zalince ta ya zalinci mahaifinta dan komai zai fada bazata taba ganin laofin mahaifinta ba nashi zata gani,

  dan raba jikin ta yayi da jikin sa yana kallon fuskarta da gaba dayanta ra wanke da hawaye

26 / 74