sai ga wasu mutanen wajen guda shida manyan maza dan su ko uniform ma irin na bayi babu ajikin su suna shigowa sarki ya umarcesu da su ɗauke su baba afita dasu inda yace,
mutum ɗaiɗai aka fara ɗaukan su baba aka fara ɗauka Azeema nata kuka tana rirriƙeshi taƙi saki daga ƙarshema saida tasamu tuƙwicin mari zafafa guda biyu sannan tasakeshi aka fita dashi itama wasu suka ɗauketa suka fita da ita sai matar da ta shigo tana tayi musu masifa su sauketa wallahi zata ɓata musu rai amma basu saurare ta suka fita da ita, sunzo ɗaukan hamza, Hamza yace musu dalla malamai kar ku taɓani zan fita dakaina wanine yabiyo ta bayan sa gabuga masa katako akai yace kai akomai saika nuna taurin kai ko to bari muga iya ƙarshen taurin kannaka dafe kansa yayi take yaji yana yimasa wani irin ciwo bibbiyu yafara gani yana niyar faɗuwa wani yajawosa ya miƙar dashi ya tsaya da ƙafafun sa sannna suka shiga tura ƙyayar sa suna dukan sa suna turasa ahaka suka fita dashi daga fadar,
bayan fitar su sarki da masu rufa masa baya suka bi bayansu suma suka fita,
afarfajiyar masarautar aka jeresu da ƙuƙƙule musu hannuwa da ƙafafu,
ƙarasowar sarki kawai ake jira afara zartar da hukuncin da yace ayi musu gefe guda kuma wasu mugayen wuƙaƙene masu kaifin gaske wanda ana ɗora ma ita zata iya yanka ka,
guri har yafara taruwa da mutane sunzo kallo,
sarki na ƙarasowa gurin yasa aje akirawo fulani dan tazo a yanke hukuncin agabanta,
kowa na gurin sai mamaki me suka aikata haka za a yanke musu hukuncin kisa dan andaɗe ba ayi hukuncin kisaba Saida ahukun ta mutum ta wani fannin daban amma banda kisa yau kuma gashi za ayi daga gani to ba ƙaramin laifi suka aikata ba wasu kuma sunsan laifin da sukayi wasu su tausaya musu masu jin haushin Hamza kuma nayi masa Allah yaƙara duk dade sun tausayawa masa saboda duk wanda yaga halin da yake ciki sai ya tausaya masa basu kaidai bama har sauran gaba ɗaya abun a tausaya musu ne domin sunji jiki ba kaɗan ba gashi kuma za aƙara musu da kisa.....
magana har ta fara karaɗe masarauta yau za ayi hukun kisa har mutum huɗu tofa kowa fitowa yake yaga suwaye haka kuma wane irin laifi suka aikata,
ana cikin haka saiga motar sam nan ta shigo tundaga nesa yake kallon gurin taron da mutane suka cika amma dai baidamuba saboda inda sabo yasaba ganin yasan bazai wuce halin nasu suke ba na cutar bayin Allah tsaki yaja tare da cewa gobe inyanzu wani zancen aike ba wannan ba kuyi na ƙarshe ku gama yaune ranar ku ta ƙarshe cike da taƙaicin halayen su na masarautar ya ƙarasa parking lot shidaman arayuwar sa ya tsani wannan mulkin da sukeyi da bashida wani amfani dan baiga amfanin sa saboda ba abun da akeyi asauran masarautu suke ba su nasu na mahaukata suke bana mutane ba abu kwata kwata babu tsari ba a san me yakamata ayiba da abun da bai kamata ba yamaji daɗin zuwan waɗannan bayin Allah, haka yai ta saƙe saƙen sa shikaɗai, saboda shikaɗai ya shigo, ya ajiye shettima agida,
fitowa yayi daga motar ya nufi part ɗin fulani jikin sa duk akasalan ce babu daɗi so yake kawai yaji sa akwance yana buƙatar hutu sosai kwakwalwar sa ta huta..,
akan hanya sukayi karo da fulani ta fito afusace cikin fushi ko takansa bata biba ta wucesa fuuu kamar zata tashi sama,
binta yayi da kallo kawai tare da girgiza kai yayi wucewar sa ciki,
kamar anjefota gaha fulani tashiga wajen taron tunda tashiga kanta yana kan hamza ganin sa cikin mawuyacin hali irin wannan hakan ba karamin dadi yayi mata ba,
gaban sa taje tare da dago da kansa tana kallon sa tare da sakin wani shu'umin murmushi tace to karamin dan iska ina cika bakin naka yaje waye yau agaban mutane cikin mawuyacin hali kuma yanzu zan saka arabaka da duniyar ma gaba daya bance kafita hanyata ba bance karka sake shiga gonata ba amma bakajin magana kullum cikin nuna isa da takama kake kaidin waye me kake dashi me katara me ka ajiye me ubanka yatara me na kasa yaci bare yaba na sama kaidin asararre ne kazo a asara kuma zaka koma asara,
tana gama fadar haka ta mike tare da canza kalar fuskarta ta koma ta marassa imani ta kalli sarki tace amatsayina na mahaifiyar ka ina umarrar ka da kakasheshi da hannun ka so nake kasa wuka ka fillemin kansa anan gurin kafin kafara ina so wani ya fito ya fara saukewa tsohon nan kansa a fille masa kai agaban sa in ya isa ya hana sannan ga budurwar sa nan tunda ita yakeso ina so itama akashe ta agaban sa sannan adawo kansa sarki da kansa nake so yayi min wannan aikin hakan sai yafimin farin ciki inaso dan da nahaifa acikin cikina ya daukar min fansar cin zarafin da wulakan ci da rainin da yake min inga jinina ne zai kashe shi ina fatan kungane,
"bamu gane ba muna bukatar karin bayani maryama,
da sauri fulani ta juya jin muryar da bata taba tunanin jintaba agurin,
kafin fulani tace wani abu matar tayi saurin dakatar da ita tare da cewa kisa akunceni,
cikin tsawa sarki yace baza a kunceta ba mama yanda za akashesu itama yazama dole asauke kanta anan gurin,
fulani ce tayi saurin daga masa hannun tare da cewa ya isa haka kar nakara jin muryar ka anan,
da kanta taje ta kunceta tana cewa wai ya akai waye yayi miki haka me kike yi yaushe ma kikazo bansaniba,
banza tayi da ita tana kunceta ta mike tsaye itama cikin bacin rai ta kalli fulani tace ki gaggauta sawa akunce wadannan mutanen gaba dayan su,
fulani itama cikin bacin ran tace akan wane dalili zakice haka,
kedai kawai kiyi hakuri akan abun da yayi miki acikin rashin sanine baidan matsayin ki awajena bane amma hakan kar yasa wai kice sai ansakesu wannan hukunci ne da nariga na yanke tun wuri kuma dole a zartar dashi babu wanda ya isa ya hana tayi maganar cikin daga murya, kuma hurumin ki bane meye alakar ki dasu kima canza magana wadannan mutanen dakike gani ba mutanen kirki bane basu da mutun ci ko kadan basu sansaba musamman wannan dan iskan yaron da yagama rainamin hankali yau dole ya karbi abun da ya dade yana aikatawa,
ko kuma ke ki karba ba nace masa kisake shi wallahi aka kashe shi sai namiki abun da baki taba tunani, matar take fadawa fulani tare da kada mata hannu afuska,
bakaramin mamaki fulani tayi ba da jin batun ta aikam cikin bacin rai tace sarki afara takansa yanzunnan tagani agabanta,
dariya matar tasaka tace da kwa kin tafka babban kuskure arayuwar ki ko kina tunanin alakawarin da na daukar miki yakai karfin da bazan iya karyawa ba to kiyi abun da nace miki inbaha ba kuma hmmm kinsan mai zaibiyo baya, dan dagatawa tayi sannan taci gaba dacewa ko dayake karfin alkawarin ne yasa nakai har yanzu ina danne wa to kar kibari ki kaini karshe da hakan zai gagara rikewa agareni yanzuma ba karamin kokari nayi ba wajen danne duk abun da yafaru agaba na batare da na dau mataki ba amma daman nafiso inma rashin juriyar ne da daukar mataki to yazamana agabanki ne kuma gaki dan haka idan baki dakatar da komai to nimafa kisani zanyi abun da yadace ina fatan zaki gyara barnar da kike shirin yi domin idan baki gyara wannan ba to waccen ta tashi daga gyaran da take kina bata wannan waccen zata baci gaba dayanta ina fatan kin fahimce ni da kyau, takarasa maganar tana watsa mata wani irin kallo me cike da gargadi,
cike da bacin rai da fulani ta dade batayi irin saba muryar hardan dasdaskare wa take ta daga murya da iya karfin tare da tsawa tace HAJIYA SARAH.....!!!!! batare da ta sausauta murya ba tace yakamata ki iya bakin ki kisan abun da yakamata kiringa fada anan gurin domin nan bada gani sai ke bane awajen ki gaggauta janye wannan bukatar taki saboda ba mai yiyuwa bace ki canza wata bukatar taki amma ba wannan ba,
juyowa hajiya sarah tayi cikin sanyin murya tace "ni kuma wannan bukatar nake so kuma dole ayi yanda nake so,
kamar fulani zata rufeta da duka ta kara daga murya kamar zata cire mako garon ta tace SABODAME DOLE SAI WANNAN......?
itama hajiya sarah cike da daga murya kamar yanda tayi mata itama tace SABODA DANA NE...!!!
dif gurin yayi bakajin motsin komai sai can daga baya fulani ta dan saki murmushin mamaki sannnan cike da rashin fahimta fulani DA kuma bangane ba yi min bayani yanda zangane kodai kinsha wani abunne kafin ki taho inaga,
babu abun da nasha wannan dai yaro dakike gani dana ne inbaki yarda ba kuma ki kallesa ki kaleni zaki ga kamar da muke indai kuma ba dusace a idon ki ba ko dayake naga alama da dusa acikin idon ki shiyasa tun wuri kika kasa gane hakan duk tsawon zaman da mukayi dake kuma kukayi dashi amma baki iya ganewa ba kinga kwa bazaki taba ganewa ba,
kamar yanda tace ai bama iya fulani ba gaba daya mutanen wajen sai da suka shiga kallon su ba karya kam suna kama kana gani zaka gane hakan,
jin fulani takasa magana yasa ta shiga zagayata tare da cigaba dacewa "duk wani abu da yake miki ninake sakashi kuma kamar yanda nagaya miki baisan komai ba to baisani ba din nice na dorasa yaringayi miki duk abun da kika ga yanamiki kuma ni nacire mishi tsoron ki sannan nasa karyaji tsoron kowa daga ciki hardake idan kuma kika zafafa ta kura masa yace miki zai tona miki asiri idan yace miki haka zaki daina takura mishi sannan yana da damar dazaiyi duk abun da yaga dama zaiyi sa batare da an dakatar dashi ba ke kinsan baisani bane dan da yasani wannan wahalar da aka bashi da tun kan afarata ma zai kunce miki zani sanin shi yarone bazai iya rikewa ba yasa naki gaya masa saboda ban taba tunanin irin wannan ranar ba amma da tuni na sanar dashi ke kinsan ko ni wacece duk abun da zanyi a lissafai nake yinsa shiyasa nasa aka kawoshi nan tun yana yaro inbaki saniba kisani duk zuwa gidan nan da nakeyi bawai dan ke nakeba dan shi nake kuma nayi hakane dan insakashi yasaka min ido akanki duk abun dakike yi akan idonsa ko wannan ranar batazo ba daman daf nake da toma miki asiri sai kuma gashi kin jawo lokacin da kanki dan haka lokaci yayi dole kowa yasan abun da kikayi tsawon lokuta,
jikin fulani ba karamin sanyi yayi ba kuma ta tsorata sosai da maganganun hajiya sarah duk da tana tunanin duk barazana take mata ba iya fada zatayi ba kawai kurarine amma saboda kar yan gurin suyi zargin wani abun sai kawai ta basar tashiga dariyar borin kunya tare da cewa au sharri kuma zaki min ni nake da wani siri to in baki fasa fada ba ba kya tsoron Allah,
"au haka kika ce?
"eh haka nace,
girgiza kai hajiya sarah tayi tana so ta fada amma idon wani dake kallon ta a filin wajen cike da gargadin ta kar tafada yasa tayi shiru taka sa fada amma da dan fulani ne da tuni ta dade da fada amma idan aka kaita karshe wallahi sai ta fada saidai duk abun da zai faru yafaru amma sai ta fada,
ganin tayi shiru yasa fulani sauke ajiyar zuciya a boye tasan daman bazata iya fada ba kurarine kawai amma saboda kar taje ta fada din idan tasa akashe mata da tasan dole zata fada dan haka ta juya kamar ba ita ba ta kara hade rai sai tace yanzu adakata da hukun ci akan yaron nan sai nakara bincike akan sa kafin azo ayanke masa nasa hukuncin mai muni da yafi kisa tare dashi da mahaifiyar tashi abisa kazafin da tazo tayi min agaban ku wani satin irin rana tayau za ku dawo azartar musu da hukun ci agaban ku,
maida dubanta tayi ga sarki da ya riga da yazaro wuka jira yake kawai takara basa umarni yakaita kan hamza sai kuma yaji wannan batun ransa yaji yayi mummunar baci dan haka tunda yazaro ta bazai baza ta koma ba sai tasha jinin wani,
yanda take kallon sa shima haka yake kallon ta tasan ne yake shirin yi dan haka tsce masa "ka kwantar da hankalin ka ai ga wasu nan ka dauki daya acikin su kabawa wukar ka abinci nasan tunda tafito sai tasha zata koma,
kawar da idonsa yayi daga kanta tare da matsawa kusa da Azeema har yadaga wuakar zai sauketa akanta sai kawai maganganun hajiya sarah suka shiga dawo masa maganganun da tayi masa akan baba hakanne yasa yafasa da Azeema yanufi inda baba yake saboda yana so ya kasheshi yaga abun da ta isa tayi masa,
yana zuwa yadaga ta zai sauketa yaki anrike masa hannu da mamaki yashiga bin hannun da kallo mamaki ne yakara kamasa wai mai wannan matar take nufi dashi ne duk inda akace za ataba sai ta hana,
bashi kadai bama kowa kallon ta yake cike da mamaki sarki guda ta rikewa hannu lallai ta wuce gona da iri wuyan ta ya isa yanka,
shikam baba yarufe ido dan har yafara kalmar shahada ya riga da yagama saddakarwa ya mutu,, sai kuma yaji shiru,
Azeema kam jikinta sai rawa yake muryart ta dashe tanaso tayi ihuma amma miryar ta taki fita sai uhm uhm take hawaye ma rahama ne amma sobada tsabar tashin hankali sun kafe sunki zubowa so take tayi ko zata samu sassauci Amma suma sunki fitowa,
fulani ce tace hajiya sarah wai lafiyar ki kalau me yake damunki me yasa kikeyin irin waddannan abubuwan kinsan kwa wa kika rike,
ko kallon inda fulani batayi ba ta sa hannun ta kwace wukar hannun sa tare da yin cilli da ita gefe guda inda ba mutane shidai sarki saboda mamaki yama kasa motsawa dan kamar ma baya cikin hayyacin sa har ta samu damar kwacewa daga hannun sa,
cilli tayi da hannun nasa data rike idon ta sun canza kala sunyi ja saboda bacin ran da ta shiga yanzu,
cike da daga murya, muryarta har rawa take saida ta kalli fulani sannan ta kalli inda ake kallon ta suna hada ido aka zazzare mata ido alamar gargadi kar tace komai,
kawar da kanta tayi ta kalli sarki da fuskar sa ta canza idon sa shima yayi
jajur,
saida ta kalli kowa nagurin sannan tace nagaji nagaji bazan iya cigaba da jurewa ba wannan abun naku yayi yawa ina zaku kai rashin imani ne bazan iya ganin anyi kisan kai agaba na bazan iya ba wallahi kuji tsoron Allah me yasa me yasa tafada tana kara daga muryar ta sama,
sarki da yagama kaiwa karshe ya juyo afusace bai duba girmanta ba kawai ya ware ya tsunsa biyar tana huyowa ya kwashe ta da wani gigitaccen mari da saida taga ster atake kwa yatsun hannun sa suka fito,
da sauri hamza yayi kukan kura yakarasa kunce igiyar da aka daure sa daman tun dazu yake ta kokarin kuncewa sai yanzu yakarasa kunceta kansa yayo da nufin yaramawa mahaifiyar sa marin da yayi mata,
hajiya sarah tayi saurin dakatar dashi tace "rabu dashi kar ka karaso nan gurin,
kamar yanda ta umarceshi haka yaja yatsaya cak daga inda yake,
har yanzu hannun ta na dafe akan fuskarta inda ya mareta ta karasa gaban sa ta kalle sa ido cikin ido sannan cikin sanyin murya saboda hawayen da yake fitowa daga idon ta, tace "ni kamara ko? akan ina kokarin yi maka gata, ina kokarin dakatar da kai daga aikata da nasani, ina kokarin dakatar dakai daga aikata laifi irin na yan wuta, ina kokarin dakatar dakai daga fushin ubangiji, shiru ta danyi sannan ta canza murya cikin daga murya tace ina kokarin dakatar dakai daga aikata mummunan laifi da yafi komai muni awajen uabngiji,
"kasan waye shi?
kasan wa kake so kakashe da hannun ka to inbaka sani ba bari insanar dakai ko shi waye agere ka, to shidin MAHAIFINKANE.....!!!
NACE SHIDIN MAHAIFINKANE, MAHAIFINKA KAKE SON KASHEWA DA HANNUN KA...............!!!!!!!!!
🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️
More comment more tying,🧏🏻🧏🏻
inba comment ba tying🙅♀️🤷♀️🤷♀️🤷♀️🤷♀️
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 91
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"kasan waye shi?
kasan wa kake so kakashe da hannun ka to inbaka sani ba bari insanar dakai ko shi waye agere ka, to shidin MAHAIFINKANE.....!!!
NACE SHIDIN MAHAIFINKANE, MAHAIFINKA KAKE SON KASHEWA DA HANNUN KA...............!!!!!!!!!!!
shiru gurin yaɗauka kowa ka kalli fuskarsa kasan tsantsan mamaki ne akanta wasu sun zaro ido waje saboda tsantsan mamaki kowa yayi shiru yakasa magana,
Hajiya Sarah ce ta cigaba da cewa "wannan dai da kake gani shi ya haifeka nan gidan ba gidan kubane kai ba ɗan sarki bane ɗan wannan mutumin ne da kake son kashewa da hannun ka '"idan kuma ka ƙaryata ko baka yarda da abun da nake faɗa maka ba ga hujja ina da ita saboda haka daman na ajiyeta zaro wani abu tayi ajakarta kamar plash ta miƙa masa sannan tace zaka iya zuwa ka kalla ko kuma ka tambayi wacce kake gani amatsayin mahaifiya kace tagaya maka waye ya haifeka idan ita ta haifeka in ta isa ta ƙaryatani anan wajen,
amugun furgice