ɓatan hanyar bari injuya wataƙil bana nan bane yafaɗa tare da ɗan juyawa kamar zai koma tayi saurin dakatar dashi murmushi sukayi gaba ɗayan su sannan yasamu kujera yazauna itama zama tayi sannan suka shiga gaisawa cike da kewar juna na andaɗe ba ahaɗu ba,
tace "wallahi yaron nan baka da kirki yanzu ga baki ga hanci amma sai infi shekara bangan ƙeyar kaba acikin gidan nan,
"kinsande ai ba agarin nake zama ba kuma idan nazoma bawani daɗewa nake ba, nake komawa shiyasa,
"daman haka kake cewa kullum idan anyi maka magana yanzu ko kwana 2 kake a garin bazaka iya bada awa ɗaya ba kazo mugaisa ba bare ma kanafin kwanakin 2 bade kayi niya ba kawai,
"tode yanzu kiyi haƙuri hajjaju abar abun da yariga ya wuce tundade yanzu gani agabanki,
"kace haka mana yanzn ma ni banyarda dakai ba nasan wani abunne yakawo ka,
"aidai nazo ke nifa idan kika takura min sai intashi in tafiyata,
"hmmm to ai shikenan nayi shiru da bakin amma kuma wannan yarinyar fa bansan taba a ina ka samota,
kallon sumy yayi da ta wani takure guri ɗaya tunda ta suka shigo ta gaida matar bata ƙara ko motsawa ba kamar wacce take a tsorace haka take zaune awajen,
"wannan baƙuwa ce nakawo miki ita,
ɗan harar wasa tayi masa tace" bangane baƙuwa ba kode sirikar ce sai yanzu Allah ya kawota,
"kinga matsalara dake kenan shiyasa bana son zuwa wajen ki to ba wata sirika tana cikin wani haline shiyasa nakawo ta nan ki ɗan riƙe min ita kafin nan da wani loƙaci zanzo na ɗauketa, yanzu de bani da loƙacin yi miki bayani zan dawo gobe sai muyi maganar,
"tofa wane irin hali kuma ai yau yakamata kayi min bayani ko sai infi jin daɗin zama da ita amma kawai ka kawota kace zaka wani dawo gobe salon innemeka in rasa dan nasan halin ka bakada tabbas,
"Allah hajjaju zan dawo tunda nafaɗa yanzu sauri nake ne zanje wani wajenne shiyasa nabiyo nakawo miki ita kuma nasan ke kaɗai ce zaki iya yimin wannan abun,
"nifa bana son wani daɗin bakin ka daka saba yi min amma de shikenan na rabu dakai kaje kadawo ɗin ina jiran ka,
"yauwa hajjajuna nagode bari inje yafaɗa tare da muƙewa tsaye sannan ya kalli sumy da takejin kamar tace masa bazata zauna ba amma ba hali dole ta zauna duk da bata san ko ina ne yakawo ta ba tade san kawai bazai taɓa cutar da itaba,
"kizauna anan zan dawo gobe zamuyi magana dake kisaki jikin ki anan wannan kakata ce bakida matsala da ita komai kikeso ki tambayeta kinji?
kai ta ɗaga masa sannan tace "nagode cikin sanyin murya,
jiyayi tausayin ta yaƙara kamasa yanasane yaƙi tamabayar ta abun dake faruwa da ita saboda yasan yanzu take cikin halin ba lalle tagaya masa komai ba idan ma zata gaya masa to sai tayi masa kuka shikuma bayaso shiyasa yabarta zuwa gobe koma jibi dan baya tunanin zaizo goben faɗe dai kawai yayi yasan zuwa loƙacin ta dawo cikin nutsuwar ta...,
sallama yayi da su sannan yafita daga gidan,
tanaji tana ganin yafita yabarta badan tasoba hakannan taji gidan bai kwanta mata araiba,
yana fita hajjaju ta kalleta awani wulaƙance tace keɗin wacece daga ina ya ɗauko ki shi duk wani shirgi ya iya jajubowa kansa yarasa inda zai zuba bolar sa sai gidana,
gabanta taji yafaɗi daman shiyasa taji batason gidan yanzu agaban sa ta nuna komai nml amma daga fitar sa zata fara yi mata wannan abun to inaga taci gaba da zama aikwa yana zuwa gobe zata bisa gwanda yamayar da ita gida tasaba daman da waccen wahalar amma wannan bata san ya kallar halin ta yake ba,
tsawa ta daka mata "ba magana nake miki ba kinyi min shiru wata kon ga ƴar iska namiki magana ko,
aɗan zabure tace "a'a " kiyi haƙuri amma nima kaina bansan ko ni wacece ba nade taso a hannun mahaifina kishiyar mahai....
"ke ke ke dakata ni ba dogon zance na tambaye kiba meye alaƙarki dashi me ya haɗaku,
hawaye har yafara zubo mata cikin muryar kuka tace "babu abun da yake tsakanin mu,
ƙarya kike banyarda ba to barima kiji ingaya miki idan ma bacci kike ki farka Sameer ba sa'an yin kibane yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba kifita daga harkar sa inma kina tunanin wani abun akansa to kicire tun kan loƙaci ya ƙure miki,
shiru sumy tayi tana tunanin ikon Allah yau taga takanta daga zuwa sai faman uban surutu takeyi da wani abunma bata gane me take nufi ko wayace mata tana da wata manufa akansa shikenan yanzu mutum bazai taimake ka ba sai da wata alaƙa a tsakanin su tab aikam yazama dole tabar gidan dan bazata juri cin mutumci da zarafi ba bataji ba bata gani ba ta gwammace ta koma gida aci gaba yimata tasan wannan gidan ubantane kuma tasaba dashi,
haka matar nan taitayi mata bala'i ta inda take shiga batanan take fita ba daga haɗuwa sai masifa sai kace daman ƙiris take jira,
saida tagaji dan kanta sannan ta tashi tabarmata falon tare dayi mata gargaɗin koda wasa tasake ta sanar sam wani abun na lahira sai yafita jin daɗi,
zaune tayi afalon duk jikin ta babu daɗi tana tunanin kode tayi tafiyar tama kawai yanzu sai kuma tayi wani tunani gwanda ta tsaya inyazo gobe sukayi maganar ita tayarda ma yakaita inda ya rufe mata mahaifi itama ya haɗa da ita ya rufesu hakan sai yafi mata kwanciyar hankali,
da wannan shawarar ta barwa ranta tayi haƙuri taci gaba da zaman falon ita kaɗai,
(wannan matar itace ƴar autar su Ammah ƙanwa take ga Ammah saidai ita halin su baizo ɗayaba dan bata iya zama da mutane ba ita komai sai nata idan kaga kuna shiri da ita to kai najikin tane ko kuma tana son wani agurin ka sai kaga tana nan nan dakai abun da yasa kuma take son sam shikuma saboda tanaso ahaɗa auren su da jikarta itama kaf jikokin ta tafi ji da yarinyar shiyasa take jansa ajiki wannan kenan,,
************************
*Maama*
bayan maama tagama basu labari tabari ta fashe da kuka tare da komawa kan kujera ta zauna gaba ɗayan su cike da tausawa suka shiga bata haƙuri,
Ummy ce tafara magana "gskiya waɗannan mutanen basu da imani yanzu mutum da gidan mijin sa da ƴaƴan amma arabasu ta ƙarfi da yaji saboda da tsabar son abun duniya meye abun soma asuarauta nasan duk dan saboda itane suka rabaki da iyalan ki irin waɗannan bai kamata ana barin suba ai wannan abun da suka aikata miki maama bake yakamata ki ɗauki mataki da kanki ba da hukuma yakamata ahaɗasu duk wani wanda yake cikin masarautar sai ankamasa zasu fito da wanda yashirya miki wannan ƙullin kamar fa kisan kai sukai yara tun suna ciki aringa kashe su ansamu kuma ɗaya yazo duniya shima arabasa da mahaifiyar sa wataƙil ma kuma kashe shi sukayi fa ai wallahi maama yanzunnan basai anjima ba za muje gidan mutafar musu da hukuma abi miki haƙƙin ki dan wallahi sai inda ƙarfinmu ya ƙare, ummy sai faman zuba take ko numfasawa batayi jitake kamar ita akayiwa haka ko kuma wani ɗan uwanta najiki abun ba ƙaramin haushi yabata ba,
Abu ma ya ɗora da nasa nima hakan nayi tunani ai bawani ɓata loƙaci kawai muje yanzu mu shigar da report sannan mu tafi gidan ba gidan sarki ba ko gidan shugaban kasa ne yau sai hukuma ta shiga kuma anyi sharri'a ko shi sarkinne da laifi wallahi sai ankamasa tunda ga hujjoji abayyane ba a ɓoye ba, abun haushin ma indai basa sa hannun saba meyasa tsawon loƙacin nan basu nemetaba ai kamata yayi ba ko ina su baza neman ta gari gari basai iya garin suba amma duk sunyi burus to kowa sai ya kwashi kashin sa ahannu duk wani me sa hannun a al'amarin,
ummy tace "dole kuwa koma waye sai anɗau mataki akansa, gashi kuma duk de mugun tarsu Allah yayi bazata mutuba kuma gashi Allah yanuna musu ishara ya haɗata da jikarta ta hanya mefi sauƙi kuma in sha Allah ɗanki bai mutu ba sai anbinciko mahaifin ta aduk inda yake yanda baki mutuba da yardar Allah ma gaba ɗaya ƴaƴan ki suna raye babu wanda yarasa ransa sai kun koma cikin gidan ku ko suna so ko basa so Allah yafisu,
Abu yace insha Allah wannan azaune take shigarta gidan kamar ta shiga ne domin yanzu za ayita ta ƙare basai anje ko ina ba dan haka zama bai ganmu ba ku tashi gaba ɗayan ku mutafi,
MEER ne yayi saurin miƙe tsaye yace ba wata hukuma da za akira ni nan da kaina zanyi maganin ko wane ɗan iska ɗaya bayan ɗaya sai na halaka su wallahi bazan barsu ba,
maama sai murmushi jin daɗi take tasamu masu ƙwato mata ƴancin ta ba dangin iya bana baba amma gashi sunzame mata gatan rayuwa badan suba tasan da tuni wani labarin ake ba wannan ba,
cike da farin ciki tace "tace"kuyi haƙuri bari inkatse muku hanzarin ku ta bakin yaron nan wannan ba maganar hukuma bace nima nafiso inɗau mataki da kaina inyaso daga baya idan aka gama tara komai akasan masu hannu aciki sai a shigar da ƙarar daga baga baya ina ganin hakan sai yafi mana sauƙi, yanzu tunanin ta inda zamu fara yakamata muyi tunda tace wasu sun fara bincike aciki yakamata ta haɗamu dasu inyaso sai muji wane abu suka gano daga nan sai mu ɗora daga inda suka tsaya,
ina so ta farar ɗaya inyi musu dirar maƙiya tayanda kowa sai ya girgiza da lamarin ina so inbasu mamaki amma saida haɗin kanku sai mun haɗu ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar maƙiya, domin wannan faɗan ba mutum ɗaya bane da hannun mutane da yawa aciki bayanda za ayi ace wannan shirin duk Mutum ɗaya ne yayi shi kuma batare da sanin kowa ba dake cikin gidan wannan ƙarya ne bazai taɓa yiyuwa,
Abu ne yace "gaskiya ne wannan maganar taki haka take dole sai anyi shiri yanzu meye abunyi,
"abunyi ai shine kawai ku taso mutafi ita wannan yarinyar ta kaimu gidan waɗancen ɗin inda kakar ta take,
"shikenan ma kawai ƴata zadai ki gane gidan ko yanzu idan muka tafi,ummy ta tambaye ta tana riƙo hannun ta,
ɗaga mata kai tayi dan ita zuwa yanzu kanta yayi mata nauyi wani irin ciwo take ji yanayi mata shiyasa bata da bakin yin magana abun yafi ƙarfin ta har yanzu takasa yarda wai kakar tace wannan akusa da ita wacce ta haifi mahaifin ta daman tana da rabon ganin dangin ta aduniya kafin tabar duniya abun saba ta taɓa tunani ba bata taɓa kawowa aranta ba ita duk a lissafin ta bata taba kawo wai masarautar da taje ta kwana ba ita ake magana yanzu akai kwata kwata bata kawo wannan aranta ba wani tunanin take daban,
maama ce ta kamo hannun ta ta miƙar da ita tsaye sauran duk suka miƙe meer ne kan gaba dan kafinma suyi wani yunƙuri har yafice daga falon saboda jikin sa har tsuma yake ji yake kamar ace masa ga masu laifin agaban sa yafara dukan su haka yakeji hannun sa har ƙaiƙayi yake masa nason duka Allah Allah yake suyi sauri suje ai mutum ko ƙishin ƙishin rashin gaskiya ne dashi acikin al'amarin sai ya daku bazai barsa ba,
fitowa sukayi gaba ɗayan su suka shiga motar Meer da Abu agaba sai su ummy abaya tundaga cikin gidan yafara gudu tunkan yaƙaraso kwa bakin gate ɗin yadanne wajen horn ba shiri me gadi yayi saurin wangale masa gare ɗin yaja motar aguje yafita daga gidan,
Abu ne ga kalle sa yace malam karage gudun nan mana duk gaggawar asara ai ta jira samu ko kasan gidanne basai anyi maka kwanta ce ba,
"Ummy tace "ina fa saurin kawai shida ko unguwar ma baisaniba taya zai san gidan,
yana jinsu yarage gudun dan shi saida suka faɗama yatuna ashefa baisan inda za"aba,
ummy ce ta tambayi Ameesha sunan unguwar nan take tafaɗa musu maama tace ai tasan unguwar dan haka ba ɓata loƙaci Ameesha tayi musu kwatance har gidan dan haka suna tafiya maama nayi masa kwatancen hanyar da zaibi, dan har yanzu bata manta cikin kano ɗinba ita kuma Ameesha tade san sunan unguwar kuma tasan gidan ammade bata san inda za'abi aje gidan ba,
ahaka suka cigaba da tafiya maama na kwatance har sukaje unguwar Ameesha kuma ta karɓeta taciga da nuna kwanar da zasu bi har sukazo ƙofar gidan,
horn sukayi abakin gate ɗin akabuɗe musu suka shiga inda suka ga anyi parking anan Meer yayi sannan suka fito,
Ameesha ce agaba suna binta abaya har suka kai falon nocking sukayi amma shiru ba abuɗe ba sai sukayi sallama nan ma shiru kuma suna jiyo hayaniya aciki,
ummy ce ta gwada murɗa handle ɗin sai taji ta buɗu dan haka suka shiga ciki gaba ɗayan su suna ƙara yin wata sallamar sai loƙacin ƴan falon sukaji da suna ta ihun dady yadawo yajawo musu tsaraba sun tsaya ana ta raɓawa shiyasa basuji sallamar da suke yiba sai yanzu,
Ameesha na fita duk hankalin su yakoma kanta bossay kam yama ƙame agun dan yafi tunanin kode mafarkin ta yake ba gaskiya bane ko kuma gizau take masa yadai kasa tantancewa,
da sauri Ammi ta tashi tsaye tare da cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Allah kaine abun godiya Ameesha ke nake gani kode mafarki nake ƙarasawa Ameesha tayi gurin ta tare da rungume ta tace nice Ammi,
gaba ɗaya babu wanda ya lura da su maama duk hankalin su yakoma kan Ameesha sai murna Ammi take bossay kwa har yanzu bai iya buɗar baki ba yayi magana,
saida Ammi ta sake ta sanann idon ta yasauka kan su ummy dake tsaye suna kallon su kamar tv,
sannu ku da zuwa bayin Allah hankalin duk yayi kanta ban lura dakuba Bismillah kuzauna zama sukayi sannan suka shiga gaggaisawa yaran ma suka gaisar da su Abu sannan suka bar falon zuwa ɗaki haka suke daman indai akayi baƙi babu wanda yake zama agurin wannan tarbiyyar Ammi ce ahaka ta horar dasu,
Ameesha ganin bossay bai kulataba yasa taji wani iri aranta tanaso taje wajen sa amma Ammi ta riƙe mata hannu dan haka ta tsaya bata jeba amma hankalin ta na kansa,
shiru falon ya ɗauka na ƴan da kiƙu,
Abu ne yayi gyaran muraya zai fara magana,
da sauri maama ta miƙe tsaye tana zazzara ido ta miƙa hannun ta tana nuna wani waje wallahi shine.......
ɗagowa sukayi ɗayansu suka bi gurin da take nunawa da hannu suka kalla........✍️✍️
tofa🤔🤔🤔
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[7/9, 8:47 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 85
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"ɗagowa sukayi ɗayansu suka bi gurin da take nunawa da hannu suka kalla........✍️✍️
tsaye suka tashi gaba dayan suna mamakin jin kalaman ta babu wanda ya iya yin magana acikin su duk sun zuba masa ido suna kallon sa kamar yanda maama take kallon sa itama,
adan tsorace ya shiga takowa zuwa gurin su cike da rashin fahimtar kallon masa da sukeyi yace me yake faruwa ne naga duk kun mike lafiyade,
Ammi ce tace muma bamu sani ba munga de ta tashi kuma tana n h naka tace kaine,
kasan tane ko ince kunsan junane?
girgiza kai yayi yace ko kadan bantaba ganin ta ba yau nafara ganita,
karyane wallahi karya kake kasanni nizakacewa bakasan wacece niba idan kamanta ni banmanta ba bazan taba mance kaba,
Ummy ce tayi saurin kamota ta zaunar da ita sannan tace dan Allah ki hakuri ki nutsu sai kiyi mana bayanin inda kika sanshi baikamata kina dafa murya hakaba kodan saboda iyalen sa koma me yayi miki yakamata ai abi komai ahankali, yanzu gaya mana a ina kika sanshi,
shiru tayi takasa magana sai tayi niyar budar baki zatayi magana sai taji bakin kamar anrike mata harshe takasa magana,
shide dady na tsaye kamar gunki mamaki yagama cikashi shi baitaba ganin mataba amma tazo tanayin wasu maganganu dashi bai gane kansu ba, shi da baya kasar ma kuma baifiya zaman kasar ba to a ina tasanshi kode mahaukaciya ce to idan ba mahaukaciya ba wace daga ganin mutum farar daya takama nuna sa tana cewa shine, shi abun ma haushi yabashi dan haka ya koma kan kujera yanama so yaji SUWAYE SU, me yakawo su gidan sa,
Ammi dataga abun nasu wani iri batasan ko su suwaye ba ta matsa kusa dasu tare da cewa baiwar Allah inaganin dai ko batan hanya kukayi ne daman nima ban waye ku ba yakamata afara sanin juna,
baiwar Allah a ina kikasan mijina dawor sa kenen yau yaudin nan daga wata kasar ammade bansani ba ko tun kafin yatafi kuka hadu,
kallon ta kawai maama take takasa magana dafa ta kalle ta sai ra juya ta kallesa,
sude yan falon kowa yayi shiru yana jiran yaji me zatace kowa ita yake jira,
jin shirun yayi yawa yasa meer dake tsaye kekam tunda suka shigo daman yake a tsaye bai zaunaba,
takawa yayi har zuwa gabanta sannan ya tsugunna tare da riko hannun cikin nasa sannan yace yana daya daga cikin wadan daga cikin masu cutar dake?
kai ta daga masa alamar "eh" mikewa tayi tare da cewa angama kashiga hannu yafada yana kallon dady da ya zaro ido jin abun da yake cewa,
a masifance dady ya mike tsaye yace "bangane maganar kuba wai kudin suwaye me ya kawo ku gida na da har kuke wani banzan zance ban gane nufin kuba akaina,
zaka ganene nan gaba meer yabashi,
Bossay dayaga abun