Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   10 / 74

27K to 30K   out of 221K words

yafada yana kallon ta danjin me zatace itama murmushin ta mayar masa dashi tace naganta yanzu nadawo daga wajenta ai ba bakuwa bace wannan yarinyar ce da da nake gaya maka baki asake yace yarinyar kuma kuma naga waccen fara ce fa ba baqa ba waccen yarinyar kuma da nagani ai baqace na tambayi yaron nan kuma na hadu dashi yace hartaji sauki tana daki tana bacci shiyasama kikaji bantambaye ki tana inaba kalloma Ammah tayi tana yar dariya tace tode wannan daka gani itace bawani bacci da tayi nasaka tade ta wanke fuskarta shiyasa kaga tayi haske kwaliyar datayi ne yasa tayi baqi amma itace de da mamaki yace kai amma kamar ba itaba to wadancan matsora tan sungantade ko tace a'a sun fita amma nasan wata kil suna hanyar dawowa ai shiyasa nasa ta wanke fusakarta dan sufi ganinta da kyau dan sudena tsoratan ta eh hakan kuma yayi ai ba wanda zaice itace yajikin nata kuma me yaje damunta Ammah tace kawai doguwar suma tayi ne amma bansan dalili ba zande tambayeta sonake sai ta qara samun nutsuwa yace to Allah ya kiyaye gaba Ameen tace sannan ta nufi toilet shikuma yakoma kan gado yadauki littafin da yasaba dubawa yafara dubawa,

Azeema datayi zaune awajen tarasa wane irin tunani zatayi ita rashin maganar da batayi mata ba yafi tsaya mata arai taso tace mata wani abu amma tayi shiru batasan wane irin mataki zata dauka ba tana gurin har papa yaahigo saida taga ya wuce sannan ta miqe da kyar ta tafi daki zuciyar ta namata wani iri duk adagule take jinta duk dade a wani bangaren taji dadin ganin bata koreta ba kuma batayi mata fada ba to amma hakan bazaisa tayi sukuni ba har saitaji abun da zatace mata kafin ta saki jikin ta kayan jikin ta tacire ta shiga ta dauro alwala tazo tayi sallah aranar de bata jin zata iya cin wani abu kuma bazata sake fita ba dan haka tana idar da sallar tayi nafila tare da roqon Allah Allah yashige mata gaba akan abun da tazo yi Allah yasa tacika alqawarin da ta daukarwa kanta addu'a sosai tayi kafin ta cirehijab din tahau kan katifar dakin ta kwanta tareda nannadewa guri daya tana kwanciya taji shigowar mary ga mamakin ta saitaji mary nayi mata magana cikin lallami batare da daga murya ba tace kitashi kici abinci gashi nakawo miki dan Allah kiyi hakuri akan abubuwan da namiki bazan qaraba dan murmushi tayi aranta tace lalle ma matar nan haryanzu tsoron be bartaba kenan tashi tayi zaune tace ba komai komai ya wuce amma de nakoshi da abincin bacci nake ji kinga bandade da cin abinci ba (kunsa tade daman bawani abinci take ciba sosai saboda bata daci)
duk yanda taso tace abincin nan amma taqi ci bayanda ta iya haka tafita da abincin dan mayarwa kitchen daman Ammah ce tace ta takurata taci kuma taqi ci dan haka kawai ta mayar dashi saidai kuma bata gayawa Ammah cewa bata ciba kawai taje taci abinta ta qoshi sannan ta dawo dakin lokacin da tadawo har Azeema tayi bacci tunanin tafara anya kuwa ta kwanta akusa da ita dan itafa har yanzu bata gama yarda ba aljana bace a tsorace take da ita dan lallabawa tayi ta leqa idon ta dan ta tabbatar tayi baccin ko batayi ganin de da gaske bacci take yasata daukan abun rufar kan katifar ta shinfida aqasa ta dauko filo daya tayi kwanciyar ta aqasa dan sai tafi jin dadin hakan sai tafi samun kwanciyar hankali,

*shettima*
yana fitowa zuciyar sa taf da tambayoyi kala kala me yakawo yarinyar nan dole yasan dalilin zuwan ta gidan da wuri badan dare ma yayi ba da ayau zaije gidan su yaji ko ansani agida amma yabarwa gobe ki beje gidan suba idan yaje asibiti zai tambayi yayan ta yaji da haka yaqarasa wajen motar sa kdaman yagaji da neman sam shiyasa kawai ya yanke shawarar sai gobe yasan dole zasu hadu bude motar yayi yatafi gida dan zuciyar sa da tunanin sa gabada suna kan ganin da yayiwa yarinyar nan da tunane tunaneta yaja motarsa yabar masarautar yatafi gida,

Sam ya na ganin fitar sa yafito daga cikin wata mota yana bin motar sa da kallo aransa yace nasan da na tsaya da tuni kacika min kunnuwa da surutan banza kazo ma ka qara min ciwon kai inji da wanda yake damuna yana ayyana hakan yana tafiya har yakai bakin parta din Ammah sannan ya bude qofa yashiga saboda daman akwai maganar da yakeso suyi tun dazu amma waccen banzanr aljanar tazo ta bata masa lokaci da yaga be ganta a falo ba sai kawai yanufi dakin ta kai tsaye dan yanaso suyi sugama yaje ya kwanta dan bacci yakeji kwan kwasa qofar yayi aka bashi izinin shiga ya bude ya shiga abakin gado yazauna yana jiran Ammah ta idar da sallah suyi yatafi papa ne yace qaton banza kawai baka ga mutane ba kashigowa mutane guri ba sallama shiru yayi be kula masa ba papa yaci gaba da cewa au ga dan iska yana maka magana ko ciki ciki yace papa nayi fa saidai idan bakaji ba yafada yana hade rai saikace wanda akayiwa wani abun papa shiru yayi masa dan baya so yaci gaba da magana ransa yabaci saboda har yanzu haushinsa yakeji akan abun da yayi masa dazu shiyasa shirun sai yafi alkhairi dan zai iya gaya masa ba dadi shikuma daman ba hankali garesaba komai yazo bakinsa zai iya gaya masa shiyasa ya maida hankalin da kan littafin sa,

Sam yana sane yayi masa haka shikuma anasa tunanin idan yabiye masa zai iyayimasa maganar yarinyar cen shiyasa ya hade masa rai dan karyasamu fuskar yi masa maganar kuma hakan da yayi sai yaga yaci nasara be kulasaba hakan ba qaramin dadi yayi masa ba Ammah ce da ta idar dasallah tayi masa magana dacewa ina abokin naka yace yatafi gida tace gida kuma ince yakira ka kuci abinci shine yakama hanya ya tafi to kwa zaidawo yasame ni kai taso muje yace Ammah nima na qoshi muje de waje ina son magana dake tace aikam baka isaba sai kaci inba hakaba kuma ba maganar da zanyi dakai daganan ma ka tashi kaitafiyar ka tafada tana juyar dakai gefe irin taji haushinan saida yagana binta da kallo aransa yace idan akace maka tsoho tofa sai ahankali burkitattune sai kabisu yanda sukeso ahankali ya bude baki yace naji muje inci tace karma kacidin yace Ammah....yafada cike dagajiyawa da surutun dasuke yace wai bani nace zan ciba kuma sai kin qara batamin lokaci yafada yana miqewa tare da nufar qofar wake itama miqewa tayi tabi bayansa tana mita mutum sai bakin hali shi yayi yanda yake so amma kai idan kayi masa sai yanuna maka yaji haushi tana mita tafita lokacin har yakusan fita daga falon tayi saurin dakatar dashi cak yatsaya dande yanaso suyi maganar ne amma da baze saurarera ba dan haka kawai sai yajuyo be kalli inda take ba kawai ya wuce kan dinning kaitsaye yana zama tazo ta zuba masa saida yadauke kai sannan yafara ci beci wani me yawa ba yace mata ya qoshi ganin fuskarsa ahade yasa bata takura masa akan sai ya qara dole ba ta rabu dashi sannan tace to ina sauraron ka gyara zama yayi yana fuskantar ta da kyau itama duka hankalin ta ta miqa garesa dan taga kamar magana me muhimmaci zamata tunda taga ya tukara kansa haryayi abun da baiyi niyaba dan badan maganar ba tunda yace bazaici ba da baze taba ci din ba ko mai zatayi masa
ina sauraron ka taqara cemasa akaro na biyu...........

*BOSSAY*
ransa abace yakoma dakinsa rub da ciki yayi ya kifa kansa aqasa shikadai yasan radadin da zuciyarsa take masa akan wannan kwacen da sukayi masa wayar sace ta soma ruri banza yayi da ita har kiran ya katse wani yaqara shigowa be motsa daga inda yake ba saida yajide inba daga wa yayi ba baza adena kiraba ransa abace yadago daga kwanciyar dayayi tare da kai hannu yadauki wayar dake kan bed side drawer zaro ido yayi sakamakon ganin me kiran shifa gaba dayama yamanta da rayuwar ta yama mata da ita aduniyar nan gaba daya yana kallon number tata har be daga ba har tasake katsewa wani ne yasake shigowa yace mayya ai nasan bazaki dena ba ko zaki kira sai dari daga wa yayi tare da saka wayar a Hans free sannan yayi shiru yana jiran me zata fara cewa itama anata bangaren shirun tayi tana jiran yafara magana amma shiru ahankali tace hello baby uhm hum ykk jin muryarsa yasata sauke ajiyar zuciya sannan tace ba lafiya yace me yake damunki tace tambayata ma kake yanzu dan Allah kayi min adalci kenan idan bankiraka ba baza ka taba kirana ba ko kadena kirana ka dena zuwa gidan mu yanzu kusan 3 weeks rabona dakai tun lokacin dakazo gidan mu banfito ba kace zaka dawo haryau banganka tafada tana sakin wani marayen kuka shiru yayi yana sauraron ta saida tadena dan kanta sannan yace kingama tace a'a yace to cigaba yafada yana ajiye wayar gefe tareda kwanciya ya rufe idon sa yana sauraron tagana nata haukan shima ya nuna mata nasa tunda bata da hankali shifa arayuwar sa yatsani mutum marar zuciya da zubar da mutun cinsa kana jin taqara cewa tacikin wayar banza yayi mata be bata amsaba hakan be dameta ba ta dora da cewa tunda naga abun hakane nacewa dad dina kawai yayiwa mahaifinka magana asa ranar auren mu nan da wata daya dan naga alamar idan nayi wasa zan iya rasaka mamakin maganar ta yayi shi duk atunanin sa da yaji tace tunda abun hakane to nafasa auren amma sai yaji akasin haka wai nan da wata daya lalle yaqara yarda taci kai batasan kishin kanta ba sai ya fito mata amutum saida yabari takai aya sannan yace nikuma bazan yi aure nan da wata dayaba duk ma uban dakika gayawa kije kice ni banshirya ba kuma ba wanda ya isa yasa ni inyi abun da banyi niyaba inma zaki dena wannan maganar ki dena sannan kuma kibini ahankali inba hakaba kuma hmmm yafada yana cije baki kamar yana gabanta a zafafe ta fara magana yanzu nikake zagi abun yabar kaina ya koma kan ubana ince maka nagayawa dad dina shine zakace duk ma uban da nagayawa inje ince kai baka shirya ba to kasani zancen gama yariga da yagama auren mu nan da wata daya babu fashi sai ya tabbata saboda already sun gama magana da abban ka inkuma bakajin maganar iyayen ka sai kagayamin tsawa ya dakamata dakata ke harkin kai matsayin kigayamin magana son ranki to nikuma Aliyu nace nafasa auren ki ko ana dole kije ki nemi wani nima ina da wacce nake so yanzu banason ki ke nifa wlh ingaya miki gaskiyama hankaline baki dashi da baki gane banason ki har jakar kwakwalwarki take baki inasonki to daman zanbi umarnin mahaifiyata neshiyasa zan aure ki amma tunda kinzabi sanin ko waye ni gwara ingaya miki ni Aliyu bana sonki bana sonki bana sonki!!! Yanzu kuma na tsaneki kifita daga rayuwata kar kisake kirana sai kije kigayawa wanda yake daure miki gindin yin abun da kika ga dama kice wanda kikeso ya tsaneki bayason ganinki idan ya isa kuma yazo yasani insoki idan anaso dole banza ballagaza marar kamun kai be jira cewarta ba yayi katse kiran tare da wurgi da ita gefe yana faman huci kamar wanda yayi gudu tashi yayi yawuce bathroom yasakarwa kansa ruwa saboda yanda yake jin zuciyar sa nayi masa radadi,,

*RASHEEDA*

wani jakin ihu tasaki tare da durowa daga kan gadon da take har tana kifawa sannan tayi saurin tashi ta bude qofa tafita aguje tana kwadawa mom dinta kira mom mom nashiga uku na lalace wayyo Allah na wayyo Allah na nashiga uku duk da girman jikin ta jin kukan diyar tata hakan be hanata kwasowa aguje ba tayo inda taji kukan yar tata aguje ta fito daga kitchen tafara hawowa kan step din benan kicibus sukayi dan daura kadan mom ta gangaro qasa Allah ya taqaita wahala tayi saurin riqe qarfen benan tana haki dan ba qaramar wuya tace ba adan gudun nan da tayi ba saboda tsabar daukewar da numfashin ta yakeyi tama kasa yiwa yarta tata magana saidai kallon ta datake itakuma sai cewa take mom zan mutu wlh mutuwa zanyi nashiga uku tafada tana girgiza mom din tata mom kuceci rayuwata dan Allah wallah idan na rasashi mutuwa zanyi zan iya rasa rayuwata shine bugun nufashina kinji mom tafasa fuskar ta shabe shabe da hawaye lokaci guda duk ta fita a hayyacin ta tazama tamkar zararriya sai yanzu mom da taji numfashin ta yadan daidai ta cikin tashin hakalin tace ke kimin baya ni me yake faruwa waye kike magana akansa kinzo duk kindaga min hankali ni wallahi ma na dauka wani mugun abunne ya cijeki abanda ki me waye zai rabu dake mom bossay bossay ne yace yafasa aure na wai ya tsaneni mom kutaimakamin banason inrasa shi arayuwata jin abun da tace yasa itama tadanji wani iri saboda maganar tazo mata abazata kamo hannun ta tayi suka koma sama dakin ta tajata suka zauna abakin gado saidai suna zama kamar wadda ta zauna akan qaya haka ta miqe tsaye zata fita daga dakin aguje mom tayi daurin riqota tace ke wai baza ki nutsuba kinyi haukane kitsaya kiyim kwakwkwaron bayani bangane ba me ya hadaku yace yafasa auren ki watakil kinje kiyi masa haukan naki ko wlh mom ba abun da nayi masa hakan nan daman yadena kirana awaya kuma yadena zuwa gurina shine naked masa magana me gasa shine yadena sona baya sona harda zagina yaringayi yana cemin jaka mahaukaciya ballagaza marar kamun kai bani da hankali duk shi yake gaya miki wadannan maganganun cewar dad da shigowar sa kenan dakin yaji abun da take cewa aguje tanufi inda yake tare sa fadawa jikin shi tana sakin wani sabon kukan cikin kukan take cewa wlh dad duk shiyake gaya min wai danace ma kaje kayiwa babansa magana asaka ranar auren mu nan da wata daya shine yace wai koma uban waye yaje yafada inje ince be isa yasashi abun da bayaso ba sai abun da yayi niya kuma indai aure ne yafasa baze aure niba tafada tana rushewa da wani kukan sosai ran dady yabaci yace ya isa haka shine kuma keke tada hankalinki haka ai ko ubansane be isa yace anfasa auren nan ba bare kuma shi ki kwantar da hankalin ki kidena asarar hawayen ki aure kamar anyi shine angama aure dole ayi ko yana so ko baya so sai ya aureki kisa aranki yazama mijinki kuma ke kadai sai yanda kikaga damar juyashi ko wata be isa ya aura ba dake zai rayu mutuwa ce kawai zata rabaku yaqarasa fada yana rabata da jikin shi sannan yasa hannu ya goge mata hawayen ta yace yanzu abun da nake so da ke shine kar kisake damun kanki akan batun auren ku sannan kar kisake kiqara kiran shi kirabu dashi zanyi maganin sa itade mom tana zaune tana kallon su batace komai ba amma itama aranta tana kiyasta abubuwan da zatayi akan wannan cin mutum cin da yayi wa yarta tilo daya aduniya zai gane kurensa sosai dad ya rarrashi rashida har saida yaga ta kwantar da hankalin ta sannan ta koma dakin ta wayar da ta jefar ta dauka tana binta da kallo tare da sakin shu'umin murmushi tana jinjina kai.........✍
(kema kinzo kin taka sahun barawo bake kika kar zoman ba amma yanzu ya dora miki alhakin yin kisan yasau ke fushinsa akanki mutum daman baso yake ba kuma akazo masa da magana yana cikin fushi kinga kwa ko wane irin hukun ci zai iya zartarwa nikama bazance komai ba akai kar nima ya dawo kaina dan naga alamar Ameesha na neman tasa shi yafara dukan mutane saboda idon sa yafara rufewa koma ince ya rufe)
[5/14, 6:34 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿17&18
Bismilah.......✍


*shettima*
cike da tunanni iri iri a ransa yaqarasa gida horn yayi ne gadi ya wangale masa gate shikuma ya danna hancin motar ya shiga ciki parking lot ya nufa bayan yagama daidaita parking ya fito yanufi cikin gidan yana shiga yaga babu kowa afalon yana qoqarin nufar dakin hajiyar sa sai gata tana saukowa daga upstairs tana ganin sa ta fadada fara'ar fuskarta tana sakin murmushi ganin tilon danta tanajin tausayin sa kodan rasa mahaifin sa dayayi shiyasa akullum sonshi yake qara nunkuwa cikin ranta ganin tana murmushi shima yasahi kawar da duk wani tunani da yazo dashi ya ajiye shi gefe da murmushin shima tunkan taqaraso yaqarasa inda take tare da yin hugging din ta sannan yace hajiya what happened ne naga kina ta smiling wani taqara saki tace ba dole inyi smiling ba nasamu 'ya mace wlh bakaji yanda naked jin dadi ba tunda muka dawo kasan me nayi mamakin yarinyar nan yanda ta saki jikin ta dani kai kace daman munsan juna sosai tare ma muka shiga kitchen mukayi girki nayi mamakin yanda naga ta iya abubuwa wani yau girkin kanwarka zakaci wani rin murmushi yake ta faman saki tunda tafara bashi labarin yake jin wani dadi na ziyartarsa cike da zumudin ganin ta yace hajiya tana ina hajiya tace ai har ta kwanta tayi bacci kasan jikin ta ba wani lafiya ne dashi ba shiyasa da tan tayani nace tayi wanka ta kwanta bayan taci abinci tundazu fa ta kwanta yace gaskiya banji dadin kwanciyar ta ba naso nadawo naganta kafin na kwanta dan hararar wasa hajiya tayi masa tace to

10 / 74