Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   59 / 74

174K to 177K   out of 221K words

fulani tace ƙarya kike na ƙarya taki ɗin wannan wacce irin banzar magana ce naga alamar kinsha ƙwaya hauɗin nan ni zakuce bani na haifeshi ba idan ba ni na haifeshiba uwarki ce ta haifeshi kai kuzo kufitar min da wannan mahaukaciyar daga gurin nan, tafaɗa tana kallon fadawan wajen,


da sauri fadawan sukayi kan hajiya sarah dan aiwatar da abun da uwar masarauta ta umarce su dashi saidai sun karasowa gurin zasu kai mata cafka sarki salahuddeen yayi saurin daga musu hannu tare da dakatar dasu daga shirin kama tan dasuke,

fulani na ganin haka ta zaro ido tare sa hadeye wani katoton bakin ciki da tashin hankali da suka rufar mata lokaci daya suka tsaya mata a makogaro,

a kidime tayi tayi wajen sarkin tare da riko hannun sa tace wallahi karya take kar ka yarda da ita wannan matar da kake gani zararriya ce bata da hankali bata dade da dawowa dafa asibitin mahaukata ba kar ka yarda da ita taya ma za ayi ace kazama ba dana ba kaidin dana ne ni nahaifeka acikin muje ka tambayi mahaifinka kaji zai gaya maka gaskiya zo muje idan ni baka yarda dani ba muje idan kaji ta bakin sa zakafi yarda,

tunda tafara magana yake binta da kallo kamar yasamu tv yakasa koda kwakkwaron motsi saboda gaba daya kansa ya kulle yarasa maganar wa zai dauka kuma tawa zai bari ga kansa da yaji yana yi masa wani rin mahaukacin ciwo,

sanbatu fulani ta shigayi tana ta faman jansa amma ina ko motsasa takasa yi,

kwace hannun sa yayi daga nata yana kallon ta saboda yanaso yagano gaskiyar zancen sai kawai yadaka mata tsawa tare da cewa ki fada min gaskiya kece uwata ko ba ke bace abu daya nake so naji daga gare ki "eh" ko "a'a"???

yayi maganar yana zazzare mata ido kamar zasu da fado waje gashi sun canza kala daga fari sun kima ja ran maza ya baci,

"Fulani kam ba karamin tsorata tayi da yanayin saba dan tunda take dashi baitaba nuna mata irin haka duk da tunyana yaro tasanshi da saurin fushi abu kadanne yake bata masa rai,

atake kwa jikin ta yadau bari sai karkarwa take amma duk da haka ta kara daurewa bata karaya ba itama cikin daga masa murya tace masa "EH, nice na haifeka idan kuma baka yarda ba nace kaje ka tambayi uban ka,

hajiya sarah ce ta tako zuwa gaban su sai ta tsaya saitin fulani cike da dakiya tace haba maryama ko kifadi gaskiya ko baki fada idon ki da jikin ki sun bayyana ma kowa gaskiya domin kwa ga tsoronan karara akan fuskarki da kika kasa boyesa duk da son hakan da kikeyi amma kin kasa malama ba wani boye boye yanzu ki fito kigaya masa ko ke wacece agaresa kigaya masa a inda kika dauko sa inkuma kin bani wuka da nama yanzu zan yankasa in soya kuma in rabasa afaranti ko yagani kuma yaci ki daina wahalar da kanki daman ance rana dubu ta barawo raba daya tak ta mai kaya to yau gaki barauniya kuma gamai kaya azaune agabanki yakamaki kuru kuru dan haka bake ba wani yin kwana kwana da kike cewa yaji ya tambayi mahaifinsa ke atunanin ki yanzu zai kara yarda dake ko kinmanta saradin bokan naki ai ba sarki kadai ba daga yanzu bakin kowa zai bude akan wannan yaron saboda duk wanda yake cikin hayyacin da hankalin sa ya kalle sa yasan baiyi kala da yan gidan nan ba ba jinin sarauta kamannin sa sun bambam ta da kowa dake cikin gidan nan dan haka ko baki fadi gaskiya ba da bakin kiba idanun mutane zai gane musu hakan dan haka daga yau zuwa gobe sai ki nemo mafita ni daga yau baza ki kara ganin naba abun da hadamu ya rabamu zan dauki dana mu koma inda muka fito shawarata agare ki kinemi makaman kare kanki,

tana gama fada mata haka ta juya kan sarki shima tace masa zanso intsaya har zuwa gobe dan innemi yafirya ka domin harda saka hannun akan rabaka da iyayen ka na asali wannan da kake gani zaune shine mahaifinka waccen kuma kanwarka ce uwa daya uba daya gashi Allah ya hadaku guri daya da kanka kaje ka shigo dashi itama kuma sanadin shigowarta Allah yayi shine sanadin haduwarku saboda badan itaba bana jin asirin nan zaitonu kuma ita ma sanadin dana hakan ta kasance, kuma ka....

sarki yayi saurin da katar da ita sanadin daga mata hannu hakan yasa tayi shiru,

ahankali yashiga buda bakin sa sannan yace "ke duk taya kikasan ba itace ta haifeni ba kuma taya kika san wannan shine mahaifina alhalin ita bata san da hakan ba,

dan murmushi hajiya sarah tayi sannan tace "kar kadamu da wannan duk ka tambayeta zatayi maka bayani komai dalla dalla amma dai bari inbaka amsa daya ni da kaina naje na daukoka akan gadon asibiti agaban mahaifiyar ka wannan duk shirin mune aka gaya musu cewar dansu ya mutu sannan aka kawo musu wata gawar yayan wata mata da yan biyu da suka mutu sai aka nunawa matar daya sannan aka nunawa mahaifiyar ka daya akace mata abun da ta haifa ya mutu ni da kaina kuma na sanar da mahaifinka mutuwar ka, kaji ta inda nasan shine mahaifinka amma ita bata sanda hakan ba shiyasa amma da tun ranar da ka kawosa da kanka da tun ranar zatasa yabar gidan amma bata saniba kuma aranar da na fara karo dashi nagaya mata ta koresa taki, kin yin hakan kuma gashi nan zai jawo mata da nasani,

"Umma Hamza ya kira sunan ta cike da mamakin labarin da ta bayar dan shi baitaba sanin abun da ta aikata ba kenan wannan ai ita kanta zalinci ta aikata kuma kanta ta tonawa asiri ba wani ba,

tunda ya kirata ta juya tana kallon sa tare da amsa kiran da yayi masa, kafeta yayi da ido tare da takowa ahankali har yakaraso gabanta bai dauke idon sa ba daga kanta, sunan ta yakara kira still dai idonsa akanta ko kiftashi bayayi kuma ya hade fuska tamau kamar baisan wani abu aduniya ba wai shi murmushi ko kuma farin ciki haka ya koma mata,

cikin bacin rai yace "kina sane kika aikata wannan abun kuma kinsan da zaman sa meyasa baki taba gaya min ba daman duk abun da kike fada min ba gaskiya bane me yasa me yasa kika aikata haka da hannun ki kika raba da mahaifan sa kika kawosa nan aka dorasa akan zalintar mutane da cutar dasu yanzu da ban kiraki ba yakashe mahaifinsa da kansa kina tunanin iya shikadai za ayankewa hukun ci ke da kika rabasa dasu kuma kika sani baki sanar dashi ba hukuncin ki awajen ubangiji sai yafi nakowa kinsan gaskiya kuma kin take wannan wace irin rayuwa ce kika dorawa kanki nayi da nasanin kasancewa ta da agareki me yasa me yasa zaki aikata hakan amatsayin ki na musulma wannan wane irin mugunta ce wallahi bana ganin laifin kowa sama da naki kinfi kowa laifi aciki ahaka kuma kike cewa wai zaki tafi ki tafi ko ni da nake da awajen ki bazan bari kibar gurin nan ba batare da an hukuntaki daidai da abun da kika aikata ba yanda za a hukunta kowa kema dole ki tsaya ki karbi sakamakon ki duk da ke kika fallasa abun hakan bazai hana a hukun takiba,

wallahi bantaba tunanin zaki iya aikata haka ba nawa ake biyanki da har kikayi wannan danyen aikin umma? yayi maganar cike da bacin rai yana tsatstsareta da ido,

tunda yafara maganar hajiya sarah take zubar da hawaye yau wai yau dan cikinta ne yake gaya mata magana, tasan tabbas ta aikata kuskure amma shima baisan dalilin ta nayin hakan ba itama bada son ranta tayi ba dan ba yanda ta iyane shiyasa ta aikata hakan,

kamo hannun sa tayi tana kallon sa yayin da hawaye suka gama wanke mata fuska suna hada ido yajanye idon sa gefe ta budi bakima zatayi magana sai kawai ya dakatar da ita tare da kwace hannun sa daga nata hannun ya juya mata baya ya koma gurin baba tsugunnawa yayi ya kuncesa sannan yaje ya kunce Azeema ma sannan ya shiga basu hakuri,

yaudai yan masarauta sunga abun mamaki kuma sunji abun da basu taba tunanin ba basu taba kawowa ba kowa yana tsaye agun yana jiran yaji karshen zancen amma ba wanda yasamu damar yin magana saboda suna tsoron aji bakin ka agun yanzu wasu su sauke haushin su akansu shiyasa kowa yake zancen sa shikadai daga shi sai zuciyar sa amma kowa munafurci cinsa yake so yake yayi da dan uwansa amma ba dama dole sukayi shiru kowa ya zuba ido yana bawa idonsa abin ci,

abangaren fulani kam tunda hajiya sarah tayi magana takasa koda motsawa bare tasamu karfin halin yin magana agun saboda tasan karshen ta yazo tunda har ta riga ta fallasa shikenan komai ya karye kamar yanda bokan yace duk sanda aka samu wani ya fadawa akunne mutane da yawa sukaji tofa asirinta zai tonu kowa dawo gani daidai sannan papa ma bazai kara yarda da itama shima kuma zai dawo cikin hayyacin sa ta daina juyasa yanda take so ya daina yi mata biyyya kamar yanda yake mata abaya daga yanzu komai zai canza,

baba bakaramin mamaki yayi ba yanaso ya gasgata abun da suke fada amma yakasa gani yake duk kamar mafarki yake yaza ayi ace wai dan sarki guda shine dansa kai gaskiya wannan matar ba gaskiya ta fada ba idan hakane me yasa shi bai gane taba kuma dansa sa hannun sa ya binne sa ya riga da ya mutu kuma kawai kwatsam lokaci daya tawani zo tace wai dansane gaskiya karya take shi baida wani da araye bayan saleem da Azeema shikadai shima yake ta faman saka da warwarar sa,

abangaren Azeema kam tayi mamaki batayi mamaki ba domin tunda matar tace dan babane ta kura masa ido sosai taga kamannin sa da yan gidan su kuma ta yarda da yayan natane duk da ba ataba gaya mata suna da yayan da ya mutu ba amma aranar da ta fara ganin sa taga mugun kamar da suke da yayan ta saleem saida abun da yasa bata tada hankalin taba tayi tunani gizo yayi mata aranar ko kuma tsorone yasa taga kamar dasuke kuma tunda ga ranar bata kara ganin sa ba face to face kamar yanda ta gansa ranar shiyasa tayi watsi da maganar kamar da suke saboda bashi ya kawota ba daman khma basu kuma haduwa ta gansaba duk sanda zasu haduma kanta na kasa,

sarki da jikin sa yayi mugun sanyi saboda yagama yarda da maganar matar nan gaba daya saboda ya fahimci mahaifiyar sa fulani bata da gaskiya amma duk da haka bai gama tabbatar wa ba sai yakara samun hujjoji aransa yana ayyana mudun hakan ta kasance gaskiya bazai bar duk wanda ya rabasa da iyayen sa na gaskiya ba gashi ya kamo mahaifin sa da hannun sa yasa kuma an hukuntasa agaban sa da Allah bai rufa asiri ba da tuni ya kashe mahaufinsa da kansa ji yayi kansa gaba daya yadau wani irin matsanan cin ciwo shi kadai yasan halin da yake ciki ayau din nan,
ahankali yafara takawa har zuwa gaban baba ga mamakin mutane sai sukaga sarki sukutun da guda ya tsugunna agaban baba cikin kasa da murya yace "da gaske kaine mahaifina ?

kawar da kai baba yayi sannan yace "a'a ni banda wani da dana ya dade da mutuwa kai ba dana bane domin indai kai jini nane baza kataba zalintar mutane ba irin yanda kake dan haka bani da hadi dakai,

da sauri Azeema ta karaso wajen su sannan tace "baba wallahi da gaske ne wannan danka ne bakaga kamar da suke da yaya saleem ba Allah baba wannan matar da gaske take nifa tun ranar nafara ganin sa naga yana kama da yaya saleem kodai baka gane kamannin nasaba, ko kallon inda take baba baiyiba kuma bai kalli sarkin ba ya kawar da kansa gefe kawai,

jin batunsa yasa sarki mikewa tsaye jikin sa babu kwari dan yaji ajikin sa duk yanda akayi da gaske shine mahaifinsa kuma ya tuna lokacin da yazo wucewa yarinya takira saleem da karfi sai yanzu da tafada ya tuna lokacin da ta taba fadadin hakan kuma yakara tabbatar masa da zancen da ake gaskiya ne ahankali ya dora hannu akansa zai fara warware rawani kansa yaji anyi saurin rike masa hannu, hannu ya shiga bi da kallo har zuwa fuskar me rike masa hannun idon sane suka sauka akan Ammah da zuwan ta cikin gurin kenan,

zaiyi magana kenan ta kar kada masa kai ma'ana kar yayi magana kallon yan gurin tayi sannan ta daga murya tace "kowa yakama gabansa banason ganin kowa anan sum sum sum suka fara watsewa daga gurin har suka tafi gaba daya amma wasu ba haka suka so ba sunso har sai sunga karshen komai anyi agaban su,

cikin bacin rai Ammah tace "yanzu meye hakan kukazo kukeyi agaban mutane koma me yafaru ai baikamata ace kun tsaya gaban mutane bayi kuna kace nace agaban su suna jin sirrinku wannan abun da kukayi babu abun zai jawo sai zubewar mutuncin masarauta da rage mata kima da martaba da mutunci wannan abun da kukayi kwata kwata bai dace ba bai kamata ba da girman ku sai kace wasu kana nun yara kuna kallon sa amatsayin sa na sariki yana niyar kunce sarautar sa abainar jama'a koma meye ai a kunceta cikin mutunta da martaba wallahi kun batan rai kun ban kunya ni duk bansan meke faruwa ba sai yanzu aka sanar dani da ban bari hakan ta faru ba da tun wuri na dakatar da komai haba dan Allah sai kace wadanda basa tunani,,
maida dubanta tayi ga fulani da ta sunkuyar da kai sannan tace "wlh ni duk laifinki ma nafi gani da kika kasa
dakatar da abun har takai ga haka ya kuke abu kamar ba manya agidan me yasa ba asanar da papa ba tun wuri ko waziri ko galadima idan kin kasa su ai duk zasu iya ji da komai tunda su mazane idan ke abun yafi karfin ki duk da kina da ikon fada aji amma kika kasa yin hakan,

sosai Ammah ta rufe ido ta hausu da fada babu wanda batayiwa fada ba acikin su sannan tace kowa ya tafi makoncin sa gobe da safe za ahadu afada kuma kada wanda yayi gangancin tafiya daga cikwa harda hajiya sarah,

sannan Ammah tace baba shima ya koma dakin sa shi da hamza gobe za anemesu Azeema kuma ta koma part dinta kartaje part din fulani inyaso ita kuma fulani su tafi da hajiya sarah tunda kawar tace suje su cinye kansu ko kuma su san yanda zasuyu su samowa kansu mafita kafin safiya ba yanda suka iya yau Ammah ita ta koma mai juya kowa har fulani yau bata da wani ikon fada aji dole tabi yanda akace saboda gudun abun da ka iya faruwa nan gaba ji take dama idan ta koma part dinta Allah ya dauki ranta shikenan basai anyi zaman da ita ba da wane idon zata kalli sauran mutane idan maganar nan tagama karade ko ina tasan da kyar idan baza akoreta daga masarautar ba korar ta da za ayi shine babban abun da yafi daga mata hankali ahaka tana tunani bata iya cewa komai ba ta juya tafara tafiya dan bata da bakin magana ahalin yanzu tana tafiya hajiya sarah tabi bayanta da sake sake itama fal acikin ta,,

baba shima saida taimakon hamza ya iya mikewa daga gurin sannan yatai makasa suka tafi nasu wajen,

Ammah da kanta taja sarki takaisa har part dinsa sannan ta gargadi matansa da su bashi kulawa,

sannan ta juya zatabar falon ita da Azeema yayi saurin dakatar da ita,

tsayawa tayi tare da juyawa ta kalle sa da kyar ya iya budar baki yace "ki barta awajena,

Azeema dake gefen ta ta kalla da har zatace a'a sai kuma kawai tace ba damuwa tana fadar haka kuma ta fice daga falon,

Azeema tsaye tayi agurin takasa gaba ta kasa baya daya daga cikin matasane tayi mata magana da ta dawo kan kujera ta zauna jiki babu dadi duk atakure take jinta haka ta dawo zata zauna akan wata kujera sarki yace mata " dawo nan yafada yana nuna mata gefen sa da hannun duk kallon sa suka shigayi saboda su basu san me yake faruwa ba kuma sunga yana cewa wai tazo ta zauna kusa dashi shi da ko su da suke amatsayin matansa ba kasafai yake sakar musu fuska ba bare har yace suzo su zauna akusa dashi haka yaransa ma baifiya jansu ajiki ba, sai yaga dama ko kuma idan yan mulkin basa kusa shine zakaga wataran yadan yi musu wasa,

kamar yanda yace haka taje ta zauna kusa dashi kallon yake sosai yakai wajen minti biyar yana kallon yakasa magana saidaga bisani sannan yace "tashi ki kunce min wannan abun kannawa ba musu kam ta tashi tashiga ware masa rawanin kansa saida ta kunce masa gaba daya sannan ta nannadai abun ta ajiye gefe sudai matan sa suna zaune suna kallon ikon Allah da abun mamaki,

saida ta kunce masa ta kara ganin kamannin sa da saleem sosai suke kama kamar yan biyu saidai kawai bambancin su manyan ta kuma wannan yama fi kama da mama akan saleem bayan kamar da yake da saleem kana ganin sa zakaga kamannin mama afuskar sa,

kura masa ido tayi shima ita yake kallo yana so yayi mata magana amma yakasa sai kallo kawai ji yayi son yarinyar na shigar sa dukan sa akayi mata dazu yafara tunawa da sauri ya rufe idon sa ji yayi bama yason tunawa gaba daya yanzu idan hakan ta kasance da wane ido zai ringa kallon su dan ya cuci mahaifinsa duk da ba asanin sa yayi hakan ba kuma ba laifin sa bane dorashi akayi akai dan idan yayi tunanin abubuwan da yayi sai yaji ya tsani kansa, duk son yayi mata magana amma yakasa sai kawai ya mike tsaye ya nuna dayar matar sa yace akaita ta kwanta sannan

59 / 74