Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   54 / 74

159K to 162K   out of 221K words

motar banga kowaba aciki har ya fice saboda murfin motar ma abuɗe yabarta banga fitar saba......

danaga yanda  ta bugu sosai sai kawai nakira motar asibiti na kwatan ta musu inda nake shine suka zo suka ɗauketa bayan munje kuma sai akace bata mutubu kuskuren da masana nayi shine gudawar da nayi nabarta amma shima banayi bane dan son raina sai dan jin yanda aka lissafo kuɗaɗen da zanbiya loƙacin kuma banda su banda dalilin su bansan ta inda zan samesu ba dalilin hakanne yasa na gudu daga asibitin sannan kuma number mutumin da nakarɓa wanda ya karɓi yaron banyi saving ɗin taba namanta na share ta shiyasa bankira saba amma duk dahaka daman nayi niyar kiranshi insanar dashi halin da ake ciki ko zai iya taimaka mata sai kuma narasa number har gurin da abun yafaru naje na tambaya koda wanda yasan gidan mutumin akace ba asan daga inda yake ba bantafi ba saida nabada number ta awajen nace musu dan Allah duk sanda akaga ko wucewar sa ne adakatar dashi sannan a haɗani dashi amma shiru shiru babu wanda ya kirani tun abun na damu nama har na fara cire shi araina sai da nagan ta yanzu nafara tunanin inda nasanta hirar da kukayi kuma yanzu ita ta ƙara tunamin inda nasanta wannan shine gaskiyar abun da nasan nayi,

inna lillahi wa inna alaihi raji'un nashiga uku ni Aminatu,
Ammi tashiga yin salati tana tafa hannu dan jitake kamar shi yaso yayi kisan kan Allah yaso bata mutuba, sai sallallami take takasa magana hawaye kuma nabin kan fuskar ta bossay kam jin kansa yayi a sama kamar a wata duniyar yake ta daban saboda shima anasa bangaren yanda Ammi take tunani haka shima yake tunani,

Meer da ya kafesa da ido yana so yagano gaskiyar maganar sa amma yakasa tantancewa ya ɗago ya kalli maama itama shi ta kalla ganin yanda yake kallon tasa tayi masa alama da ido akan ya rabu dashi kada tace komai hakanne yasashi yin shiru tare da kawar da kansa,

a tsanake  maama tafara magana,

"kallon dady tayi tace "a labarin da ka bayar na yarda dakai idan da gaske kake idan kuma ƙarya kafaɗa to kasani zamu gano ka kuma idan hakan ta faru bazakaji da daɗi ba domin ko wani ya ɗaga ma ƙafa kasan wannan yaron bazai ɗaga maba dan haka ka nutsu da kyau kayi bayani da kyau idan kasan wanda yasaka ka buge gwanda tun kan loƙaci ya ƙure maka ka hanzarta sanar damu kafita daga cikin zargin mu saboda inba mu gano ko waye ba kai zamu riƙa saboda nidai da idona kai nagani kuma kaima kasan da hakan kamar yanda kabada labari yanzu ina me jan kunneka da kaje kasake tunani kasamo mafita tunkan binciken mu yafara aiki agano kana ciki yanzu ina ɗaga maka ƙafa ne saboda iyalen ka dan darajar su kake ciki ina fatan ka fahimta,

dady ya buɗi baki zaiyi magana ta ɗaga masa hannun tare da cewa "kar kace komai yanzu zan nemeka yanzu na barka kayi nazari tukunna zaka iya tashi kar kuma kasa kanka adamuwa kasaki jikin ka kaci gaba da harkarka da iyalen ka, ku kuma nadawo kanku ta maida dubanta ga su Ammi tace "ku kwantar da hankalin ku kuma babu abun da za'ayi masa har sai munyi bincike akai banason ɗayan ku yayi wani tunani akansa marar kyau baku kaɗai bama kowa dake falon nan banason kowa ya ƙara tada zancen harsai loƙacin yin hakan yayi ina fatan kun gane kowa yasaki ransa,

Ammi ce ta tsugunna agabanta tana zubar da hawaye tace dan Allah dan Annabi kuyi haƙuri abisa abun da yayi muku sannan kuma mungode sosai da karamcin da kikayi mana domin ba kowa bane da zai fuskanci irin abun da ki fuskanta kuma yaɗa gawa wani ƙafa nasan kinyi mana karamci sosai kuma ina fatan kada Allah yasa mijina yanadasa hannun aciki idan hakan ta kasance bansan inda zan saka rayuwata da ta ƴaƴana ba nasan sai nayi danasnin auren sa bazan taɓa yafewa kaina na auren sa batare da nasan halayen saba nazaɓeshi amatsayin uban ƴaƴana ba bazan taɓa j........

da sauri ummy ta tsugunna agabanta tare da dafata tace ya isa haka ki daina irin waɗannan maganganun ki kwantar da hankalin ki in sha Allah mijin ki bashi da laifi kamar yanda yafaɗa in Allah ya yarda hakanne gaskiya dan haka kar ki ƙara cewa komai kiyi shiru,

Ammi na shirin yin magana kenan sukaji anyi nocking ɗin ƙofar falon bossay ne yataka da ƙyar yaƙarasa bakin ƙofar ya buɗe da dadda suka fara karo da sauri ya sunkuyar da kansa dan sai yaga kamar zasu gane abun dake faruwa su tsanesa,

saura kaɗan dadda ta bugesa ta shigo falon cike da masifa ko kallon ƴan falon ma batayi ba idon ta akan Ammi tace wallahi wallahi wannan matar inajin sai na koma naci mata uwa dan wallahi bazan haƙura ba ai duk kuka jamin kubarni da abun dake damuna ma amma kunkai ni waccen me zubin albasa me lawashiɗin tazo tana gaya min magana shegiya da kai kamar fitilar ɗan iska  ya wani mulmule ita bajiki ba sai ɗan iskan ƙaton kai bakin rijiyar ƙauye,

bossay ne ya kalle ta da mamaki yace "dadda ke dawa kuma Ni kinzo kinsaka ni agaba saikace ninayi miki laifin,

duk ai ka kajawo mi da baka fitar min da jika ba ai da banfita daga cikin gidan nan ba wallahi danasan zan haɗu da wacce agwagwar da ban fitaba banza da ita kamar tsohuwar saniya,

"Dadda dan Allah ya isa haka kishiga ciki ki kizauna,

bazan shiga ɗin ba kai wallahi idan ban sauke haushina akan kaba Allah ya kwashe min albarka,

sam dake bayanta yace " daman ai bakida ita andaɗe da kwashe ta,

juyowa tayi zata kaimasa bugu yayi saurin shigewa falon tabi shi abaya tana cewa wallahi yanzu kayi min iskanci sai nayi maganin ka yanzu ba ɗazu bane bare kace zaka kashe ni da motar kuma nan ba motar kabace bare ka hanani magana yoo inbanda iskanci Allah ya yanka ma baki dan kabuɗa shi kuma ace za ahanaka magana bare kuma anyi maka laifi......,

Mugu kawai azzalumi nadawo kanka wallahi sai Allah yasakamin cutar dani ɗin da kayi yau wallahi alhakina nayau bazai barkaba kaidai Allah wadai da halinka kuma wallahi kasani duk wanda yaci tuwo dani miya yasha domin dadda bata yafiya ko ba daɗe ko ba jima sai narama wulaƙancin da kayi min yau,

ɗan ɗaga murya sameer yayi yace saidai ki rame kuwa san kurwata tafi ƙarfinki bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane idan kika kuskura kika bari muka ɗaura dake to wallahi saina baki kashi,

da sauri ta ɗaga ƙafa zataje inda yake tare da cewa saidai kabawa waccen figargiyar uwar taka kashi marar mutunci yaro wallahi sai.......

cak ta tsaya  da tafiyar da take tare da yin shiru sakamakon tozali da tayi da Ameesha agaban ta, dan ita duk wannan zubar da take bata kula da itaba tadai san da mutane afalon amma bata tsaya tantance fuskokinsu ba

kasa motsawa tayi har saida dadda ta ƙaraso gabanta ta kira sunan ta sannan tace dagaske ne ko mafarki nake ko kuma gizo ne,

ɗan murmushinn jin daɗin ganinta Ameesha tayi sannan ta faɗa jikin ta ta rungume ta tana cewa dadda nice fa ba mafarki kike ba kuma ba gizo bane niɗin ce da gaske dadda ta,

itama rungumeta ta tayi sosai kamar zata mayar da ita cikin jikin ta saida suka daɗe suna rungume da juna sannan ta riƙe fuskar ta tace da gaske ne shalelena ce wannan ina suka kaiki  suka ɓoye min ke ina ta nemanki babu abun da ya sameki jiya dan nayi mafarki kina cikin mawuyacin hali faɗa min abun da yasameki danni naji ajikina mafarkin danayi bana banza bane dole da kwai ƙanshin gaskiya aciki wallahi saboda idan nayi mafarki da wuya baizama gaskiya ba....,

Ameesha ta buɗe baki zarayi magana kenan maama tayi saurin dakatar da ita tare da cewa ya isa haka ku shigo ku zauna jin baƙuwar murya yasa dadda saurin maida dubanta ga inda tajiyo muryar suna haɗa ido da maama, maama tasakar mata murmushi,  murmushin da yasa dadda saurin ɗaukewa gaba ɗaya al'ajabi da mamaki da tashin hankali da shiga ruɗu duk aloƙaci ɗaga suka risketa domin kallo ɗayan da tayi mata tagama karantar ta gaba ɗaya,

fuskarta ɗauke da mugun mamaki ta shiga kallon maama ta kalli maama na ƴan daƙiƙu sannan ta kalli Ameesha haka ta shiga yi ta kalli wannan ta kalli wancen,

Ameesha ce tasaki lallausan murmushi ganin yanda dadda take kallon ta tasan dole tagane kamannin su shiyasa take binsu da irin wannan kallon,

cike da murmushin da yaƙi ɓoyiwa akan fuskar ta ta kamo hannun dadda tace "dadda kingane tane irin wannan kallo haka mu zauna kisha labari wannan da kike ganin ta kakatace itace mahaifiyar ɗanki mahaifina.....,

wani irin yimm dadda taji ajikin ta yana mata yawo kamar sokuwa haka Ameesha take janta ita kuma na binta har takaita kan kujerar kusa da maama ta zaunar da ita sai kawai ta shiga kallon su abun sai burgeta ba ƙaramin farin ciki taji yana ratsata ba yau ga kakannin ta guda biyu agabanta tana kallon su mayar da idonta tayi kan meer yanzu shima ɗan uwanta tane sannan ta kalli Abu da shima yake kamar uba agare ta yau gata cikin dangin ta kuma nan bada jimawaba zata koma cikin gidan su abun da bata taɓa tunanin zai faruba arayuwarta tayi tunanin ahaka zata ƙare rayuwarta cikin wahala ashe akwai ranar farin ciki gashi yau tagani..........,

duk abun da takeyi kowa ya zuba mata ido cike da tausayin ta ko ba afaɗa maka ba kana ganin yanayin ta kasan halin datake ciki,

har yanzu murmushin da take baibar kan fuskar taba "tace dadda kinyi shiru kitayani farin ciki yau gani ga dangina,

har loƙacin dadda takasa magana tayi shiru kurum ko mai take tunani da yasa ta kasa magana🤔..........✍️✍️✍️


*Special thanks 2 u♥️ina godiya da haɗin kan da kuka bayar jiya da waɗanda suka yi da waɗanda ma basuyi ba duk ina godiya gareku Allah yabar zumun ci yaƙara danƙon♥️*

bansan sunankiba amma nagadai kina amfani da ALAHAMDULILLAH,
ina godiya da irin comment ɗin inajin daɗin sa ɗari bisa ɗari amasu comment kece 1,

kuma sauran masu yi ina godiya irin su👇

Maman amira
Maman fateema
Maman arman
Maman faruk
Mamma
Rabi'atu mu'azzam
Zulailkha
ummu houria and Sameer
fateema

Usman Muhammad
Ɗahiru mu'azzam

duk wanda baiga sunan saba kuma yana yin commente to yayi haƙuri dan akwai waɗanda da Number ɗinsu ahaka nayi saving ba suna amma zan tambaye ku nan ba insha Allah sai mu haɗe ina fatan kun fahimce ni,

Masu wannan number hardaku acikin

+234 703 648 4184
+234 704 258 2726

    
                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/13, 10:20 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 88

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

 
    "har loƙacin dadda takasa magana tayi shiru kurum ko mai take tunani da yasa ta kasa magana🤔..........✍️

ashe ba ita kaɗai take mamakin ba a ɓangaren su sam ma hakan take mamaki yagama cikasu jin maganar suke kamar amafarki,

saida Ameesha ta girgiza ta tace  "dadda wai bazakiyi magana ba,

kallon ta dadda tayi sannan tace"dagaske ne wai abun da naji kina faɗa kuma nagani da idona dan Allah idan bacci nake kar ki tasheni dan nasan wannan mafarkine ba gskiya bane nasan hakan bazai taɓa kasancewa gaskiya ko amafarki bantaɓa gani ba sai yau Allah ya nuna dan Allah karda wanda ya yashe ni daga baccin nan,

mintsi ninta Ameesha tayi tare da yin wani murmushin tace dadda kin tabbatar yanzu ba mafarki bane ko in ƙara miki wani nasan idan kikaji zafi sosai zakifi yarda,

kallon ta kawai dadda take amma duk da haka bata yarda ba kuma bata bar kallon taba saboda sai yanzu komai yadawo mata sabo fuskar sameer ɗanta take kallo kawai afuskar Ameesha sai taga kamar shine loƙacin da yake kamar ta daman Ameesha kamannin sa ta ɗauko sak shi kuma kamannin mahaifiyar sa ne (maama)
dan haka duk wanda ka gani acikin su sai kagane kamannin su ɗaya,

Ammi da ta lura da dadda fa kamar bata cikin hayyacin ta har yanzu yasa ta ajiye halin da take ciki agefe sannan ta dawo kusa da dadda ta riƙo hannun ta tace daddar mu ko nima sai nayi miki ta Ameeshan ne zaki dawo hayyacin yakamata idan ma mafarki kike ki farka ki kalli mahaifiyar ɗanki da kuma yayan ɗanki da ɗan sa gasu agaban ki nan duk dangin kine,

dadda ta kalli Ammi sannan tace taya hakan zata faru nifa banyarda daku ba taya mahaifiyar sameer zatazo nan taya hakan zata kasance haba dan Allah ya kuke abu kamar shirin film,

Ammi tace "to ki kalle su mana bagasunan agabanki ba kuma kema nasan kinga kamannin ko ba afaɗa miki ba sai kinfi kowa gane me kama da ɗanki,

"eh nagani amma wannan ai idona ne yake min gizo nasan ba gaskiya bane kuma nasan ba gaske kuke ba tsokanata kawai kuke dan haka mubar wannan wasan tun wuri wannan bamai yiyuwa bane,

tofa duk mamakin dadda suke da furucin ta duk wanna hujjoji gashi angaya mata kuma itama tagani da idon ta amma taƙi yarda sai antaro ta tanan sai ta kufce tacan taƙi fahimta har yanzu,

maama ce ta tashi da kanta taje gaban ta ta tsugunna sannan tace baiwar Allah ba mafarki kike ba ki kalle ni da kyau nice mahaifiyar sameer kuma kakar jikar ki Ameesha sannan wannan da kike gani shima ɗana ne wancen kuma jikanane tana yi mata maganar tana nuna mata su duk wanda ta faɗi sunan sai ta nuna mata da hannu,

da ƙyar dai dadda ta dawo hayyacin ta ta yarda sannan maama da kanta tabata labarin duk abun da yafaru, har haɗuwar su da su Abu da ganewar da tayi shima ɗan tane da aka sace mata shi acikin masarauta sai gashi yanzu Allah ya haɗasu duk aloƙaci ɗaya, amma bata bata labarin cewar baban su bossay shine wanda ake zargi ya bugeta ba a motar saboda tana jin tsoron abun da zatace akansa tunda taga itama bata da haƙuri kar take tayi masa tijara agaban matar sa da ɗansa shiyasa taƙi gaya mata wannan maganar,

tana gama bada labarin dadda ta fashe da kuka ta jawo Ameesha ta rungume tana cewa Allah na gode maka Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana ashe burina zai cika kafin inbar duniya haka tashi ga jero godiyar ta ga Ubangiji tana kuka tana murmushi haka ta haɗa abu biyu aloƙaci guda yana yin da take maganar saida tabawa kowa tausayi Saida tasaka Ameesha kuka haka suka ringayin kukan su sannan suka raba jikin su da na juna,

su sam ma ba ƙaramin mamakin wannan labarin sukayi ba shikenan suna sa ran zasu sha wahala sosai wajen gano su sai gashi Allah yakawo musu sauƙi sosai suka taya dadda da Ameesha murna,

haka Abu ma yazo suka gaisa da dadda Ummy suka gaisa ummy nata tsokanar ta dan taga faɗan ta ita tun kan taganta taji matar ta kwan ta mata arai yanzu kuma da taganta sai taji abun yamafi wanda aka bata labari gaba ɗayadai falon bayan sun gama koke koken su suka dawo kuma taya juna murna cike da farin ciki amma duk wannan bidirin da akeyi banda sam ɗan yana tsaye inda yake ko motsawa baiyi ba shi ko gajiyama da tsayiwar bayayi kamar tsohon soja haka yayi musu aka kuma yaƙi buɗe baki yayi magana sai ma haɗe rai da yaƙarayi kamar anyi mishi albishir da gidan wuta haka ya haɗe rai tamau kamar anƙulle kunnu alaida haka yake ga idon nan har yanzu kalar su bata dawo daidai ba yana nan ajansa tun marin da Abu yayi masa baibar yi masa yawo akansa ba dan ji yake yau da wanine ya maresa ba Abu ba da wallahi saiya kaisa inda ba a dawowa sai ya rabasa da ransa,

kiran sallar la'asr ne ya katse su sannan kowa yaje yayi Sallah suka dawo suka ɗora daga inda suka tsaya,


bayan duk sundawo sun zauna dadda tana so tayi magana akan Meer amma takasa saboda taga ba kalar tabane tunda tazo bai kalli inda take ba kuma taga babu wanda yayi masa magana dan haka tayi tunani ma ko sojane shi idan yana abu ba tanka masa shiyasa iyayen sama suka kasa yi masa magana, ina ga ita kuma taje tayi masa magana ya zuciya ya harbeta agun bada itaba wannan kasadar shiyasa taja bakin ta tayi shiru amma duk da haka akai akai sai taɗan saci kallon sa ta gefe cikin rashin sa'a tayi masa wani kallo shima loƙacin ya ɗago jajayen idon sa suka haɗa ido da sauri ta kawar da idon ta tana tsoron Allah yasadai kar yace ta fito tundaga loƙacin bata ƙara gigin kallon inda yake ba ta maida hankalin ga hirar da akeyi acikin mutane tabar batun wancen me zubin yahudawan,

sam dai yakasa yin sukuni agurin saboda tunda yaji an ambaci masarauta kuma baiji masarautar inba hankalin sa yaƙi kwanciya dan yana tsoron yaji ance masarautar suce akayi wannan zalincin duk da inma hakan ta kasance akwai wacce yake zargi daman aikwa idan yakasance gaskiya masarautar su ake nufi ai kai tsaye ita zasu damƙa basai sunjira wani dogon bincike ba,

bossay ne yaƙara inda suke su biyu shima ya zauna akusa dasu tunda sauran ma duk suna surutu dan haka ba lalle aji maganar da zaiyi ba,

kusa da kunnen sameer

54 / 74